FreeArewaPen original
HANGEN DALA
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter one
" HANGEN DALA" 1 ByABDULHAKIM UMAR GODIYA TA TABBATAGa Allah Subhanahu wata Ala da ya bani iko da dama har na samu ikon rubuta wannan labari ina ƙara miƙa dubun godiya ga Allah da yayiman baiwar tunanin rubuta abinda zai anfani al'umma har ya zama iznah kuma DARASI ga wasu al'ummar, ina godiya mai tarin yawa ya Allah, Allah kasa yadda na fara lafiya na kammala lafiya, Amin ya hayyu ya ƙayyum. TUKWICIGAYar uwa kuma makwabciya ta gari Hadiza Bara'u Gidan Iko, Allah ya bar zuminci ya ƙara ɗaukaka Amin ya Allah. Sadaukarwa Ga uwa mai bada mama hajiya Hauwa ɗiya Halliru kwanarya mamana ina alfahari da ke Allah yasa Aljanna makoma, Baba bazan mancekaba Don kai bangone abin jingina, na sadaukar da littafina gareku Allah ya bar kauna. Fatan Alkhairi Ga kungiyar Bakandamiya Hikaya Allah ya barmman ku Allah yasa afi haka Allah ƙara ɗaukaka da hazaƙa Allah ya cika maku burikanku na alkhairi Amin ya Allah, Ina maku fatan Alkhairi. . Yan uwa rabijin jiki Nuraddin Umar ɗan bugajeFadila Umar ɗan bugajeAbdurrahman Umar ɗan bugaje Muhammadu Umar ɗan bugaje Amirah Umar ɗan bugaje Fatima Umar ɗan bugaje Abdullahi Umar ɗan bugaje Al'ƙasim Umar ɗan bugaje Mu'azzam umar ɗan bugaje Shamsiyya Halliru kwanaryaAminatu Ali Telah HANGEN DALABook 1Free book ByABDULHAKIM UMAR Dan BUGAJE Page 1Ji nai dukkan illahirin jikina ya ɗau ki karkarwa tamkar wacce aka joganama shocking Na hutar lantarki , Kai na ya ɗau zafi sakamakon zaɓaɓɓakar da kwakwalwata keyi tamkar Tafasasshen talgen da ya Isa tuƙi a Saman murhu. Dum! Dum!! Dum!!! Haka zuciyata take bugawa da ƙarfi Kuma da sauri saboda tsabar tsoron da nake ciki , a hankali Na ɗago kaina Na buɗe idanuna dake rufe Ina kallon ma'aikatan da suka zagayeni sukai man atak da bindigu. Kallon filin jirgin nake cikin tsoro da firgici ,kallo irin Na bakunta , kallo irin Na Allah ya haɗani da fuskar da nasani, kallo irin Na tsananin kewar gida da rayuwata ta baya, kallo irin na nadama da dana sani, kallo irin na Al'ajabi da mamaki, kafin nai Wani yunƙuri Naji an ƙargamaman hangcock a hannu, kafin aka ajiye jikkar da Na sheda tawace a gabana aka zazzage kayan ciki ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.