Chapter 2
HANGEN DALA
by
ABDULHAKIM UMAR
Page 2
Free book
�***
“Wane shegenne yabaki kaza, bin mazan waje da auranki Ahana a gidana ”.sai ya ɗaukeni da Wani gigitaccen mari kafin nai Wani yunƙuri ya ƙaramani.
Tsoro firgici da mamaki suka Sani nafara ja da baya don na firgita da ganin yanayinsa amma tuno irin daular da zanshiga yasa Na Dake nace“ Na sandai kaji abinda nace tunda Kai ba kurma bane don haka kabani takaddata nai gaba ba fushinka nake son gani ba kuma ba hargowa na ke son jiba .........”
Wata irin shaƙa yayiman wacce tasa sauran maganata maƙalewa amaƙoshina Na Fara kakarin wahala idanuna sukayo walwaje.
“idon har kika ƙara cewa nasakeki Sai Na kasheki har lahira, Ko da yake laifina ne nayi sake ɗan Zaki ya Girma amma zanyi maganin abin idon har shawara aka baki to kin hau keken ɓera don Ina Mai tabbatar maki Babu saki atsakaninmu Ni dake mutu ka raba takalmin kaza duk duniya Babu Wanda ya Isa yasa nasake ki.”
Sai ya tillar dani gefe ganin Na kusa mutuwa, wata irin tsanarsa ta Fara bijiroman huɗibar shedan tai tasiri akaina don haka nace
“wallahi Sai ka sakeni Ko nakai ƙararka ga hukuma, Ko ka manta akwai kotu nashirya rabuwa da Kai Akan ƙudirina Shari'a daga police situation har kotun ƙoli wallahi Sai ka sakeni ”.
Ganin idon har ya biyeman zai yiman illah sai ya fice kawai abin sa rai a ɓace, zuciya a jagule yana ta huci kamar kumurcin maciji.
Yana aza ƙafarsa zauren da nufin fita, itama tana sako ƙafarta gidan.
Baya yaja yana mai komawa cikin gidan ransa ya fara yimasa sanyi yana maiyin murnar ganin mama.
“yawwa Allah mama kinzo a dai dai dama gidan ki zanije yanzu don akwai matsala a gidan nan Ahanah ce ta tsareni wai sai na bata takardar ta tagaji da zama dani shine zanje na sanar maki a zo a zauna ayi mata faɗa da nasiha idon kuma wani abun nai mata sai ta faɗa sai na gyara mu zauna lafiya ”.
Kallon sa take irin kallon raini da tsana sai da ta cunkushe fuska kafin tace
“ To me kake jira ai maƙasudin zuwa na kenan na tafi da ita don aure da kai ya ƙare, saki dole kuma rabuwa ta har abada don babu kome ko biko, ” cewar mamar tana hararasa
Duk wani abin da ake kira mamaki Al'ajabi sune sukai fitar bulace daga zuciyar Abbas zuwa kwanyarsa take ya hau jifar mama da wani irin mugun kallo kafin yace“ mama kin kuwa san abinda kike faɗa ko na kurmance ko kuma ɓacin rai ne yake shirin gusar mani da hankali. ”
“Ko ɗaya wallahi baka kurumceba kuma hankalin ka bai gusheba abinda mama ta faɗi shine abinda kunnuwanka sukajiyo maka don haka tun muna mu biyu ka gaggauta sakina nai gaba salin alin ”.
Ahanah ta kai ƙarshen maganar tana fito daga ɗakinta
“ Banni da shi tunda na iso ai dole ya sauwaƙe maki kije ki auri ɗan arziƙi ɗan mutunci irin albarka, ” mama ce ta amshe zancen tana mai ƙara ɗaure fuska
“ inna lillahi wa inna ilaihir raju'un, habzinallahu wani imal wakil duniya tazo ƙarshe mama yanzu kece kike ikirarin na sauwaƙe ma Ahanah ta tafi soboda na kasance talakka wannan rayuwa sai addu'a bantaɓa zaton haka daga garekuba mama wai me nene acikin rayuwar da za amutu a barta, mene ne acikin duniyar da zata ƙare, bafa zamu dauwwama a nan ba zamu mutu mu iske ubangiji, kuma duk abinda ka aikata shi zaka girba, ko kunsan abinda kuke ƙoƙarin aikatawa haramunne.......
“ Haramo nace Haramo Abbas bafa wa'azi da nasiha nazo jiba kuma ba ɓata lokaci nake son yi ananba ka aikata abinda na umarceka kawai shine sauƙi agareka. " cewar mama cikin ƙaguwa da jiran Abbas ɗin domin batai zaton zai tsaya jayayya da ita ba ta ɗauka da tazo tafiya kawai zatai da ƴarta
Kai gaskiya bazan iyaba idon nasaki Ahanah to wacece zata zauna dani inama zan sami kuɗin yin wani sabon auren bama wannan ba ni ina son matata don haka ba zan saketaba, to meye abinyi kai masu nasiha ko zasuji su haƙura tunda idon rai ya ɓaci hankali baya gushewa , haka yake ta tsara zance a zuciyar sa kafin yace
“ mama Da dama mata baku ɗauki zaman gidan miji a matsayin addini ba, mafi yawan mata kun ɗauki zaman gidan miji a matsayin Bussiness idon ana samun kuɗi buƙata tana biya to za aima miji biyya, idon ko mai gida yana fama da talauci to lokacin ne za' ayi masa fitsara da iyasshege a cikin gida, kamar shi ya ɗaura ma kansa talaucin ba jarabawaba ce daga Allah ba, to kusani idon har baku gyara ba to zai zamo babbar matsala ga rayuwar ku da ta ƴaƴanku don kun rusa gida, 'ya'yan zasu taso da irin wannan ɗabi'ar mummuna ta son abin duniya, don haka ina tunatar da ku kuji tsoron Allah karku shiga jerin matan da duniya ta shiga zuƙatansu wanda da yawansu aure don dukiya suke yinsa,ancire dokokin ubangiji da faɗar manzosa, kuma hakan ba ƙaramin hatsari bane ba acikin Al'umma , kun ɗauka cewa idon mace tai sa'a da gidan kuɗi an gina mata plate Hause an samata tarazo da mabulos da enter loucking da air condision ga tuma tuman kujeru lizars chairs, bata shan ruwa sai faro ko faradeis, an ɗauko mata masu girki da goge tayis da masu pulosion ban ɗaki da masu wanki to a wajan mata wannan itace tai sa'ar miji, mijin yana sallah ko baiyi ba damuwasu bace, ɗan giya ne ko mazinacine ba damuwasu bace, Ɓarawone dukiyar talakawa yake ci ko ɗan fashine ba damuwarku bace, kawunan mutane yake saidawa bakuda matsala da wannan, duk iskancin da zaiyi a duniya ba damuwaku bace indai ya tarama ƴarku dukiyar da zataji daɗi ta sheƙe ayarta ta gwangwaje, ya sawo mata zani mai tsada super wax ko super Holland ko Aura ko siwix lex, tana fantamawa a gidan biki tana faɗin from dubai, shine jin daɗi da dace gidan aure ko, to wallahi idon baku gyara ɗabi'un kuba zai zama from Dubai To Jahannama, duk da sannu zaku kai kanku wuta ”.....
"Ya isa haka Abbas ka saki Ahanah kawai shine yaren da zan gane bana fahimtar komai idai ba yaren takardar sakin ƴataba.
“ Tunda haka kuka zaɓa sai mu zuba mugani idon anayin aure kan aure don wallahi ba zan saki matata ba " yana kaiwa ƙarshen maganar ya fice rai ɓace fiye da ɗazu. ya barsu sake da baki suna kallon ikon Allah, sai mama ta hau faɗin
“ Ai wallahi karya kake Abbas karyarka ta sha ƙarya kayi kaɗan kace bazaka sakamman ƴataba inko kaƙi to zaka kunno gobarar da baka tanaji ruwan kasheta ba a cikin gidan ka, don sai ka raina kanka wallahi. ” takai ƙarshen maganar tana ɗaga murya
Bata tsaya jin kalaman da Ahanah take faɗa mataba ta fice tabi bayan Abbas. bakin titi ta isa tahau mashin na acaɓa zuwa gidan uwar Abbas Hajiya Larai da ke nan gobarau.
Mai mashin na sauketa Gobarau ta bitashi ta hau shiga lunguna har bayan hasumiya inda gidan Hajiya Larai yake
“ Assalama alaikum ”
Mama ta faɗa cikin ɗaga murya tana kutsa kai cikin gidan
“ Amin wa alaikumussalam ” Cewar mahaifiyar Abbas tana mai fitowa daga ɗakin ta kafin ta ɗaura da faɗin “ lale maraba marhabun da manyan baƙi sannunku da zuwa ya hanya ”.