A NEW BEGINNING
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER THIRTY-THREE: 33
A NEW BEGINNING
JIDDAAH BARKUM
————
Hasken safiya ya gauraye da sanyin iska mai daɗi, yana ratsawa ta cikin labulen ɗakin Inteesar, ta farka da wani sabon yanayi da ya gauraya da farin ciki, fargaba da kuma matsananciyar kunyar tuno kalaman Aliyu na daren jiya, zuciyarta ta kwana tana rera waƙar ƙauna, kalamansa sun zama tamkar magani da ke ratsawa cikin jininta da jijiyoyinta, kafin ta sauko daga kan gadon, wayarta ta soma ruri, sunansa ne ya bayyana a screen ɗin, ta haɗiye miyau, sannan ta ɗaga wayar cikin muryar bacci mai ɗauke da shagwaɓa, “Assalamu alaikum,” daga ɗayan ɓangaren, Aliyu ya saki wani daddadan murmushi mai cike da shauƙi da nasara, “Wa alaikumus salam, good morning, Mrs. Aliyu-to-be,” wani irin jiri na daɗi ya ɗauke ta, ta ja bargo ta rufe fuskarta saboda tsananin kunya, “Haba ni dai… Don Allah, ka daina faɗin haka,” ta faɗa cikin tsantsar shagwaɓa, ita kanta ba ta san lokacin da ta fara yi masa hakan ba, shi kuwa Aliyu, kamar ya narke ne saboda jin muryarta, “Meye na jin kunya bayan kin riga kin zama tawa?” Ya tambaya cikin wata murya mai taushi, “Ba zan ɓata lokaci ba, Intee, na yi miki alƙawarin zuwa gidanku ta hanyar da ta dace, kuma yanzu zan cika wannan alƙawarin, ina son na fara shirye-shiryen zuwa na gana da Daddy domin neman izininsa kafin na turo magabata na,” nan take gabanta ya yi wani irin mugun faɗuwa, tsoro ya daki ƙirjinta, Daddy bai gama murmurewa sosai ba, ga kuma yadda abubuwa suka kasance tsakaninta da Yaya Abubakar, sannan har yanzu akwai fargabar zama mace ta uku da ta manne mata a zuciya, ta yi ƙoƙarin daurewa kafin ta ce, “Uhmm… Inaga a ɗan jira tukuna, a bi komai a hankali, don Allah,” “Kada ki damu, komai zai tafi cikin tsari da mutunci, babygirl,” ya ba ta ƙarfin gwiwa, ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta amsa cikin sanyin murya, “Toh,” bayan sun ɗan ƙara magana, suka yi sallama, ta kashe wayar.
Bayan sun gama waya, Humaira ta kira ta ta hanyar video call, ganin yadda fuskar Inteesar take annuri, duk da cewa akwai alamun damuwa a tare da ita, Humaira ta ɗan yi murmushi kafin ta ce, “Intee, na san dukan rudanin da ke ranki game da zama mace ta uku, but listen to me, yanzu lokaci ne na ajiye fargaba a gefe guda, ki koma ga Allah, ki yi Istikhara, ki nemi zaɓin Allah, shi ne mafi alkhairi kuma zai ba ki nutsuwar da ba za ki samu daga tunanin ɗan Adam ba,” kalaman Humaira sun sauka a zuciyar Inteesar cikin sanyaya rai, ta gyada kai, tana jin daɗin samun yar uwar kirki da ke ƙoƙarin nuna mata hanyar da za ta bi cikin wannan yanayin.
A ranar, Daddy ya sami ƙarfi sosai, har aka taimaka masa ya fito babban falon gidan, ya zauna a kan doguwar kujera, yayin da Mommy Haleema da sauran ‘ya’yansa ke kula da shi, Inteesar ta fito daga ɗakinta da fuskarta cike da annuri da farin ciki, kowa a falon ya ɗauka cewa farin cikin samun sauƙin lafiyar Daddy ne kawai ya sa fuskarta ke haskakawa, ta zauna kusa da ƙafafun Daddy, tana masa hira cikin shagwaɓa, tamkar tsohuwar Inteesar ɗin da suka sani wadda take cika musu zuciya da farin ciki duk lokacin da suka zauna tare, amma akwai mutum ɗaya da ya fi kowa sanin Inteesar daki-daki, Yaya Abubakar, yana zaune a kujerar da ke kallonta, ya kafa mata idanunsa masu kaifi irin na mikiya, ya lura da duk canje-canjen da suka bayyana a tare da ita, tana yawan satar kallon screen ɗin wayarta da ke gefenta, tana kallon wayar, sannan ta yi murmushi ita kaɗai, yanayinta gaba ɗaya ya sauya zuwa na wata daban, mai cike da shauƙi da annuri, Abubakar ya yi murmushi a ransa, ya yi farin cikin ganin ƙanwarsa tana murmushi bayan kwanakin wahala da ta sha, amma duk da haka, ɗacin da ke zuciyarsa da kuma tsoron ko wanene wannan Aliyu ɗin ya ƙara ruruwa, wane ne wannan Aliyu ɗin? Yana da kyau na hanzarta kiran Sagheer in ji abin da ya gano game da binciken da na sa shi yi, ya faɗa a ransa, idanunsa cike da tuhuma yayin da yake bin duk motsinta, ya riga ya fara bincike a ɓoye ta hannun wasu abokansa na hukuma domin gano ainihin asalin Aliyu, inda yake zaune da kuma irin harkar da yake yi, kafin Inteesar ta yi nisa a cikin wannan soyayyar.
Bayan wucewar dogon lokacin rana, sanyin yammacin ranar ya zo da wani irin daɗi na musamman, a babban compound ɗin gidan, iskar yamma tana kaɗawa a hankali, tana girgiza ganyen bishiyoyin da ke kewaye da wajen, a daidai wannan lokacin, Yaya Adam, wanda yake shirin komawa Lagos, da Yaya Umar, wanda shi ma yake shirin komawa Abuja, sun shiga daidaita kayansu da shirye-shiryen tafiya, sun ga jikin Daddy ya yi sauƙi, don haka suka yanke shawarar komawa gida, shi kuwa Yaya Abubakar, yana nan yana taimaka musu wajen shirya komai domin raka su filin jirgin sama, saboda za su bi jirgin dare (night flight), Nana da Inteesar suna zaune a kan kujerun da ke cikin compound ɗin, suna shan iska cikin nishaɗi, Nana ta juyo ta kalli Inteesar, fuskarta ɗauke da murmushin ƙauna irin na ’yan uwantaka, “Toh, Auta, tunda dai gashi Alhamdulillah, jikin Daddy ya yi sauƙi, yanzu kuma kin nutsu kin dawo cikin hankalinki, ya kamata dai ki yi haƙuri ki zo mu koma FCT tare, lectures na can suna tafiya sosai, remember, this is your final year,” Inteesar ta juyo ta dubi Nana, fuskarta ta sake gaurayewa da wani daddadan murmushi wanda a kwanakin nan ya zama tamkar sitika a fuskarta, ta gyara zamanta cikin natsuwa, sannan ta ce, “Zan dawo fa next week, kada ki damu,” Nana ta zura mata idanu, tana mamakin sauyin da ta gani a tare da ƙanwarta, “Inteesar, wannan murmushin naki yana ba ni mamaki wallahi, kawai sai kika dawo smiling princess cikin ’yan kwanaki kaɗan, anya babu wani abu kuwa?”
Inteesar ta sake yin wani gajeren murmushi wanda ya kasa ɓoye farin cikin da ke zuciyarta, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta, kafin ta ɗago cikin muryar raɗa, “Nima haka na tsinci kaina… Someone is taking good care of my heart,” Nana ta fashe da dariya mai cike da farin ciki da nishaɗi, ta tafa hannayenta, “Awww! Really? Lallai Auta, akwai labari kenan!” Ta faɗa tana kashe mata ido ɗaya, Inteesar ta zaro idanu, tana murmushin kunya ita ma, Nana ta matso kusa da ita, ta ɗan sunkuyar da kanta kaɗan, “Uhmm… Wannan friend ɗin naki ne ko? I guess,” Inteesar ta kasa daurewa, kawai sai ta saka dariya mai daɗi, Nana ma ta taya ta, sannan ta ƙara rage muryarta tana kallon Inteesar, “Uhmm… A friend before a lover,” duka suka saka dariya a tare.
Da dare, duk masu tafiya suka yi sallama da mutanen gidan, suna yi wa Daddy addu’ar samun cikakkiyar lafiya mai ɗorewa, bayan sun gama sallama, suka kama hanyar zuwa airport, da dare, bayan Inteesar ta fito daga bathroom ta yi wanka, ruwan ɗumin da ta yi wankan da shi yana ɗiga kaɗan daga jikinta, yayin da ƙamshin sabulunta mai daɗi ya cika ɗakin, tana ɗaure da wani farin towel mai laushi daga saman ƙirjinta zuwa daidai cinyoyinta, a hankali ta taka zuwa gaban dogon mirror ɗinta, ta tsaya cak, tana kallon hoton kanta, na wasu daƙiƙu…
Inteesar Kabeeru, princess ɗin Alhaji Kabeeru, yarinyar da aka raina cikin gata da tsantsar ƙauna, wadda kyawunta yake da wani irin natural elegance da ba ya buƙatar ƙarin ado domin ya fito, akwai wani irin soft feminine charm a tare da ita, wanda yake sa fuskarta ta zama abin kallo ba tare da ta yi wani ƙoƙari ba, Allah Ya yi mata wata irin fata ta musamman, mai launin chocolate da ɗan gaurayen caramel, fatarta tana da warm caramel glow, mai santsi da sheƙi na halitta, irin fatar da hasken ɗaki kaɗai yake iya ƙara fito da kyawunta, baƙaƙen fata za su iya kiranta fara saboda hasken fatarta, amma a cikin fararen mata ba za ta kasance cikin masu tsananin fari ba, wata irin beautiful medium-brown complexion ce mai ɗaukar ido, her skin was naturally radiant, ba wai don wani cream ko makeup ba, a’a, haka Allah Ya halicce ta, da wani irin haske da ya dace da launin fatarta, ba gajera ba ce, ba kuma doguwa sosai ba, tana da madaidaicin tsayi da ya ƙara mata elegant appearance, tsayinta da yanayin jikinta suna haɗuwa cikin wani irin tsari mai kyau, wanda yake ƙara mata kamannin cikakkiyar mace, jikinta kuwa… Ba za a ce siririya ba ce, ba kuma za a ce mai kiba ba ce, tana da a naturally curvy figure, mai daidaitaccen tsari da armashi, kugu da sauran sassan jikinta sun yi daidai da juna, suna ba ta wata irin soft feminine silhouette mai jan hankali ba tare da ta rasa kamannin mace mai mutunci ba, tabbas… Inteesar ta kai mace, ba wai kyawunta ya tsaya a kan siffar jikinta kawai ba ne, akwai wani irin graceful aura a tare da ita, wanda yake sa ta yi kyau ko da ba ta yi ƙoƙarin ƙawata kanta ba, fuskarta mai siffar oval tana ɗauke da wani irin taushi da natsuwa, fuskarta ba ta da tsananin kaifi, sai dai dukkan sassan fuskarta sun haɗu cikin perfect harmony, idan ka kalle ta, za ka ga kyawun da yake da sauƙin fahimta amma mai wahalar mantawa, girarta baƙaƙe ne, masu cika sosai, kuma sun zauna daidai a saman idanunta, suna ƙara musu kyau, gashin idanunta kuwa… Dogaye ne, masu kauri da lanƙwashewa, irin waɗanda suke ƙara fito da kyawun idanunta ko da ba ta shafa komai ba, and her eyes? Su ne abin da ya fi ɗaukar hankali a fuskarta, manyan idanunta masu zurfi suna ɗauke da wani irin soft, captivating look, idan ta yi shiru tana kallon mutum, akwai wani abu a cikin idanun nata da yake sa ka yi tunanin tana ɓoye wani sirri a zuciyarta, wani lokaci suna nuna innocence, wani lokacin kuma suna ɗauke da wani irin unintentional charm da ita kanta ba ta san tana da shi ba, sexy eyes, haka Humaira take kiransu, tana tsokanarta a duk lokacin da suka haɗu, hancinta madaidaici ne, ba babba ba, ba ƙarami ba, irin wanda ya dace da fuskarta tamkar an tsara shi ne domin ya zauna a wurin, sai leɓɓanta… Ƙaramin bakinta yana ɗauke da leɓɓa masu kyau, masu laushi da wani irin natural pink tint, ko ba ta shafa lipstick ba, leɓɓanta suna da nasu kyawun da ya dace da sauran sassan fuskarta, naturally pretty, without even trying, dogon gashinta baƙi mai laushi ya kai har gadon bayanta, har yanzu yana ɗan jike bayan wanka, yana manne a bayanta, wasu ɗigon ruwa kuma suna gangarowa a hankali zuwa kafaɗunta, ta karkatar da kanta kaɗan tana ci gaba da kallon kanta a madubi, a hankali, wani ɗan murmushi ya bayyana a gefen leɓɓanta, she was beautiful, amma ba irin kyawun da yake neman attention ba ne, kyawunta yana da wani irin quiet elegance, wanda yake sa mutum ya sake kallonta ba tare da ya shirya yin hakan ba, a beauty that felt effortless, a charm that was entirely hers, ta yi murmushi kaɗan, tana girgiza kanta kamar tana mamakin yadda ta zauna tana kallon kanta haka, amma murmushin bai daɗe ba, domin nan take wani tunani ya daki zuciyarta, wannan ita ce… Inteesar Kabeeru, the princess of Alhaji Kabeeru’s home, yarinyar da aka raina cikin soyayya da gata, wadda ba a taɓa barinta tana jin kamar ba ta da muhimmanci ba, wadda ta saba da samun kulawa daga iyalinta, kuma ta san cewa akwai mutanen da za su iya yin komai domin ganin murmushi a fuskarta, amma yanzu… Ita ce za ta shiga gidan da akwai mata biyu kafin ita, ita ce za ta zama wife number three, murmushin da ke fuskarta ya dusashe a hankali, ta sauke idanunta, tana jin wani irin nauyi ya mamaye zuciyarta, “Ya Allah…” Ta furta cikin sanyin murya, “Wace irin rayuwa ce nake shirin shiga? Anya zan iya kuwa?” Hoton Aliyu ya bayyana a zuciyarta, murmushinsa, muryarsa, kalaman alkawarinsa, da yadda yake kallonta cikin wani irin yanayi da yake sa ta ji kamar ita kaɗai yake gani a wannan lokacin, the way he made her feel special was becoming her sweetest weakness, wani irin dumi ya ratsa zuciyarta, ta lumshe idanunta a hankali, tana tuna kalaman da ya yi mata a daren jiya, ta so ta yi imani da shi, ta so ta yarda cewa komai zai yi kyau, amma wani ɓangare na zuciyarta har yanzu yana tsoron abin da ke gabanta, domin kyawunta ba zai iya kare ta daga ciwon zuciya ba, kuma gata da ta saba da shi ba zai tabbatar mata da cewa rayuwar aurenta za ta kasance mai sauƙi ba, ta sake buɗe idanunta, tana kallon reflection ɗinta a madubi, a princess she had always been, a woman she was becoming, amma shin za ta iya rayuwa a matsayin mace ta uku, ta raba mutumin da take ƙauna da wasu mata, ba tare da ta rasa kanta a cikin wannan soyayyar ba? Da ƙyar ta sauke numfashi a hankali, kafin ta juya daga gaban mirror ɗin.