NI DA YA NABIL

001

by @swrites22

_ NI DA YAYA NABEEL _



  _YOUNG WRITER✍️




_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

_ Kamar yadda zan fara rubuta littafin nan lafiya ina roqon Allah ya bani ikon kammalashi  lafiya. AMEEN_

_ ina roqon allah ya bani ikon rubuta daidai ya kubutar da hannu na daga rubuta kuskure_


* 001 *


"Nabeel wai me kake nufi da mu ne tunda kasa kafa Ka dauki matarka kabar garin nan kusan shekaru uku kenan, ka ma manta da batun mu. Wannan yana nuna ko bayan ran mu baza ka duba yan uwan Ka ba ko? Tho Ka sani ba jumaymah kadai ke da hakki a kanka ba muma muna dashi a matsayin mu na iyayan ka. Sannan kuma kana sane ai da batun Assum, kuma kasan itama tana da hakki a kanka tunda matarka ce. Ka kuma san halin mahaifin Ka sarai whl lokacin da ya sa na cika ba karamin aikin sa bane ya dauko ta ya biyo Ka da ita, dan kai dai baka isa Ka ɓata musu zumumcin su ba, dan ba kanka aka fara wanna auran zuminci ba kuma ba kanka za'a gama ba".

Da wata irin sassanyar murya me cike da nutsuwa ya ce, "kiyi hakuri mommy, ban manta ba in sha ALLAH muna hanya, zuwa next week zamu shigo". 

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce, "Shikenan Allah ya kawoku lpy, kuma zan baka shawara wannan boye boyen da kakewa Jumaymah duk ba zai kai ka ba, ya kamata by now Ka sanar da ita dan tasan ba ita kadai bace".

Dan jim yayi kafin a sanyaye ya ce, "Amma mommy......".

"Kai dallah rufemin baki, na gaji da jin wanna shashancin naka, ga ka dai kamar namiji amma a bangaren gidanka kana son zama shagiri girbau. To ka bar ganin Ka haka abinda zan hango ma ko jirgin sama Ka hau baza Ka hango ba shiyasa nake baka wannan shawarar".

Jin yayi shuru bai sake cewa komai ba ya sata faɗin, "In kaga dama ka dauka in kaga dama ka zubar ya rage naka". Tana faɗin haka ta kashe wayar tana mita haka kawai in sha wahalar dan nawa ni kaɗai yanzu kuma daga sama wata takurarriyar yarinya tazo ta canjawa yaro na tunani, to ba zai yiwu ba Whl. 

Maganarta ta katse ne sakamakon shigowar wasu yan mata guda biyu dayar na dauke da wata baby da bata fi 1 year ba, dukkan su sanye suke da jilbab ɗin da har jan ƙasa yake.

Murmushi ne ya wanzu akan fuskar mommy ta kalle su tana faɗin, "Oyoyo yan albarka, Assuma har kun dawo kenan?". Zama sukayi a gefe da gefenta sai ya zama sun sa mommyn a tsakiya. Sauke yarinyar dake kan kafaɗarta tayi ta kwantar da ita kan gadon, cikin zazzaqar muryar ta mai dadin sauraro tace, "Whl kuwa, mun dawo mommy".

"Ai baki ga irin wahalar da muka sha ba Mommy, kamar zanyi ihu haka nakeji kuma duk laifin Asum ne da shegen taurin Kan tsiya kamar mutanen farko, saida nace mata mu jira hamma sameer tunda naga fita zaiyi sai ya sauke mu, tunda su direbobin gidan nan sai Ka tashi fita Ka neme su Ka rasa. Amma fir baiwar Allah nan tace baza a tsaya ba, ita kuma adda sofy kamar wadda take tsoron ta tace Eh Muje kawai mu tsari abun hawa, haka suka dibe mu a wata akwalar napep muka dinga fadawa ramuka ni saura kadan ma na gangara lamba 2". Dayar ta faɗa.

Dariya Asum ta kwashe da ita harda tafa hannu. 

"Shegiya ai kinsan me kikayi dole kiyi dariyar mugunta".

Mommy tayi murmushi tana dubansu ta ce, "Tho ni dai yanzu duk ba wannan ba yayan ku Nabeel na hanya, next week in sha allahu yana garin nan dan haka ku fara shirin tarbansa".

Haɗe rai Asum tayi tana turo baki ta ja tsaki a zuciyarta, sai kuma ta miqe ta sake ɗaukan yarinyar data kwantar tana fadin, "Mommy ni barin shiga wurin Umma. Ke Hamdah in zaki shigo ki karbo min sakona wurin Adda sanaya, kuma whl karki manta".

" Dake ga yar aiken ki ba, Allah assuma ki fita a ido a kan rufe tam". Ta ja kwafa. Ita dai Asum bata kulata ba sai cewa da tayi mommy sai anjima, tayi ficewarta.

Tana fita bangaren dake hannun damar ta ta shiga, a kan kujera ta zube bayan ta ɗaura yarinyar Kan cinyar wata budurwa dake zaune a falon tana kallo, jilbab din ta cire tana kallon dan saurayin dake zaune a kujerar ƙarshe tace, " Hamma Abid saukar yaushe?".

"Ai bari kawai Asum, ni ai gudowa nayi dan whl bazan iya ba. Ashe haka ake shan wahala wurin training ɗin nan ni ina tunanin zama airforce su suna ƙoƙarin sawa mu baqunci lahira lokacin mu baiyi ba". Cikin dariyar dake ɗauke da zallar mugunta tace, "A'a su hamma Manya, haka akayi ashe? Gashi kuwa ka sha aski me kyau whl. Kanka sai daukan ido yake. Our great .....".

Katseta yayi ta hanyar faɗin, " Ke ya isheki kuma, ke komai sai kin maida shi wasa ne?". Yarinyar da Asum ta shigo ta samu ne tace, "Yanzu dama shigowarkan nan Hamma gudowa kayi? Amma gsky ka bamu kunya, yanzu su ya Nabeel kuma su ce mene".

Asum ce ta cafe da faɗin, "Ke ya ma akayi baki kira ni ba, ai naso ganin yadda ya shigo whl". 

"Bai daɗe da shigowa ba afujajan, nima shuru na masa na bari ya gama dawowa hayyacinsa sai inji daga ina ashe ma wai gudowa yayi".

"Umma ta sani ?". Ta tambaya a ƙage. Kafin ta bata amsa ta sake faɗin , "Ke Matsalata dake in zakiyi abu yadda kika san marar lakka a jiki".

"Ni dan Allah karki fara min masifar nan taki. Umma bata nan". Tsaki Asum taja kafin tace, "Haka dai".

Hamma Abid da ya sake kurbar ruwan sanyi kafin yace, "Ke Asum aka barki da mutum masifarki kawai ta ishe shi, ga shegen taurin kai da rashin ji uwar diyar aljanu, duk kin bi kin takurawa Naseemah baiwar Allah. Ni ai ba dan ku yan biyu bane d..."

Katse shi tayi da faɗin, "Ni whl hamma Abid bazan iya jakanta irin ta Naseem ba, in tayi wani abu ji nake kamar na hambare ta, haka fa ko a scul za ai ta cin zalin ta saidai in ina nan in shigar mata. Sanyinta yayi yawa whl, kamar dai ba gware tayi da Asum tazo duniya ba". 

Wata dattijuwar mata ce me tsananin kama dasu tayi sallama ta shigo, lokaci guda Asum ɗin ta nutsu har tana riga su amsa sallamar ta daura da faɗin, "sannu da zuwa umma na" 

Amsawa tayi tana bin su da kallo kafin ta karasa shigowa ta samu wuri ta zauna sannu da zuwa suka mata ta amsa cikin kulawa tana fadin kai kuma fa?". Ta tambaya tana kallon Hamma Abid da ya kama susa kai, kafin yace, "Umma hutu nazo".

" Hutu a yanzun ?".

"Eh..a..ai....". Katseshi tayi da faɗin, "Shikenan, bari ai zan tambayi yayan naku inji". Ai kafin ta rufe bakin ta ya dawo gabanta, ya riqo kafarta, kamar zaiyi kuka ya shiga faɗin, "Umma dan Allah karki tambayi ya Nabeel, ni zance masa bani da lafiya ne shiyasa nazo na dan huta, Umma Whl .....".

Katse shi tayi da faɗin, "Kaga ka tattara gobe ka koma in da Ka fito, ina cewa nan ka kafa ka tsare kai sai a kaika makarantar Airforce, to ba ruwana kuje can ku karata kai Ka jiyo".

Asum data kawowa umma ruwa ne tace, "Kuma whl yanzu mommy take fada mana next week zai shigo".

Karbar ruwan tayi tana murmushi tare da shafa kanta tace Allah ya Miki Albarka assumi tah. Ai gwara ya dawo ɗin".

"Ameen". Ta amsa cikin jin dadi. Harararta Hamma Abid yayi kafin yace, "To umma ni da ba kullum kike gani na ba fa?".

Murmushi ta sakeyi kafin tace Allah ya muku Albarka gabadaya, ya kare mun ku".

" Ameen Ameen umman mu. To ya muka sameku?".

"Lpy kalau alhamdulillah, ya Kaduna ya kuma training din ? ".

"Ba wani daɗi Umma sai wuya whl".

"Ai babu abinda ake samu ta sauki Abid, Allah dai ya bada sa'a, Allah yasa a gama lpy. Asum je ki haɗamun ruwan wanka na kwaso gajiya whl".

"An gama ummana". Ta fada tana tashi ta wuce ɗakin, itama tashi Umman tayi ta bi bayanta .

Kallon Naseemah da tayi shuru tana murza kafarta a carpet din yayi har ya tashi zai fice sai kuma ya dawo, "Naseem wetin?". Ɗagowa tayi idon ta cike da kwalla tace, "Hamma wai dan Allah me nayi wa su umma ne suka tsaneni". 

Dawowa yayi ya zauna kusa a ita yana faɗin, "Subahanallahi, tsana kuma Naseem? Meysa zaki fadi haka? Umma fa mahaifiyar kice taya kike tunanin zata tsaneki, ko kin mata wani laifi ne?".

"Ni ba abinda na mata, kawai dai sunfi son Asum ne, komai Asum komai ita haka Abbah ma, duk wani abu nasu ita suke sawa. Ni kawai Abuja ma zan koma wurin Aunty badia, sai yafi min da zaman gidan nan".

"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un. Naseem ya kike ƙoƙarin barin shaidan ya kissima miki abinda ba haka ba a zuciyarki. Abinda nake so ki fahimta shi ne iyayen mu na amfani ne da banbancin dake tsakanin ki da yar uwarki akwai abubuwan da zata iya yi wanda ke baza ki iyayi ba. Ke kina da sanyi hali da kuma rauni ne Naseem. Basa son su dinga saki abubuwan da suka san zai baki wahala Naseem. Amma ba ta yadda za'ayi iyaye su haifi ya'ya suce basa son su, karki manta ke da Asum yan biyu ne, yadda suke son ta haka suke sonki ko ma fiye da ita. Da Allah ki daina ware kanki ko ki bari shaidan ya dinga saƙa miki abinda bashi ba". Daga masa kai tayi alamar to.

"Yanzu tashi ki bisu dakin".

"Ayyerh Hamma kenan, yanzu ina shiga ɗakin nan Asum zata fara habaice habaice tana faɗin da banje ba sai da na ganta". 

"Kina son sa min ciwon kai Naseem. Kamar dai baki san halin yar uwar taki ba. Ki daina kallon hakan da wata fuska mana, hakan zai iya bawa shaidan damar shiga tsakaninku fa. Ke bakiga yadda suke da Hamda ba ne, ashe gskyr Asum ɗin da take faɗin.....". Kafin ya rufe baki ta tare shi da faɗin, "Ai ka gani kai ma yanzu Asum ɗin dai, ka yarda da maganar ta, shikenan". Ta faɗa tana tashi ɗauke da yarinyar dake bacci, ta goge hawayen da ya goce mata ta wuce ɗakin Umman.

Baki sake Hamma Abid ya bita da kallo kafin ya tashi ya fice daga falon yana jinjina kai.

A ɗakin ta samu Asum na fitowa da Umma kayan da zata sanya in ta fito daga wanka, tana yi tana raira yan wakokinta. Kwantar da yarinyar dake hannunta tayi kafin ta zauna a kan bedside drawer tana kallon Asum ɗin dake tambayarta ko Hamma Abid ya bar bangaren nasu? Amma sam bata ji ta ba. 

Ita kuwa tana gamawa ta nufi ƙofa tana faɗin, "Naga alama biyoni kikayi mu raba ladan to gashi nan sai ki turara mata ɗakin da tace". Ta Ƙarashe tana ficewa, Naseem ɗin ta bita da kallo kawai. 

Ita Asum ba wai jera zama bane bata so da Naseem, kawai halayyar su ne bata zo daya ba. Ita tafi son zama da mutum me surutu irinta, ita kuma Naseem shuru shuru ce, sam bata da rawar kai, wadda hakan ke sa ana mata kallon miskila. Sannan sanyi ne da ita sosai, abinda za'ayi a minti biyu sai ta kwashe mintuna shida, shiyasa ko girki zasuyi Asum zata ce in ita zatayi a barta tayi ita kaɗai in kuma Naseem ce to tayi ita kaɗai dan ita Madam oya oya ce, ba kuma zata iya jera aiki da Naseem ba.