BA NI DA MADOGARA

Chapter 15

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*













  
 
*Ba ni da Madogara*
  (Sai Allah...)




 

015

Wata uwar tsawa ya daka mata lokaci guda suka razana, Zaliha tuni ta saki fitsarin da take riƙewa tana ƙanƙame Murja saboda tsoro. Cin amon muryarsa mai cike da ƙaraji ya ci gaba da cewa

"Ƙarya zamu yi miki!!! Kece farkon wacca ta fara rusa mana shiriii!!! A sanadiyyarki wasunmu sun zama guragu saboda azabaaaa!!! Tafi ƙarfinmuuuu!!! Tafi ƙarfinmuuuu!!! Ita da ahalinta sunfi ƙarfinmuuuu!!! Dole ne mu ɗauki fansarmu akan babban ɗanki wanda yake hannun yayan mahaifiyarkiii!!! "

Da  sauri Murja ta ɗago da kanta, gabanta sai dukan uku-uku yake.Hannunta ta saka a kai ta ƙwalla wata ƙara tana faɗin

" Wayyo Allah ni Murjaaa!!! Na... "

Wata uwar tsawa ya sake daka mata yana faɗin

" Kun san da Allah kuka zo wurinmuuu!!! Makiraa mai fuska biyu!!! Ai muna sane da makircin da kike ƙullawa munfukaa!!! Ku tashi kubar min gidaaa tun kafin fushina ya sauka a kanku"

Babu shiri su Murja suka miƙe, rige-rige suka shiga yi wurin fita daga ɗakin, har Zaliha na bigewa a ƙafarta, ta ji zafi sosai amma bata tsaya dubawa ba sai da suka bar gidan tare da yin nisa sosai sannan suka samu wuri suka zauna. Sai a sannan ne Murja ta fashe da matsanancin kuka, Zaliha ƙafarta ta duba d saboda zafin da take mata, ƙila idan sun koma gida sai ta je wurin mai ɗaurin ya duba mata ƙafar ko ta yi targaɗe. Bata damu da kukan da Murja take dirza ba hasalima daɗi ta ji a ranta tana mata Allah ya ƙara. Murja kuwa sai da ta yi kuka ma'ishinta sannan ta tsagaita tana duba Zaliha ta ce

"Yanzu Zaliha ko jimami tare da bani haƙuri ba ki yi ba bayan kin ji da kunnuwanki abin da boka ya ce asirin zai koma akan Jabiru, amma baki damu ba kamar ba ƴar uwarki ba" 

Sai da ta gama tsittsine mata a ranta sannan ta ɗan taɓe baki ta ce

"Allah sarki Innar Balki wallahi a ruɗe nake don ban ma saurari abin da boka ke cewa ba tsabar firgici, sannan ban san kan maganar ba" 

Sake goge wani sabon hawayan Murja ta yi sannan ta ce

"Ni yanzu na ma rasa abin faɗa gashi Kawu Isah ya kirani shekaran jiya a waya ya ce cikin satin nan za a kai kuɗin auran Jabiru. Kai amma Hannatu ta cuceni wallahi, bazan taɓa bari ɗana ya koma sata ba sai dai ayi mutuwar kasko kowa ma ya rasa, bani ɗin ba, ba Zaytunan ba, ba kuma Hannatun ba, don wallahi saina ma yaron  kowannansu asiri ya koma kalar ɗana. Da ni suke taɗin wallahi"

Ita kaɗai take kiɗinta kuma take rawarta domin Zaliha ta daɗe da lulawa kogin tunani, tana ayyana abubuwa da dama a ranta musamman zaƙuwarta na auran Alhaji Zakari, fatanta ke nan a kullum saboda tana da burika da dama wanda sai ta auresa kafin za ta iya ckasu. Jin shiru Zaliha bata tanka mata ya yasa Murja ta ɗan taɓata, firgigit ta juyo cikin hayyacinta tana inda-inda ta ce

"Amm Na'am me kika ce ma" 

Mamaki ne ya cika Murja ganin duk surutun da take ashe hankalin Zaliha bama a wurinta yake ba. Cike da ɓacin rai Murja ta ce

"Haba Zaliha wai meke damunki ne da ana miki magana amma hankalinki baya jikinki " 

Ɗan sosa kai Zaliha ta yi sannan ta ce

"Na lula kogin tunanin yadda za mu shawo kan matsalar ne, wallahi ban ji kina magana ba" 

"Yanzu tashi mu tafi zuwa gobe sai mu shirya tafiya Ƙwarin ɗan dodo wurin malam Tani mai allon ƙarfe, shi ma aikinsa kamar yankan wuƙa ne. Rashin sani ne yasa na zo wurin wannan bokan wallahi" 

Cike da farin ciki Zaliha ta ce

"To Allah ya kaimu goban lafiya, tun farko ma da wurinsa muka je tunda Inna ma can take zuwa" 

Miƙewa Murja ta yi tana cewa

"Tsautsayi ne yasa  na zo wurinsa, tun fil'azal wurin Malam Tani mai allon ƙarfe muke zuwa ni da mama kafin ta rasu, sannan innarki bata da wani malami sai malam Tani, wurinsa kaɗai take zuwa" 

Ita ma Zalihan miƙewa ta yi tare da cewa

"Hakane To yanzu abu biyu zai kai mu wurin malam Tani gobe ko" 

"Eh, maganar mallakar Alhaji Zakari sai na Jabiru, don yanzu jini na a ƙumba yake wallahi. Tsoro nake  kar wani abu ya samu Jabiru, Allah  ya tsaresa daga sharrin wannan bokan" cewar Murja suna tafiya 

"Karki wani damu babu abin da zai samu Jabiru, ba gobe zamu wurin malam Tani ba, sai ya karya asirin ai" 

Sauke ajiyar zuciya Murja ta yi sannan ta ce

"To Allah yasa" 

"Ameen" cewar Zaliha tana yamutsa fuska saboda zugin da ƙafarta take yi. 

Haka suka ci gaba da tafiya har suka baro Layin boka mai zamani daga bisani suka tari masu mashina kowa ya hau sai suka wuce. Kowa hanyar  garinsu ya nufa sai zuwa gobe za su sake haɗuwa don zuwa wurin malam Tani mai allon ƙarfe. 

*Ƙarin bayani*

Jabiru shi ne ɗaga na biyu a wurin Murja kamar yadda Hannatu ta bada riƙon Jamilu ga mahaifiyarta haka Murja ta bada riƙon Jabiru ga yayan mahaifiyarta hakan ya faru ne tun lokacin da aka ce Mansur ɗan Zaytuna ya rasu daman tare aka kaisu almajiranci wanda kakansu Hujayrah ya yi jagora a lokacin yana raye, bayan rasuwar Mansur a dalilin almajiranci yasa su Murja da Hannatu yanke shawarar kai yaransu wurin iyayansu, kasancewar mahaifiyar Murja ta rasu sai dai yayan mahaifiyarta wanda yake zaune a Maraba sannan ƙanwar mahaifiyar w Innar Zaliha wacca take zaune da Ƙwarin ɗan dodo.

Sai dai shi Jamilu ya samu karatu sosai saboda ƙanin Hannatu ya yi boko sannan yasan amfaninsa, tun Jamilu na ƙarami Muntari yaba Hannatu da Alhaji Zakari shawara akan su turo kuɗi a saka Jamilu makaranta, babu musu suka fara tura masa kuɗi saboda ya yi musu bayani  muhimmanci yaro ya yi karatu a wannan zamanin. Shi kuma Jabiru bai samu hakan ba sai dai aikin noma wanda aka horar dashi a kai. Yanzu haka ya gida ɗakin da zai saka matarsa a ciki sannan har an kai kuɗin aurensa gidan iyayan budurwarsa.wannan ke nan

*Cikin labari*

Bayan  mai mashin ya sauke Murja a wajan ƙofar gidansu sai ta sallamesa sannan ta shiga ciki. Tana zuwa tsakar gidan kafin da shiga sashenta ta yi turus! tana kallon Ikon Allah. Su mammin Hujayrah, Fatsima da Hannatu ne ta gani a tabarma ɗaya suna hira har da dariya da shewa, ta yi matuƙar mamakin ganin Hannatu zaune tare da su Fatsima suna hira, me hakan yake nufi ke nan ta shirya da su ne ko kuwa. Wani malolan baƙin ciki ne ya taso mata tun daga ƙahon zuciyarta ya hato fuuu! Ya tsaya mata cak! A daidai maƙogaronta. Cike da ɓacin rai ta wuce ta gabansu fuuu! Kamar tashin iska. Sai a sannan ne su Hannatu suka lura da ita, da kallo suka bi ta har ta shige sashenta tare da banko ƙofar sashen kamar ita ta yi mata laifin . 

Taɓe baki Hannatu ta yi tare da cewa

"Kyaji da shi dai"

"Allah shi kyauta" cewar Fatsima 

Mammi kuwa bata ce komai sai dai tabi sashen Murja da kallo tana murmushi tare da girgiza kai. Ci gaba da hirarsu suka yi suna dariya. Bayan Murja ta shigo ɗakin lokaci guda ta wullar da jakanta tare da yakice gyalen sai dunƙule hannu ɗaya tana tafi tare da kai-kawo a falon, sosai ran Murja ya yi matuƙar ɓaci ganin Hannatu tare da su Mammin Hujayrah alamu sun nuna tana shiri da su ke nan, kar dai a ce ta gane halinta yasa ta janye jikinta daga gareta ta koma shiri dasu Fatsima. Cak! Ta tsaya wuri ɗaya tana tunani, a ranta tana cewa 'Da Murja kike , sai na kai ki ƙasa wallahi, bari Zaliha ta shigo ciki sai mun saisaita ki,wato haɗa kai da makiyayata kika yi, kina cin dunduniyan...'  bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba sai ta ji wayar ta na ringing, ba tare da ta kawo komai a ranta ba ta ɗauko jakar ta cire wayan. Lokaci guda ƙirjinta ya yi matsanancin bugawa ganin numban Kawunta ɓaro-baro a screen ɗin wayar, nan da nan ƙwaƙwalwarta ta tuno mata kalaman boka. Har zufa ta  fara yi mata sallama a duk ilahirin jikinta, jiki a matuƙar sanyaye ta ɗauki kiran tare da kara wayar a kunnanta ba tare da ta ce komai ba. 

A can Kawu Isah ya ce

"Assalamu Alaikum Murja" 

Yadda ya yi maganar sai ta ƙara tsinkewa da lamarin. Cikin murya mai rauni ta ce

"Nnna'aaamm Kawuuu" 

A can ya ce

"Murja duk abin da kike a garinku ki bar shi maza-maza kizo, don na kira wayar Zaliha na sanar mata ta zo Ita da innarta Maraba yanzu-yanzu, Kema ina so ki bar abin da kike ki zo" 

A nan ta kai Murja ta rikice tare da fareti a ɗakin kamar wata soja tana faɗin

"Shi kenan ya tabbata Boka mai zamani, ya illata min Jabiru, wayyo ni Murja na shiga uku na lalace!" 

Jikinta na rawa ta ɗauki jakarta tare da riƙon gyalan a hannu ta fito daga ɗakin. Ko samun damar kulla ɗakin ba ta yi ba balle ya kai ga sashenta. Allah ya sa ta saka takalminta kafin ta fito. Da sauri-sauri gudu-gudu ta fito zuwa waje ba tare da ta kalle su Hannatu ba, duk wanda ya ganta a wannan lokacin zai yi zaton an yi mata kiranye ne saboda yadda yanayinta yake. Da kallo su Fatsima suka bita da shi, Hannatu Taɓe baki ta yi sai Mammin Hujayrah ta ce

"An ya Murja lafiya take kuwa" cike da damuwa a fuskarta wanda ya kasa ɓoyuwa

"Gaskiya da wuya akwai lafiya saboda yanayinta ya nuna hakan" cewar Fatsima tana sake bin hanyar wajen da ido 

Hannatu ba ta ce komai ba kuma bata da niyyar cewa komai domin ita tasan wace ce Murja da halayanta,ci gaba da hirarsu suka yi.

Murja na fito daga gidan ta ga mai mashin ya sauke wata maƙociyarsu, da sauri Murja ta ƙwalama mai mashin kira kamar wacca ta ari baki. Bayan ya sauke matar sai ya zo wurinta,maƙociyar ta su na gaisheta amma ina ƙwaƙwalwa da tunanin Murja sun daɗe da barin gangan jikinta. Ba tare da ta amsa mata ba mai mashin ya wuce da ita. Sai a hanya mai mashin ya tambayi ina zai kai ta sai ta ce Maraba, Hanyar Maraba ya nufa da mashin ɗinsa. A lokacin har wasu masallataiyye sun fara kiran sallar Asr. Sun daɗe suna tafiya daga bisani ya sauketa a daidai ƙofar gidan Kawunta wanda yake a Maraba. Bayan ta sauka ta sallami mai mashin za ta shiga ciki sai ga mashina biyu sun goyo Innar Zaliha da Zaliha.Fasa shiga gidan ta yi ta tsaya tana jiransu, bayan sun sallami mai mashin sai suka dugunzuma baki ɗayansu zuwa cikin gidan. Murja ce a gaba su Zaliha na biye da ita. 

Tana sawo kanta cikin gida ta fara jin surutun mace tana guɗa da shewa a tunaninta ko matan gidan ne, tana shigowa tsakiyar gidan ta yi turus! Zuciyarta ta na halbawa da ƙarfi,Suman tsaye Murja ta yi tsabar firgici. Zaliha da inna na shigowa cikin tsakar gidan suka tsaya, murya Zaliha na rawa ta ce

"Jaabiruuu!!!" 

Wanda aka kira da Jabiru na kai dubana garesa, matashi ne wanda ba zai gaza shekara 29 a duniya ba. Baƙi ne ƙakƙarfa amma shigar da ke jikinsa na mata ne, kayan ƴan matan gidab ya saka har da shafe-shafe kamar  mace. Yana tsakiyar gidan yana rangwaɗa da karairaya, yara da matan gidan duk sun zagayeshi. Da yake Kawun Murja matansa uku ne sannan kowaccansu na da yara amma babu laifi yana da ɗan arziƙinsa daidai gwargwado hakan ne ma yasa tun farko Murja ta kawo Jabiru gidan kasancewar suna ɗasawa da uwar gidan. Jin an kira sunansa yasa Jabiru waiwayo yana ƙarema su Zaliha da Murja kallo, ɗangwas-ɗangwas yake takowa yana rausaya zuwa wurinsu bakinsa ɗauke da chewing gum yana ci yana bada sautin ƙas-ƙas. Murja bata gama tsinkewa da lamarin Jabiru ba sai da ta ji ya dubi Zaliha ya ce

"Yau naga iskannnci da bura uba! Ni kike sauyawa suna zuwa Jabiru! Waya faɗa miki sunana Jabiru!" 

Mamaki ne ya cika Zaliha har ta ma kasa cewa komai sai kallonsa, gyara tsayuwa Innar Zaliha ta yi sai ta dubi Jabiru ta ce

"Meke damunka ne da kake irin waɗannan abubuwa kamar wani ɗan daudu! Lafiyarka kuwa Jabiru "

Kallon ƙasa da sama Jabiru ya yi ma Innar Zaliha sai ya ce

"Da hankalina sarai, taya zan bari a canja min suna  wai Jabiru sai kace namiji, Mts! Ni sunana  *JABRITY PRINCESS* tauraruwa mai haskawa a cikin garin Maraba" 

    Nan da nan wurin ya kaure salati da sallalami,kowa na mamakin sauyawan Jabiru lokaci guda. Sai a sannan ne Murja ta saki wani marayan kuka mai ratsa zuciyar duk wani mai sauraro. Su inna sai bata haƙuri suka amma ina taƙi shiru. Zuciyarta ta kasa yarda wai yau ɗanta ne ya koma riƙakƙyan ɗan daudu har yana canja sunansa, amma kuwa ba za ta taɓa yafe ma Hannatu ba domin tasan ko kaffara ba za ta yi ba, ita ce ta yi wannan kitumurmurar da tasa boka ya dawo da asirin jikin ɗanta, to ba za ta yarda ba sai dai ayi mutuwar kasko kowa ya rasa har da Zaytuna. Murja babu bakin magana sai Kuka babu ji babu gani. Suna a haka suka ji  sallamar Kawu Isah shi da babban ɗansa sun shigo cikin gidan. Shiru wurin ya yi, ba tare da ɓata lokaci ba Kawu Isah ya ce ma su Murja su biyoshi sashensa. Babu musu suka biyoshi har ɗakinsa wanda  baƙinsa suke sauka. Murja, Zaliha da Innar Zaliha sai uwar gidansa da babban ɗansa suke a ɗakin, bayan kowa ya zauna sai Kawu Isah ya dubi Murja ya ce

"Murja Kinga abin da ya faru da ɗanki ko da rana tsaka" 

Murja da ke  gunjin kuka har da sharar majina ta gyaɗa masa kai. Duban uwar gidansa ya yi sannan ya ce

"Mariya basu labari abin da ya faru da Jabiru " 

Cike da damuwa Mariya bayan ta gyara zaman ta fara magana 

"Lafiya lau Jabiru ya tashi har ya je gona ya dawo, lokacin muna zaune dukkaninmu a tsakar gida muna hira sai kawai muka ga Jabiru ya yanke jiki ya faɗi kasa sumamme. Da gudu muka zo kansa muna salati, jiki na rawa na ɗibo ruwa a kofi na shiga yayyafa masa. A daidai wannan lokacin Yayansu ya shigo cikin gidan nan ta kai muka ci gaba da yayyafa mai ruwa, sai bayan kusan mintuna goma ya yi wata iriyar miƙa tare da rangaɗa guɗa kalar na mata, mun yi matuƙar mamakin jin Jabiru na guɗa kamar mace. Wani Sabon mamakin ne ya ƙara shigar mu lokacin da Jabiru ya miƙe da gudu zuwa ɗakin ƴan matan gidanmu. Ganin yana abu kamar wani marar lafiya yasa muka biyosa cikin ɗakin da saurin mu hankalinmu a matuƙar tashe. Turus kowannanmu ya yi ganin Jabiru ya cire kayansa daga shi sai wandon ciki, jikinsa na rawa ya jawo jakar kayan Baraka ya ciro doguwa riga ya saka, A'a! A gaskiya kanmu ya yi matuƙar ɗaurewa. Bayan ya saka kayan sai ya ɗauko kayan shafe-shafana ya fara shafawa, cike da mamaki na tambayesa 'Wai lafiyanka kuwa Jabiru' buɗar baƙinsa ya ce 'shirin biki nake gashi ni ne babbar ƙawa' zaro idanunmu muka yi waje, Yayansu ya ce 'Wani biki kuma' miƙewa Jabiru ya yi yana rangaɗa ya ce 'Bikin gimbiya Yalisa zani' kun ji dai mafarin komai, daga haka Yayansu ya kira Babansa ya shaida masa abin da ke faruwa shi kuma ya zo sai ya kira ku "

Shiru ɗakin ya yi tun bayan Mariya ta fara bada labarin abin da ya rafu, ba ka jin motsin komai sai shassheƙan kukan Murja da jan majinanta. Bayan Mariya da ɗige aya a zancenta, cikin kuka  Murja ta ce

" Wallahi! Wallahi! Wallahi! Kawu Ko kaffara ba zan yi ba, aikin matar Zakari ne don bata sona a gidan tun ba yau ba take bi na da sharri Allah na kare ni, gashi yanzu ta yi sanadin ɗana ya zama ɗan dauduuuuuu yiiiiiiiiiii!!! Yiiiiiiiiii!!!!" 

Cike da tsantsan ɓacin rai Kawu ya ce

" Yanzu matar Zakari ne ta yi ma Jabiru wannan muguntar "

Gyaɗa masa kai ta yi, sai ya ci gaba da cewa

"To wallahi ƙaryarta ta sha ƙarya don munfi ƙarfinta da malamanta da Kusfa, yanzu Murja wace shawara kika yanke" 

Share hawayanta ta yi sannan ta ce 

" Daman Kawu na yanke shawarar zuwa gobe wurin malam Tani mai allon ƙarfe za mu "

" Yawwa shi ma aikinsa yana yi kamar yankan wuƙa" cewar Innar Zaliha 

Ɗan muskutawa Kawu ya yi sannan ya ce

"To ku fara gwada  malamin ku gani, idan aikinsa bai yi ba ni ina ba malamin da nake amsar sa'ar noma wurinsa, babba ne kuma shahararre don aikinsa yanayi kamar yankan wuƙa, na daɗe ina amsar sa'ar wurinsa. Idan waccan aikinsa bai yi ba sai ku gwada wannan "

Godiya sosai Murja ta shiga yi ma Kawunta don tasan zai taimaketa sosai har Jabiru ya dawo normal. Ganin yamma ta yi sai kawai Kawu ya ce su kwana zuwa gobe sai su koma gidansu. Nan take Murja ta kira Zubairu ta shaida mishi abin da ke faruwa sannan za ta kwana sai zuwa gobe za ta dawo. Bai ce da ita komai ba ya katse kiran, halinsa ne na miskilanci bai ƙi ya wuni bai ce komai ba ko kuma bai ce da kowa komai ba. Shirunsa a nan yana nufin ya amince...✍️

        🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Alhaji Zakari bayan ya turo mai unguwa da wani abokinsa an yi komai an gama sun dawo masa da labarin saka ranar shi da Zaliha, ya shiga ruɗu sosai don abubuwa sun fara yi mishi yawa a kai, na farko matsalar Murja na dole sai ya auri ƙanwarta in yana so karta tona  asiri, sai  kuma wani sabon tashin hankali wanda bai ji bai gani ba Alhaji Sambo Dala yake niyyar ɗora masa. Haka ya kusan kwana yana tunani sai can cikin dare bacci ɓarawo ya sacesa. 

Washe gari bayan ya gama kari shi da Hannatu da autansa Faisal sai ya tafi kasuwa inda ya buɗe shagon saida hatsi. Da yake akwai yaran da suke tsare masa kaya, wuri kawai ya samu ya zauna. Can yana zaune ya lula kogi tunani ya ji wayarsa na ringing, cirota ya yi ya duba mai kiransa, waro idanunsa ya yi waje ganin mai kiran nasa, Alhaji Sambo Dala ne ya kira, tsam! Ya miƙe daga inda yake sai ya koma can gefen wata bishiyar lemu inda babu kowa ya yi sauri ɗaukan kiran saboda ta kusa yankewa. Cike da girmamawa ya ce

"Ranka shi daɗe barka da Safiya" 

A can Alhaji Sambo Dala ya ce

"Ya batun yarinyar fatan ka ɗaukota daga inda ka ɓoyeta ko" 

Ƙirjinsa ne ya bada sautin Ras! Jin ya sake ambata masa Hujayrah, a tunaninsa ya kira sa ne don ya sanar masa yaga Hujayrah. Cike da damuwa Alhaji Zakari ya ce

"Wallahi tallahi na rantse da Ubangijin halittu ban san da guduwar Hujayrah ba, ka yarda dani bazan taɓa gigin yi maka ƙarya ba, wallahi idan da na ganta ni da kaina zan kira ka ka aiko da yaranka su tafi da ita" 

A can Alhaji Sambo Dala ya ce 

"Look Zakari karka maida ni mutumin da bai san mai yake yi ba, kar ka manta Ina da masu saka min ido a garinku sannan ba za su taɓa min ƙarya ba, sun ce kai da hannunka ka ɗauki yarinyar ka gudu da ita. Ka ga idan kana son kwanciyar hankali tare da zaman lafiya kai da iyalinka tun wurin ka yi gaggawan ɗauko yarinyar daga inda ka ɓoyeta ka kirani ka sanar min na aiko yarana su ɗauketa, idan ba haka ba zaka sha mamakina, don duk wanda yamin karan tsaye kai shi ƙasa nake sannan duk wanda ya yi jayayya da ni to babu shi babu shan ruwa a gidansa, kasan da  wanda kake zance. Banda mutunci sannan banda imani, zan iya hallaka kowa in dai burina sai cika. Bana sassauci ga kowa sai ga ahalina idan ba ka yi wasa ba kana gab da kai ahalinka ga halaka ne gwara tun muna mutunta juna ka ɗauko yarinyar salin-alin ka kirani na aiko a ɗauketa "

Tun lokacin da Alhaji Sambo Dala ya fara magana gumi ya fara kwaranyo masa a duk ilahirin jikinsa, tabbas yasan Alhaji Sambo Dala bai da imani domin wanda yake yanka yara to ina yaga imani, shi sai yanzu yake da na sanin tun farko ƙulla alaƙa da shi, da ya haƙuri ya zauna da talaucinsa da ƙila Allah ya yi masa wani buɗin, amma gashi ya saka kansa ga halaka wanda bai san ranar fitarsa ba. Sauke nannauyar ajiyar zuciya Alhaji Zakari ya yi sannan ya ce

"Yallaɓai wallahi duk wanda ya faɗa maka ya ce ni Zakari ya ganni na ɗauki Hujayrah na ɓoye wallahi ƙarya ya..." 

Bai ƙarasa abin da ya yi niyyar faɗa ba Alhaji Sambo Dala ya daka masa wata uwar tsawa yana faɗin

"Yi min shiru maƙaryacin banza da wofi, Ni har za ka ma daɗin baki, kasani wanda ya faɗa min bazai taɓa min ƙarya ba domin na yarda dashi shekara da shekaru ban taɓa samunsa da ƙarya ba ko cin amana. Ka sani a cikin kwana goman da na baka ka ci kwana biyu saura kwana takwas, bazan sake kiranka ba sai dai ka jira nawa aikin akan ahalinka "

Kittt! Ya yanke kiran, wani nannauyar ajiyar zuciya Alhaji Zakari ya sauke kamar Alhaji Sambo Dala ya tafi ya lumfashinsa ne lokacin da ya yanke kiran. Ya daɗe a wurin daga bisani ya koma shagonsa ya zauna. A zahiri yana kallon yadda mutane suke kai-kawo a kasuwan a baɗani ya lula kogin tunanin yadda zai shawo kan wannan gagarumin bala'in da yake shirin tunkarosa shi da iyalinsa... ✍️

          🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gida dubu, Gubi Housing Estate Bauchi State, Nijeriya*

A ɓangarensu Hujayrah bayan sun sauka daga mota kai tsaye suka nufi part ɗin Hajiya momma, Hajiya Nafisa na gaba Hujayrah na biye da ita suka isa falon.Bayan sun shiga falon suka tarar da Hajiya Ramla, Tahseen da su Razina har da Hajiya momma suna zaune a falon suna cin abinci. Babbar darduma suka shimfiɗa suna cin abincinsu hankali kwance. Hajiya Nafisa ce ta ce ma Hujayrah su ƙarasa suma su ci abincin. Babu musu ta bita wurin,Hujayrah za ta zauna tare da su sai Tahseen ta yi saurin cewa

"Where are you sitting madam?  Da mu za ki ci abinci" 

Hajiya Ramla tana duban Hajiya momma ta ce

"Yanzu yarinyar da baki san daga inda ta fito ba kika yarda da ita har da barinta ta zauna ku ci abinci a tare? An ya Hajiya Mubina kin yi tunani kuwa?" 

Ƙayattacan murmushi Hajiya momma ta saki sannan ta ce

"Hajiya Ramla ke nan ai ɗa na kowa ne, Sannan Hujayrah da kike gani na ɗauketa a matsayin ɗiyata ce, kamar yadda Razina take da daraja a wurina to haka ma Hujayrah take da matuƙar daraja a wurina" 

Galala Hajiya Ramla ta saki baki da hanci tana kallon Hajiya momma, can ta yatsina fuska sannan ta ce

"Kidai sani tsintacciyar mage bata taɓa zamantowa mage, ki yi taka-tsantsan da wannan yarinyar don zuciyata bata yarda da ita ba" 

Ta ƙarasa maganar tana cilla ma Hujayrah wata uwar harara kamar idanunta za su faɗo da yake Salame ta bata labarin abin da Hujayrah ta yi mata. Tun lokacin da Tahseen da Hajiya Ramla suka fara magana Hujayrah ta kafesu da mayatattun idanunta ko ƙyaftawa ba ta yi a ranta tana ayyana yadda za ta ci uban Tahseen da Hajiya Ramla lakada a waje. Hajiya Nafisa ta katse mata tunani da cewa

"Hujayrah kamar ɗiya take a wurinmu ko ni nan zan iya riƙeta, kar ki jiki komai Hujayrah ta dabance " 

Taɓe baki Hajiya Ramla ta yi sannan ta ce

"Eh za ki ce ta dabance ko dan baƙinta kamar  kamar baƙin tukunya, ga idanunta kamar idanun Mayu, Ni an ya yarinyar nan ba mayya bace" 

"Mom mayya ce wallahi, ɗazu magen Ya Arqam taƙi yarda da kowa sai ita kaɗai" cewar Tahseen tana cilla ma Hujayrah harara 

"kun gani ko ai na faɗa muku mayya ce" 

Kowa banza ya yi da ita, Hujayrah ko zama ta yi abinta wanda hakan ya saka Tahseen saurin miƙewa cike da shagwaɓa ta dubi Hajiya Ramla ta ce

"Mom a gaskiya I can't eat with this ugly black gurl here, Idan dai da ita za a ci abincin to wallahi bazan ci ba" 

Shiru ɗakin ya yi kowa na mamakin wannan baƙin hali irin na Tahseen. Murmushi Hujayrah ta saki sannan ta dubi Tahseen ido cikin ido ta ce

"Hmmmm ni kuma bazan tashi ba, yanzu na yi niyyar cin abincin sai dai ki tashi amma wallahi banga abin da zai tasar da ni a wurin nan ba. Mutane biyu ne a wurin nan suke da ikon ce min na tashi kuma na tashi ba tare da na yi jayayya dasu ba, daga mammina sai Hajiya Nafisa Auntyna bayansu babu wanda ya isa ya tasar dani a wurin nan. "

Tana ƙarasa maganar ta gyara zamanta sai tabuɗe food warmer da izzarta ta ɗauki plate ta zuba tuwan da miyar tare da zuba pepper soup ɗin a gefe, gyara zamanta ta yi don ta ji daɗin cin abincin da kyau sannan ta fara saɓa loma hankalinta kwance kamar ba ta jin yadda Hajiya Ramla da Tahseen suke watsa mata mugun kallo, har da ƴan waƙe-waƙenta take tana faɗin

"Wai! Wai! Waiii! A gaskiya mammina girkin nan naki ya yi matuƙar daɗi,chakwala daɗi luwai!!!" 

Sosai ran Hajiya Ramla ya yi matuƙar ɓaci ganin bare tana ma ƴan gida rainin hankali, sannan shirun da Hajiya momma da Hajiya Nafisa suka yi ya ƙona mata rai, ke nan sun goyi bayan wannan baƙar yarinyar akan ɗiyarta, ke nan sunfi son ɗiyarta ta tashi daga wurin akan yarinyar lallai da sauran aiki, a ranta tana cewa 'Da sauran rina a kaba, dole na kira Hajiya Lubna na tambayi mai yasa aikin bai mamaye Hajiya Mubina ba sai dai ya tsaya akan amincewarta da auran Arqam da Tahseen, dole na sake wani sabo gaskiya wannan bai min ba'  tsakin Tahseen ne ya katse mata zancen zucinta, dubawan da za ta yi sai ta ga Tahseen har ta kai ƙofar falo. Cike da ɓacin rai Hajiya Ramla ta dubi su Hajiya momma ta ce

"Yanxzu kun zaɓi bare akan na gida ko, ai kun kyauta" 

Miƙewa ita ma ta yi  tare da barin wurin kai tsaye ta nufi ƙofar fita ita ma ba tare da ta sauri amsar su ba. Taɓe baki Hajiya Nafisa ta yi sannan ta ce

"Ai wannan rashin gaskiya ne wallahi, Hujayrah kin burgeni da kika gaggasa mata magana ba tare da kin ji tsoran ta ba" 

Murmushi Hujayrah ta yi sai ta ci gaba da cin abincinta tana santi. Da murmushi a fuskar Hajiya momma ta dubi Hujayrah ta ce

"Excellent my daughter haka nake son mutum da rashin tsoro, na gode da kika bata amsa daidai da ita, kusan halinku ɗaya da Arqam sai dai shi baya magana irin taki amma fa idan ya faɗa ma mutum magana zai kwana yana tunanin maganar " 

Dariya suka yi daga bisani kowa ya ci gaba da cin abincinsa hankalinsu kwance. 

A ɓangaren Tahseen bayan ta fito daga ɗakin a fusace kai tsaye ta nufi garden tare da zama a kujerar wurin. Wani malolan baƙin ciki ne ya taso mata tun daga sansanin zuciyarta ya keta hazo bai tsaya a ko'ina ba sai a daidai maƙogaronta, ya tsaya cak! Yaƙi tafiya sai huci take a ranta tana cewa 'Wallahi wallahi sai na yi maganinki yarinya, sai na nuna miki ke ba kowan-kowa bace a gidan nan, da Tahseen kike wallah...' bata ƙarasa zancen zucinta ba ta ji muryar mahaifiyarta a bayanta tana kiranta 

"Tahseen" 

Banza Tahseen ta yi mata, sake kiran sunanta ta yi Still bata amsa mata ba balle ta yi tunanin za ta juyo ta dubeta. Ganin ba za ta amsa mata ba yasa ta tako har inda take tare da zama kusa da ita tana faɗin

"My Angel Tahseen sorry kin ji" 

Wani kuka ne ya taso ma Tahseen lokaci guda ta fara rairawa tare da faɗawa jikin mahaifiyarta, bubbuga bayan Tahseen Hajiya Ramla ta shiga yi tana faɗin

"It's OK Tahseen zan yi maganin yarinyar kin ji, su ma karan kansu zan yi maganinsu, ba dai sun taɓamin ke ba, to kamar sun taɓo ma kansu tsukiyar dodo ne, idan na koma gida zan sake kiran Hajiya Lubna don na tambayeta aikin a iya amincewar auranki da Arqam ya tsaya ne ko kuwa.Nafi so mu mallaketa ta ko'ina ya zamana duk abin da ya shafeki tana haba-haba dashu, sannan ina so ki yi duk iya yinki na ganin kin sace zuciyar Arqam kin ji Gudalliyata. Arqam naki ne ke kaɗai "

Sauke ajiyar zuciya Tahseen ta shiga yi akai-akai, bayan Hajiya Ramla ta gama maganar sai ta ɗago kanta da dubi Hajiya Ramla cike da shagwaɓa ta ce

" Mom just do something gaskiya, Don I can't take this rubbish from Hajiya momma, ba wai don ina son Arqam yana nufin zan iya juri wulaƙancinta ba, taya za a yi ina matsayin ƴar gida taƙi goyon bayana sai wannan baƙar yarinyar mai kama da mayu, Allah yasa ba mayya ba ce, wallahi I hate that gurl with the whole of my heart, kuma sai na yi maganinta wallahi "

" I trust you dear, ki ci ubanta lakada a waje don da ina kusa har dani za a yi maganinta, Karki raga mata ko da farcen susa ne, yanzu zan wuce gida your Dad is waiting for me at home, take care of yourself and don't tolerate any rubbish from anyone Ko da kuwa Hajiyan ce da kanta, kowa ya shiga konarki ki tabbata kin nomesa yadda ya kamata "

Ƙarasa maganar ta yi tare da miƙewa Tahseen ma miƙewan ta yi suka bar garden ɗin. Tahseen ta koma ciki sai Hajiya Ramla ta taho zuwa parking space. 

A nan da haɗu a abokiyar hammayarta Hajiyan sama, ita ma ta fito za ta unguwa. Harara suka shiga aikawa junansu. Cike da izza Hajiyan sama ta ce

"A'ahhh an zo fadanci ne wurin manya,wato Tahseen ta dawo gidan nan saboda a laƙabawa Arqam don anga yana da ƙumbar susa" 

Wani kasalalan murmushi Hajiya Ramla ta saki sannan ta ce

"Izzatu ke nan ai na gaba ya daɗe da yin gaba na  baya kuwa  sai dai ya ɓige da tsintar huta, kan ki ake ji wallahi domin kuwa Tahseen ita ce matar Arqam ɗaya tilo, idan ma gasa kike shirin yi dani to gwara ki tattara makaman yaƙinki ki ajiyesu gefe guda, domin koda kuwa kin shiga ba nasara za ki yi ba, na daɗe da sanin kina so Fauziyya ta auri Arqam don ki ji daɗin cin dukiyar Hajiya Mubina, to ki sani ba za ku taɓa yin nasara ba, domin ni ɗin nan da kike gani kainuwa ce dashen Allah, mai ja dani sai ya shirya "

Wata bazawarar dariya Hajiyan sama ta yi sannan ta dubi Hajiya Ramla ƙasa da sama  ta ce

" Yaro bai san wuta ba sai ya taka,to ai ga fili ga mai doki, mu zuba mu gani shege ka fasa ɗan halak sai yanka, Ni yanzu banda lokacinki wallahi Mts! "

Bata jira amsar Hajiya Ramla ba ta shiga rantsattsiyar motar. Taɓe baki Hajiya Ramla ta yi sai bodyguard ya yi saurin buɗe mata murfin mota ta shiga sannan suka tafi wanda motan Hajiyan sama na gaba na su Hajiya Ramla na biye suka bar gidan. 

A can gida kuwa Tahseen kai tsaye ta nufi part ɗin Arqam, ta yi knocking ƙofar yafi so goma amma shiru ba a ce mata komai ba haka nan ta haƙura tabar wajen zuwa ɗakinta wanda ta sauka a ciki. 

Su Hajiya Nafisa sun daɗe sosai a gidan sai daga baya Mas'ud ya zo ɗaukarsu bayan ya ƙona tarkacen asirin. Sai da ya biya part ɗin Arqam sannan ya zo suka wuce gida. A ɓangaren Arqam yana jin lokacin da Tahseen take knocking ƙofar banza ya yi da ita saboda bai son hayaniya yana da buƙatar hutu yanzu.Bashi ya fito daga ɗakinsa ba sai lokacin sallar Magrib yana kammala sallah ya nufi part ɗin Hajiya momma, a nan ya ɗan ci abincin kaɗan sai ta haɗa masa coffee saboda shi yafi tun yana yaronsa, wani lokacin baya cin komai sai dai ya sha coffee da cupcake ya yi kwanciyarsa. Sai  a sannan ne Hajiya momma ta ce masa bayan birthday ɗinsa za su yi wata muhimmiyar magana. Gyaɗa mata kai ya yi sannan ya wuce part ɗinsa ya kwanta saboda ya gaji sosai. Daman bodyguards ɗinsa da P.A an basu wani sashe babba wanda za su dinga kwana a cikinsa kasancewa gidan akwai extra parts da yawa. 

Tuni su Hujayrah suka koma ɗakinsu tun lokacin da suka kammala cin abincin rana, ko na daren ma a ɗakinsu suka ci,saboda Razina na amfani da daren tana koya ma Hujayrah Karatun boko da sun gama sai su kwanta abinsu. 

*Washe gari*

Da safe ma'aikatan gidan suka fara shirye-shiryen birthday ɗin Arqam tare da murnar dawowansa ƙasarsa Nijeriya, tun a yau suka fara shiri saboda bikin ana so ya  ƙayatar sosai sannan friends ɗinsa na wasu jahar za su hallarci bikin birthday ɗin. Mazansu da matansu kowa aikinsa yake tuƙuru. Bayan su Hujayrah sun karya kumallo sai Hajiya momma ta ce ma Hujayrah ta ɗauki flask ta kai ma Arqam a part ɗinsa don tasan da wuya ya zo nan ya yi break fast, babu musu ta ɗauki flask ɗin cike da murna da fito zuwa part ɗinsa tana ƴan waƙe-waƙenta tana jin daɗin za ta haɗu da magenta. (My Esteem fans ku tayani dubawa yaushe Arqam yabama Hujayrah mage🤭🤭🤭🤭😂😂😂😂) 

Da sallama a bisa labɓanta ta turo ƙofar ɗakin da mamaki a fuskarta ganin ashe ma a buɗe take, kai tsaye ta shiga ciki da sake kwaɗa wata sallamar tare da kiran mage tana cewa

"Mus! muss!! muss!!! " 

Da gudu magen ta zo wurin Hujayrah, fuskarta ɗauke da murmushi ta duƙa tana shafa magen tana faɗin

"Kyanwata na yi kewarki wallahi, jiya na so zuwa na ɗauke ki mu yi baccinmu tare amma ban san dama ba, kar ki damu yau zan zo na ɗauke ki mu kwana tare mu yi ta wasa abunmu" 

Miƙewa ta yi hannunta riƙe da flask ɗin, sai a sannan ne ta lura da Arqam wanda yake aikinsa a laptop, a ɗaya kujerar Tahseen ce sai faman watsa mata harara take, ko a jikin Hujayrah ta tako har zuwa inda Arqam yake, ita ma magen na biye da ita. Duban Arqam ɗin ta yi sannan  ta ce

"Ammm Ya Raqam qam ga flask mammi ta ce na kawo maka, sannan ta ce ka tabbata ka sha don tasan halinka bata son cin abincin, ta daɗe tana jiranka a teburin cin abinci sai ta kirani ta ce 'Hujayrah zo ki kai wa yayanku flask ɗin nan Sannan Kice ya tabbata ya sha coffee ɗinsa don nasan halinsa baya son cin abinci' Ehm! Na ce ba Ya Raqam qam"

Tun lokacin da ta fara magana idanunsa yake kanta baya ko ƙyaftawa, ga wani sabon suna da ta saka mishi wai *Ya Raqam qam* bai dai ce komai sai  ta ci gaba da magana tana cewa

"Don Allah za ka aramun kyanwarka tunda ka ce ba za ka bani kyauta ba, Allah ina son mage..." 

Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba ta ji sukan maruka hagu da damanta ji kake Tass!!! Tass!!! Da sauri Hujayrah ta juyo don ganin wani ɗan bura uba ne ya ɗauketa da maruka har biyu. Mamaki ne ya cikata ganin Tahseen tsaya a gabanta, hannunta riƙe da ƙugu tana wani jijjiga tare da watsa mata harara. Saukan marukan sun yi daidai da shigowa Razina cikin ɗakin Cak! Ta tsaye cike da mamakin Tahseen a ranta tana faɗin ko me Hujayrah ta yi mata da za ta ɗauke ta da maruka har biyu. Arqam kuwa mamaki ne ya cika sa ganin ƙarfin halin Tahseen, jira ya yi yaga wani action Hujayrah za ta yi taking, shin surutun kawai take dashi ko kuwa tana da ƙarfi. Abin da ya yi matuƙar ɗaurewa kowannansu kai shi ne madadin Hujayrah ta rama sai kawai ta kwashe da wata bazawarar dariya har tana riƙe ciki, Sosai hakan da ta yi ya ɗaurewa Arqam da Razina kai balle uwar gayya Tahseen a ranta tana faɗin 'kar dai a ce aljana ta mara' . Sosai Hujayrah take dariya tana nuna Tahseen tana dariya. Bayan ta yi dariyar son ranta sai ta dubi Tahseen fuskarta ɗauke da murmushi ta ce... ✍️






*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***