Chapter one
" HANGEN DALA"
1
By
ABDULHAKIM UMAR
GODIYA TA TABBATA
Ga Allah Subhanahu wata Ala da ya bani iko da dama har na samu ikon rubuta wannan labari ina ƙara miƙa dubun godiya ga Allah da yayiman baiwar tunanin rubuta abinda zai anfani al'umma har ya zama iznah kuma DARASI ga wasu al'ummar, ina godiya mai tarin yawa ya Allah, Allah kasa yadda na fara lafiya na kammala lafiya, Amin ya hayyu ya ƙayyum.
TUKWICIGA
Yar uwa kuma makwabciya ta gari Hadiza Bara'u Gidan Iko, Allah ya bar zuminci ya ƙara ɗaukaka Amin ya Allah.
Sadaukarwa
Ga uwa mai bada mama hajiya Hauwa ɗiya Halliru kwanarya mamana ina alfahari da ke Allah yasa Aljanna makoma, Baba bazan mancekaba Don kai bangone abin jingina, na sadaukar da littafina gareku Allah ya bar kauna.
Fatan Alkhairi
Ga kungiyar Bakandamiya Hikaya Allah ya barmman ku Allah yasa afi haka Allah ƙara ɗaukaka da hazaƙa Allah ya cika maku burikanku na alkhairi Amin ya Allah, Ina maku fatan Alkhairi.
. Yan uwa rabijin jiki
Nuraddin Umar ɗan bugaje
Fadila Umar ɗan bugaje
Abdurrahman Umar ɗan bugaje
Muhammadu Umar ɗan bugaje
Amirah Umar ɗan bugaje
Fatima Umar ɗan bugaje
Abdullahi Umar ɗan bugaje
Al'ƙasim Umar ɗan bugaje
Mu'azzam umar ɗan bugaje
Shamsiyya Halliru kwanarya
Aminatu Ali Telah
HANGEN DALA
Book 1
Free book
By
ABDULHAKIM UMAR Dan BUGAJE
Page 1
Ji nai dukkan illahirin jikina ya ɗau ki karkarwa tamkar wacce aka joganama shocking Na hutar lantarki , Kai na ya ɗau zafi sakamakon zaɓaɓɓakar da kwakwalwata keyi tamkar Tafasasshen talgen da ya Isa tuƙi a Saman murhu.
Dum! Dum!! Dum!!! Haka zuciyata take bugawa da ƙarfi Kuma da sauri saboda tsabar tsoron da nake ciki , a hankali Na ɗago kaina Na buɗe idanuna dake rufe Ina kallon ma'aikatan da suka zagayeni sukai man atak da bindigu.
Kallon filin jirgin nake cikin tsoro da firgici ,kallo irin Na bakunta , kallo irin Na Allah ya haɗani da fuskar da nasani, kallo irin Na tsananin kewar gida da rayuwata ta baya, kallo irin na nadama da dana sani, kallo irin na Al'ajabi da mamaki, kafin nai Wani yunƙuri Naji an ƙargamaman hangcock a hannu, kafin aka ajiye jikkar da Na sheda tawace a gabana aka zazzage kayan ciki .
Tsoro firgici da ɗimaucewa suka Sani nafara guntun fitsari a Wando,
Dan da nan aka fara ɗaukar fotona da kwayoyin dake gabana.
Na shiga ukku Ni Ahana “ wallahi ba kayana bane ban San da suba .”
Babu Wanda ya kalleni Domin da alama basuma Jin abinda nake faɗa.
Yanzu ya zanyi waye Zai fuskanceni kwayoyi Kuma ajikkata , to Ina Samir yake? Yanzu kasheni zasuyi Ko gidan Yari zani, shin Zan tsira Ko ƙarshena ya zo Ni Kuma haka ƙaddarar tawa tazo Da ga zuwa honey moon Sai haɗuwa da bala'i inko haka ne Samir ya cuceni ya kashe Mani rayuwa, HANGEN DALA ya kawoni cikin birnin masifa.....
Tas wani ya ɗaukeni da Mari Yana Magana cikin yaren da ban iyaba , haka suka Sani agaba muka nufi wata hanya, wajan da ake ajiye motoci muka bullo aka Sakani awata ƙaramar Mota fara irin ta police na ƙasar ( sweetharland ), tafiya Mai ɗan tsawoce ta kawomu situation ɗin aka buɗe sell aka tillani aka rufe.
“Inna lillahi wa'inna illaihiraju 'un” nashiga faɗa saboda Wani irin baƙin duhun da ya mamaye dukkan illahirin ganina, wani irin bugu zuciyata take da ƙarfi saboda tsabar tsoron da nake ciki, Ina Zama ana shigowa sell ɗin ,Wani babban ɗansanda ne ya shigo Sai wasu mutane biyu bayansa.
Kusa da ni yazo ya tallafo fuskata kafin yace “ke da suwaye ku ka shigo ƙasar nan Ina sauran suka buya da wa kuke kasuwanci ? maza gayaman middin kina so mu tseratar da ke”.
Kallon sa Kawai nake hawaye na zubowa a kwarmin idanuna ,nasan Magana yake amma banajin abinda yake faɗa Kuma Ko naji bansan ta inda Zan Bashi amsa ba haka ya ƙare maganganunsa ya fice a fusace ga alama Shirun da nayi ta hassalashi, kuma ta tabbatar masa cewa bani da gaskiya .
Yana fita Suna shigowa matane majiya ƙarfi da suka horu Akan aikinsu Kai na suka iso ɗaya takamo jelar kaina ta buga man Kai da bango take goshina ya fashe jini ya Fara fitowa, Dan da nan Kai na ya ɗau zafi ya Fara sarawa.
“zakiyi Magana Ko Sai Mun chasaki”. Ɗayar ta faɗi cikin turanci
Kaicona Na furta a zuciyata Inama ace sadda ake turani makarantar Boko Ina zuwa da Yau ilimin yayiman Rana , Ni anawa gurɓataccen tunanin ilimin Boko baida amfani a wajan mace soboda aurar da ita Za ai sai yadda mijinta yai da ita Dan haka da anturani Sai Na tafi yawon shanawa da samari Ina samun ƴan kuɗi Na, gashi tun a yau na fara fuskantar muhimmancin ilimi a rayuwata.
Hannayena na haɗe waje ɗaya Na langwaɓar da kaina gefe alamar banhakuri , Ni da baki na amma na Koma bebiya.
“ba zakiyi magana ba Sai kin bugu ko”
Da sauri na ɗaga kaina alamar eh don basan abinda tace ba
Aiko take suka shiga dukana Kamar Allah ya aikosu wata a ciki , wata a fuska dan da nan kamannina suka sauya na fasa ihun! Wahala Ina Mai hango mutuwa nan kusa, tsananin azabar da Naji ya haddasaman tuno rayuwata ta baya.
TUNA BAYA
Suna na Ahana Idi , ni ɗaya ce mace a cikin 'ya 'ya sidda da Allah ya azurta iyayena da su, nayi aure har da yaro ɗaya , mijina Abbas ba mai kuɗi bane amma Yana da rufin asiri Domin Yana matsa fetur ne a gidan mai.
Zaune nake abakin ƙofar ɗakina Ina tankaɗan garin tuwo Wanda zanyi abincin Rana da shi naji anrafka sallama anshigo.
Baki washe na amsa sallamar Ina mai farin cikin ganin Mamata Yau a gidana don bata taɓa zuwa Ko da Wasa ba saboda ta tsani mijin da nake aure.
“mama sannu da zuwa ya hanya?”.
“Ƙalau”
Ta bani amsa tana Mai cigaba da faɗin
“wajanki nazo zamuyi Magana....”
“To mama mushiga daga ciki ki zauna kisha ruwa ko”.
“ba Zama ya kawoni ba don baki ganni da karyayyen ƙuguba, ba Kuma ruwa nazo Shaba don Ke baki da Ruwan da Zan Iya sha don Ko (pure water) Bana sha Sai na roba, bare Kuma na jarkar da kike Fama dasu Dukgurɓaci.”
“Taufa mama me yayi zafi?.”
“ komai ma yayi zafi Ahana don Yau da shirina Na zo umarni nazo baki ba Shawarma ba ,karɓi nan”.
Ta Kai ƙarshen maganar tana bani wata takarda Mai ɗauke da lambar waya
“ lambar sabon saurayin da nai makice don kar ya Kira kice ansaɓa lamba”
Dam! Dam!! Rudududum!!! Gabana yai wata mummunar faduwa na ɗago Kai na a firgice ina kallon mama kafin nace “ mama 'yar kicefa Ahana ko dai ɓatan Kai kikai ?”
“ ubanki ne yai ɓatankai nace ubanki ne yai ɓatankai da ya aurar da Ke ga miji ɗan ci ku bamu, yanzu Kuma Allah ya amsa rayuwarsa Babu shi don haka dole ki kashe auranki ki auri zaɓina inko ba haka ba to Sai dai ki sake uwa amma bani ba .”
“inna lillahi wa'inna illaihiraju'un ”
na shiga furtawa ina Mai maitawa cikin tashin hankali da ruɗani .
“yo ai salati ba naki baneba Ahana zakiyi salati amma ba yanzu ba sai Randa kika wulaƙanta Samir zakiga fushina ,ina mai jaddadamaki na tsani Abbas bana son sa Kuma na tsani auranki da shi, don haka naci alwashin rabaku middin Ina Raye, shawara ta rage ga Mai shiga rijiya ,na barki lafiya”.
Fuuuu! Ta fice Rai ɓace.
Daɓas na zauna ƙasa riƙe da takarda ina kallon ta cikin tashin hankali hannuna na makyarkyata ana dara ga dare yayi naga ta kaina ni Ahana.
Ina tsaka da wannan tunanin wayata tahau ƙara na ɗauka na duba mai Kiran,
Ras! Ras!! Ƙirjina ya buga da wani mugun ƙarfi ganin lambar hannuna jere reras Akan fuskar wayata.
Karki ɗaga wata zuciya ta kwabeni da sauri, Zama nai Ina kallon wayar Na kasa ɗauka Kamar yadda anƙi dai na Kiran Wani Na katsewa Wani na shigowa.
Karfa Abbas ya dawo ya zargi Wani abu,Wani yanki na zuciyata yace da ni yana haskoman irin matsalar da Zan shiga idon Abbas ya sameni a haka.
Da sauri na ɗauki wayar da sallama kafin ya bani amsa na tari lumfashinsa da faɗin “ bawan Allah don Allah kayi haƙuri karka sake kirana don ni matar aurece kaje ka nemi dai dai Kai ka rabu dani karka Sani cikin fushin ubangiji.”
“Dama ai nasan Ke matar aurece don mamanki ce ma ta bani lambar wayarki tai mani bayani bata ƙaunar Wanda kike aure ga talauci ,tace kina Shan wuya don haka zanzamemaki Gata ki yarda Dani ki kashe auranki mu rayu cikin daula don ina ƙaunarki zakiji daɗi mai yawa amma kiyi tunani”.
Kettt Na katse wayar na saketa Kan kujera Ina sharce zufar da Ke tsattsafomani ako Ina Na jikina nasan mama ta tsani aurena da Abbas amma banyi zaton zata Iya aikata haka a gareni ba.......
Ƙarar wayar itace ta katseman tunanina amma naki ɗauka har ya gaji ya haƙura don kanshi.
Din Din naji ƙarar shigowar (message).
Ido waje nake kallon wayar ɗauke da mamaki ganin alert na (1,000,000) jiki na rawa na fara karanta saƙon da ya biyo baya Kamar haka:
“kiyi maleji wajan sanyan Ruwan sanyin da zasu sanyaya ranki kiyi tunani Mai kyau a kaina don wannan somin taɓine acikin tanajin da nai Maki middin kika aminta da ni, Sai Naji daga gareki my Nurul hayat .”
Kuɗi masu gidan Rana kuɗi masu Saka babba ya bi yaro tuni huɗubar shedan ta yiman shigar ɓera arami cikin kunnuwana, Dan da nan naji ƙaunar manana na ƙaruwa a zuciyata tabbas ƙauna ce tasa mama son fiddani acikin wannan talauci.
“Assalamu alaikum Wai ance gashi”.
Kalaman da naji ana faɗi kekan atsakar gida , Ina fitowa naga wani Almajiri tsaye baƙin ƙofa da uwar Leda a hannunsa.
“wa yace ka kawo ? ”na tanbaya
“wani ne Kuma ya tafi ”ya bani amsa ataƙaice
Ɗin Ɗin saƙo ya shigo wayata (ga saƙonan Na Aiko da shi).
Amsa nai na bama Almajirin naira hamsin na shige ɗaki na buɗe ledojin kajine guda biyu manya sun gasu Sai ƙamshi suke Sai lemu five alive Mai sanyi ɗayar ledar Kuma turarukane da maya mayai, jiki na rawa na fara Cin kazar hannu baka hannu kwarya don rabona da kaza tun ta amarci Sai Naman kasuwa Wanda ake Saidawa abakin titi irin na tumakai da shanu, shima ba koda yaushe ba sai randa rabo ya rantse.
Wata irin Ni'ima da annashuwa Naji Suna shigata da Naji naƙoshi da kazar , kafin nai Wani yunƙuri Naji wayata na ƙara , mamace ta Kira don haka na ɗaga da sallama
Daga can akace
“Ahana kinga Ikon Allah mai saka tulu yai gashi ko kujerar hajjin bana harda ni yanzun nan akashedaman na Rasa inda zansaka Rai na don murna don haka Ina maki magana da Babbar murya ki gaggauta dawowa gida da takardar saki kinji na gayamaki.”
“yo mama ai ba a bori da sanyin jiki da zafi-zafi Akan bugi ƙarfe wazai yima arziƙi kulli aini gaba ta kaini gobarar titi a jos , Ko dubu goma Abbas bai taɓa baniba haka Kawai, amma Yau gani da one million acikin account don haka aurena da Abbas ya ƙare.”
“ Daɗi na dake saurin ɗaukar haske da ya dawo kici mutuncinsa ki zagai ki zagi uwarsa har ya fusata ya sakeki.”
“Angama mamana ta kaina Sai kin ganni”.
Ina ajiye wayar Yana shigowa Kamar an tillosa“ Ahana baki da lafiya ne Naga Ko ina na gidan ahargitse, ga sanwa anbarta wutar tayi murus, ga gari anfara tankaɗe anbarshi Duk Iska ya watsar da shi”.
Kallonsa nai tundaga ƙasa har Sama kafin nace
“jinai bazan iya taɓa komaiba”.
“Kamar ya baki Iya taɓa komai? To ni yunwa nakeji me zanci?.”
“Gasauran abinda naci nan ɗauka Kaci amma kabi sannu karka taune harshe don nasan ba asababa”.
Durkusawa yayi ya buɗe ledar kafin ya Fara kallona da mamaki Kamar me koyon Magana yace
“A.... A Ahana kaza kuma daga ina?.”
“ Daga wajan saurayina kasan arziƙi ya ƙwanƙwasoman ƙofa Kai kadai nake jira kazo kabani takkadata.”
“ wannan wane irin wasane ki daina bana so”.
Ya faɗi fuskar sa ɗauke da tarin mamaki
“ ba wasa nake ba da gaske nake kasake ni kawai nai gaba Arziƙi na can yana jira na ”
na faɗi babu alamun wasa akan fuskata
Dan da nan naga idanunsa sunyi jajur gashin jikinsa yafara tashi, cikin tashin hankali da ɓacin Rai da hargowa yace“