THE APPROVAL
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER THIRTY-FIVE: 35
THE APPROVAL
JIDDAAH BARKUM
——-
Bayan tafiyar Yaya Adam zuwa Lagos da kuma komawar Yaya Umar Abuja, gidan Alhaji Kabeeru ya sake komawa cikin nutsuwa, Alhamdulillah, jikin Daddy ya ƙara samun sauƙi sosai, ko da yake Mommy Haleema da sauran mutanen gidan sun hana shi yawan zirga-zirga, hakan bai hana shi fitowa babban falo da safe ko kuma zama a compound da yamma yana shan iska ba, Inteesar kuwa… Tun bayan amincewarta da Aliyu, wani sabon annuri ya zauna a fuskarta, murmushinta ya dawo, shagwaɓarta ta dawo, har Daddy kansa ya yi mamakin yadda Princess ɗinsa ta sake zama tsohuwar Inteesar, amma duk lokacin da ya tambayeta dalilin farin cikinta, sai kawai ta rungume shi tana dariya, “Daddy, ai saboda ka samu lafiya ne,” shi ma ya yi dariya yana shafa kanta, “Princess ɗina,” amma mutum ɗaya bai daina kallonta da idon nazari ba, Yaya Abubakar, tun ranar da ya tura Sagheer ya binciko masa Aliyu, hankalinsa bai kwanta ba, sai dai rahotannin da ya samu duk sun nuna abu guda, Aliyu mutum ne mai mutunci, mai addini, mai kuɗi, mai cikakken suna, mai kula da iyalinsa, kuma babu wata matsala da aka taɓa ji a kansa, Abubakar ya sauke numfashi a hankali, ko da yake bai gama sakin zuciyarsa ɗari bisa ɗari ba, amma bai samu wani dalilin da zai sa ya hana Aliyu kusantar ƙanwarsa ba, a wani ɓangaren kuma… Aliyu yana zaune a office ɗinsa, gabansa na bugawa kamar na ƙaramin yaro, duk irin manyan yarjejeniyoyin da yake shiga, duk irin manyan mutanen da yake haɗuwa da su, babu abin da ya taɓa sanya shi cikin irin wannan tashin hankalin, ya kalli agogon hannunsa, sannan ya ɗan yi murmushi shi kaɗai, “Aliyu…” ya faɗa wa kansa, “Ka nutsu,” amma ina! Zuciyarsa ta ƙi nutsuwa, domin yau ba kasuwanci zai je yi ba, ba taro zai je ba, yau zai je wajen mahaifin matar da yake so.
Da misalin ƙarfe huɗu na yamma, wata baƙar mota mai tsada ta tsaya a harabar gidan Alhaji Kabeeru, Aliyu ya ɗauki wayarsa ya kira Inteesar, da ta ɗaga, sai ya ce cikin sanyin murya, “Ina waje,” cikin sarkewar murya ta amsa, “Toh, ka shigo, Daddy ya san da zuwanka,” bayan sun yi sallama, ya kashe wayar, ya danna horn, aka buɗe masa gate, ma’aikatan gidan suka yi saurin karɓar baƙon cikin girmamawa, a lokacin, Daddy yana zaune a babban falo tare da Yaya Abubakar da Khalil, suna hira cikin annashuwa, Khalil ne ya fara hango shi, “Baƙon ya ƙarasowa, Daddy,” Daddy ya ɗago kansa, a hankali Aliyu ya shigo, sanye yake da farar shadda mai tsananin kyau, hula a kansa, agogo mai tsada a hannunsa, amma duk da waɗannan abubuwa, babu alamar girman kai ko kaɗan a tattare da shi, da sauri ya durƙusa cikin girmamawa, “Assalamu alaikum,” “Wa alaikumus salam,” Daddy ya amsa cikin fara’a, Aliyu ya gaishe su ɗaya bayan ɗaya, har Yaya Abubakar ya ji daɗin yadda mutumin yake magana cikin nutsuwa da ladabi, “Zauna mana,” Daddy ya faɗa, “Na gode, Daddy,” Aliyu ya zauna cikin girmamawa, sai dai tun daga yadda yake murɗa yatsunsa, Khalil ya fahimci cewa baƙon nasu yana cikin tashin hankali, Khalil ya yi murmushi a ransa, lallai, soyayya ta iya saka mutum cikin halin da bai saba da shi ba, Aliyu ya ja numfashi, sannan ya sauke idanunsa ƙasa cikin ladabi, “Daddy…” “Ina fata ba zan zo a lokacin da bai dace ba,” “A’a,” Daddy ya amsa, “Ina sauraronka,” Aliyu ya haɗiye miyau, “Daddy, na zo ne cikin girmamawa da mutunci, kuma ban zo domin in ɓoye komai ba, na zo ne domin neman izininku,” Abubakar ya ɗan gyara zamansa, Khalil kuma ya daina wasa, hankalinsu gaba ɗaya ya koma kansa, Aliyu ya ci gaba, “Daddy, na san cewa yanzu ba ni da baƙonci sosai a gare ku, kuma ina godiya da irin karɓar da kuka yi mini tun lokacin rashin lafiyarku,” ya ɗan yi shiru, sannan ya ci gaba cikin muryar da ta nuna tsantsar gaskiya, “Daddy… ina son Inteesar,” ya ɗan ɗaga kansa, “Saboda haka na zo ne domin neman izininku kafin in turo magabata na,” shiru ya ratsa falon, Khalil ya kalli Abubakar, Abubakar kuma ya zuba wa Aliyu ido, Daddy ya yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ya yi masa tambayar da ta fi muhimmanci a gare shi, “Aliyu, kana da mata?” Aliyu bai yi ƙoƙarin ɓoyewa ba, “Eh, Daddy, ina da mata biyu, kuma Allah Ya albarkace ni da yara huɗu,” Daddy ya gyada kai a hankali, “Toh, duk da haka kana son Princess ɗina?” Aliyu ya sauke idanunsa, wani irin murmushi mai cike da taushin zuciya ya bayyana a fuskarsa, “Wallahi, Daddy, ina sonta fiye da yadda zan iya bayyanawa, kuma ina roƙon Allah Ya ba ni ikon kula da ita cikin mutunci,” ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa, “Ba zan yi muku alƙawarin cewa ni cikakken mutum ne ba, amma zan yi iya ƙoƙarina wajen kare mutuncinta da farin cikinta,” Daddy ya yi shiru, sai wani tsohon hoto ya dawo masa a zuciya, Ahmad… Yadda ya taɓa zama a gabansa, yadda yake kallon Inteesar, yadda yake magana da shi cikin ladabi, wani abu ya motsa a zuciyarsa, ya ɗago ya kalli Aliyu, “Aliyu,” “Na’am, Daddy,” “Princess ɗina amanata ce, ban san abin da Allah Ya rubuta a tsakaninku ba, amma idan har ƙaddararta tana tare da kai, ka kula da ita,” idanun Aliyu suka cika da wani irin haske, “Na yi muku alƙawari, Daddy, zan yi iya ƙoƙarina,” Daddy ya yi murmushi, “Allah Ya sanya alheri,” ya ɗan dakata, sannan ya furta kalaman da Aliyu yake jiran ji tun zuwansa gidan, “Na amince,” a take, zuciyar Aliyu ta yi wani irin sauƙi, Alhamdulillah.
Bayan Daddy ya amince, wani irin sanyi da annuri ya mamaye zuciyar Aliyu, duk da cewa ya yi iya ƙoƙarinsa ya ci gaba da zama cikin nutsuwa, Khalil ya lura da yadda idanunsa suka canza, kamar an sauke masa wani babban nauyi daga zuciya, Mommy Haleema, wadda ta shigo falon a daidai lokacin, ta tarar da su cikin annashuwa, “Aliyu ne?” ta tambaya cikin murmushi, da sauri ya sauke kansa ƙasa cikin girmamawa, “Mommy, ina wuni?” “Lafiya lau, Alhamdulillah,” ta amsa cikin fara’a, Khalil ya yi murmushi, Mommy Haleema kuma ta ɗan kalli Daddy, wanda yake murmushi cikin nutsuwa, “Alhamdulillah,” ta furta, Abubakar kuwa yana kallon Aliyu cikin zurfin nazari, sai bayan wasu mintuna ya miƙe tsaye, “Aliyu,” “Na’am, Yaya,” “Muje waje kaɗan,” Khalil ya ɗaga gira, shi kuma Aliyu ya miƙe ba tare da wata-wata ba, “Toh, Yaya.”
A compound ɗin gidan, iskar yamma tana kaɗawa cikin sanyinta, Abubakar ya tsaya kusa da wata bishiya, hannayensa a aljihu, Aliyu kuma ya tsaya a gabansa cikin girmamawa, shiru ya ratsa tsakaninsu na wasu daƙiƙu kafin Abubakar ya ɗago ya zuba masa idanunsa, “Na bincike ka,” Aliyu ya ɗan yi murmushi, “Na yi tunanin haka,” Abubakar ya ci gaba, “Kuma ban same ka da wani abin zargi ba,” “Alhamdulillah,” “Amma…” Aliyu ya gyara tsayuwarsa, “Ina jinka, Yaya,” Abubakar ya sauke numfashi, “Inteesar ba ƙanwata kaɗai ba ce, zuciyata ce, wataƙila ma ba za ka fahimci girman abin da nake nufi ba,” Aliyu ya yi shiru yana sauraro, “Mun raineta cikin gata, mun ɗauketa kamar taska, ko kuka ta yi, sai mu rasa nutsuwarmu, idan kuma ta yi dariya, gidan gaba ɗaya zai yi farin ciki,” muryarsa ta yi ƙasa, “Kuma tun bayan rasuwar Ahmad…” Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, “Wani sashe na zuciyarta ya mutu tare da shi,” Aliyu ya lumshe idanunsa a hankali, domin ya san hakan, ya gani da idanunsa, ya ga yadda take kuka, ya ga yadda take karaya, kuma ya fahimci cewa akwai raunin da murmushi ba ya iya ɓoyewa gaba ɗaya, Abubakar ya sake dubansa, “Ban hana ka ba, Daddy ya amince, ni ma na amince,” ya ɗan dakata, sannan ya ƙara da cewa, “Amma kada ka zama dalilin hawayenta,” muryarsa ta ɗan yi nauyi, “Saboda wallahi, Aliyu, ba zan taɓa yafe wa duk wanda ya cutar da ƙanwata ba,” wani irin shiru ya ratsa tsakaninsu, Aliyu ya sauke idanunsa ƙasa, sannan ya ce cikin nutsuwa, “Wallahi, Yaya, ba zan ce muku ba za mu fuskanci ƙalubale a rayuwa ba, amma ina muku alƙawarin zan yi iya ƙoƙarina,” ya ɗan yi murmushi, “Kuma idan akwai abin da na fi tsoro a rayuwata, to, shi ne ganin hawaye a idanun Inteesar,” Abubakar ya zuba masa ido na wasu daƙiƙu, sai a hankali wani ɗan murmushi ya bayyana a gefen bakinsa, ya miƙa masa hannu, “Allah Ya sanya alheri,” Aliyu ya yi saurin kama hannunsa, “Ameen, Yaya,” Abubakar ya ɗan jawo shi kusa da shi, sannan ya ce cikin murmushin da ya sa Aliyu ya ɗan saki jikinsa, “Kuma wani abu,” Aliyu ya ɗaga ido yana kallonsa, “Na’am?” “Ka ga Khalil?” Aliyu ya ɗan ruɗe, “Kafin ka ce wani abu, ka sani cewa idan Princess ɗinmu ta yi kuka, ni zan yi fushi,” ya ɗan dakata, sai kuma ya saki dariya, “Amma Khalil… Khalil zai iya zuwa Yola ya dawo ba tare da ka sani ba!” Dariya ta kuɓuce wa Aliyu, shi ma Abubakar ya yi dariya, a karon farko tun zuwansa gidan, Aliyu ya ji kamar ya tashi daga matsayin baƙo ya fara zama ɗan gida, kuma wannan ma, wani irin farin ciki ne a gare shi.
Yayin da Aliyu da Yaya Abubakar suke tsaye a compound suna tattaunawa, a can sama kuwa… Inteesar tana cikin ɗakinta, sanye take da doguwar rigar bacci mai launin cream, gashinta a sake yake a bayanta, wayarta kuma tana hannunta, amma hankalinta gaba ɗaya ba ya kanta, tun bayan da Aliyu ya gaya mata cewa zai zo gidan yau, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, sau nawa ta ɗauki wayarta tana son kiransa ta tambaye shi ko ya shigo, sau nawa ta so saukowa ƙasa, amma kunya ta hana ta? Ta tsaya a bakin window tana kallon yadda rana ke shirin faɗuwa, “Ya Allah…” ta furta a hankali, “Allah Ka sa na ji alheri,” ta dafa saitin zuciyarta, wadda ke ta bugawa babu ƙaƙƙautawa, ta tuna Daddy, ta tuna Yaya Abubakar, ta tuna irin kallon da yayanta yake mata idan ya ga wani abu da bai gamsar da shi ba, gabanta ya sake faɗuwa, “Allah dai Ya sa komai ya tafi lafiya,” a daidai wannan lokacin aka ƙwanƙwasa ƙofar, ta juya, “Shigo,” ƙofar ta buɗe, sai ga Yaya Khalil, da wani irin murmushi a fuskarsa, tun kafin ya yi magana, Inteesar ta lura da murmushin nasa, ta miƙe tsaye da sauri, “Yaya?” Khalil ya haɗe hannuwansa a ƙirji yana kallonta, “Princess…” Ta haɗiye miyau, “Na’am, Yaya?” “Me kika ba mutumin nan ne?” Ta zaro idanunta, “Wane mutum?” “Wane kuma?” ya faɗa yana dariya, “Alhajin naki mana!” Nan take idanunta suka yi rau-rau, “Yaya!” Shi kuwa Khalil sai dariya yake, “Wallahi, Princess, mutumin nan ya ba ni mamaki,” ta matso kusa da shi da sauri, “Yaya, me ya faru?” Khalil ya ci gaba da tsokanarta, “Uhmm… ban sani ba ko zan iya faɗa miki,” “Yaya, don Allah!” Ta faɗa tana kama hannunsa, “Don Allah ka faɗa min,” Khalil ya yi dariya, “Kai! Yau har ni kike lallabawa? Da alama soyayya ta gama aiki,” “Yaya Khalil!” Ta faɗa cikin shagwaɓa, dariyar da ya yi ta cika ɗakin, sai kuma ya lallaba muryarsa, “Princess…” Nan take murmushinta ya ɗauke, ta zuba masa ido, “Na’am?” Khalil ya yi murmushi, “Daddy ya amince,” wani irin shiru ya mamaye ɗakin, Inteesar ta kafe shi da ido, kamar wadda ba ta ji da kyau ba, “Me?” “Daddy ya amince, Aliyu ya zo, ya yi magana, kuma Daddy ya amince,” hawayen farin ciki suka cika idanunta lokaci guda, ta rufe bakinta da hannunta, “Da gaske?” Khalil ya yi murmushi, “Da gaske mana! Har Yaya Abubakar ma ya gama yi masa tambayoyi,” Inteesar ta kasa magana, hawayen farin ciki suka fara zubowa, Khalil ya yi mamaki, “Ke kuma meye na kuka?” Ta girgiza kai cikin sauri, “Ba kuka nake ba,” amma muryarta ta kasa fitowa saboda yadda zuciyarta ta cika da farin ciki, ta zauna a gefen gado tana share hawayenta, “Alhamdulillah… Alhamdulillah…” Kawai ta iya furtawa, Khalil ya zuba mata ido, wani irin tausayinta ya kama shi, tun bayan rasuwar Ahmad, wannan shi ne karo na farko da yake ganin irin wannan haske da farin ciki a fuskar ƙanwarsa, ya zauna kusa da ita, “Princess,” ta ɗago tana goge idanunta, “Na’am, Yaya?” Ya shafa kanta a hankali, “Ki yi farin ciki, kin ji? Allah Ya sa alheri ne a tsakaninku,” wani sabon hawaye ya sake zubo mata, ta jingina kanta a kafaɗarsa, kamar ƙaramar yarinyar da ta saba yi masa tun tana yarinya, “Na gode, Yaya,” ya yi murmushi, “Ni kika gode wa? Daddy da Yaya Abubakar za ki je ki gode wa,” duka suka yi dariya, sai kuma ya ɗan lumshe ido yana kallonta, “Amma…” Ta ɗago, “Na’am?” “Alhajin naki yana ƙasa,” idanunta suka buɗe sosai, “Me?!” “Eh mana!” Ya saki dariya, “Kuma wallahi, mutumin nan kamar ya lashe ƙasa saboda tashin hankali!” Inteesar ta dafe ƙirji, “Yaya!” “Wai yana nan?” “Eh, kuma yanzu ma yana tare da Yaya Abubakar,” ta miƙe tsaye da sauri, sai kuma ta tsaya cak, “Ni… Yaya… ba zan sauko ba,” Khalil ya fashe da dariya, “Wa ya ce ki sauko? Wallahi, ko kika sauko, ni zan mayar da ke sama!” Ta yi dariya cikin kunya, shi kuwa ya miƙe, yana isa bakin ƙofa, sai ya juya ya sake kallonta, ya gan ta tana murmushi, murmushin nan da ya daɗe bai gani a fuskarta ba, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa, ya yi murmushi a hankali, Ahmad… ya faɗa a cikin ransa, na san ba za ka so ta zauna cikin baƙin ciki har abada ba, Allah Ya sanya alheri, sannan ya fita ya bar ta ita kaɗai, Inteesar kuwa ta zauna a bakin gadonta, ta rungume pillow ɗinta a ƙirji, hawaye na ci gaba da zuba daga idanunta, amma wannan karon ba na baƙin ciki ba ne, hawayen farin ciki ne, ta lumshe idanunta, hoton Aliyu ya bayyana a zuciyarta, murmushinsa, muryarsa, kalaman alkawarinsa, sai ta sauke numfashi a hankali, ta dafa zuciyarta wadda ke bugawa cikin wani irin daɗi mai wuyar bayyanawa, sannan cikin sanyin murya, mai cike da kunya da soyayya, ta furta, “…I love you too, Aliyu,” ba tare da ta san cewa Aliyu yana zaune a motarsa yana murmushi shi kaɗai ba, kamar zuciyarsa ta ji abin da nata zuciyar ta faɗa.
Dare ya yi, Inteesar tana zaune a bakin gadonta, wayarta a hannunta, tun bayan da Aliyu ya tafi, bai kira ta ba, ita ma kunya ta hana ta kiransa, amma zuciyarta tunani ɗaya kawai take yi, ya tafi lafiya kuwa? Allah Ya sa Yaya Abubakar bai yi masa wani abu ba? Sai da dare ya yi sosai, wayarta ta haska, nan take murmushi ya bayyana a fuskarta, ganin sunansa kaɗai ya sa zuciyarta yin wani irin tsalle, ta gyara zamanta, ta gyara muryarta, sannan ta ɗaga wayar, “Assalamu alaikum,” murmushin Aliyu ya bayyana a cikin muryarsa, “Wa alaikumus salam…” Dukansu suna murmushi, sai Aliyu ya saki wani numfashi, “Babygirl…” Ta ɗan yi shiru saboda jin sunan da ya kira ta da shi, sannan ta amsa a hankali, “Na’am?” “Wai da gaske ne?” Ta yi murmushi, “Me?” “Da gaske ne yau na zauna a gaban Daddy ɗinki ina neman izininsa saboda ke?” Ta saki ƙaramar dariya, “Ni ma har yanzu ban yarda ba,” Aliyu ya yi dariya, “Wallahi, ni ma,” ya ɗan yi shiru, sai muryarsa ta sauya, ta koma mai laushi, mai cike da godiya, “Babygirl… na gode,” ta yi shiru, “Saboda me?” “Saboda kin amince kika ba ni dama, saboda kin sake yarda da soyayya, saboda kin sake buɗe zuciyarki bayan duk abin da kika fuskanta, saboda kin zaɓe ni,” Inteesar ta ji zuciyarta ta yi wani irin laushi, sai ta yi murmushi, “Ni ya kamata na gode maka,” “Saboda me?” “Saboda ka jajirce, saboda ba ka gaji da ni ba, saboda ka tsaya tare da ni lokacin da nake cikin duhu,” Aliyu ya yi murmushi, “Wallahi, ko da shekaru goma ne zan jira ki,” ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara da cewa, “Daga ranar da na gan ki a cikin jirgin sama, na san zuciyata ta kama wata hanya dabam,” Inteesar ta lumshe ido, har yanzu, duk lokacin da ya tuna mata wannan ranar, sai ta ji wani irin daɗi a zuciyarta, sai Aliyu ya ce cikin wasa, “Amma akwai mutum guda da ya ba ni tsoro yau,” ta yi dariya, “Waye?” “Yaya Abubakar!” Nan take Inteesar ta fashe da dariya, “Ka ji tsoronsa kenan?” “Babygirl, wallahi na ji! Mutumin nan idanunsa kamar X-ray ne!” Dariya ta ƙwace mata, “To, ka san me?” “Me?” “Shi ma yana sona sosai, kuma duk wanda zai zo wajena sai ya fara wucewa ta wajensa,” Aliyu ya yi dariya, “To, Alhamdulillah, na ci jarabawar ne?” Ta yi murmushi, “Da alama,” “Da alama?” “Eh,” “Wato har yanzu akwai supplementary?” Inteesar ta sake fashewa da dariya, Aliyu ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya sauke numfashi, muryarsa ta sake canzawa, ta koma mai taushi, “Babygirl…” “Uhmmm?” “Yau yana cikin ranakun da ba zan manta da su ba,” ta yi shiru tana sauraro, “Saboda yau ne karo na farko da na ji kamar kina gab da zama tawa da gaske, ba a mafarki ba, ba a cikin buri kawai ba, a zahiri,” Inteesar ta ji hawayen farin ciki suna taruwa a idanunta, sai ta yi ƙasa da murya, “Aliyu…” “Na’am, Babygirl?” “Ka sani?” “Me?” “Ina jin tsoro,” nan take ya gyara zamansa, “Tsoron me?” “Tsoron kada wannan farin cikin ya yi mini yawa, tsoron kada na farka daga mafarki,” Aliyu ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin taushin murya, “Ki saurare ni, Babygirl,” ta yi murmushi, “To, ina jinka,” “Ba mafarki ba ne, kuma in Sha Allah, zan yi iya ƙoƙarina na zama dalilin murmushinki, ba dalilin hawayenki ba,” nan take Inteesar ta lumshe idanunta, ta jingina da pillow tana murmushi, sai ya sake magana, “Ina jin kina murmushi,” ta ɗan yi dariya, “Uhm,” “Gaskiya ni dai yau sai kin canja min suna,” ta yi murmushi, “Ba yau ba…” Ya katse ta da sauri, “Ni gaskiya yanzu!” “Ka bari sai gobe,” ya sake katse ta, “Ni dai gaskiya yanzuuu!” Inteesar ta girgiza kai tana murmushi, wannan shagwaɓar tasa ta sa ta kasa daina dariya, a hankali ta furta, “Goodnight, mi amor,” kafin Aliyu ya samu damar cewa komai, ta kashe wayar da sauri tana dafe ƙirjinta, ta jingina da pillow ɗin, murmushi ya ƙi barin fuskarta, mi amor… Ta sake maimaita sunan a ranta, tana jin kunya ita kaɗai, a ɗayan ɓangaren kuma, Aliyu ya zuba wa wayarsa ido na wasu daƙiƙu kafin murmushi ya bazu a fuskarsa, “Mi amor…” ya maimaita a hankali, sai ya girgiza kansa yana murmushi, amma duk da kalamansa, babu wanda ya fi shi farin ciki a wannan daren, domin a yau, bayan dogon jira da fatan alheri, ya fara jin cewa ƙaunar da ke zuciyarsa na samun gurbi a zuciyar Inteesar ma, kuma ga Aliyu, wannan ya fi duk wata nasara da ya taɓa samu a rayuwarsa daɗi.