Chapter 9
by @authorrukie
Gwaggo ta ɗora hannu a ƙugu, tana kallon Baba cikin fushi.
“Ni dai gaskiya nake faɗa maka, Malam. Duk lokacin da za ka kawo wa Rammu wani abu, sai ka sa sauran yaran nan suna kallonta kamar ita ce kaɗai ’yarka. To, me ta fi su ne?”
Baba ya ɗago kansa a hankali, ya kalleta da wani irin kallo da ban iya fassara ma’anarsa ba.
“Tapito, me ya sa duk abin da na yi wa yarinyar nan yake damunki haka? Na ba ta abu ne saboda na ga dama. Shin dole sai na nemi izininki kafin in ba ɗiyata wani abu?”
Da jin kalaman Baba, na ɗan ɗago kaina. Ban taɓa jin ya yi wa Gwaggo magana irin wannan a kaina ba.
Gwaggo ta zaro ido.
“Ɗiyarka? Ai dukansu ’ya’yanka ne! Amma ita Rammu, kullum kai ne za ka tuna da ita. Ka kawo mata rogo, ka ba ta kuɗi, yanzu kuma kana kiranta a ɗaki kana ba ta wani abu. Ni dai ba zan yarda da wannan bambancin ba!”
Baba ya sauke numfashi, sannan ya ce, “To, me kike so in yi? In daina ba ta komai saboda kina jin haushi?”
Na ji gabana ya faɗi. A raina ina roƙon Allah Ya sa wannan magana ta ƙare lafiya. Ban san cewa abin da Baba ya ba ni zai zama sanadin wannan rikicin ba. Har na fara nadamar karɓar abin da ya miƙo min, duk da cewa ban yi wani laifi ba.
Gwaggo ta juyo ta kalle ni.
“Ke kuma, me kike tsaye kina sauraronmu? Fita daga nan!”
Ban jira ta sake maimaitawa ba. Na sunkuyar da kai na ce, “To, Gwaggo,” sannan na fice daga ɗakin.
Ina fita, sai na ji ta sake magana da Baba, amma ban iya jin abin da take faɗa ba.
Na nufi ɗakinmu a hankali, ina riƙe da abin da Baba ya ba ni. Hawaye sun fara taruwa a idanuna, amma na share su da gefen mayafina.
Ya Allah, me ya sa duk lokacin da na ji kamar na samu ɗan farin ciki, sai wani abu ya biyo baya ya ɓata min shi?
Na zauna a gefen katifata, na buɗe tafin hannuna ina kallon abin da Baba ya ba ni. Amma tunanina ya tafi wani wuri daban.
Shin da gaske Baba yana ƙaunata ne, ko kuwa akwai wani dalili da ya sa yake nuna min wannan kulawar a wasu lokuta?
Ban san amsar ba. Abin da na sani kawai shi ne, ni ma ina son a riƙa ɗaukar raina da muhimmanci. Ina son in ji cewa ni ma ɗiya ce da ta cancanci kulawa, ba wadda za a riƙa kallonta kamar ta yi laifin kasancewa a gidan ba.
Ina cikin wannan tunanin ne na ji takun sawu a bakin ƙofar ɗakinmu.
Na ɗago kai.
Kuluwa ce ta shigo.
Kuluwa tana ɗaya daga cikin yaran Mama, kuma jininmu ya haɗu. Tun muna ƙanana muke da fahimtar juna sosai. Allah Ya sa tana sona, domin idan wani abu ya faru da ni, ko ta ga ana min wani abu da bai dace ba, takan nuna rashin jin daɗinta.
Sau da yawa, idan aka ba ni wani aiki, Kuluwa takan labe ta biyo ni domin ta taimaka min. Wani lokaci ma ba sai na nemi taimakonta ba; da kanta take zuwa ta tayani, musamman idan ta ga aikin ya yi min yawa.
Amma duk lokacin da Mama ta gan ta tare da ni, sai ta fara yi mata faɗa. Wani lokaci har takan ce mata ta daina bin sawuna ko taimaka min kamar ni ce ƙanwarta ita kaɗai.
Kuluwa kuwa, irin yaran nan ce da ba sa saurin jin magana. Idan Mama ta yi mata faɗa, takan yi shiru a gabanta, amma da zarar Mama ta juya, sai ta dawo wajena kamar ba abin da ya faru.
Wannan halin nata yana sa ni ƙara jin sonta, domin duk da yadda ake kallona a gidanmu, Kuluwa ba ta cika barina ni kaɗai ba. Idan na shiga damuwa, takan zauna kusa da ni, ta yi ƙoƙarin ganin na saki fuska.
A wasu lokutan nakan ji kamar ita ce kaɗai take fahimtar abin da nake ji a zuciyata, ba tare da na yi mata dogon bayani ba.