005
by @swrites22
_ NI DA YAYA NABEEL _
_YOUNG WRITER✍️
* 005 *
Daga bayanta taji ance, "Baza a raba auren nan ba Asum, kiyi hakuri da abinda kikaji, na kasa ɗaure zuciyata ne, amma whl a yanzu ko Ya nabeel shi kadai ne ya rage namiji a duniyar nan na hakura dashi". Ƙarasawa Asum tayi ta riqo kafaɗunta tana kallon cikin idanun ta tace, "Ko ɗaya Naseem, ni dama kinsan ba wani sonsa nake ba, amma tunda har ke kina son sa, zaki iya zama dashi a hakan to ba wadda tafi cancanta da auran sa bayan ke".
"Dan Allah Asum ki bar maganar nan ta wuce, nayi kuskure dana kasa controlling ɗin kaina har na bari maganar nan ta shiga kunnen ki. Dan Allah Umma kar ku bari su Abbah suji zancen nan, ita kanta Asum kunyarta nake ji whl".
"Ke billahillazi Naseem tunda kika furta kina sansa shi ne farin cikin ki to ki sa a ranki Ya Nabeel naki ne, dan sai nayi duk yadda zanyi wurin ganin kin mallake shi". Tana gama faɗin haka ta fice daga kitchen ɗin. Naseem ta bita da kallo a tsorace dan tasan in har hakan zai yiwu to yana nufin kashe Auran yar uwarta ta ne, wadda bata fata.
A daki Umma da Naseem suka sameta, tana kwance a rigingine, ƙafafunta a ƙasa, tayi matashi da hannuwanta ta tsurawa POP ido Kawai. Rufe ta da faɗa Umma tayi, "Wannan wani irin wasan kwaikwayo ne kukeyi? Wanna ai abun kunya ne ma kuke neman janyo mana, to ba a zurriyata ba, gwara tun wuri ku shiga hankalin ku kafin rai na yayi matuqar baci daku dan naga alama kun maidani kamar wata sa'ar wasan Ku". Tana kaiwa nan ta fice a fusace tare da gabzo musu ƙofar dakin rai a ɓace.
Durkushewa Naseem tayi a wurin tana kuka, "Kaicona², wayyo ni. Gsky na tabbata wawiya". A hasale Asum tace, "Ke ni dallah in baza ki min shuru ba tashi ki fita". Da sauri ta kai hannunta baki dan hana sautin kukanta fita cikin nadamar abinda ta janyo.
***************
Asum bata tare a part ɗin su Nabeel ba dan ƙoƙarin da Abbah ya iya yi Kenan game da maganar da Nabeel ɗin ya fada masa dan Baffah mutum ne mai kafiya da zafin zuciya dan kuwa Abban ma saida ya samu rabon sa saboda yace a tsaya a fuskanci Nabeel da kuma korafin sa. Ai kuwa ya masa tas sannan ya kira Nabil ɗin ma ya masa wankin Babban bargo.
Hakan ya zama ko da suka fara shirye² komawa Russia tare da Asum akeyi, sai ana gobe zasu wuce Nabeel yaje ya dauko Jumayma daga gidansu dan itama tunda abin nan ya faru ta tada borin sai dai ya maidata gida daƙyar ya samu ya lallabata amma yana fita tayi tafiyar ta yanzu ma saida ya sha fama da ita kafin ta yadda ta biyoshi.
Washe gari ko da suka gama shiri a falon Baffah suka haɗu dan ayi sallama, Asum ce kawai bata falon. Sosai Nabil ya gama kuluwa sai kallon agogon hannun sa yake ganin yadda take ƙoƙarin sawa su yi missing flight, ita kanta Jumayma sai cika take tana batsewa. Shigowa sukayi da sallama hannayen su cikin na juna kana kallon Naseem kasan ta sha kuka har lokacin kuma hawaye bai bar sintiri daga Idanun ta ba .
Asum kuwa idanunta sunyi ja amma ko ɗigon hawaye babu a ciki, tana sanye da doguwar riga English wear sky blue & ash tayi rolling da ash veil, haka jaka da takalminta ma duk ash ne, tayi kyau sosai dukda ba makeup akan fuskarta. Ƙarasawa sukayi suka gaishe dasu Baffah. Ita kuwa Jumayma a kiɗime tabi Asum da kallo, dan a kwanakin da tayi bata ganta ba sai taga kamar wadda akayiwa wankin engine, tayi wani masifaffen kyau da cika. Kamar zata haɗiyi zuciya haka ta dinga ji dakyar ta shiga tattaro ragowar yawun da ya rage mata a baki tana haɗiya. Baffah ne ya kamo hannun Nabeel ya haɗa da na Asum kafin yace, "Nabeel ga amanar yata nan na baka, whl daidai da kwarzane Ka bari wani abu ya sameta Ka kuka da kanka dan bazan yafe ma ba. Ke kuma Asum ga Nabeel nan, kibi mijinki sau da ƙafa, ki zauna da abokiyar zamanki lpy, dan zaman lpyrku shine nasa, ki kuma rage wanna zafin ran naki amma in kinga zaki cutu to ki kwaci kanki. Allah ya muku Albarka, Allah ya kaiku lpy".
"Mun gode Baffah, Lokaci na tafiya mu zamu wuce". Ya fada a ƙage saboda hannunsu da har lokacin Baffah bai saki ba.
Abbah ne ya ɗora da faɗin, "To Allah ya tsare, ya Kare mana ku. Allah kuma ya muku albarka, Allah ya faranta muku".
Ita dai Asum tana samu Baffah ya saki hannuwansu ta kwace nata ta karasa gaban Mommy, riqota Mommy tayi ta rungumeta tana shafa kanta tace, " Allah ya miki Albarka ƴata, Allah ya zaunar daku lpy, ya albarkace ku da zurriya ta gari". Bata iya amsawa ba sai daga mata kai da tayi, ta ƙarasa tayi sallama da sauran yan uwan nata kafin su fice itada Hamdah da Naseem dan tuni su Nabil sunyi gaba.
Kafin su ƙarasa wurin motocin Naseem taja ta tsaya tana share hawayenta, dawowa da baya Asum tayi ta rungumeta tana haɗiyar abinda ya tsaya mata a maqoshi ta shiga share mata hawaye. Cikin muryar kuka Naseem ta shiga faɗin, "Dan Allah Asum ki saki wannan maganar, ki rungumi mijin ki ko dan farin cikin su Abbah. Ki ajje wanna alwashin naki, kinga tun shekaran jiya nake roqon ki dan Allah....". Sakinta tayi kawai ta juya ta koma inda Hamdah ke tsaye tana jiranta suka ƙarasa wurin motocin.
Mota daban² suka shiga Nabeel da Jumaymah sai driver, Asum kuma da Hamma Shafik, a hanyar su ta zuwa airport din ma Nasiha sosai Hamma shafik ya dinga yi mata daidai gwargwadon saninsa, har suka ƙarasa.
"Nagode sosai Hamma am, Allah ya bar zuminci, ga dai Umma da Naseem nan dan Allah ka Kula min da su". Murmushi yayi tare da faɗin, "In sha allah Assumin mu, karki damu, in kun ƙarasa zamuyi waya". Jinjina masa kai tayi kafin ta zaro sun glasses ɗin ta a jaka ta maqala, wanda ya kusa cinye rabin fuskarta.
Buɗe ƙofar motar tayi ta fita, tana hango su Jumaymah da har sun shige ciki, bata wani damu ba ta cigaba da tafiyar ta cikin nutsuwa har ta karasa aka mata duk abinda ya dace sannan ta samu wuri ta zauna tana latse latsenta a waya, har zuwa lokacin da aka fara Kiran fasinjoji, tashi su Jumaymah sukayi maqale da juna suka wuce kamar basu gan ta ba dan suna opposite da juna ne.
Tsaki taja kafin ta tashi ta bi bayan su. A cikin jirgin ma VIP section aka kaisu, suka ja suka zauna shi da ita kamar zata shige cikinsa. Itama neman wuri tayi ta zauna ta ɗaura belt ɗin ta tun kafin ma a faɗa. Daƙyar ta iya maintain composure din ta har jirgi ya daidaita a sararin samaniya kafin ta sauke ajiyar zuciya a ɓoye. Sai kuma taja tsaki kasa² tace, "Mutum dai ya cigaba da gwada rashin adalci, Allah yana ganinsa". Batayi zaton zai iya ji ba saida taga ya ɗago slowly sun haɗa Ido, saurin kawar da kanta tayi tana sake haɗe rai.
Har suka isa Russia ba wanda yace da wani ci kanka, tana dai kallonsu suna ƙus ƙus ɗin su shi da matarsa. Wani irin muqu muqun sanyi suka tarar anayi a garin, ai kuwa suna fitowa daga jirgi ta fara rawar ɗari, sojoji ne birjik suka zo taryen su, tsaye tayi tana sake kankame jikinta ta shiga raba ido dan ta rasa ina zata nufa cox tuni su Nabeel sun ɓace mata. Wani Soja ne yazo yayi mata Excuse, ta dan dago tana kallonsa ba tare da tace dashi komai ba, nan ya buqaci tazo su je. Kamar wadda take jira kuwa tun kafin ya rufe bakinsa ta shige gaba kamar tasan inda zasu, wurin wata mota suka ƙarasa ya buɗe mata baya ta shiga sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver yaja suka wuce.
Cikin wani qaton gida mai shegen kyau suka shiga, sojoji ne tako ina a harabar gidan kamar masu shirin yaqi sai muzurai suke. Suna yin parking ta hango su Nabil ɗin na fitowa daga wata mota, da sauri itama ta buɗe ƙofar motar da take ciki ta fito tabi bayansu. Ganin yadda duk inda suka sa kafa suka cire sai Asum tasa yasa Jumaymah juyowa tace, "Ke wai ina zakije ne haba?".
A fusace tace, "Gidan uwarki zani ko ke kika daukoni ne?". A hasale Jumaymah ta yunqura amma sai Nabil ya riqo ya jata suka wuce ciki. Kwafa Asum taja tare da ɗan daga murya tace, "Da ka bari tazo ai na koya wa shegiya hankali". Ai kuwa kafin ta rufe baki ta shiga maido mata da raddi.
Neman wuri tayi ta zauna tana hamma, tunanin wanna sabuwar rayuwar da zata fara kawai ta shiga yi. Wata baturiya ce tazo tace mata ta taso ta nuna mata dakinta. Ba musu ta tashi tana ɗan murmushi ta bita, wani qaton ɗaki ta kaita, yaji kayan alatun more rayuwa, ba abinda babu a ciki na kyale kyale, godia ta yiwa matar kafin ta fice ita kuma ta rufo ƙofar.
Kayan jikinta ta rage ta shige toilet ta haɗa ruwa me zafi kafin tayi wanka ta fito, kaya ta gani ajiye a bakin gadon, ta ƙarasa ta ɗauka tana dubawa wata Long Sleeve Turtleneck Maxi Dress ce milk, sai hular sanyi me irin kunnen magen nan itama milk, sai socks na kafa da hannu, duba ledar data gani a gefe tayi, set na lotion ne me kyau da kuma inner wears. Lotion ɗin ta buɗe ta hau shafawa tana gamawa ta shiga shiryawa, sosai tayi mamaki yadda inners ɗin suka mata daidai, dan ita ko a gida in ba da kanta ba ba wanda yake iya siyo mata inners ɗin da sukeyi mata daidai, ko dai suyi kaɗan ko suyi yawa. Amma wannan sun zauna mata sosai, haka dai ta ture mamakinta gefe ta karasa shiryawa sannan ta haye gadon tayi kwanciyarta, ba jimawa bacci yayi awun gaba da ita.
Ba ita ta tashi ba sai wuraren 8pm ta, kasancewar tana jiran tabbatar da ko period ɗin ta ya gama tafiya, yasa fuskarta kawai ta shiga ta wanko sannan ta fice neman abinda zata sawa cikinta. Kasancewar bata san kan gidan ba yasa ta bata, haka ta dinga lalume harta samo kitchen din, wanna baturiyar ce ta dazu da wasu mutum biyu a ciki suna haɗa abincin dare, tana ganin Asum ta shiga gaisheta haka sauran ma suka bi sahun ta. Amsawa tayi cikin kulawa tana ƙarasawa ta dauki plate ta dibi abinda zata iya ci sannan ta nemi wuri ta zauna a nan kitchen din, tana ci tana kallon yadda suke aike aiken nasu har ta gama sannan ta tambayi sunayen su duk suka gaya Mata cikin harshen nasara. "To yanzu ke Jenny muje ki nunamin kan gidan". Cikin jin dadin yadda ta sake musu Jenny ta bita suka fice a kitchen ɗin tana ta zuba mata zance, dan dukkansu ba ƙaramin farin ciki sukayi ba da ganin yadda Asum ta karbesu dan tsakanin su da Jumayma babu wani dad'i, daga harara sai kwaɓ, komai sukayi basu iya ba.
Haka suka dinga zagaya gidan ita da Jenny, tana sake Introducing kanta wurin ma'aikatan gidan a Matsayin matar me gidan saboda jin yadda Jenny ke koɗa girman Nabil ɗin yasa taji itama zata iya jingina kanta dashi dan ta samu wannan griman. Saida ta gaji dan kanta sannan ta ce su koma ciki.
Tana shigowa ta hangosu a dining, wucewa tayi cikin falon ta zauna tare da kunna tv ta kamo tashar Al hadath tana kallo har suka gama, shigowa cikin falon Jumaymah tayi tana yauqi daga ita sai wasu fitinannun riga da wando ita ko damunta sanyin garin ba yayi ko dan ta saba ne oho. Asum ta kalla a yatsine tace, "Ke tashi kije ki kwashe kwanukan can sannan ki dauko min drink ɗi na, gashi can a dinning na manto shi".