SAWU BIYU

PAGE 25

by @khadijahsulaiman406

SAWU BIYU 

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1

Page 25

Da mugun mamaki yake kallon Bilal,ya haɗiye wani abu mai tauri ya ce"mai ka ce?"
Bilal ya sake maimaita masa ganin kaman ya fi shi rikicewa.
A hankali ya maimaita innalillahi wainna ilaihi raju'un.
"How,like babu mai rai a cikin su?"
"Duk sun rasu,an wuce dasu asibiti for autopsy".
Ganin yadda hankalin shi yayi mugun tashi yasa shi fita daga office ɗin.
Sadauki bai taɓa shiga tashin hankali kamar ranar ba,ya kasa yarda da wannan mummunar labarin.
Matar da ya gani jiya yayi magana da ita tare da yaranta ita ce ta rasu?
Lokaci ɗaya wani ciwon kai ya ziyarce shi,idon shi ya kaɗa don kallo ɗaya za ka masa kasan akwai abinda ke damunsa.
Bai sake shiga tashin hankali ba sai da saƙo ya shigo wayarsa,yasa hannu ya janyo wayar da ƙyar.
"Captain Umar Sadauki...
Mun san zuwa yanzu ka sami labarin mutuwar matar Olatunji da ƴaƴanta Tobi da Bisola.
Gargaɗi na ƙarshe a kan ka Umar,ka fita daga abinda bai shafe ka ba,idan ka nuna taurin kai haka za ka cigaba da samun ire iren waɗannan labaran a ko yaushe,mun bar ka lafiya".
Da wani irin expression yake kallon text ɗin, jijiyoyin kanshi sun fito raɗau.
Yayi jifa da wayar ya tallabe kan shi dake barazanar fashewa,ya miƙe da sauri wani irin jiri ya kwashe shi ya faɗi ƙasa.

**********

A tsorace ta ɗago,ya sake hannun yana kallon cikin idonta ya ce"I like it,ya sunan shi?
Da sauri ta juya ta bar ɗakin da gudu,jiki na rawa ta koma part ɗin Mami.
Mami dake tare da wasu friends ɗinta dake ƙoƙarin wucewa ta bi ta da kallo,bayan sun tafi ta tafi ɗakinta straight don ta san tana can.
Tana kwance kan gado ta zubawa wuri ɗaya ido, ta taɓe baki don aikin kenan,kwata kwata ba ta son motsa jikinta.
"Lafiya na ga kin shigo duk a firgice?"
Ta juyo da sauri ta ce"babu komai Mami".
"Akwai sauran abincin nan ko?Umman ku na hanya,na aika driver ya ɗauko ta".
Ta juyo da sauri ta ce"Umman Bauchi?"
Mami ta zauna kusa da ita ta ce"eh ita,ina kayan ki na Wushe Wushe don na san ƙaramin aikin ki ne ki ce ba ki san inda suke ba".
Ta turo baki ta ce"kai Mami,suna ɗaki".
Firdausi ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama.
"Mami Umma ta iso tana parlour".
Mami ta miƙe da sauri ta ce"shine kika bar ta a can Firdausi,da kin hauro da ita ai".
Zarah ta miƙe ta bi bayanta,Umma na ganinta ta buɗe mata hannu,ta ƙarasa ta rungume ta da sauri.
Mami ta zauna tana fuskantar su ta ce"Sannu da zuwa,kun sha hanya". 
Zarah ta koma gefenta ta zauna,Umma na murmushi ta ce"hanya Alhamdulilah,ya jama'a,mun same ku lafiya?"
Mami ta ce"Alhamdulilah,Zarah tashi ki shiga da kayan ɗaki ta samu ta huta".
Mami ta miƙe ta ce"mu je ki huta kin sha hanya".
Ba tayi musu ba ta miƙe ta bi bayan su.

***********

Shigowar Emmanuel office ɗin riƙe da file ya tarar da shi kwance a ƙasa ba numfashi.
Yayi wurgi da file ɗin ya kwalla wani ƙara hankali tashe,ya ƙarasa inda yake ya hau jijjiga shi yana kiran sunan shi amma ko motsi bai yi ba.
Da sauri ya fita daga office ɗin,a hanya suka haɗu da Bilal da Adebayo,nuna musu ƙofar office ɗin kawai yake da hannu.
Da sauri Bilal ya bangaje shi ya tura ƙofar ya shiga suka bi bayan shi,babu ɓata lokaci suka ciccibe shi da ƙyar suka nufi clinic.
Ƙarfe huɗu na yamma ya buɗe ido,ya sa hannu ya tallabe kan jin irin nauyin da ya masa.
Yana ƙokarin tashi ya ji an dafa kafaɗarsa,sai a lokacin ya lura da inda yake.
"Ka koma ka kwanta Falcon,Dr ya ce kana bukatar hutu".
Lumshe ido yayi yana sake tunano fuskar matar da ƴaƴanta,wani siririn hawaye ya gangaro ta gefen idon shi,
da mamaki Bilal ya zuba mishi ido,anya wannan zafin ciwo ne ko dai da wani abu.
"Falcon?"
Ba tare da ya buɗe idon ba ya ce"da ban je wurin ta ba maybe da har yanzu ta na da rai".
A little bit confused ya ce"ban fahimce ka ba?"
"Jiya na tafi gidan Ola,nayi magana da matarsa,na ga yaranta guda biyu".
Ya tashi ya zauna idon nan jazur ya ce"dan Allah ka sanar dani mafarki nake Bilal,dan Allah".
Lokaci ɗaya ƙirjinsa ya buga,ya matso kusa dashi ya riƙe kafaɗarsa ya hau jijjiga sa ya ce"why,me ya kai ka,me yasa ba ka faɗa min ba why?"
Sadauki ya riƙe kan shi jin zai tarwatse ya ce"i don't know,nima regretting na keyi Bilal,dan Allah ka tashe ni a wannan baccin".
Shigowar Dr ya sa Bilal ya koma gefe,yanayin da ya tarar da Sadauki ya sa ya kalli Bilal ya ce"why officer,I explained his condition to you,he dont need all this stress".
Ya sassauta fushin sa ya ce"I'm sorry".
Sadauki ya kalli Dr ya ce"i want to go home please".
Da sauri ya girgiza kai ya ce"I'm sorry you  can't do that Captain,sai dai ko zuwa gobe".
Bai sake cewa komai ba ya koma ya kwanta,Dr ya cire mishi drip ɗin ya ce"za ka iya yin Sallah,idan ka idar sai a mayar Sir".
Ya miƙe da kyar kamar wanda ya sha ya bugu ya shiga toilet,Bilal ya sauke numfashi ya kwantar da kanshi.
Bayan ya fito ya shinfiɗa darduma ya ta da sallah,Bilal ya cigaba da kallon shi har ya idar da sallollin dake kanshi.
A hankali ya ce"I'm very sorry,I overreacted".
Yayi guntun murmushi ya ce"it's alright,I understand".

**********

Bayan an idar da sallar Isha aka fara shirye shiryen tafiya Wushe Wushe,Zarah na kwance a ɗakin Mami aka turo kofar,ta ɗaga kai da sauri.
Ganin Mami ya sa ta tashi ta zauna da sauri tana turo baki,Mami ta nuna mata hanyar ƙota ta ce"zo ki fita".
Ta sauko ta ɗauki hijabinta dake gefe ta fita Mami ta bita da harara.
Extra room dake kusa da ɗakin su ta tura ta shiga,Aunty Zeenah da Aunty ke zaune ko waccen su ta sha kwalliya kamar ka sace su ka gudu sanye da kayan gargajiya na kanuri,sai make up artist dake yiwa sauran ƙawaye daga can gefen ɗakin.
Aunty Zeenah na ganinta ta miƙa mata hannu,ta kama hannun ta shiga jikin ta ta kwanta kamar wata mage.
Naima ta taɓe baki ta harare ta,Zarah ta kalleta ƙasa ƙasa tayi dariya.
"Kika min rashin kunya duka za ki ci".
Ta turo baki ta ce"kin ganta ko Aunty Zeenah,ni fa babu abinda na ce".
"Ki ce mana idan ban fasa bakin ba".
Aunty Zeenah ta riƙe hannun Zarah ta ce"bana son neman magana Zarah na san halin ki,wuce ki shiga wanka ki zo a miki kwalliya".
"Bana so Aunty Zeenah"
Aunty Zeenah ta ce"to ai shikenan,wuce kiyi wanka,kayan ki na ɗaki".
Ta miƙe ta fita a ɗakin ta koma nasu ta shiga wanka,har aka fara fita Zarah na ɗaki bata fito ba kamar mai canza fata.
Lokacin da ta fito duk an gama tafiya da motocin amare,ta shirya cikin dogon rigar atampa ta fito riƙe da mayafinta.
Dai dai nan Hajja ta fito ta cakare cikin wani Hollandaise,ta yafa mayafi mai uban stone sai walwali take kamar ita ce amaryar Abdallah biye da ita.
Yana ganin Zarah ya kafa mata ido kamar ko yaushe, Hajja da ke bashi labari jin shiru babu amsa ya sa ta juya,ganin wacce ya ke kallo ya sa ta taɓe baki ta ce"dallah wuce mu tafi,ka saki baki da hanci saboda ka ga mace".
Ya juyo ya watsa mata harara ya ce"sai dai ki tafi a ƙafa don babu inda zan kai ki".
"To in banda dole mai zai sa in shiga motar ka ni Fatuu,tuƙi kamar wani mahaukaci Mallam,ka ƙara gaba".
Ya jinjina kai ya bar wurin, Zarah na ƙoƙarin komawa ciki don har wani daɗi take ji babu mota ya ce"ki zo ki shiga".
Ta ɓata fuska don har ga Allah ya fara bata haushi,shi bai san irin tsanar da ta mishi bane halan.
"Ko sai na ɗauko ki da kaina?"
Ta watsa mishi harara ƙasa ƙasa ta yafa mayafin ta zaga ta buɗe front seat ta shiga,ya figi motar da wani irin speed ya wuce gaban Hajja, kamar zai wuce sai kuma ya dawo ya tsaya dai dai saitinta ya sauke glass ya ce"ba don halin ki ba".
Ta ɗauke kai ta ce"Kai ma ka san na wuce wulaƙanci Abdullahi,ba zan shiga ba,na yafe".
Ya buɗe ƙofa ya fito ya ce"ko ki shiga ko in ɗauke ki kin san zan aikata".
Ta watsa mishi harara ta buɗe back seat ta shiga sai cika take tana batsewa.
Lokacin da suka isa har an fara program ɗin,Hajja ta fincike ƙofa ta fita rai ɓace,Allah Allah kawai take su haɗu da Oum ta sanar da ita abinda ɗanta ya aikata.
Zarah ta kai hannu kan ƙofa yayi saurin sa lock,da sauri ta juyo ta kalle shi hankali tashe,ya ɗage mata gira ya kwantar da seat ya kwanta.
Wani ɗan iskan harara ta watsa mishi,ta juya ta sake kallon waje,ganin sai bidiri ake yasa ta ce"ka buɗe min dan Allah".
Ya buɗe ido da kyar ya ce"magana kike?"
"Dan Allah ka buɗe min in fita".
Banza ya mata ya koma ya kwanta,ta watsa mishi wani banzan kallo ta ɗauke kai.
Bata sake cewa komai ba har kusan minti talatin,ya buɗe ido ya zuba mata su kamar zai haɗiyeta.
Wani irin kyau take dashi mai daukar hankali.
Ƙarfe shida saura ya buɗe mata kofa,ko kallon shi ba tayi ba ta fita,ya shafa kai ya bi ta da kallo ya ce"beautiful".
Ko da ta shiga an gama program ɗin ana daukar hotuna,takaici kamar ya kasheta,haka dai ta shiga rai ɓace.
Ko da wasa ba ta kalli inda yake ba bayan sun fito,da sauri ta shiga motar amare.
Da daddare Mami ta shiga ɗakin da aka sauke Umma,ta zauna kan kujera ta ce"wai ni kam kun yi magana da Faruq kuwa?,tun ɗazu nake kiran wayarsa a kashe".
Umma tayi murmushi ta ce"wayar tawa a kashe take".
"Ai da kin yi magana da ansa miki ita a caji,maybe ya yi ta kiran wayar taki a kashe,kawo mu gani".
Ta miƙe ta buɗe handbag ɗinta ta ciro wayar ta miƙa mata,Mami ta miƙe ta ce"ina zuwa".

**********

Gari na wayewa ya kalli Dr ya ce"Please ka sallame ni,idan ba ka sallame ni ba za ka neme ni ka rasa"
Dr yayi dariya ya ce"zan sallame ka Captain,kar ka gudu ka barni da allurai na,but sincerely speaking, wannan ciwon kan naka ya fara yawa,idan stress ne ka nemi hutu ka huta sosai,idan kuma damuwa ne dan Allah ka rage shi saboda it's not good for your health".
"Thank you".
Ya miƙa mishi hannu ya ce"za ka iya tafiya,Allah ya ƙara sauƙi".
Dai dai nan Bilal ya shigo,bayan sun gaisa da Dr ya fita ya bar ɗakin,Bilal ya kalli Sadauki ya ce"Brigadier ya ba ka hutu,ya ce ka huta na sati ɗaya".
Ya wani kalle shi ya ce"na aike ka ne?"
"Saƙo aka bani,ka same shi ka sanar da shi ba ka buƙata".
Haka aka dinga shigowa gaishe shi, saboda baccin da ya dinga yi jiya shi yasa bai samu gaisawa da kowa ba.
Idayat ta shigo ɗauke da basket ɗin abinci,bayan ya amsa gaisuwarta ya miƙe ya fita.
Ademola, Emmanuel da Bilal dake ɗakin duk suka bishi da kallo,Bilal ya karɓi basket ɗin ya ce"thank you Adeyemi,kin ceci gwauraye,muna isa gida zamu gama dashi".
Tunda suka isa gida yake bacci saboda har lokacin magungunan basu gama sakin sa ba,sai dab da azahar ya farka,ya shiga ya watsa ruwa ya ɗauro alwala ya fito.
Bayan ya idar da salla ya koma bakin gado ya zauna ya kunna wayarsa, messages ne suka dinga rige rigen shigowa daga abokan aikin sa da basu sami damar ganinsa ba.
Kiran wayar Mami ya shigo wayar,ya ɗan rintse ido don sai lokacin ya tuna da maganar biki kuma Umma ta sanar dashi tana nan zuwa.
Yayi sallama ya ce"Mami barka da rana".
"Haba Faruq, ina ka shiga kwana biyu sai kiran layin ka nake a kashe?"
"Ki yi haƙuri Mami,aiki ne ya min yawa kwana biyu har wayar ta mutu ban sani ba".
Ta sauke numfashi ta ce"to shikenan ya aikin?"
"Alhamdulilah Mami".
"Ga Ummanku a nan,tun jiya ta iso".
"To Mami zan shigo In Sha Allah".
Bilal ya turo ƙofar ya shigo riƙe da plate ɗin abinci,rice and stew ne da beef,ya ajiye kusa dashi ya ɗauko ledar magani ya ajiye".
Ya bi abincin da kallo ya ce"ina ka sami wannan abincin?"
"Mallam idan za ka ci abinci ka ci,bana son iyayi".
"You don't have respect Bilal,sai na sa an kulle min kai a guardroom za ka daina min rashin kunya".
Ya miƙe da sauri ya sara mishi ya ce"sorry Sir".
Ya shafa beard ɗin shi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce"you're mad".
Bilal yayi dariya ya koma ya zauna ya ce"dole in yi biyayya kar in yi kwanan cell".
Ya ɗauki plate ɗin abincin yayi bismillah ya fara ci.
Bilal yayi gyaran murya ya ce"so,did you get any information from her?"
Sadauki ya ɗan zuba mishi ido,ya ajiye spoon ɗin hannun shi ya ƙurawa waje ɗaya ido.
A hankali Bilal ya ce"I'm sorry".
Ya kalle shi yayi murmushi ya ce"Bilal ! I regretted going to that house,maybe, just maybe da ban je ba da har yanzu tana raye tare da yaranta,bata gama warkewa daga mutuwar mijinta ba Bilal".
Ya dafe kai ya ce"my bad".
Wani mugun tausayinsa ya kama sa,ya tashi ya karasa kusa dashi ya dafa kafaɗarsa ya ce"kar kayi saɓo,ko ka je ko ba ka je ba kwanan ta ya ƙare a wannan duniyar,kai musulmi ne ka san da hakan".
Ya ɗan ɗago ya ce"thank you".
"Ɗauki abincin ka ci Please".
"Babu wani information da ka samu kenan?"
Without looking at him ya ce"ban samu komai ba,na so komawa ko da zuwa wani satin ne sai ga wannan labarin".
Bilal ya jinjina kai alamar gamsuwa,Sadauki ya ce"an samu labari daga asibitin ne?"
"Ban sani ba gaskiya,so nake in kira Emmanuel in tambaye sa ko sun ji wani labari".

Book 1 ya kusa ƙarewa which is free,Book 2 na kuɗi ne.



Oum Rijalain 
***