004
by @swrites22
_ NI DA YAYA NABEEL _
_YOUNG WRITER✍️
* 004 *
Tana fita bata tsaya ko ina ba sai bangaren su. Dakin umma ta wuce ta fara labarta mata abinda Baffah yace. "To Allah yasa hakan shi yafi alheri. Allah ya nuna mana lokacin, sai muzo mu fara shirye shirye ai". Umman ta faɗa. Kumbura fuska Asum tayi kamar zatayi kuka tace, "Umma, Umma whl ni bana san mai mata. Ni bana san mijin wata".
"Ba mijin wata bane Asum, ina hankalin ki yake? ita fa ta aure miki miji tunda kece matar sa ta farko, kece uwar gidan sa. In kikayi hakuri kika janyo hankalin sa gareki bama zaki taɓa tunanin kina da wata kishiya ba bare har kice mijin wata ne. Ke yanzu shakkar wannan ballagazar matar tasa kike? Da mai ta fiki, ni fa nasan yayan da na haifa, na kuma san tarbiyyar dana basu, ba kishiya daya ba ko uku ne, ƴata ta shiga a ta hudu saita zama mowar gidan, karki bani kunya mana Assumi".
Asum tayi tsuru tsuru kafin tace, "Umma mahaukaciya ce fa whl" .
"Saiki manna Mata haukanta can taje tai tayi, ina ruwanki da ita". Da haka da haka Umma ta dinga jan hankalin ta tana mata nasiha hadi da bata shawarwari masu kyau har sai da taga hankalin Asum ɗin ya kwanta kafin ta barta ta fita.
Dakinsu ta koma ta zauna a bakin gadon su ta fada duniyar tunani, bata dade da zama ba sai ga Naseem ta shigo, gefenta ta zauna tare da taɓata, firgigit ta ɗago tana kallon Naseem din tare da sauke ajiyar zuciya tace, "Dallah ni har kin ban tsoro?".
"Me ya faru? Me Baffahn yace?". Naseem ta tambaya tana kallon fuskarta.
"Bakomai Naseem, me kuwa Baffah zai ce kuwa, yayi masa faɗa ne dai kawai. Ke bakiji yadda mukayi da mahaukaciyar matar Ya nabeel ɗin nan ba". Gyara zama Naseem tayi Asum ta shiga bata labarin abinda ya faru. Shuru tayi kafin tace, " Asum dan Allah ki rabu dasu ki daina shiga tsakanin ma'aurata hakan ba daidai bane, kinga sanadiyyarki an yiwa Ya Nabil faɗa, hakan zai sanya masa jin haushin ki whl". (Cox Naseem bata san da zancen auran Asum da Nabeel ɗin ba, dan abu ne da aka ɗaura a sirri aka bar zancen har sai lokacin da zata tare) wani kallon 9/5 Asum ta mata kafin tace, " Allah yasa tattabaru ne su karewar aure. Kinga ni tashi ma muje part din Mommy, yau banga Hamdah ba ko breakfast ma ni ban yi ba fa". Tashi Naseem din tayi suka fice.
***********
9:22pm
Da sallama ta shiga falon yana zaune Kan kujera da laptop a gabansa amma waya yake. Wuri ta samu a kasa ta zauna kanta a ƙasa, ya dade yana wayar kafin ya gama ya jawo laptop ɗin sa ya cigaba da aikin sa kamar bai san da zaman mutum ba cikin falon. Kokarin aro jarumtar yar uwarta tayi, kafin tace, "Ya Nabeel nazo ne in baka hakuri kan abubuwan da suka faru, in sha allahu hakan baza ta sake faruwa ba".
Tsayawa yayi da aikin da yake kafin ya dago ya kalleta ta wutsiyar ido, kallo daya ya mata ya ɗauke kai ya cigaba da abinda yake, shuru ne ya ratsa kafin can ta tsinkayo muryar sa, "Get out". Ya fada a tsawace, duk yadda taso cijewa kasawa tayi, ta tashi da sauri ta fice jiki na rawa. Bin bayanta yayi da kallo har ta rufo kofar falon, tsaki yaja ya cigaba da aikin sa yana mitar Baffah ya jawo masa raini wurin yara.
Cikin sati daya Asum ta canja saboda gyaran da take samu ta ko wani bangare ba ga umma ba baga mommy surukarta ta ba. Kamar kullum suna zaune a falo Hamma Abid, Asum, Hamdah da kuma wata mai kama da Asum ɗin. Naseem ce ta shigo da sallama kafin tace, "Yauwa Adda Yusra gwara da Allah yasa na ganki, ni dan Allah waye ne mijin Asum da ake boyewa mutane har yanzu anki bayyana mana shi, gashi sai shirin tafiya take ta barni". Ta faɗa kamar zatayi kuka. Hamma Abid ne yace, " Zo ki zauna in gaya miki".
Kusa dashi ta ƙarasa ta zauna, yayi ƙasa da murya kafin yace, "Kinsan waye ne?". Girgiza masa kai tayi alamar ah ah. Murmushi yayi yana kallon Asum dake hararar sa. Adda Yusra kuwa cewa tayi, "Allah ya kawo shi, zakaci ubanka ne ba kai marar ji ba dama ai nasan tara ka yake in Kayi wasa kafin ya bar kasar nan sai yasa ka a kwana a asibiti, kai marar lpy ko, whl a tafin hannunsa yake kallonka dan in ka bibiya ma ya samu labarin gudowar da kayi kawai ya zuba ma ido ne. Dan naga alama ka manta da abinda ya faru da Abdulkareem kafin ya tafi Jordan, lokacin da sukaje sukayi car drift har suka samu accident ɗaya daga cikinsu ya rasu, ina cewa yana gadon asibiti ya tuso keyarsa zuwa gida ya dora masa da punishment".
"Ni fa Adda Yusra karki min baki, ai gobe ma zaku nemeni ku rasa dan tunda kikayi maganar nan bansani ba ko yan ameen na kusa, na shiga hannun Ya Nabeel ai na kade, dan bawan ALLAHn bai san tausayi ba ko kaɗan. Ke kinaji". Ya ƙarashe yana juyowa wurin Naseem yace, "Ya Nabeel ne fa mijin Asum". Susa kunnenta tayi da fadin, "Hamma Abid kunne na yaji daidai kuwa".
"Kina mamaki ne?".
"Tho a yaushe akayi auran duk bamu sani ba?".
"Kai an daɗe, tun kuna jss 3 fa, lokacin kuna kwailaye, shi ne Baffah yace sai kun gama secondary za'a ɗaga maganar, mu kan mu ba wani daɗewa mukayi da sani ba". Miqewa tayi jiki na rawa, duk yadda taso riqe hawayen ta kasawa tayi. Hamdah tace, "Ke kuma kukan rabuwar ne tun yanzu". Bata iya bata amsa ba ta wuce ɗaki da gudu tana mai fashewa da kuka me sauti. Tashi Asum tayi tabi bayanta jikinta a sanyaye ita ma.
Hamma abid ya bisu da kallo Kafin yace, "Adda yusra Allah yasa ko bayan ran su baffah zumincin da suka gina familyn ɗin nan akai ya daure".
"Ameen dai Abid, whl nima wani lokacin har mamakin zumunta irin tasu nake, ka duba fa umma da mommy ba uwa ɗaya uba ɗaya suke ba amma saboda su Baffah kai kace ciki ɗaya suka fito".
"Hmmm, to Adda Yusra in ba dan zumincin ba ma ki duba fa yadda Baffah yake riqe dasu Aunty Laila, ga mijinta da ƙarfinsa da komai amma baya aikin fari bana baqi, shi ne duk wasu buqatu nasu kai har ta kai ta kawo an tashe su a gidan haya Baffah ya basu ɓangare ɗaya a estate ɗin nan. Amma ko kunya Uncle Yusuf ɗin nan baya ji haka zakiga yana ta wani burga, shi kuma Baffah dake kinsan baya san show up shiyasa ba wanda yake sanin shi yake taimaka musu, in an faɗa ma karyatawa yake".
Adda Yusra ta karɓe da faɗin, "Ita ma Aunty lailan ai haka take, duk basu da kara daga ita har mijin, Ka duba duk yaran gidan nan wurin mu 18 banda jikoki, kaga Mommy na da ya Nabeel ko tunda shine babban da a gidan nan sai hamma Sameer, Hamma Adel, Adda Sofy, Adda muneera, Awwab, khulud , Hamdah, sannan ga Umma ma Hamma Safwan, Hamma Shafik , Hamma muneeb, ni , sanaya, asmah, Kai, Abdulkareem sannan asum da naseem Banda jikoki, yayan Hamma Sameer da sanaya, Ni da hamma Adel, Adda sofy da hamma safwan, yayan Adda muneera , khulud, asma Ka duba duk yawan wanna family ɗin kuma duk a cikin estate din nan muke, su adda Muneera da khulud, asmah, hamma muneeb sai uban gayyar ne kawai basa cikin estate din nan amma duk da haka baza ka taɓa ganin Aunty Laila taja wani a jikinta ba. Ba ruwanta da kowa daga ita sai mijinta ko zuwa kayi gaishe ta haka zata dinga ma wani gani² ita kadaice ta fita zakkah a cikin su Baffah whl dan bata da hali, kamar ba kanwar su ba".
"To ita ta sani kanta tayi wa, ni yanzu ma muna gama training muka dawo ai tuni zan yiwa Baffah Magana kan Hamdidi". Hamdah da ke kallon wani series a mbc Bollywood ta tashi da gudu ta bar falon Adda Yusra na kiranta amma taqi tsayawa.
Cikin dariya tace, "Kaga ka korata ko".
"Ni me nayi? daga nayi zancen aure?". Ya karashe yana dariya. "Amma fa Abid kayi tunani me kyau, dan nasan su Abbah zasuyi farin ciki sosai, kaga ka yiwa su Awwab wayo, gsky zan basu shawara karsu yadda whl, su ma su motso".
" Ai ni har kinsa na fara tunanin ko ma in samu Ya Nabeel da maganar ne kawai". Dariya tayi kafin tace, "Kanka na rawa Abid, Ina taroka ta nan kana bullo ta can, amma in dai dgsk zakaje ɗin ni zan ma rakiya whl".
"Eh ai dake kinji mugunta ba".
"Ah ah to kai fa kace zakaje kuma sai nace karka je, dadin dadawa tambayar aure zakaje yi kaga kuwa ai wasalan wasalan kawai ni in Ka shirya Ka fadamin".
****************
Tun kafin ta ƙarasa cikin ɗakin take tsinkayo muryar ta, "Noooo, not Asum taya hakan zata kasance? Me sa sai ita? Abbah baku min adalci ba, kun cutar da Zuciyata kun yi min katangar ƙarfe tsakani na da farin ciki na. Meysa zaku nisanta ni da Ya Nabil, meysa zaku katse min buri na. Wayyo ni rayuwata ta ƙare ". Ta karashe tana gunjin kuka kamar ranta zai fita. Ba karamin kiɗima Asum tayi ba da jin waɗannan kalamai na Naseem sai kawai ta shiga tafiya da baya² kafin ta juya ta fice ta nufi kitchen da sauri, tana zuwa ta rungume Umma ta fashewa mata da kuka. Hankali tashe Umma ta juyo tana riqo ta, ta shiga tambayarta abinda ya faru, cikin kukan ta shiga fada mata abinda taji kafin ta rufe da faɗin, "Akwai sauran lokaci Umma, Naseem tana son sa, ni kuma dama bana son sa biyayya ce kawai. Ku raba auran nan ita ku bata shi. Dan Allah Umma kar a karyawa Naseem zuciya".
Daga bayanta taji ance, "Baza a raba auren nan ba Asum.......