MIJIN AMAL

Chapter 19

by @reza12

MIJIN AMAL

Chapter 19

Cikin sauri likitar tai yunƙurin rike ta amma ta sake daka mata tsawa akan ta rabu da ita, gara ta mutu kawai idan ba zata faɗa mata abun dake damunta ba. Sai ta ce "To ki natsu zan miki bayani, ki daina wannan maganar kinga bakin ki na zubar da jini". Amal ta tsayar da kukan tana kafe ta da ido gabanta na faduwa, ƙirjinta na hawa da sauƙa yana mata wani zafi. Kawai maganganun da Yasir yay mata jiya ne suke mata yawo akai. Wai to ta mutu ɗin ma mana. Kafin ta ce wani abu sai ga Yasir ɗin ya shigo ɗakin da sallama. Ganin su a haka ne ya ce "Mai ya faru? Ta farko ne?" "Eh ta farko yanzu". Likitar ta bashi amsa. Ya ƙaraso gurin da take ya ce "Sorry Amal ya jikin naki?". Sai ta daɠo tana kallonsa, ta sa hannu ta shafo bakinta da yake jini. Ta kalli jinin, sai ta sake fashewa da kuka. Tana son yin magana amma bakinta zafi yake mata sosai, duk maganar da take yi dariya ce da ƙarfin hali. Likitan ta ce "Bari a mayar miki da ruwan tukunna. Please ki kwantar da hankalinki kinji ba abun da zai faru dake in sha Allah". "Cikin kukan ta sake faɗin "Mai yake damu na kunƙi faɗa min, kuna ganin halin da nake ciki. Kunsan irin wahalar da nake sha kuwa? Ku kalli jini ne fa yake fitowa daga bakina, ko wannan ba zai sa ku tausaya mim b". Tana faɗa sai taji kamar wani abu a ƙirjinta dalilin tarin da tayi, kuma dama tun ɗazun take jin gurin na mata zafi. Hakan yasa ta leƙa cikin rigar asibitin dake jikinta. Sai ta ga bandeji. Hakan yasa da sauri ta ɗaga rigar tata sai taga bandeji ne a ƙirjin nata. Ta shafa kan abun domin ta gani ko dai maƙalewa yayi. Sai dai ta ji shi gam, har da wani zafi ma da ya ziyarce ta. Cikin wani sabon tashin hankalin ta fara tambayar su kamar zata shiɗe tsabar kukan fitar haiyacin da yake yi, ga jin bakin nata duk ya ɓata mata riga da bakin. "Mai ya kawo wannan jikina? Mai kuka sake cire min a jiki? Waiyoo ni Allah ka fitar dani a cikin wannan masifar, innalillahi wa innalillahi mai nai muku, Yasir mai nai maka har haka, dani kake son yin kuɗi kenan?". Ta ƙarasa tana sunkuyar da kai, har lokacin duk magana ɗaya bakinta ƙara zubar da jini ya keyi. Likitar ta kama hannunta ta mayar mata da ƙarin ruwan. Kuma bata ce komai ba. Haka tayi shiru tana jin lokacin da likitar ta fita ya rage su biyu a fakin. Bata yarda Yasir zai iya cutar da Ita ba a da, amma tun lokacin da ya fara gudunta ta tabbatar da cewar tabbas idan wani abu ya sameta ba zai iya zama da ita ba, gashi kuma yanzu yana amfani da ciwon yana sayar da wani abu daga jikinta. Ya ce "Faɗuwar da kika yi jiya ne kika bugu akan ƙirjinki, shine jini ya taru a gurin. Hakan yasa aka miki aiki. Babu abun da aka cire a jikinki. Ki kwantar da hankalinki, kin fi kowa sanin ni ba mugu bane". Yana gamawa ya fita daga ɗakin. Bata ce komai ba, domin bata yarda ba, daga yanzu ba zai sake faɗa mata abu ta yarda ba, kuma wallahi sai an faɗa mata abun da akai mata ko ta kai asibitin ƙara. Kuma dole sai sun faɗa mata abun da yake damunta da gaske, domin izuwa yanzu ta gane suna ɓoye mata wani abu ne.

Yana shiga ofis ɗin likitar ya sameta tana ta zagawa ta kasa zama. Yana shiga kuwa ta juyo da sauri a tsorace tana faɗin "Yasir kai nake jiya hankalina ya kasa kwanciya. Ya ake ciki yanzu? Wallahi yanayin yarinyar nan ya bani tausayi, tana jin jiki sosai, kuma zata iya bamu matsala idan bata kwantar da hankali ba". Ya ce "Ta yarda dani, ba abun da zata iya yi, na mata bayani yanzu. Yana faɗa ya ɗora da faɗin "Yaushe likitan zai tafi?" "Abun da ya kawo shi kenan kuma ya gama. So ina jin gobe da safe zai bi jirgi ya koma". Yasir yayi shiru. Ta ce "Sannan yace yana son magana da kai". Ya ɗago da sauri da mamaki. Ta ɗaga masa kai. Ta ce "Biyoni" tayi gaba ya bita har ofis ɗin da yake. 

A lokacin da suka fito daga ofis ɗin likitan daga ita har shi fuskokinsu babu annuri. Ta miƙa masa wata takarda ya amsa yana shiga ɗakin da Amal take. Ya jingina jikinsa da ƙofar yana kallonta. Gaba ɗaya ya gaji ba zai iya ba, wannan abun yafi karfin sa, ace daga wannan sai wannan. Ya na tsaye a gurin likitar ta sake dawowa ta duba jikin Amal ɗin. Sai da ta fita kafin ya karasa bakin gadon ya jawo kujera ya zauna. Sai da yayi kamar minti biyu yana kallonta itama tana kallonsa Kafin ya ce "Ina so ki fahimce ni, ban san yadda zaki ɗauki maganar ba, amma dai ki min adalci kuma ki natsu". Sai kuma ya kasa ci-gaba da maganar kuka yazo masa. Ya tashi ya fita yana toshe baki. Amal da take sauraronsa da kallonsa. Tayi ƙarfin halin faɗin "Idan maganar tana maka nauyi ne ka rubuta min a takarda sai ka bani. Ko ka manta ina iya fahimtar abun dake zuciyar ka kafin ka fitar?". Ya tsaya chak a bakin kofar. Kamar ya juyo sai dai ya fita. Ya shiga mota ya zauna ya kasa tafiya. Sai da ya sha kukansa ya ƙoshi a cikin motar kafin ya fara tunanin mafita mai ɓullewa. A karon farko da damuwa ta hana Yasir kallon Ball, har ma ya manta da suna da wasan. Yana ta tunanin yadda zai iya faɗa mata wannan maganar da yadda zata fahimta. Duk da ya san halinta, kuma tana fahimtar sa kamar yadda tace, but yasan ba zata fahimci wannan ba. Take wani tunani ya faɗo masa. Yana jin wayarsa na ƙara amma yayi banza da ita. Ya ja motar ya nufi kamfani.

Tun daga nesa yake addu'ar Allah yasa tana nan. Ai kuwa ya hango motar ta a gurin da take pakin. Bai ma gama daidaitawa ba ya sakƙo ya nufi ciki. Sai da yakai ƙofar zai shiga kuma tsoro ya dirrar masa. Anya kuwa wannan da ta tsane shi zata yarda!. Sai yayi ta maza ya buɗe ya shiga da sallama. Ya sameta tana waya tana aiki. Dama ita ba dai mai da hankali akan aiki ba, yana tunanin shine ma dalilin da yasa aka bar mata jan ragamar aikin kamfanin. Domin irin kokarin ta ba duk namiji ne zai iya ba. Ganin shine yasa ta tsaya da rubutun kamar da ɗan mamaki domin dai bata ne me shi ba. Yasir ya gaidata a dake. Bata amsa ba sai ma alamar tambaya da tai masa da abun rubutun hannunta. Babu wani kwana-kwana ko kauce-kwauce ya fara faɗa mata abun da yazo da shi. 

Suhailat ta ajiye abun rubutun ta ƙura masa ido. Wani irin murmushin farinciki ne ya mamaye ta. Har ta kasa ɓoye hakan. Ta miƙe tsaye ranta fess. Ta zagayo har gabansa har yana jin kamshin turarenta, da hucinta. Ta tsaya tana kallonsa Kamar zata shige jikinsa. Ta ce "Ar You serious?" Ya ɗaga mata kai ya ɗora da "Dan Allah ki taimaka min wallahi..." Da sauri ta ɗaga masa hannu. Sai kuwa ya tsaya daga dogon roƙon. Ta ce "Naji zaka iya tafiya". Sai ya kalleta da mamaki. Ya ce "Kin amince kenan?" Ta ce "I say get out of here my friend". Ta faɗa da karfi. Yasir yayi waje yana juyowa yana kallonta, a ransa dama yasan haka za'ayi. Yana fita ta ɗauki waya ta latsa kira ranta dad'i gamar an tsoma ta a kokin zuma. Ga dama tazo har gida tana zaune. 

Yasir ya shiga ofis ɗin sa ya ƙarasa abun da zai ƙarasa ya fito. Ganin kamar an buɗe ofis ɗin tane an shiga yasa ya tambayi masingan ta. Ya tabbatar masa da cewar ƙanwarta ce tazo yanzu. Yace ya gode sannan ya bar kamfanin gaba ɗaya. Asibiti ya nufi. Yana zuwa kuwa ya samu Mama da Nana da wasu mata hudu. Yan Mata biyu da manya guda biyu, duk ya san su, family ɗin ta ne. Yana ganinsu ya juya zai fita domin baya ko son ganin su ma wallahi. Amma maganar da ɗaya daga ciki tai masa ce tasa ya tsaya. "Mun zo mu tafi da ita gida ne kafin ka ƙarasa kashe mana ita. Bayan cutar da ita da kuka yi yanzu an fara cire mata wani abu a jiki. To ba zata saɓu ba, wallahi sai mun tafi da ita, kuma idan baku faɗa mana abun da kuka mata ba kotu ce zata rabu mu da wannan asibitin". Yasir ya karasa ciki ya bisu da wani irin kallo ɗaya bayan ɗaya. Sai ya kalli Amal da take shan tii. Aransa yana mamakin kenan ta faɗa musu hakan ne. Ya ce "Ya jikin naki?" Ta kawar da kai. Ya ce "Kina son binsu?" Ya faɗa a hankali?" Sai ta ɗago da sauri ta kalleshi. Ya ɗaga mata kai shima. Sai itama ta ɗaga masa. Sai kuwa ya ce "Ku shirya ku same ni a Mota sai na ajiye ku a gida". Ya faɗa yana barin ɗakin idanunsa akan kwanon da yaga kamar abinci taci, kuma yasan farfesu ne, duk da tasan an hana ta ci. Ɗaya daga cikin budurwayen gurin ta ce "Ba ma sai ka kaimu ba, zamu iya zuwa ko da ƙafa ne". Bai bi ta kan maganganun da suke yi ba, ya bar ɗakin. Ya shiga mota ya zauna. Ya dauko waya. Sai yaga kiran Yaya. Kamar kar ya ɗaga sai kawai ya ɗaga da sallama. Ta cikin wayar ya ce "Yasir, ashe ƙiyayyr da kake min har ta kai matar taka tayi ɓari baka faɗa min ba, kuma sannan aka kwantar daku a asibiti nan ma baka faɗa min ba? Dama haka ka ɗauki lamarin yan uwantaka, wa kake da shi a duniya da ya wuce ni.? Yanzu kana ina? Gida ko asibiti?" Ya jiyo harda muryar Anty Maryam tana tambayar ya jikin Amal ɗin. Ya ce "Ina gida, yanzu aka sallamo mu". "Tom shikenan in sha Allah muna nan zuwa yanzu". Daga haka suka kashe wayar. Sai da kusan minti uku ya sake kiran Ali. Yana ɗagawa ya ce "Na ta kiranka tun muna tare da su baka ɗaga ba, yanzu basa nan amma dai sun bani number su, akan idan ka yarda akan hakan to suma sun amince". Yasir ya ce "Akan nawa?" Ya ce "Yadda dai yake a farko". "Tom na amince". Ya faɗa kansa tsaye. "To yanzu kana ina?" Ya buɗe baki zai bashi amsa kenan yaga fitowar su kuma sun nufi bakin titi. Ya fito da sauri yana cewa Ali yana zuwa. Ya ƙaraso gurin ya ce "Ga mota ta cen ku nake jira?" "A'a ba sai mun shiga motar ka ba, ko keke ne zamu samu. Ya kama hannun Amal da nufin ya jata. Amma ya fasa. Sai kuwa ya sunkuceta yayi mota da ita. Ya buɗe motar ya ajiye ta a gidan gaba ya kunne motar ya bar gurin. Babu irin zagi da ihun da basuyi masa ba, harda cewa baro ne. Bai ce mata Komai ba, itama sai kuka take yi ƙasa-ƙasa. Bayan sun isa gida ya buɗe ta fito. Bata tsaya jiransa ba tayi gaba tana kuka. Yana ƙoƙarin pakin sai ga motar yaya ta shigo. Shima ya paka. Anty Maryam da yaran suka gaida shi kafin suka shige ciki. Yaya ya kalli motar ya ce "Gaskiya ne ma'aikaci. Irin wannan ɗanyar mota haka". Yasir ya kawar da kai kawai. Yayi gaba ya bishi. Lokacin da Anty Maryam ta ga Amal bata ganeta ba, sai cewa tayi ina matar gidan. Da yake ta sameta a duke kuma tana kuka. Amal ta ɗago da sauri jin muryarta. Ai kuwa ta saki salati tana ɗan ja da baya, ganin yadda ta rame kuma fuskarta duk.ƙuraje irin masu chakudewa mutum fuskar nan. Ta ce "Amal kece haka?" Suna cikin haka mazan suka ƙaraso. Shima dai Yaya da mamaki yake kallonta. Ya ce "Wani irin ciwo ne haka?" Yasir ya faɗa masa. Sai yace "Wani asibiti kuke zuwa?" Nan ma ya faɗa masa. "Amma da gaske ciwon ne kawai yake damunta?" "A'a wai da wannan ɓarin da tayi". Anty Maryam ta ce "Ɓari kuma? Daga yin ɓari sai wannan ciwon, ina karya ne, dole akwai abun da yake damunta". "To yanzu ma daga asibiti muke, kuma haka suka ce mana, ga maganin da muke amfani da shi ma". Ya faɗa yana shiga daki ya kwaso. Ita dai Amal tana tsaye a gurin sai binsu da ido take. Bayan sunga maganin ya ce "Ta yaya zamu gane maganin babu gidan sa, haka suka baku shi?" "Eh shi baya zuwa da gida". "No dole zamu Kaita wani Asibitin domin su duba ta da kyau. Kai baka ganin yadda ta koma ne, wai ma anya kuwa kaine wannan Yasir? Jifa yadda Amal ta koma kamar ba ita ba, ko dai ba ita ba ce?" Ya faɗa ganin yadda Amal ɗin ma bata iya cewa komai ba. Anty Maryam ta ce "Nima dai abun da nake tunani kenan ko kuma kun samu wata matsala ne?" Kafin yace wani abu sai ga tawagar Mama sun ƙaraso cikin gidan dauke da buhunhunan tashin hankali niƙi-niƙi a kansu. Suka ce wallahi sai an basu ƴarsu sun tafi da ita, an gama auran daga yau, kuma sai sun kai ƙarar sa. Nan Yaya yayi ƙoƙarin shiga tsakanin su amma ina suka fara haɗawa da shi suna zagi. Shi kuma yace ba inda matarsa zata tafi. Sosai rikici ya ɓarke a gidan kowa na faɗin nasa. Amal dai guri ta samu ta zauna ta dafe kai domin yadda kanta ke sarawa da hayaniyar, ga jiri da yake son zubar da ita. Yaya ya ce "Muma yanzu maganar da mukeyi kenan anan cewar zamu kai ta asibiti. Amma Mama ta ce ina sune zasu tafi da ita. Ran Yasir ya ɓaci, yan zuciyar suka zo. Ya ce "Idan har suka fita da ita ba zai je ya dawo da ita ba". Mama ta ce "Kar ma Allah yasa ka dawo, amma ya sani duk abin da aka kashe na asibiti shi biya biya". Har sun fara tafiya yayi wani tunani yace bai yarda ba. Karshe dai zagin Mama ne kawai baiyi ba. Har Yayan nasa ma da yazo yake goyan bayansu. Ana cikin haka Amal ta zube a gurin. Take suka yi shiru suna kallonta. Hakan yasa suka aka fara ƙoƙarin daukar zuwa asibiti. Yaya yace babban asbiti za'a Kaita. Yasir ya ce asibitin da suke zuwa za'a je. Nan ma sai da aka sha daga, wanda har sai da yan unguwa suka san abun da yake faruwa. Nan ma aka bawa Yasir rashin gaskiya har ma wasu na zaginsa. Ai kuwa suna zuwa babban asbiti aka basu babban gado kaman yadda Yaya ya faɗa. Har bayan sallar magariba gaba ɗaya suna tsaye. Har lokacin Yasir bai zo ba. Hakan yasa suke ta faɗin kunga abun da suke faɗa ya tabbata ko, gashi yaƙi zuwa. Suka cikin haka kuwa sai ga likitan ya ƙaraso gurin yana kallon su. Ya ce "Waye babanta?" Mama ta ce "Ya rasu nine?" "To ina mijinta?" Ɗaya matar ta ce "Baya nan amma ga yayansa?" Likitan ya ce "Ko zamu iya zuwa ofis yanzu". Haka suka tafi harda Mama. Bayan sun zauna ya fara basu bayanin da tun kafin a ƙarasa Mama ta saki wani irin ihun da tasa likitan ya dakata da bayanin. Shi kansa yaya da yana da damar yin ihun da yayi....📝