Chapter 39
by @barista
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 39
Sayyada barrister
YOTA 13
The five ink legends
Abuja Nigeria
Jirgin da ya ɗauko su daga Ghana kai tsaye ya dire su a Nnamdi Azikiwe international airport Abuja, cike da farin ciki suke sauƙowa daga matakalan jirgi, suna masu shakkar iskar ƙasarsu. Dr Waahab riƙe da luggage nasa bayan ya ɗauko, da sauran kayan sa wayarsa ta yi ringing yana dubawa yaga Daddy, ya sauke numfashi ya ɗauka tare da cewa
"Daddy..
"Son welcome, juyo ka ganni"
Da mamaki ya kama waige waige ya hango Daddynsa a tsaye yana yi masa murmushi, da sauri ya ƙaraso yana me farin ciki, yana isowa cikin girmamawa ya ce
"Daddy, surprised!"
Murmushi Daddy yayi ya ce
"Jiya da yamma na shigo Abuja, na ƙi fada maka ne"
"Oh! Ka yi min bazata"
"Mu je masaukina"
"Ok Dad zan sanar da OG"
"Ba damuwa"
Ya iso wajen su Dr Faisal ya yi wa OG magana
"Sir ina tare da mahaifina, za ku wuce ne ko sai gobe"
"A'a sai mun huta zuwa gobe"
"Ok daidai ne ma, gobe mu tafi dukkanin mu"
Ya yi musu sallama ya dawo wajen Daddy suka wuce hotel da Daddy ya kama, Dr Waahab ya watsa ruwa ya shirya cikin ƙananan kaya, Daddy yasa aka kawo masa abinci, bai ci sosai ba, ya mik'e kan resting chair bacci ya ɗauke sa...
Sai dare suka fito tattaki da Daddynsa, don ya fita ya bar Dr Waahab a hotel don gudanar da aikin da ya shigo da shi Abuja sai da ya kammala sannan ya dawo. Dr Waahab ya wuce masaukin su OG suka tattauna ya dawo wajen Daddynsa sun kusa raba dare suna hira kamin suka kwanta.
WASHE GARI
Jirgin safe suka hau na max Air ba ki ɗayansu zuwa Maiduguri, suna sauƙa a airport suka rabu da sauran ma'aikatan, Sageer Mustapha KIRAWA da Abdullahi Umar KIRAWA suka zo daukansu, sai murna suke yi ganin Dr Waahab ya dawo, Umar KIRAWA ya ce
"Ya Waahab sannu da dawowa"
"Yawwa Umar na same ku lafiya"
"Alhamdulillah"
"Ma sha Allah"
"Big bros ƙasar Ghana ta karɓe ka, kamar ba kai ba"
Murmushi ya yi ya ce
"Kuma fa tun da na tafi aiki mu ke yi tukurum ban zauna ba"
Daddy ya ce
"Mu wuce ko"
Suka sanya luggage na Dr Waahab da sauran kayan sa a boot na mota sannan suka shiga kai tsaye suka iso milloniars Quarters. A parking space Umar ya yi parking suka fito, nan aka fito yi masa oyoyo Hauwa da gudu ta iso wajen Dr wahaab tana cewa
"Ya wahaab sannu da zuwa?"
"Yawwa sunnu Hauwa"
Daddy ya ce
"Mamana shi ne ko a kula daddy ta yaya ake"
Dariya ta yi ta ce
"Daddy sannu da zuwa"
"Ban amsa ba"
Haka sauran yaran gidan sai sunnu da dawowa suke yi wa Dr wahaab, ya yi farin ciki sosai ganin yadda kowa ya yi kewarsa, Daddy ya ce
"To ku kyale shi ya huta zuwa anjima sai a zo ayi masa sannu da dawowa"
Suka wuce ciki, side na Mamie ya wuce yana shiga ya iske ta tana waya, ta ajiye wayar cike da farin cikin ganin ɗanta ta ce
"Lale maraba mutan Ghana"
Murmushi ya yi ya ce
"Mamie na yi kewar ki"
"Zauna nan baban gida ni ma nan cikin kewarka nake"
Hauwa ta shigo mishi da ruwan sanyi a gora da cup ta ce
"Ya wahaab ga ruwan sha"
Mamie ta karɓa tare da cewa
"To ke abinci za ki kawo masa ko kuma ruwa"
Murmushi ya yi ya ce
"Mamie wata uku ban sanya ki a idanuna ba sai yau, da fatan na same ki lafiya"
"Lafiya kalau Babangida, sannu da gajiya"
Ta tsiyaya masa ruwan a glass cup ta miƙa masa tare da cewa
"To ki kawo masa abinci mana"
Hauwa dake tsaye tana kallon yayanta cike da farin ciki ta ce
"Ya Ashfat ta kai masa side nasa"
A hankali ya ɗago ya kalli Hauwa dake ta faman murmushi, Mamie ta ce
"Ayya yau bata fita aiki bane?"
"Eh Mamie, tun asubar fari take ta yi wa yaya hidimar tarɓa"
Ya sauke numfashi, kamar zai ce wani abu kuma ya fasa, ya ajiye cup dake hannunsa ya ce
"Mamie zan je na huta zuwa anjima sai na shigo"
"To Allah huta gajiya"
Ya mik'e ya iso side nasa ya tadda Umar KIRAWA da Abdullahi KIRAWA suna tsaye a bakin ƙofar ɗakin, ya sauke numfashi tare da cewa
"Ku yi hakuri ina gaisawa ne Mamie"
"Mun yi maka uzuri babban Yaya"
"Ƙofar a buɗe take ku shiga"
Suka shigar da kayan, sannan su ka yi masa sai anjima, ya kurawa ɗakinsa idanu yaga har wani madaidaicin deco aka yi masa da ɗan guntun rubutu na welcoming nasa, sai kuma kayataccen teburin da aka jera masa abinci akai shi yasan ba shi da shi a ɗakinsa, sabo aka saka masa, ya iso ya karewa wajen kallo sannan ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet ya jima yana sakarwa kansa shower yana tunanin Angel kwana biyu bai ji muryar ta ba, jiya da yau.
Ya fito ya shirya cikin riga da wando ɗinkin shadda ya yi kyau sosai ya zauna a bakin bed yana ɗaure wrist watch nasa ya tashi ya fito ya shigo side na Ammie a hankali ya yi sallama a palour, ta amsa cike da farin ciki ta tako zuwa inda yake tsaye, ta san ya yi kewarta shi yasa ya zo side nasu.
Ganin kyau da cika ido da ya yi ne ya sake burkita ta...
"Ashfat Ammie na ciki?"
Wani bakin ciki ne ya tokare mata zuciya, kenan ba don ita ya shigo ba, tun safe take shirya masa abin tarɓa amma ya dawo ko ta kanta bai yi ba, a hankali ta ce
"Ya Waahab sannu da dawowa"
"Yawwa sannu Ashfat na same ku lafiya?"
"Alhamdulillah Ammie tana ciki"
"Ok yau ba ki je wajen aiki ba ne?"
Kamar ta yi ihu don haushi, amma ta dake ta ce
"Eh"
Ya zauna ya ɗan sauke numfashi ya ce
"Ki yi wa Ammie magana"
"To"
Ta faɗa ta shige ciki, ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta, duk wanda ta yi arɓa da shi da kwalliyar ta sai ya yaba, ga shi lace da ta saya na musamman ta ɗinka sabo da wannan ranan amma ko kare mata kallo bai yi ba. Ta sauke ajiyar zuciya...
"Ke kuma da waye kike tsaki haka?"
Ta ji muryar Ammie tana fitowa daga cikin toilet, ta sauke numfashi ta ce
"Ba komai, ya Waahab yana palour"
"To har ya iso kenan"
Bata ce komai ba ta fito ta bar Ammie tana saka niqabi, ta tadda yana zaune ya kishingiɗe ya lumshe idanunsa, ta kura masa idanu wani farin ciki ne yake ziyartan ta, ya Waahab kyakkyawa ne.
Kamar an ce ya buɗe idanunsa, yana buɗe su ya sauke su cikin nata, ta yi saurin cewa
"Ammie tana fitowa"
"Ok thanks"
Ya faɗa ta fice daga palour ta wuce ɗakin su...
Ammie tana fitowa ganin Dr Waahab ta ce
"Likita har ka iso?"
"Ammie na same ku lafiya?"
"Lafiya kalau sun sauƙa lafiya?"
"Alhamdulillah"
"Kun yi saɓani da Daddynka"
"Ai tare muka shigo Maiduguri"
"Au haba! Jiya fa ya tafi Abuja"
"Eh haka ya ce, ina Abba?"
"Yana cen bangaren Abbie"
Ya mik'e ya yi mata sai anjima, ya fito, kai tsaye ya iso side na Abbie Daddyn Suhaima ya tadda duk suna zaune har da Daddynsa, Abbie ya ce
"Ah likita na ce sai ka huta mu gaisa"
Ya ɗan sunkuyar da kansa cikin girmamawa ya ce
" Abbie, Abba na same ku lafiya"
Abban Ashfat ya amsa da
"Lafiya kalau, ikon Allah kamar yau ka tafi sai ga shi har ka dawo"
"Eh Abba"
Abbie ya ce
"Yau da gobe ba wuya, sannu likita"
"Abbie ya jikin Mommi?"
"Jiki Alhamdulillah sati me zuwa ma za su dawo"
"Ma sha Allah"
Bai jima ba ya fito ya wuce cikin gida ya tadda sauran babanninsa ya gaishe su sannan ya dawo side nasa ya kwanta bacci, sai azahar ya tashi ya idar ya sake kwanciya sai la'asar ya tashi, yana idar da sallah ya buɗe abincin da aka ajiye masa tun dawowarsa, kaɗan ya ci, ya ɗau wayarsa ya kira layin Angel a kashe...
Sai dare ya shigo side na Mamie tana zaune tana shan fruits ya yi sallama ta amsa ya zauna, ta ajiye masa plate ɗin kusa da shi ya ɗauka yana sha suna hira, ya jima a side nata sannan ya dawo ɗakinsa, ya yi shirin kwanciya wayarsa ta yi ringing yana dubawa yaga Angel, ya sauke numfashi ya yankar ya kira ta ɗauka tare da cewa
"Yallaɓai likita"
Ya sauke ajiyar zuciya cikin farin ciki ya ce
"Mon Ange"
"Na'am Uncle"
"Au har an janye sabon sunan da ake kira na da shi?"
"A'a mon amour"
"Ki daina kashe wayar ki"
"To mon amour"
"I miss you mon ange"
Shiru ba ta yi magana ba, ya ce
"Shi kenan tun da ba ayi kewata ba"
"Na yi"
"Say it"
"I miss you mon amour"
Ya runtse idanunsa sosai a hankali ya sauke numfashi tare da cewa
"Same here mon ange"
"Ka sami kowa lafiya?"
"Lafiya kalau, ya Mama?"
"Tana nan lafiya"
"Ki ce ina gaishe ta"
"Za ta ji"
"Tom bani labari"
"Bani da labari"
"A'a ni dai a bani"
Murmushi ta ke yi yana jin sautin shi har cikin ransa, ta ce
"To wane iri?"
"Me daɗi"...
A tsaye ta ke bakin ƙofar ɗakin ya Waahab riƙe da madaidaicin plate da ta shirya masa abin taɓawa, jin yana waya yasa ta tsaya, akan in ya ƙarisa sai ta shigo amma abubuwan da kunnuwanta suke jiyo mata yasa ƙafafunta neman gaza ɗaukanta.
What? Ya Waahab yana soyayya har da cewa he miss her, daman yana hira har haka? Wacece wannan yarinyar? Ta juya a hankali cikin tashin hankali ta iso kitchen kamar ta ƙwala ihu ta ke ji, ta zauna jikinta yana rawa kamar me yin zazzaɓi...
"Ya Ashfat me kike yi a kitchen?"
Da ƙyar ta ɗago ta kalli Teemah, ta mik'e ta fito ba tare da ta ce komai ba, ta wuce ɗakinsu...
Dr Waahab sai jan Angel da hira yake yi kati ya ƙare ya sake sakawa kusan sau biyu sai da yaji tana hamma sannan su ka yi sallama, ya kwanta...
******************
WASHE GARI
Da ƙyar Ashfat ta shirya zuwa wajen aiki, ta fito jiki a sanyaye, kamar ba za ta fita ba, ta tadda Dr Waahab a tsaye a farfajiyar gida ya yi kyau cikin bakaken suit sai ƙamshi yake yi, yana waya ta iso za ta wuce a lokacin ya tsaida wayar kamar ba za ta gaishe shi ba ta ce
"Morning Ya Waahab"
Ya dube ta tare da cewa
"Morning Banker"
Ɗan murmushi ta yi suka haɗa ido jikinta ya yi sanyi, Ya Waahab na daban ne, babu irinsa cikin maza, ba za ta iya rayuwa da kowanne irin namiji ba in ba shi ba, har zata wuce ya ce
"Let me take you"
Sai ta ji damuwarta ta gushe, ta fiddo da key ta ce
"Daddy ya saya min mota"
"Congrats"
Ya juya ya shige cikin motar da aka wanke masa ita aka goge sai kyalli ta ke yi, bakin ciki ya kama Ashfat ita fa ba wai ta nuna masa bane za ta shiga nata motar kawai nuna masa key ta yi sai ya kaita cikin nasa...
Ta iso ta buɗe motar ta cike da takaici ta tadata ta bar cikin gida...
Dr Waahab ya iso teaching hospital ya wuce office nasa, a gyare fes, ya duba duk abubuwan da ya bari suna nan, Dr Faisal ya shigo tare da cewa
"Morning sir"
"Morning ashe ka shigo"
"Yanzu na shigo, OG yana neman ka"
"Yana ina?"
"Office nasa"
"Okay"
Dr Faisal ya fice, Dr Waahab ya fito ya tafi office na OG sun jima suna tattaunawa sannan ya dawo office nasa, ya ci gaba da aikinsa....
**********************
Tun da Dr Waahab ya dawo kullum sai sun yi waya da Angel kamin ya kwanta, wani lokacin su yi texting juna, yau ma haka yana dawowa daga masallaci sun idar da sallah ishai ya faɗa toilet da niyyar in ya fito ya kirata, ya jima yana wanka, Ashfat ta shigo ɗauke da tray ta ajiye jin yana wanka yasa ta yi ƙoƙarin fitowa wayarsa ta yi ringing, kamar za ta fice sai kuma ta dawo da baya, ganin sunan da yake jikin screen na wayar yasa ta kura masa idanu, har ya yanke aka sake kira ta kasa karanta sunan, bata fahimci komai ba, kawai ta ɗauki kiran ba tare da ta yi magana ba, ta ji muryar mace tana sallama
"Assalamu alaikum, bonsoir mon amour"
Deep.. ta ɗauke wuta, ta ji yarinyar ta sake cewa
"Hello Yallaɓai likita"
Numfashinta ya soma sama, ta sake jin ta ce
"Uncle ba ka jina ne?"
Ɗif... Aka kashe wayar, ta dakyar ta daidaita tsayuwar ta tattaro nutsuwarta ta shiga text message tana dubawa kamar ta ƙwala ihu ta ke ji.
A hankali ta share hawayen da bata san ya zuɓo ba, ta danna number ta yi blocking sannan ta goge number har da text message ɗin, jin alamun Ya Waahab zai fito daga cikin toilet yasa ta ajiye wayar kamar yadda ya ajiye ta ɗauki tray da ta shigo da shi sannan ta fito ta janyo ƙofar a hankali ta rufe, ta yi tafiyarta...
Dr Waahab ya fito daga cikin toilet ya yi shirin kwanciya, ya hau kan bed ya janyo wayarsa ya duba number Angel ya kira bai gani ba, da mamaki ya duba sosai nan ma babu ya shiga contacts nasa nan ma babu, ya duba text message da suke yi ya ɗauki number ma babu, da mamaki ya tashi ya zauna, ya kurawa wayarsa ido yana so ya tuno wani abu ya kasa, ya aka yi ya rasa number mon ange?...
______________________
Uhmm in ji me ciwon baki😂
To sannunmu da dawowa gida.
Ayi hakuri da typing errors
Comments and share fisabilillah