BA NI DA MADOGARA

Chapter 13

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*













*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)




 



   

013
Zaune yake yana wannan tunanin ya ji wayarsa na ringing da sauri ya ɗauki wayar a tunaninsa ko Alhaji Sambo Dala ne ya kira sa don ya shaida masa  ya ganta amma ina sai yaga akasin haka, sunan *MATI* ke yawo a screen ɗin wayarsa nan take jikinsa ya ƙara sanyi hankalinsa ya ƙara tashi, jiki baɓu ƙwari ya ɗauki kiran tare da kara wayar a kunnansa ba tare da ya ce komai ba. A can Murja ta ce

"Assalamualaikum Alhaji Zakari mai Nairori, kasan hausawa sun ce rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, to yau ce ranar, Ina jiranka a inda muka saba haɗuwa" 

Ƙit! Ta katse kiran, shiru ya yi ba tare da ya cire wayan daga kunnansa ba, a ransa yana faɗin 'O ni Zakari naga ta kaina, gaba kura baya damisa ban san ina zan saka raina na ji daɗi ba, wacca take saka ni farin ciki yanzu ta canja gaba baki ɗaya, ni yanzuuu ya zan yi da Alhaji Sambo Dala da ya bijiromin da wani sabon tashin hankalin da ban san hawa ba balle sauka, to niii me zan ce ma Murja idan na je wurinta, Mts! Kawai dai don babu yadda zan yi ne zan auri ƙanwarta amma idan da ba haka ba wallahi bazan ƙara wani auran ba, don a gaskiya ban san me zan ce ma Hannatu ba wannan cin amanar da zan yi mata, wayyo ni! haka ya ci gaba da zancen zucinsa daga bisani ya miƙe ya zira mukullin mashin ɗinsa ya nufa kwarin ɗan dodo.

Cikin rabin awa ya isa Kwarin ɗan dodo inda ya samu Murja a daidai inda suke haɗuwa, kamar kodayaushe tana sanye cikin dogon hijab da niƙab tana kalle-kalle. Faka mashin ɗinsa ya yi sannan ya nufa inda take, Murja tunda ta ga ya faka mashin ɗinsa take sakin murmushi a cikin niƙaf ɗinta a ranta tana cewa 'Ka gama kumbura-kumburanka za ka dawo kan hanya ne, da Murja ka ke zancan'  Har inda take ya tako ya tsaya ba tare da ya ce komai ba. Wani ƙasaitaccan murmushi mai sauti ta saki sannan ta ce

"Kai tsaye ba tare da wani ɓata lokaci ba ka sanar min da abin da ka shawarta, shin ka amince za ka auri Zaliha ko kuwa baka amince ba" 

Shiru bai tanka mata ba yana tsaye yana kallonta, ya harɗe hannunsa yana taɓa ƙasumbarsa. Kamar ba zai ce komai ba sai can ya fara magana cike da ɓacin rai 

"Murja zan amince da auran nan ba don ina so ba, sai don kar ki tona min asiri ne, amma ki sani ina da nawa sharaɗin" 

Gyara tsayuwa Murja ta yi sannan ta dubesa ta ce

"Sharaɗi! Sharaɗi kuma? To ina sauraronka " 

"Sharaɗin ba komai bane illa idan na auri Zaliha za ki goge waɗannan bideos da yake wurinki, idan baki yarda da wannan Sharaɗin ba to a gaskiya ba zan iya auran ƙanwarki ba" 

Ɗan shiru Murja ta yi tana tunani, tasan da biyu ya yi maganar don kawai ta aminta ta goge, tana gogewa ya saki Zaliha shikenan ta tashi babu komai, dubara ce kawai yake so ya yi mata, can ta ce

"Zan aminta da sharaɗin sai dai kasani ba wai na goge bideos ɗin a wayana ka yi tunani za ka saki Zaliha ka ci riba ba, wallahi idan na goge bideos ɗin daga baya ka ci zarafin Zaliha ko kuma ka saketa to ka tabbata abin da zan yi maka yafi na bideos ɗin don ita karuwar taka zan saka da kaina ta tona maka asiri a bainar jama'a,kar ka manta wannan Murja ba abar wasa ba ce ko a yi mata dubara a cuceta, kar-to-kar nake kallonka idan kasan abin da zuciyarka take riya maka kenan to tun wurin ka yi mata faɗa don karan batta dani babu daɗi"

Ƙarasa zancen ta yi tana cilla masa harara. Kamar ta karanci abin da ke a ransa, daman dubarar da ya so yi ke nan to amma shegiyar matar nan ta ɗagosa, Mts! Tsaki  ya yi sannan ya dubi Murja ya ce

"To shikenan na aminta amma ki goge sannan ba zan saketa ba ko na ci zarafinta " 

"Da kyau angon Zaliha, yanzu zuwa wani lokaci za a yi auran,don bana so a ɗau lokaci, in so samu ne zuwa nan da kwana biyar haka sannan bana so ka sanar ma matarka auran sai baya an ɗaura,ƙarin daɗi ina so Zaliha ta zauna a cikin gidanmu" 

"Wai ke Murja wace iriyar ibilishiyar mata ce mai son haddasa rigima a doran ƙasa ne, a kullum burinki bai wuce ki hana zaman lafiya , yanzu inba kina son rashin zaman lafiya mene ne na cewa Zaliha a gidanmu za ta zauna bayan kinsan Hannatu ba son kishiya take ba, kuma kin san da haka tun ba yau ba,wallahi ban taɓa ganin mace wacca bata san ciwon ƴar uwar ta mace ba sai ke, yanzu idan kika ga misali zan ƙara mata abokiyar zama ta sai inda ƙarfin ya ƙare ba, amma ke ba haka yake a cikin ranki ba, son kai ne kawai kika saka a gaba, Haba don Allah "

Wata bazawarar dariya Murja ta yi, sosai take dariya shi kuma Alhaji Zakari yana bin ta da muguwar harara. Sai da ta yi dariya son ranta sannan ta ce

" Son kai hhhhhh, baka ji ana cewa ba *So so ne amma son kai yafi* to haka abun yake a wurina, don ni ba tausayin matarka nake ba tun fil-azal kawai abin hannunta nake kwaɗayi, tun da bazan samu ba kaga ai na yi wa kaina hanya, bari ka ji Zakari ina so Hannatu za ji baƙin cikin auran sosai shi yasa na ce a gidanmu za ta zauna, kuma dole hakan za a bi idan kana son zaman lafiya mai ɗorewa da ni"

Wani hanki ɗinsa ya ɗauko ya share zufar da take a saman goshinsa sannan ya ce

"Shikenan ni dai yanzu zan tafi, kamar yadda kika ce zuwa nan da kwana biyar za a yi auran hakan zan yi, ba don ina jin tsoranki ba sai sai don a zauna lafiya, Sannan maganar zaman Zaliha a gidanmu zan duba na gani, don a yanzu haka bana cikin yanayi mai kyau, abubuwan sun sha min kai, zan turo mai unguwa da abokina zuwa gobe, a yi komai sannan a gama komai a goban, ni kinga tafiya"

Bai jira mai za ta ce ba ya juya zuwa inda mashin ɗinsa yaje, ya hau ya tada sannan ya ƙara gaba. Wani munafikin murmushi Murja ta saki sannan ta juya ta shiga gidan.

Tana shiga cikin gidan ta samu Innarta da Zaliha suna hira kwanon gyaɗa a gabansu suna cin , wuri ta samu ta zauna fuskarta shimfiɗe da murmushi. Suna ganin ta shigo da murmushi, Zaliha cike murna da ɗauki ta ce

"Innar Balki Hala ya yarda zai aureni?" 

Ɗiban gyaɗar ta yi ta ɓare ta zuba a baki tana tunawa sannan ta ce

"To Zaliha ni ta wasa ce" 

Wani irin farin ciki ne ya ɗarsu a cikin zuciyar Zaliha wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskarta, cike da nishaɗi jin ta kusa zama matar Alhaji ta ce

"Kai amma na ji daɗin wannan zance, Innar Balki ina godiya sosai da taimakona" 

"Haba Zaliha mene ne na godiya bayan ke ƴar uwata ce, ai zan iya komai don farin cikinki ni dai kawai kamar yadda na faɗa miki a baya kar ki saɓa alƙawari, Ina so idan kin shigo sai mu mallakeshi ya zamana kuɗi ta hannunki yake zuwa ba hannun Hannatu ba, Kin ga shikenan mun samu na wandaƙa a gari, wa ya sani wata shekara ya kai ki Hajji"

Wata guɗa Zaliha ta rangaɗa, tana murna mahaifiyarta ma murnar take tana shi ma Murja albarka,da yaba makircinta har ta yi nasarar tirsasa Alhaji Zakari auran ƴarta. 

"Zaliha wani ƙarin albishir cikin kwana biyar za a yi komai don haka kafin kwana biyar ta yi zamu je dake ƙauyan Ciri-tawa don na ga aikinsa yana yi sosai, don idan da ban lalata aikin da Hannatu ta yi wa Salim ba, to da yanzu yana nan yana sata" 

"To ai shikenan tunda aikinsa yana yi, amma mai yasa kika lalata aikin da Hannatu ta yi ma Salim, da kin bari asirin ya ci yaron, mu da muke neman hanyar da za mu ruguza alhalin Uwale amma shi ne kika lalata aikin" cewar mahaifiyar Zaliha tana ɓata fuska. Dariya Murja ta yi sannan ta ce

"Haba Inna ai ba ƙyale Zaytuna na yi da yaranta ba, sai dai na yi amfani da Hannatu a wurare mabambanta wurin cutar da Zaytuna, dalilin da yasa na lalata aikin da ta yi ma Salim sai don na buɗe nawa kafar da zan ci gaba da cutar da Zaytuna da ahalinta, karki manta a shekarun baya, na illata Zaytuna illa mai muni sai dai na nunama Innar Harira ne hanyar da ita ma za ta ci gaba da cutar da ita, sannan yanzu haka na gama da Innar Harira domin babu abin da ban sani ba a game da ita, duk sirrikanta na sansu, har da na mijinta, Kin ga kuwa ai na gama da ita, har da malaman duk na sansu"

Ta ƙarashe maganar da murmushi a fuskarta, lokaci guda suka kece da dariya har da Inna, kamar wasu taɓabɓau, suna cikin dariyar Inna ta ce

"Aikinki na kyau Murja kin ga Zaliha na shiga sai ta tayaki aikin, ku ci gaba da tozartasu" 

"Baki da damuwa Inna ai yanzu haka akwai wata kitumurmurar da nake shirin ƙullama Salim ɗin wanda zai kasance Innar Harira za ta yi aikin, ni dai ne zan umurceta don har yanzu bata gano halina ba, tana min kallon masoyiyarta wacca ta yarda da ita ɗari bisa ɗari"

"Yawwa Murja ki ci gaba da aikin ki, Karki nuna mata bakya ƙaunarta" 

Ci gaba da hirarsu su ka yi wanda duk yawancin zancen nasu akan Hannatu da Zaytuna ne, musamman ma Zaytuna da mahaifiyarta Uwale. (Oh ni Narrnarhh Bukar wani abu haka su Zaytuna su ka yi ma ahalin Murja da suka cancanci cutarwa a garesu,Allah ka tsare mana imaninmu🤔🤔🤔)

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎 

A ɓangaren Hannatu kuwa tun lokacin da ta je neman yafiya wurinsu su Mammin Hujayrah da Fatsima ta koma shiru-shiru,Alhaji Zakari ma ya yi tambayar duniya akan ko bata da lafiya ne amma amsar ɗaya ce, ita lafiyarta ƙalau, bata da wani damuwa a ranta hasalima yanzu tasan take rayuwa ba kamar a baya ba.Bayan kwana biyu da dawowan Hannatu daga Giwa ƙaninta ya kirata akan an yi nasarar cire aljanun da aka turo ma Jamilu yanzu haka an bashi magunguna da turaruka don ya kare kansa daga shafarsu. Sannan ya bata shawara akan kar ta yi wasa da addu'a saboda kar wata rana su ce za su dawo tunda ba ta daɗi suka bar jikin Jamilun ba. Sosai ta shiga yi masa godiya har da hawayen farin ciki ta zubar a zuciyarta tana ƙara jin tsoran Allah da neman yafiyarsa akan laifukan da ta aikata a baya. 

Duk waɗannan abubuwan da suka faru da Hannatu ba ta taɓa sanar wa Murja ba don ta ƙudiri aniyar ɓoye sirrinta da duk abin da ya shafi rayuwarta. Sannan bata canja ma Murja fuska ba sai dai ta-ciki-na-ciki. Tana zaune lafiya da su mammin Hujayrah da Fatsima suna mutunci don wani lokacin idan ta je kasuwa takan yi cefane da su mammin Hujayrah. Sosai suka saki jikinsu da Hannatu tunda tun farko gabar ba daga su  Hannatun ne. Murja bata san Hannatu ta shirya da su mammin Hujayrah domin hankalin Murja yanzu ba a kansu yake ba. Hankalinta kacokar ya koma kan auran da take so Alhaji Zakari ya yi da ƴar uwarta Zaliha kusan kullum bata gida tana hanyar Ƙwarin ɗan dodo wurin ƙanwar mahaifiyarta suna ƙulle-ƙullansu...✍️

         🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Dajin ƙare kukanka*

Bayan Sheikh Munnir ya murza zobensa ya ɓace bai tashi bayyana ba sai a wani katafaran gida wanda yake a cikin ƙasurmugin daji,gidan na da matuƙar girma da faɗi. Katangar da take zagaye da gidan doguwa ce sosai ta ji rodi da dakin. Akwai bishiyu da flawowi a gidan sosai. A daidai tsakiyar gidan Sheikh Munnir ya bayyana kamar walƙiya, sai ka ce jira ake ya bayyana sai wasu tiƙa-tiƙa mutane har shida suka fito daga cikin gidan. Sanye suke da baƙaƙyen suit kowanne da tabarau baƙi a idonsa. Suna zuwa wurin suka raƙwafar da kansu alamun gaisuwa, gyaɗa musu kai sheikh Munnir ya yi sannan ya ce

"Ina gang ɗin Linkaku(Wato yaran Alhaji Sambo Dala) " 

Wani a cikin su ya ce

"Suna kan hanya mai girma Demon King, gab suke da ƙarasowa" cike da girmamawa ya yi maganar. 

"Fine sauran yaran fa" 

"Ba a daɗe da kawo su ba sannan sun ci abincin da ka umurcemu mu basu yanzu haka sun yi likimo" cewar wani a cikinsu. 

Sheikh Munnir na shirin cewa wani abu sai suka ji horn, da sauri mai gadi gidan ya buɗe tafatsetsan gate ɗin, manyan motoci ne har biyu suka shigo cikin gidan, a tsakiyar gidan kusa da inda su Sheikh Munnir suke tsaye a nan suka tsayar da motocinsu. Manya ne motocin irin waɗanda ake zuba kayan lambu ko kayan miya idan za a kai wuri mai nisa. Motocin ƙofofi biyu suke da shi, daga na driver sai na mai zaman banza. Buɗe ƙofar kowanne a cikinsu ya yi sannan suka fito, biyu daga cikinsu suka ƙaraso in da su Sheikh Munnir suke. Drivers kuma suka nufi bayan motar tare da buɗe ƙofofin. A nan gaba ya yi mugun faɗuwa ganin yara ƙananu waɗanda basu gaza shekaru sha biyu a duniya an ɗaure musu hannu da ƙafa kamar wasu akuyoyi, sannan idanuwansu da bakunansu na a rufe suke. A cikin kowani booth akwai mutum ɗaya wanda nake kyautata zaton member ne na Black Scorpion Squad waɗanda suke ma Alhaji Sambo Dala aiki. Ɗaya bayan ɗaya suka shiga ɗaukar yaran zuwa cikin gidan, yarana ne da yawa wanda adadinsu zai kai kimanin ashirin ko sama da haka domin motar shaƙe take da yaran har babu masaka tsinke. Ƙattinan da suka zo wurin Sheikh Munnir raƙwafar da kansu suka yi alamun gaisuwa sannan ɗaya daga cikinsu ya ce

"Mai girma Demon King ga yaran da muka samo daga Calaba, zuwa gobe za mu ɗauko na Kaduna" 

Jinjina kansa Sheikh Munnir ya yi sannan ya ce

"Excellent! Yara nawa kuka samo a can Calabar?" 

"Yallaɓai yara kusan ashirin da biyar" 

"OK da kyau, ammm Bado!" 

Wanda ya yi ma Sheikh Munnir bayani da farko ya amsa da cewa

"Na'am shugaba Demon King" 

Gyara tsayawa Sheikh Munnir ya yi sannan ya ce

"Da zarar sun kammala kai yaran ciki, ku basu abincinsu domin zuwa 9:00pm dot zan wuce da su main ƙunciya" 

Cike da girmamawa Bado ya ce

"An gama Demon King" 

Juyawa suka yi zuwa cikin gidan tare da sauran Black Scorpion Squad Shi kuma Sheikh Munnir ya nufa wani ɓangare na gidan. Suna shiga cikin gidan direct wani part suka nufa in da aka kai yaran lokacin har an kwance ɗaurin hannayansu da na ƙafa sannan selotape ɗin da aka rufe musu baki tare da ƙyallan da aka rufe musu ido duk an kwance. Yaran sai zare idanu suke suna kallon juna wasunsu ma kuka suke suna kiran sunan iyayansu cikin harshensu na can jahar sosai za su ba ka tausayi idan ka gansu domin kowannansu ya fita hayyacinsa saboda yunwa da ƙishin ruwa. Lokacin da su Bado suka kawo musu abinci haka su kai ta cin abincin hannu-baka hannu-ƙwarya, har da ruwa aka basu wanda su na gama cin abincin tare da shan ruwa suka ɓingire da bacci. Babu wanda a cikinsu bai yi bacci ba, sai a sannan ne su Bado suka bar ɗakin zuwa wani ɗaki in da nan ma yara ne kamar na ɗayan ɗakin suna sharar bacci. Ɗaya bayan ɗaya suka fara ɗaukan yaran zuwa ɗayan ɗakin da suka ba yaran abinci, sun daɗe suna ɗaukan yaran daga bisani suka kammala sannan suka fito daga part ɗin. Bado ne ya nufa in da Sheikh Munnir yake ya sanar masa da sun kammala komai. Gyaɗa mishi kai  ya yi sannan sai Bado ya fito daga wurin. Bayan Bado ya fito da kusan mintuna goma shi ma ya fita zuwa cikin gidan zuwa part ɗin da yaran suke. Bayin Allah sai bacci suke basu san mai ake yi ba,a tsakiyar ɗakin Sheikh Munnir ya tsaya sannan ya yi wasu surkulansa irin na riƙakƙu kuma hatsabiban matsafa, nan take ya rikiɗe ya koma ainihin Demon King mai mummunar suffa, ga tsawo wanda yafi na asalinsa sannan ga ƙiba wannan radameman tumbin nasa yana gaba sai ƙyalli yake. Miƙar da hannayansa ya yi sannan ya yi wasu sirkullan wanda lokaci guda suka ɓace da shi da yaran gabaɗaya. 

Sheikh Munnir bai bayyana a ko'ina ba sai a cikin gidan ƙungiyarsu wanda yake a cikin tsakiyar ruwa. Kamar diran mikiya haka  ya bayyana da yaran a cikin wani tamfatsetsan ɗaki. Yana bayyana kamar walƙiya sai ga waɗannan mutanan masu tufafi mabambanta sun fito daga ƙofofi mabambanta. Cikin wani yare ya yi musu magana sai masu tufafi kalar ja suka matso wanda lokaci guda suka ɓace da yaran baki ɗaya, basu bayyana a ko'ina ba sai a wani babban ɗaki mai shegen haske, a tsakiyar ɗakin wani teburi ne babba, teburin na da huji a tsakiya mai faɗi sannan a ƙasan hujin wata ƙatuwar ƙwarya ce ɓakar mai faɗi cikinta ma ɓaƙi ne. Ɗaya bayan ɗaya suƙe ɗaukar yaran yayin da akwai wani basamuden mutum wanda yafi su girma amma shigarsa kalar tasu ce hannunsa riƙe da  sharɓebiyar wuƙar sai sheƙi take. Yaron farko da aka kawo saman teburin miƙar da shi mutumin ya yi sannan ya saita kan yaron daidai hujin da wannan ɓakar ƙwaryar take. Saka wuyar ya yi a maƙogaron yaron sai ya ja wuƙar wanda lokaci guɗa ta luma ciki kasancewar wuƙar mai kaifi ce,nan take jini ya fara zuba cikin ɓakar ƙwaryar, sai a sannan ne yaron ya fara shuri-shure yana kakarin mutuwa wanda baifi minti uku ba jikin yaron ya saki, haka suka ci gaba ya yanka yaran jinin na zuba cikin baƙar ƙwaryar wanda sun daɗe suna yanka yaran. Kusan rabin yaran suka yanka sai sauran yaran suka shigar dasu wani ɗaki. Kamar walƙiya mutanan nan masu ɓaƙaƙyen kaya suka bayyana cikin ɗakin tare da kwashe gawan yaran suka ɓace. A wani ɗaƙi suka bayyana wanda a can suka fara fiɗar yaran kamar sun samu dabbobi sannan duk wannan aikin da suke fuskokinsu rufe yake har suka gama aikin tare da yin pepper soup ɗinu wanɗa ƴan ƙungiyar cikin sali-salin dare za su bayyana su yi shagali dasu. A ɓangaren Demon king yana gama basu umarni ya ɓace wanda bai bayyana ko'ina a sai a cikin ɗakinsa wanda yake a cikin estate cikin suffarsa ta asali lokacin kusan 9:45pm na dare ne. Yana bayyana ya fito daga ɗakin suna kasa inda ya samu matarsa da ƴan biyunsa masu ƙusumbi suna falo basu yi bacci ba, a nan ya shantake da yaran suna hira har kusan 10:30pm sannan suka wuce ɗakinsu daman ba tare da matarsa yake kwana ba sai idan yana da buƙatuwa da ita ne yake zuwa ɗakinta. A ƙa'idarsa bayan kowa ya kwanta can cikin dare zai ta shi ya murza zobensa wanda nan take yake ɓacewa, sai ya bayyana a ƙungiya lokacin kowa ya bayyana sannan dodonsu shi ma a tare suke bayyana. Bayan sun tattaunawa batuttuwan da ya shafi ƙungiyarsu sai daga baya waɗannan mutane masu tufafi mabambanta za su kawo musu jini da pepper soup ɗin yaran, su ci su sha sannan kowa ya ɓace ya koma gidansa sai gidan ya nutse cikin ruwa. Wannan ke nan.

            🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Legacy Housing Estate, Bulunkutu, Maiduguri, Borno State. Nijeriya*

A can gidan Sheikh Munnir tun bayan da Halima ta yi waya da yayanta wanda ya kasance ɗa ga yayar mahaifiyarta hankalinta ya ɗan kwanta domin tasan ba zai bari Papy ya aura mata wanda bata so ba sannan idan Ya Abdul ya yi bincike akan saurayinta Mahmoud yasan bai da wata illa to zai yi ƙoƙari ya ga ta auresa. Bayan kwana biyu da tattaunawansu lokacin tana ɗakinta tana chatting da Mahmoud sai ta ga sunan Ya Abdul yana yawo a screen ɗin wayarta, Tsamm! Ta miƙe zuwa toilet don a toilet take iya ɗaukar kira indai na sirri ne saboda akwai CCTV camera a kowace kusurwa ta ɗakin sai dai banda bayi. Tana shiga ta ɗauki kira muryarta a can ƙasa ta ce

"Ina wuni Ya Abdul" 

A can ya ce

"Ya kike Halima, Hope you are fine baki da wata matsala" 

Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce

"Eh Ya Abdul I'm fine" 

A can ya ce

"Yawwa na yi bincike sosai akan ɗan majalisar da papynki yake son aura miki sannan shi ma saurayin naki na yi bincike akansa.What i have here is; shi yaron ɗan majalisar a gaskiya ba za mu goya bayan ki auresa ba domin na bincika ance min bayan mugun hali har da shaye-shaye yake, bansan mai yasa Papynki yake son aura miki shi ba amma koma mene ne zuwa next week zamu zo Maidugurin. Sannan shi saurayin naki mai suna Mahmoud mazaunin Bauchi state ne ko? "

Fuskarta ɗauke da murmushi ta ce

" Eh Ya Abdul "

A can ya ci gaba da cewa

" Shima na yi bincike akanshi sosai kuma na yaba da hankalinsa. Ashe jami'in sirri ne mai babban matsayi sannan koda yake course mate ɗinki ba yana nufin bai da karatu  sai dai akwai wata manufa a ci gaba da karatunsa kisan aikinsu ya gaji haka" 

"Ya Abdul wa ya maka bincike har haka" 

A can ya yi dariya sannan ya ce

"To ni da nake da mutane da yawa by the way Mas'ud na tambaya yaron Uncle Abdulrahman waɗanda suke zaune a Bauchi State ai kinsan shi, so he told me  friend ɗinsa ne Mahmoud sannan wurin aikinsu ɗaya. An tura shi wani babban aiki ne a Dubai wanda zai ɗau shekaru da yawa shi yasa ya ci gaba da karatunsa a can. Sannan ya ce min yaron bai da matsala don abokinsa ne sosai shi da Arqam so dalilin haka yasa na aminta da shi sannan idan mun zo next week in shaa Allah za mu yi magana akan Mahmoud mu ji ko Papynki zai amince ki aure shi "

Wani farin ciki ne ya cika zuciyar Halima har ta kasa ɓoyewa, cike da murna ta ce

" Ya Abdul ban san da wasu kalamai zan yi amfani dasu wurin gode maka ba, Thank you so much Ya Abdul I'm so lucky to have you in my life, Allah ya ƙara maka buɗi da wadata, yasa Aunty Hassana ta haihu lafiya" 

A can fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce

"Ameen my dear, ki kula da kanki kin ji" 

"In shaa Allah bye bye" 

Katse kiran ta yi sannan ta fito daga bayin fuskarta ɗauke da murmushi tana farin ciki...✍️

      🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gida Dubu, Gubi Housing Estate,Bauchi state.Nijeriya*

Hajiya Ramla ta barin part ɗin Hajiya momma da kusan mintuna goma sai Hujayrah da Razina suka shigo cikin ɗakin, Razina ce a gaba Hujayrah na bayanta suna dariya,Razina na ɗan ɗingisa ƙafa ta ƙaraso cikin falon. Hujayrah na haɗa ido da Hajiya momma ta tsaya ba tare da ta ƙaraso ciki ba, har Razina ta zauna a saman kujera Hujayrah na tsaye ta kafe Hajiya momma da ido. Hajiya momma bata san ma Hujayrah ta kallonta ba, ganin Hujayrah taƙi ƙarasowa ciki sai Razina ta ce

"Hujayrah ba za ki ƙaraso ciki ba ne kin tsaya wuri ɗaya" 

Firgigit kamar wacca aka tsikara ta dawo cikin hayyacinta sai ta ƙaraso cikin falo direct in da Hajiya momma take a zaune Hujayrah ta je wurin ta zauna a ƙasa Still tana kallonta,babu abin da idanun Hujayrah suke kallo a jikin Hajiya momma illa zallar sirihi mai ƙarfi wanda yake ɗawainiya da ruhinta, sosai ƙirjin Hujayrah yake bugawa wanda ta kasa haƙuri ta ce 

"Mammi baki da lafiya ne" 

Bambara-ƙwai Hajiya momma ta ji tambayar Hujayrah lokaci guda ta ɗago idanunta tare da zubesu akan Hujayrah, ɗan murmushi ta yi sannan ta ce

"Lafiya lau nake Hujayrah banda matsalar komai" 

Kafin Hujayrah  ta ce wani abu sai suka ji sallamar Alhaji, juyawa dukkaninsu suka yi tare da amsa masa sallama, kujera ya samu kusa da Razina ya zauna fuskarsa ɗauke da murmushi yana duban Hujayrah ya ce 

"A'ahh su Hujayrah yau sangarta ake ji da aka saka Ammie gaba, ko Razina tabar miki autancin ne" 

Zolayarta yake ita kuma sai rufe fuska take tana murmushi, Hajiya momma da Razina sai dariya suke mata. Sallama suka ji wanda ya katse musu nishaɗin da suke ciki. Salame ce ta shigo ɗakin da wasu kaya a hannunta, cike da girmamawa ta gaida Alhaji da Hajiya momma za ta shiga bedroom ɗin Hajiya momma sai Hujayrah ta daka mata wata uwar tsawa tana faɗin

"Me za ka yi mata a uwar ɗaka kin wani saka kanki ciki kamar mai ɗakin!" 

Ba Alhaji ba, Razina da Hajiya momma ba har da uwar gayya Salame idanu suj waro waje suna kallon Hujayrah, ita kuwa gogar taku ko a jikinta hasalima kafe Salame ta yi da mayatattun idanunta tana mata wani irin kallo na ƙiyayya, ga zuciyarta na buga mata da mugun ƙarfi wanda ya wuce ƙa'ida. Daman tun sallamar Salame cikin ɗakin gaban Hujayrah ya fara bugu, da suka haɗa ido da ita sai zuciyarta ta buga da matuƙar ƙarfi hakan yasa ta yi sauri dakatar da Salame shiga cikin bedroom ɗin saboda zuciyarta ta yi amanna da Salame muguwa ce. Alhaji bayan ya gama karance yanayin Hujayrah tsaf! Ya ce

"Salame" 

Cike da girmamawa Salame ta ce

"Na'am Alhaji" 

"Ajiye kayan ki wuce abinki" 

Babu musu ta ajiye kayan ta ɗau hanyar fita daga ɗakin, za ta fita ta juyo ta kalli Hujayrah ai babu shiri ta juya wanda har ta kusa bigewa da bango tsabar firgici. Hujayrah still bata bar kallonta ba har tabar ɗakin, sai da tabar ɗakin ne Hujayrah ta sauke ajiyar zuciya tare da juyowa caraf suka haɗa ido da Alhaji. Murmushi ya yi sannan ya ce

"Hujayrah miye dalilinki na cewa Salame me za ta ma Mubina a ɗaki" a sanyaye ya yi maganar

Ɗan duƙar da kanta ta yi sannan ta ce

"Abbu matar ne bata min ba" 

Murmushi ya sake saki sannan ya dubi Hajiya momma wacca ta zuba ma Hujayrah ido ya ce

"Mubina kin ji dai ƴar ki ta ce Salame ba ta yi mata ba" 

Ɗan murmushi Hajiya momma ta yi sannan ta ce

"Hujayrah ke nan Salame bata da matsala wallahi duk a cikin masu yi min aiki ban taɓa samun wacca tasan kanta kamar Salame ba, bari ki ji Salame ta kusan shekara goma sha ɗaya tana aiki a gidan nan, tun Razina na ƴar shekara huɗu ta fara aiki a gidan nan sannan duk tsawan shekarun nan da ta yi a gidan nan bamu taɓa samunta da mugun hali  ko kuma cin amana ba. Na yarda da ita sosai yasa take min aiki a part ɗina, za ta iya shiga ko'ina a part ɗina ta gyara tsaf! ba kamar sauran masu aikin ba, har  da abinci idan ban jin yin girki ita nake sakawa ta yi"

Sosai Hujayrah ta waro manya-manyan idanunta waje tana kallo Hajiya momma, cike da mamaki Hujayrah ta ce 

    "Mammi! Shekaranta goma sha ɗaya a gidan nan tana muku aiki? Ya Ar-rahmanu Azza-wa-Jalla! Hmmmm Tab!  shi kenan Mammi amma ta rage shiga miki ɗakuna tana kalle miki sirrin ɗaki, domin shi ɗan Adam da kike gani kamar hawainiya yake, yakan rikiɗa daga ainihin da kika sansa ya koma wani kalan na daban, mutane ba abun yarda ba ne a wannan zamani, Mammi kin ga koda muke a ƙauye bama yarda da mutane balle nan birni, wanda ka zo na zo ne, ba ka san asalin mutum ko kuma halayansa ba"

Shiru ɗakin ya yi sosai Hajiya momma ta natsu tana sauraron Hujayrah, Alhaji ma itan yake sauraro wasu abubuwa na kai-kawo a cikin zuciyarsa a game da Hujayrah. Bayan ta gama maganar Hajiya momma ta ce 

"Kina da gaskiya a nan Hujayrah, don duk shekarun da ka yi da mutum zai iya sauya halinsa, Allah ya tsaremu daga sharrin masu sharri" 

Ameen suka amsa, a ran Hujayrah ta ƙudiri aniyar bibiyar Salame don ita bata yarda da ita ba sannan idanuwanta suna kallon yadda sihiri ke yawo a jikin Hajiya momma dole ta zuba ido don taga alama gidan akwai matsaloli da yawa, sannan sai ta gano inda aka binne sirihin indai a gidan ne da yardar Allah . Kamar yadda suka taimaki rayuwarta haka ita ma za ta taimakesu da iya ƙarfinta.Haka suka ci gaba da hirarsu wanda kusan akan dawowan Arqam ne daga Germany sai daga bisani Alhaji ya fita su kuma suka koma ɗakinsu.

Bayan Salame ta koma sashensu sai ta samu Talatu na zaune a wajan ɗakinsu tana hutawa. Kai tsaye ya nufi in da Talatu take ta zauna. Fuskarta a ɗaure ta dubi Talatu ta ce

"Talatu ni wannan shegiyar yarinya mai kama da aljanu za ta dakamin tsawa a part ɗin Hajiya momma" 

Talatu da ke kishingiɗe ta yi saurin zaunawa tana faɗin

"Mai goreng idanu kike nufi?" 

"Eh mana wai mai zan yi a uwar ɗakan Hajiya momma" cewar Salame tana taɓe baki

Wata uwar ashar ta faɗin

"Kutumar dumadu!!! Lallai yarinyar nan ƴar rainin wayo ce, daga zuwa gida ko sati ba ta yi ba za ta fara kafa nata iko da mallaka kamar gidan ubanta Cab! To ke me kika ce mata" 

Taɓe baki ta yi sannan ta ce

"Yooo me zance mata bayan a gaban su Alhaji da Hajiya ta yi magana, kawai dai Alhaji ya ce na ajiye kayan na fita" 

Ciza yatsa Talatu ta yi sannan ta ce

"Kinsan Allah Salame dole sai mun koya mata hankali a gidan nan, sai ta gane shayi ruwa ne wallahi" 

"Ai haka za a yi kuwa nan gaba idan ta ganmu durƙusawa za ta yi ta gaishemu" 

Haka suka ci gaba da hirar yadda za su yi maganin Hujayrah cikin ruwan sanyi daga bisani suka shiga ɗaki. 

*Ƙarfe 5:23pm na yamma*

A daidai wannan lokacin wasu rantsattsun motoci har uku suka shigo gidan, kai tsaye suka nufi parking load, da sauri wani bodyguard ya buɗema Tahseen murfin mota, sai da ta kusan minti biyu a cikin motar bodyguard ɗin na tsaye, daga bisani a hankali ta sako ƙafafunta waje nan ma ta ɗau kusan second talatin sannan  ta fito complete daga motar. Sanye take da doguwar riga fitted gown na atamfa ɗinkin ya matseta sosai,ta sha baƙin glass wanda ya rufe kusan idanunta complete, hannunta riƙe da hand bag. Bayan ta fito daga motar sai ta nufi cikin gidan, bodyguard biyu na biye da ita har zuwa main falo sannan suka juya bayan ta amsa wata ƴar babbar jaka a hannun bodyguard wanda nake kyautata zaton kayanta ne ciki. Part ɗin Hajiya momma ta nufa wanda ta kusa shiga sai ta ci karo da su Razina da Hujayrah za su je garden shaƙatawa. Razina ce ta gaida Tahseen tana faɗin

"Good evening Aunty Tahseen" 

Fuskar Tahseen babu yabo babu fallasa ta ce

"How you doing dear" 

"I'm fine" 

Idanun Tahseen na kan Hujayrah wacca ita ma kallonta taje. Ganin Hujayrah bata gaishe da ita ba yasa ta kalle Razina ta ce

"Who is she?" 

Fuskar Razina ɗauke da murmushi ta ce

"Aunt ai na samu sister ne, she is nice and kind wallahi" 

Taɓa baki Tahseen ta yi don haka nan ta ji Hujayrah bata kwanta mata a rai ba don ta tsani disrespect a rayuwarta. Can ta ce 

"But yarinyar bata da kunya, she can't even greet me" 

"Aunt ai tana ciwon magana ne yau" ta faɗi hakan ne don ta kare Hujayrah 

 Bata sake ce musu komai ba ta wuce  cikin falon Hajiya momma. Su kuma suka fito wajen gidan. Bayan sun zauna a kujerar garden ɗin sai Hujayrah ta dubi Razina ta ce 

"Razina budurwar da ta zo ɗazu ƴar uwarku ce" 

Razina na wasa da wata flowa da ta tsinko mai kalar orange ta ce

"Eh ƴar uwarmu ce mom ɗinta ƙanwar Abba ne, sannan mom ɗinta ita ce yayar Aunty Nafisa wacca muka je gidanta,kuma Tahseen ce za ta auri Ya Arqam, Ina tunanin saboda Ya Aqram zai dawo Nigeria ne yasa ta zo gidanmu" 

Taɓe baki Hujayrah ta yi sannan ta ce

"A gaskiya kuwa bata da aji, a ce saboda namiji ne yasa za ta zo gidanku ba don ziyara ba, Tab!" 

Matsowa Razina ta yi don ta ji daɗin gulmar da kyau ta ce

"Kin san ma Ya Arqam ba sonta yake ba?" 

Waro idanu waje Hujayrah ta yi tana kallon Razina, wawwaigawa Razina ta yi kar wani na kusa dasu ya ji me suke cewa.Sake Matsowa ta yi kusa da Hujayrah  kamar Hujayrah tasan me  take nufi, ai kuwa matso da kunnanta ta yi sai Razina ta raɗa mata wata magana, ai babu shiri Hujayrah ta yi saurin wagowa tana kallon Razina fuskar ɗauke da mamaki ta ce

"Ummmmmmmm!!!!" 

Razina ta ce

"Um umm wallahi" 

Maganar kurame suka koma duk don kar wani yana kusa dasu ya gane me suke faɗa. (Kai su Razina an iya gulma ko me aka faɗa ma Hujayrah a kunne har kuka koma maganar kurame, oho! ni da my Esteem fans and followers muna neman ƙarin bayani gaskiya🤭🤭🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️😂😂😂) 

*Washe Gari da safe*

Kasancewar jirkinsu Arqam sai Ƙarfe 12:00pm na safe zai sauka shi ya sa jama'ar gida suka fara shiri cikin natsuwa, ma'aikata duk sun fito tun asuba sun yi aikinsu sannan kowanne cikin ya saka sababbin kaya saboda dawowan Arqam mazansu da matansu. Da sassafe Hajiya Nafisa da yaranta Mas'ud da Nazima har da Mahmoud wanda ya kasance aboki ga Arqam da Mas'ud ma tare suka iso gidan a cewarsu tare dasu za a je Airport ɗauko Arqam. Hajiya momma da wasu ma'aikata suna kitchen suna taya ta girki don Arqam baya cin abincin masu aiki sai na Hajiyarsa. Shi ya sa tazage tana shirya masa haɗadɗan girki wanda tasan yafi so tun yana yaro. Nan da nan ta kammala girke-girken, tuwon semo ne da miyar ganye wanda ta ji nama da stock fish, sai pepper soup ɗin kayan ciki da fruit salad sai kunun aya da pineapple juice.

Da yake  akwai extra rooms da yawa a part ɗin Hajiya momma sai Tahseen ta kwana a wani ɗakin, sai kusan 8:12am na safe ta tashi. Nan da nan ta yi wanka ta fito tare da shiryawa cikin rantsattsiyyar atampa ɗinkin riga da skirt mai kalar pink da ash Sosai ɗinkin ya zauna ɗas! a jiki, riƙo gyalen ta yi a hannu ta fito wanda kusan 10:31am. Hujayrah da amai ta tashi yau kasancewar a duk lokacin da za ta yi al'ada sai ta sha wuya, wani lokacin amai wani lokacin ciwon mara da masassara. Magani Razina ta amso mata bayan ta sha sai ta kwanta. Haka nan Razina ta shirya itama tafi zuwa part ɗin Hajiya momma. Koda Hajiya Nafisa dasu Mas'ud suka  tambayi ina Hujayrah sai Razina ta ce tana  ɗaki kwance bata da lafiya. Haka kowa ya shirya zuwa Airport, tare da Alhaji za a je amma ban da Hajiya momma da Hajiya Sama don har da su Fauziyya da Zahriyya a ƴan tawagan ɗauko Arqam a Airport. Tahseen da Fauziyya sai aikawa junansu harara suke domin abu ɗaya suke hari wato multibillionaire Arqam Imran Abdulfatah,bayan haka kowa yasan halin ɗan uwansa babu abin da ɗaya za ta nunawa ɗaya don kar-to-kar kowacce tasan yadda ƴar uwarta ta sheƙe aya da yake a ƙasa ɗaya  suka yi makaranta. Motoci kusan gona suka tafi ɗauko Arqam da yake shi ma da bodyguard ɗinsa zai zo. Kai tsaye ABUBAKAR TAFAWA BALEWA INTERNATIONAL AIRPORT suka nufa. 

Sun Kai tsawon hour ɗaya suna jiran saukan jirginsu Arqam daga bisani jirgin  ya sauka. Bayan mintuna ashurin sai mutane suka fara fitowa,a First class section na jirgin Arqam yake su ne suka fara fita. Bayan mutane uku sun fito sai naga wani handsome and classy guy ya fito daga jirgin, bai sauka ba yana tsaye ya saka hannayansa cikin aljihun wandonsa, shaƙar iskan garin ya yi a sanyaye ya furta 

"Ƙasata"

Baƙin glass ne a idonsa, sanye yake cikin suit ash color Wanda ta yi mishi kyau sosak, a hankali ya fara tattaka matattakalan jirgin ya sauko, a bayansa wasu manya-manyan bodyguards ne suke taka masa baya, turawa da baƙaƙyen fata ne bodyguards ɗin. Suma sanye suke cikin black suit kowanne a cikinsu ya saka Baƙin glass kunnansu maƙale da Bluetooth, Haka suka sauka daga jirgin. Arqam fari ne sosai kamar Hajiya momma, yana da saje wanda ya zagaye fuskarsa, kyakkyawa ne sosai don wasu suna faɗin duk yafi ƴan ɗakinsu kyau sannan za a iya kiransa da ingarman namiji saboda cikar zati gashi da kwarjini, amma matsalar ɗaya ce wacca take saka mutane jin haushinsa, ba komai ba ce illa shegen miskilancinsa, kai masa magana goma da ƙyar ka samu amsar biyu. Halin Hajiya momma ya biyo na rashin son mutane da magana har ma ya so finta. Cike da izza da mazantaka yake tafiya su kuma bodyguards ɗinsa suna biye da shi, ɗaya daga cikin bodyguard ɗinsa yana ɗauke da wata buzuzuwan mage fara Swal! Da ita, gata da blue eyes masu ɗaukar hankali. Da ɗan gudu-gudu tana ɗingishi Razina  ta je ta rungume Arqam tana faɗin

"Oyoyoooooo my Ya Arqam!!!" 

Shi ma rungumeta ya yi yana ɗan sakinah fuska kaɗan,suna a wurin sauran mutanan suka iso in da suke, Hajiya Nafisa ceta rungume Arqam tana faɗin

"Oyoyoooooo! My son ya dawo ƙasarshi, fatan ka dawo lafiya" 

Ɗan murmushi wanda bai faɗaɗa ba ya yi yana jinjina mata kai, da yake tasan halin Arqam yasa bata damu ba,Alhaji ma rungumesa ya yi yana farin ciki, Mas'ud da Mahmoud suka gaisa. Tahseen da saurinta za ta  rungume Arqam sai ya ja da baya yana faɗin... ✍️






*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***