MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 85

by @maimunabala209

*MATAR GIDA BOOK* 2


*SHUUKRAN*/022



P85



Karfe tara da rabi na dare Alhaji Babah ne zaune cikin babban katafarin parlourn sa daga gefen kuma Hajiya ce ta bugu tagumi tana kallon Hajiya Bilƙisu tare da Hajiya Zulfa'u dake zaune ƙasan parlourn dukkaninsu kawunansu ƙasa,sun dauki sama da mintina goma zaune a parlourn,Alhaji Babah bai ce masu komai ba kawai ya sasu a gaba ya rinƙa kallonsu,wanan shirun da Alhaji Babah ya yi ba ƙaramin tayarwa Hajiya Bilƙisu hankali ya yi ba saboda har sannan bata san dalilin kiran da yay mata ba,hakan yasa ta hada zufa,wani irin zafi take ji harda A C dake aikin parlourn,tun bayan sallar magrib take ta tambayar Hajiya Zulfa'u ko ta san dalilin kiran da Alhaji Babah ya mata amma Hajiya Zulfa'u ta ce bata san dalilin kiran ba hasalima ta nuna mata itama kiranta Alhaji Babah ya yi,muryar Alhaji Babah ne ya katsewa Hajiya Bilƙisu tunani in da ya ce ''mata nawa ne cikin kungiyar da kuka kafa?" wani irin bugu kirgin Hajiya Bilƙisu ya yi sosai ta yi mamakin tambayar da Alhaji Babah ya masu a ina ya samu labarin kungiyar su shikenan sun shiga uku,a hankali ta ɗaga hannu ta share zufa da ya fitso mata a fuska lokaci guda tana tunanin amsar da zata bawa alhaji Babah,cike da hikima ta kalle Hajiya Zulfa'u da gefen ido,muryar Alhaji Babah yasa Hajiya Bilƙisu ɗago kai da sauri inda ya ce ''ba ku ji abinda na ce ba?" sosai Hajiya Bilƙisu ta tsorata amma sai ta daure ta kirkiri wata murmushi ta ce ''wace kungiya kuma Baba?''..shiru ta yi na wasu ƴan sakanni har sannan fuskarta dauke da murmushi tana gyara zama ta ce ''bama da wata kungiya'' sosai ran Alhaji Babah ya ɓaci amma bai nuna ɓacin ransa ba kawai ya yi murmushi ya ce ''za ku faɗa min gaskiya ko sai na saɓa maku,tabbas Bilƙisu ba ki da tsoro kuma ba ki da kunya,zan sake tamabayarku yanzu in kin so ki saki min karya,shin mata nawa ne cikin ƙungiyar shedanci da kuka kafa?" jin furucin Alhaji Babah yasa Hajiya Bilƙisu fahimtar Alhaji Babah ya san komai saboda haka babu dalilin cigaba da masa karya kawai zata faɗa masa gaskiya,cikin rawa murya ta ce ''mu talatin ne cikin kungiyar" Alhaji Babah ya jinjina kai ya ce ''kungiyar ta mecece sannan me dalilin kafata kuma wata gudumawa take bawa al'umma?" tambayoyin da Alhaji Babah ya jero yasa Hajiya Bilƙisu mayar da dubanta ga Hajiya Zulfa'u dan ita baza ta iya amsar tambayoyin ba sai dai in su biyun amma ga mamakin Hajiya Bilƙisu fir Hajiya Zulfa'u taƙi kallon inda take,kenan baza ta yi magana ba,tana cikin wannan yanayi Alhaji Babba ya ce ''ina sauraron ki'' wata doguwar ajiyar zuciya Hajiya Bilƙisu ta sauke kafin ta fara magana cikin rawar murya gaba ɗaya bayanai da take yiwa Alhaji Babba basu da ma'ana da ta dauko zancen kamar abin arziƙi sai ta sake ta koma wani daban,shi dai ya yi mata shiru har ta gama maganganunta marasa kan gado,bayan ta idah zancen ta ne Alhaji Babah ya sauke ajiyar zuciya ya ce ''''madallah na ji duk bayanan ki amma ina son ku sani dukan ku biyun kun ɓata min rai ni da mahaifiyarku yanzu haka muna cikin fushin ku,sannan abinda ku ka yi ba ku kyauta ba ko kaɗan'' shiru Alhaji Babah ya yi yana sauke numfashi saboda sosai ransa ya ɓaci,Hajiya Zulfa'u kowa tuni hankalinta ya tashi tabbas ta san za a yi haka amma ta zaɓi hakan kan su cigaba da cutar da jama'a,ita dai Hajiya Bilƙisu shiru ta yi tana sauraron Alhaji Babah sanin kanta ne yanzu da mahaifinsu ya san komai sai yadda hali ya yi,suna cikin wannan tunanin suka jiyu muryar Alhaji Babah ya ce ''bayan mutuwar aurenku na ce da ku kuyi wani auren ku ka ce baza ku yi aure ba kasuwanci za ku yi,na yarda da ku na yarda da tarbiyyar da na baku da nitsuwar ku,duba da irin wahalhalu da kuma kalubale da kuka fuskanta a rayuwar aurenku ya sa na amanta da ku,na dauki kuɗaɗe masu yawan gaske sama da miliyan ashirin na baiwa kowacce daga cikin ku dan ta yi kasuwanci kamar yadda ku ka bukata,na baku gida na baku mota'' shiru Alhaji Babah ya yi na wasu ƴan sakanni zuwa yanzu idanunsa sun fara riƙida daga fari zuwa ja,wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce ''Biklisu''..shiru Hajiya Bilƙisu ta yi kanta ƙasa bata iya amsa kiran da ya yi mata ba,a hankali Alhaji Babah ya mayar da dubansa ga Hajiya Zulfa'u ya ce ''Zulfa'u''.. ita ma shiru ta yi tana share hawaye cikin raunanniyar murya Alhaji Babah ya ce ''kun yi min adalci? sakayyar da za ku yi min kenan? babu yadda ban yi ba ku zauna nan garin ku yi sana'a ku ka ce sam Kaduna zaku,na aminta da ku na yarda na barku kun tafi Kaduna dan yi kasuwanci amma bayan tafiyar ku kun watsar da komai kun zama sheɗanai masu kashe aure,wadannan mata da ku ka tara su a kungiya ina ma da shawarwarin zaman gidan aure da zai taimaka masu ku ke basu ina ma ace  koyar da su zaman aure ku ke bisa sunnah da hadisan Manzon Allah (S A W) amma sai ku ka buge da kashe masu aure ku sanyawa kanku makirci da kissa irin naku na mata'' shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni kowacce da tunanin da take,bayan wasu ƴan minta Alhaji Babah ya daura da ''ku sani ba zan bar maganar nan haka ba dole zan dauki mataki,ina nan garin ina tunanin kuna can Kaduna kuna kasuwanci,ban sani ba ashe kuna can kuna ɓata mani suna,wata ƙilah duk garin an sanku ko kungiyar da ku ka kafa,in ma duka garin basu san ku da kungiyar ba na tabbata labarin ku ya zaga wurare da yawa a garin,za kuma a samu masu kwashen alhaki da za suyi ta zagina ni da mahaifiyarku za su yi tunanin bamu baku tarbiyya ba,alhali gamu nan zaune ba mu san abinda ku ke aikatawa'' gyara zama Alhaji Babah ya yi har sannan idanunsa kan Hajiya Bilƙisu da Hajiya Zulfa'u a hankali ya sauke ajiyar zuciya daga haka ya ce ''kun cuce mu,kun zalunci mu,kun ci amanar tarbiyyar da muka baku,kamar yadda na faɗa a baya zan dauki mataki a kanku tabbas zan dauki mataki zan yi maku hukunci daidai da abinda ku ka aikata musamman ke Biklisu'' daga haka ya mayar da dubansa ga Hajiya Bilƙisu ya ce ''Biklisu'' Hajiya Bilƙisu kanta ƙasa ta ƙasa cewa komai,Alhaji Babah ya ce '' in har kuna son cigaba da amsa sunakun matsayin ƴaƴana dole ku bi waɗan nan abubuwa uku da zan lissafa maku,na ɗaya daga yau babu kungiyar matan gida,kai daga yanzu ma babu kungiyar kuna jina?" kawunansu ƙasa ba su ce komai ba ''Bilkisu ina son ki dauki wayar ki yanzu ki shiga group ɗin shidanci da ki ka buɗe wanda ki ka haɗa ƴaƴan mutane ciki,ina son ki shiga group ɗin ki rubuta masu kina son ganin kowacce daga cikin su gobe da la'asar a gidan ki,kamar yadda kike rubuta duk sanda za ki haɗa taro,sa'anan kuma ni da mahaifiyarku zamu bi ku kaduna gobe,ke ki ka buɗe kungiyar aiy ko,to ke za ki tarwatsa shi,ni da mahaifiyarku zamu kasance a wajen taron za kuma ki faɗa masu kungiya ta daina aiki babu kungiya,saboda kungiyar bata haifar da alkairi ba sai musiba cikin al'ummar manzan Allah,aure sunnah ce ta ma'aiki,amma ku biyun nan you are againts that,kenan kun tabbatarwa kanku ku shaiɗane ne,bayan kashe auren jama'a da ku ke yi kun sa kanku cikin shirka da bin ƴan tsibbu







abu na biyu da nake son ku sani shine duk yaran mata da ku ka yiwa mazajensu sihiri ba da sanan su,ba tare da yardar su ba sai bayan ku yi sihiri ku ke sanar masu,duk sanda ku ka samu saɓani da waɗan nan yaran sai ku je ku ɓata sihirin dan kawai ku hana su zaman lafiya da mazajen su,to ina son ku sani duk yarinyar da ku ka yiwa sihiri za ku je ku nemi gafara iyayenta,za kuma ku je nemi gafarar mazajen da kuka yiwa sihiri za kuma ku faɗa masu komai,in sun yafe maku shikenan in kuma basu yafe ba duk hukunci da suka yanke a kanku ni ba zan hana su ba,sai kuma abu na gaba duk wani abinda na baku zan karɓa zan karɓi gida da mota da kuma kuɗaɗe da kasuwancin da na kafa maku,za ku dawo zama tare da mu ni da mahaifiyarku,dah na yi tunanin kuna da hankali amma kun nuna min baku da hankali zan kuma koya maku hankali,abu na gaba kuma shine ko da iyayen yaran da kuma mazajen sun yafe maku basu dauki mataki kanku ba ni zan hukunta ku, da kaina zan kai ku police station zan shigar da ƙarar abinda kuka aikita za kuma aika ku kotun addinin musulunci a yanke maku hukunci dai dai da abinda ku ka aikita,sannan zan kira ƴan socail media su dauki komai su haska wa duniya,daga ranar da zan kai ku police station zuwa ranar da za a yanke maku hukunci,waɗan nan abubuwa da na lissafa maku su ne hukunci da zan maku matsayina na mahaifinku da kuma matsayin wanda ya baku amana kun ci amana'' Alhaji Babah yana gama faɗin haka ya tashi bar parlourn Hajiya dai shiru ta yi tana ƙarewa ƴaƴanta kallo can ta taɓe baki tare da miƙewa tsaye ta bi bayan Alhaji Babah ita tun da can ba mai magana ba ce bata taɓa ja da hukuncin Alhaji Babah ita a wajenta duk hukuncin da yanke kan ƴaƴansa daidai ne hakan yasa tun sanda ya fara magana bata ce komai ba,ko kaɗan bata ji dadin abinda su Hajiya Bilƙisu suka aikita ba,bayan fitar Hajiya daga parlour Hajiya Zulfa'u ta daga kai a hankali ta kalle Hajiya Bilƙisu da har sannan kanta ƙasa ko kaɗan Hajiya Zulfa'u bata yi tunanin mahaifinsu zai dau zafi haka ba,a tunaninta zai ce a kashe kungiyar ne kawai gashi ya ce zai kai su police station da kotu,zai kuma sa su a media,ita bata da matsalah da media in har Allah zai yafe masu abubuwan da suka aikata media ba komai ba ce,murya can ƙasa ta ce ''ya ilahi'' jiki babu kwari ta tashi ta bar parlourn,Hajiya Bilƙisu ta dauki sama da mintina goma zaune cikin parlourn tana tunanin tsabar tashin hankali har wani ciwo kanta ke mata lokaci guda jikinta ya dauki zafi duk cikin maganganun da Alhaji Babah ya yi baban abinda ya fi daga mata hankali shi ne inda Alhaji Babah ya ce za su je neman gafarar wa'inda suka yiwa sihiri innalillahi wa inna ilaihi raji'un da wani ido zata kalle iyayen yara da mazajensu da har yanzu tana zumunci  da wasu daga cikin su,kenan duk wata isa da gadara da kuma  izza da jiji da kai da take da shi ita ce zata je neman gafara tabbas Alhaji Babah so yake ta wulakanta,ga kuma media shikenan ta rasa duk wata daraja da mutumci idon jama'a sanin kanta ne mahaifinta yana da zafi sosai amma bata taɓa kawo zai mata haka ba duba da irin son da yake mata,a fili yake nuna mata so fiye da Hajiya Zulfa'u,Hajiya Bilƙisu ta ɗaukarwa kanta alkawarin hukunta duk wanda ya tona masu asiri wajen Alhaji Babba koma waye sai  ta yi maganinsa 






*SHUUKRAN*