Page 15
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 15
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Washe gari bamu da lecture da safe sbd lecturen yace baxai samu zuwa ba, bacci na nayi sai karfe 10 na tashi na shirya na fita makaranta.
Muna zaune nida Asma'u revision muke na maths sbd muna da test, nidai revision din kawai nake amma hankali na gaba daya baya kan karatun, Asma'u dake min magana ganin nai shiru yasa ta tabo ni.
Da sauri na juya na kalle ta, ajiyar zuciya na sauke nace "mai kika ce Asma'u ban ji kiba?"
Rufe book din da muke solving maths din tai ta kalle ni tace "Batul wai me yake damunki kwana biyu ina lura dake kina cikin damuwa don Allah ki fada min mai yake damun ki"
Shiru nai ina wasa da pen din dake hannu na bana jin zan iya fada mata damuwa ta don wannan sirri nane, ajiyar zuciya na sauke nace "Hmmm ba wani abinda ke damuwa kawai mood swing ne kinga ina period"
Dariya tai tace "haka ne sannu Amma ki daure mu karasa wannan kinga test din da zai mana yace da ita zai mana amfani a semester dinnan"
Murmushi nai na janyo book din na bude muka cigaba da revision din, karfe 11 lecturen ya shigo mukai test din gaba daya a gajiye nake don ji nake kamar an min duka ga mara ta dake dan murda min kadan kadan.
Muna zaune Mijin Asma'u ya kirata akan mamanta bata da lafia, hawan jinin ta ya tashi ya taho daukan ta suje asibitin da aka kwantar da ita, tana kashe wayar ta fara kuka ni nake rarrashin ta har ya karaso dole yau ni na rakata gurin motar tasa bamu wani gaisa cikin nutsuwa ba sbd kukan da Asma'u take, sallama nai mata bayan nai mata alkawarin zuwa duba maman tata in tambayi Abba.
Komawa nai na zauna gashi yau har 6 zamu kai a school ga cilla ma bai zo ba, haka mukayi lecturen karfe 1 to 3 muka fito sai na 4 to 6 kuma, a wannan interval din duka takure nake don ina Jin yadda nake zuba da gudu gashi na manta ban taho da pad ba ga bansan inda zan siya ba da kyar ma in banyi staining Ash colour hijab dina ba.
Ta bayan office din malamai naje na zauna ji nake kamar xanyi kuka a jikina ina jin yadda nake bukatar changing pad ga kuma tsoron kar aje nayi staining hijab dina don rushing nake sosai, hade kai da gwiwa nai ina damke cikina dake murda min.
Cikin takunsa na cikakken namiji mai cike da jarumta yake tahowa bayan office din, yana sanye da Riga da wando black colour da suka matukar masa kyau kansa sanye da p-cap black itama sai boot din kafarsa black, yayi kyau sosai bama yadda shigar ta haska farar fatar sa.
Tafiya yake yana duba wayar sa don so yake ya shiga office dinsa ya tattare kayan sa ya tafi yana da aiki a companyn su, kamar ance ya dago yagan ta a daidai lokacin da itama ta dago kanta Jin takun tafiya, da mamaki yake kallon ta yana mamakin mai ya kawota nan gurin kuma bayan ba yawan mutane agun.
Nima a nawa bangaren kallon sa nake yadda shigar tai masa kyau sosai dukda p-cap dinsa ta dan rufe masa fuska, saurin kau da kaina nai na mike shaf na manta da tunanin ko nayi staining din hijab dina, a hankali na fara tafiya ina runtse idona sbd yadda marata ta fara kartawa da karfi.
Zaro manyan idonsa yai yana bin bayanta da kallo tabbas jini yake gani a bayan hijab dinta ya bata hijab din da dan yawa dan sosai ake gani, tunani ya shiga yi mai zai kawo jini jikin ta kuma sai ya ware idonsa da mamaki ya furta "badai wannan kwailar al'ada take ba". Ganin ba mai basa ansa kuma gashi tana neman karya kwana ta fita cikin mutane a haka yasa shi daga kafa sosai har ya kamota.
Cikin tsare gida yace "hey",
A hankali na juyo nace "Good Afternoon sir"
Tabe baki yai yace "Al'ada kike yine kin bata jikin ki ko ynxu kika fara baki san yadda ake gyara wa ba?"
Dan satar Kallonsa sa nai jin tambayar rainin hankalin dayai min, amma Jin yace na bata jikina yasa ni saurin juya wa in ga inda na bata sai kamo hijab din nake amma na kasa gani.
Kankance idonsa yai yace "follow me"
Da sauri nace "sir", tsura min ido yai hakan yasa ni saurin sunkuyar da kaina kasa don ba karamin kwarjini naga yai min ba.
Gaba yai sai da ya tabbatar ba mutane a gun sannan ya dawo yace "muje" ban iya masa musu ba don bai ma bani fuskar da zan masa din ba.
Cikin nutsuwa na shiga bin bayansa ina rintse idona, shi ya fara shiga office din na shiga Nima gaba na yana faduwa, tsakiyar office din na tsaya nayi tsamo tsamo kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi, ban taba Jin kunya ta kamani ba irin ta yau.
Shi kuwa Azlan zaman sa yai akan kujerar sa ya dau wayar sa ya dannawa Mufeeda Kira dake itama tana level 1 a university din, sai da ta kusa katsewa ta dauka, cikin hade gira kamar tana ganin sa yace "kina ina"
Mufeeda dake tare da friends dinta da sauri ta mike ta matsa gefe tace "Ya Azlan ynxu na fito daga lecture"
Gajeran tsaki yai yace "kije gurin mota ta ynxu zan fito zaki rakani wani waje" daga haka ya kashe wayar.
Mikewa yai yaga yadda take yamutsa fuska tana shafa cikinta ta cikin hijab, tabe baki yai yace "ciwon al'ada kike yine"
Ya salam ji nai kamar na fashe da kuka wai al'ada Shi ko kunya baya ji maimakon yadan tsakaya yace period, Shiru kawai nai hakan yasa shi tsaki ya ce "xanje na dawo kar ki sake ki fita ki Jira ni"
Bin bayansa da kallo nai har ya fita, ajiyar xuciya na sauke ganin ya rufe kofar da key ta waje, da sauri na cire hijab dn jikina ai kuwa yayi staining sosai, har rigata itama ta baci sosai kawai na fashe da kuka shikenan Mr Wicked ya gama kallona a haka waya sani ma ko daga yau kallon kazama zai dinga min, tsugunnawa nai akan tiles dan baxan xauna masa akan kujera ba naje nai staining dinta itama.
Azlan gurin parking space ya nufa a jikin motar ya tarar da Mufeeda tana tsaye tana jiransa tana ganin sa ta Kara daidaita tsayuwar ta ta nutsu, bai ko kalle taba ya bude motar ya shiga hakan yasa itama budewa ta shiga.
Fita yai daga school din ya hau titi sai kuma ya juyo ya kalle ta yace "ina ne ake siyar da kayan mata"
Da sauri ta juyo ta kalle sa tace "na'am yaya"
Hade rai yai yace "inda ake siyan da kayan mata nace miki koh"
Ajiyar zuciya ta sauke tana sosa keya tace "Yaya za'a samu a sahad ma"
Bai sake mata magana ba har suka isa, kallon ta yai yace "zo muje ki rakani inda zan samu"
Fitowa tai yana gaba tana binsa a baya har suka je inda ake siyar wan, kallon kayan yake a hankali idonsa ya sauka akan wata doguwar riga maroon colour readymade, karasa yai gunta ya dakko tabe baki yai yace "maybe ma tai mata yawa" ya fada yana bin breast curve din rigar da kallo, gurin hijab ya nufa ya dauki wani maroon colour shima dogo har kasa a basket din hannun sa ya sa har ya juya sai kuma ya tuna ai tayi staining kenan tana bukatar pad da pant.
Gyada kai yai ya nufi gurin pants, binsu da kallo yake yana tunanin wanne zai dakko tunda baisan size dinta ba, kundunbala yai kawai ya dakko wasu guda 6 XXL yace "in sun Mata yawa tasan yadda zatai dasu ai dole ma suyi mata yawa wannan kwailar"
Zaro ido Mufeeda tai ganin ya dauki pant da sauri ta share gumin fuskar ta tana kara murza idon ta, tunda take da Azlan zata iya rantse wa bata taba gani ya sai wani abu daya shafi mata ba, ko ita take son Abu in ta fada masa kudin kawai zai bata yace taje ta siya bata gama fitowa daga shock din ba taji muryar sa Yana fadin "kee ina ake siyar da audugar Mata"
Da sauri ta dago tace "audugar Mata kuma yaya?"
Harara ya banka Mata yace "wacce kuke amfani da ita in kuna al'ada mana"
Da sauri tai gaba tace "bata nan suke ba ai Yaya bara naje na dakko ma"
Yana tsaye taje ta dauko ta kawo, karba yai suka je gurin biyan kudi ya biya a bayan mota ya ajiye har zai shiga motar sai kuma ya tuna ai tana ciwon al'ada tsaki yai ya dakko wayar sa ya dannawa Junaid Kira, ringing biyu ya dauko bai magana ba sai da Junaid din yace "Zakin Baffa lafia kuwa naga kiranka"
Hade rai yai yace "ynxu Junaidu baxan iya karanka ba sai da dalili"
Dariya Junaid yai yace "ai nasan kane Kai da baka neman mutane ynxu dai fada min meyasa Ka kirani don nasan da akwai dalili"
Shiru yai kamar baxai magana ba sai kuma yace "Mene maganin ciwon al'ada?"
Da mamaki Junaid ya kalli wayar sa ganin da gaske dai Azlan ne ya kirasa yasa shi fadin "lafia Azlan mai ya hada Ka da maganin al'ada kuma"
Tsaki Azlan yai yace "zaka fada min ko kuwa a'a ina ba kai kadai ne doctor ba a duniya"
Da sauri Junaid yace "Allah ya baka hakuri, ya yanayin yadda take Jin ciwon yake"
Dan lumshe idonsa yai yace "mara ne kawai inaga"
Sunan maganin Junaid ya fada masa sannan ya kashe wayar, a hanya ya tsaya ya sai maganin ya siya yogurt da meat pie, bai sake yiwa Mufeeda magana ba har suka isa makarantar.
Parking yai ya kalle ta yace "fita saura kuma naji labarin cewa na dauke ki munje wani gurin sai na gurza bakin ki a bango"
Da sauri ta daga kai ta fita tana mamakin wace wacce yayan nata ya siya wa Kaya haka har dasu always.
Shi kuwa Azlan ledojin siyayyar sa ya dauka ya nufi office dinsa yana tafiya yana tunanin ko mai take ynxu oho shidai fatansa kar ta zauna masa a kujera ta bata masa da abin al'adar ta.
Yana bude kofar da ita ya soma cin karo tana tsaye sai gyara hijab take, bakinsa ya tabe ya ajiye mata ledojin a kusa da kafar ta.
Da sauri na dago na kalle sa sai kuma na sunkuyar da kaina kasa, Tabe baki yai ya nemi guri ya zauna akan doguwar kujerar dake office din ba tare daya kalle taba yace "dauki ledar nan kije toilet ki raba kanki da kazantar nan"
Shiru nai kamar ban ji sa ba ni yau ai baxan iya rashin kunya ba ciwon marar da nake ji kadai ma ya isa yasa ni nutsuwa ga kuma abin kunyar da nai Mutumin da nake tsulawa rashin kunya shine ya ganni cikin wannan yanayin.
Ganin taki daukar ledar yasa shi mikewa ya tako har gabanta, da sauri na yi baya Jin hucin numfashin sa daf dani, dagowa nai ba inda idona suka fada sai a cikin nasa da sukai dau da kwalli, sunkuyar da kai nai kasa ina Mirza hannu na.
Hade rai yai yace "ba magana nake miki na, dau ledar nan ki shiga toilet ki cire kayan ki ki chanja duk kin cika min office da karnin jini"
Jinai kamar na fashe da kuka Amma bani da yadda zanyi, tsugunnawa nai na dauki ledar na nufi hanyar toilet din daya nuna min, ina shiga naji ya fita daga office dn gaba daya.
Ajiyar zuciya na sauke ina bude ledar, da mamaki na fito da komai dake ciki, rintse ido nai ganin hadda pant da pad tunanin yadda zan saka na shiga yi amma bani da option duk kayan jikina sun baci dole na chanja.
Kayan jikina na cire duka na sa a cikin ledar bayan na cire kayan daya siyo na ajiye a cikin sink, shower na sakar ma kaina sai da nai wanka da sabon sabulun dana gani sannan na shirya cikin kayan daya siyo, kallon kaina nai a jikin mirror din toilet dn kamar ya auna jikina har pant din yamin daidai.
Murmushi nai bayan na daidaita hijab din a jikina sai ynxu nake Jin wata nutsuwa tana ratsani ga iska dake shiga jikina mai dadi, ledar kayan nawa na dauka bayan na bar masa ragowar pant da pad din a toilet ba tare da tunanin komai ba.
Fitowa nai daga toilet din daidai lokacin da shima ya shigo.......
***