Chapter 16
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*Ba ni da Madogara*
(Sai Allah...)
016
Sosai Hujayrah take dariya tana nuna Tahseen tana dariya. Bayan ta yi dariyar son ranta sai ta dubi Tahseen fuskarta ɗauke da murmushi ta ce
"Hujayrah Jikar Kamalu kika mara har sau biyu?"
Ta yi maganar tana kallon Tahseen, cike da ƙarfin hali Tahseen ta ce
"An mareki ɗin, ke ƴar gidan uban waye ce da ba za a mara ba, saboda iskanci da rainin hankali taya ina hira da mijina za ki zo ki damesa da surutun banza da yofi, bana ɗaukar raini wallahi, banza jaka mai kama da biriya kawai"
Murmushi Hujayrah ta sake saki Still idanunta suna na kan Tahseen bata ko ƙyaftawa, sai da ta bari ta kai ƙarahen zance sannan ta gyara tsayuwanta ta dubi Tahseen ta ce
"Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ha ha ha"
Juyowa Hujayrah ta yi ta dubi Razina wacca take daskare a wajen ƙofa, fuskarta ɗauke da murmushi wanda babu gyara babu dalili, ita kaɗai tasan manufar murmushin da take yi. Cema Razina ta yi
"Razina yaushe ne za a bikin murnar zagayowan haihuwar Ya Raqam qam"
Bambara ƙwai Razina ta ji tambayar Hujayrah kamar saukar aradu da ka, cewa ta yi
"Zuwa gobe ne in shaa Allah"
Wani ƙasaitaccan murmushi Hujayrah saki sai kawai ta duƙa ta fara shafa magen da yake magen tana wurin tana ta goga jikinta a jikin Hujayrah.
"Ƴar mageta dake zan je gobe wurin bikin, don akwai kallo sosai, kar ki damu duk wanda ya taɓaki kamar ya taɓoma kansa garwashin wuta ne, bye bye ƴar mageta Sai mun haɗu a bikin"
Tana gama maganar ta miƙe tare da yin miƙa tana salati, sake kallon Tahseen take yi tana murmushi tare da girgiza kai, sai kuma ta dubi Arqam ta ce
"Ya Raqam qam, ga flask ɗin, Ni na wuce sai mun haɗu gobe a shagalin bikin"
Juyawa ta sake yi wajan Tahseen wacca take daskare tana binta da ido, murmushi mai nakar da zuciya ta sakar mata sannan ta wuce abin ta tana ƴan waƙe-wakenta, wuce Razina ta yi ba tare da ta ce mata komai ba. Sai ita ma Razina ta juya ta fita daga ɗakin. Tahseen ma barin ɗakin ta yi cike da murna zuwa masaukinta, burinta ya cika tun da ta yi maganin shegiyar yarinyar mai kama da jinnu. Arqam suka bari yana nan zaune sai dai yabar latsa laptop ɗinsa, sosai ya shiga kogin tunanin Hujayrah a ransa yana cewa 'Da alama akwai shirin da yarinyar nan take yi akan Tahseen, yadda take dariya shows she is planing something real, wait Amma me yasa take ma Melona magana tana murmushi, ooooh! I got it! Ke nan saƙo take bama Tahseen indirectly, Hmmmm Allah ya kaimu gobe lafiya, nima zan sha kallo kamar Melona'
Murmushi ya yi sannan ya ɗauki flask ɗin da Hujayrah ta ajiye a gabansa da mug , a hankali ya tsiyaye coffee ɗin a cikin mug ɗib. Ajiye flask ɗin ya yi a gefe sannan ya jawo centre table kusa da shi ya ɗora mug ɗin a sama.cike da ƙwarewa ya fara sarrafa na'urar computarsa yana ɗan kurɓar coffee ɗin lokaci bayan lokaci. Melonsa na gefensa kwance.
A ɓangaren Hujayrah bayan ta fito daga ɗakin kai tsaye da wuce ɗakinsu, drawar da take ajiye jakar maganin ta buɗe, ciro jakar ta yi sannan ta buɗe, ladojin magunguna ne kala-kala a ciki, ɗaya bayan ɗaya take ɗauka tana ajiyewa a gefe, har daga ƙarshe ta ɗauko ƙullin da take buƙata sai ta maida sauran, ta ja zip ɗin jakar ta maidata cikin drawar, zama ta yi da kyau sai ta ɗauki ƙullin maganin ta ɗaga sama tana murmushi ta cs
"Gobe akwai kallo, ha ha ha za ki san koni wace ce, uban nawa ma za ki san ko shi waye ne, shegiya gobe akwai kwaso shoki wallahi, mari! Mari! Har biyu ban yi miki komai ba. Yooo!Allah na tuba ba a taɓani wacca aka cika balle an taɓani, ho ho ho"
Tintsirewa da dariya Hujayrah ta yi tana kallon ƙullin maganin tana dariya, ta kai tsawan minti biyu tana dariya ba tare da dalili ba, sai can ta tsagaita. Miƙewa ta yi ta sake buɗe drawar ta ajiye maganin a can ciki sannan ta rufe sai ta haye saman gado abin ta.
A ɓangaren Razina kai tsaye ta wuce falon Ammienta, ta ko ci sa a su biyu ne a ciki Abba da Ammie, da sallama ta shiga ciki fuskarta shimfiɗe da damuwa. Cike da kulawa suka amsa mata sallamar, sai Alhaji ya ce
"Autana lafiya naga kin shigo fuskarki ɗauke da damuwa what's wrong?"
Kusa dashi ta zauna tare da kwaɓe fuska ta ce
"Abba Allah Aunty Tahseen abin da take bata kyautawa"
"Me ta yi" cewar Hajiya momma
"Ammie haka nan ta mari Hujayrah hagu da dama ba tare da ta yi mata komai ko kuma ta ce mata komai ba"
Waro idanu waje suka yi suna kallonta, cike da mamaki Alhaji ya ce
"Ita Tahseen ɗin da kanta, ko dai akwai abin da Hujayrah ta yi mata baki sani ba"
Girgiza kai Razina ta yi tana cewa
"Ko ɗaya Abba ai Ya Arqam yana wurin lokacin da abin ya rafu, ita Hujayrah ta je kai wa Ya Arqam coffee ɗinsa a flask"
"Wani irin mugunta ne haka siddan-bagatatan, to ita Hujayrah me ta ce" cewar Hajiya momma tana ajiye wayarta a gefe
"Ammie babu abin da Hujayrah ta yi sai dai ta wuce abin ta waje bayan ta ajiye ma Ya Arqam flask ɗin"
Gyara zamansa Alhaji ya yi fuskarsa da murmushi ya ce
"Allah sarki Hujayrah baiwar Allah mai haƙuri babu ruwanta ta barta da Allah" (Hmmmm Alhaji bai san wace ce Hujayrah ba, in ce wani abu My Esteem fans ko na yi shiru 🤭🤭🤭)
"Hakane Alhaji zan yi ma Tahseen faɗa don wannan halin ba hali ba ne mai kyau" cewar Hajiya momma.
(Hmmmm da alama su Hajiya momma bata san shirin da Hujayrah take yi akan Tahseen ba🤭, sun manta ɗiyar Audu jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoran mutuwa aka taɓa, Ni da my Esteem fans ƴan kallo ne 💃💃💃🤭🤭🤭🤭😂😂😂)
A ɓangaren Tahseen bayan tabar ɗakin ta wuce masaukinta fuskarta ɗauke da murmushin nasara.Tana shiga ta ciro wayanta ta yi dailing numban Mom ɗinta, ringing ɗaya-biyu da ɗauki kiran, cike da zumuɗi Tahseen ko gaisheta ta ce
"Mom na sassaitawa yarinyar hankali yanzu nan"
A can Mom cike da farin ciki ta ce
"Awwwn that's great! Good job! Yanzu na gama waya da Hajiya Lubna ta ce zuwa jibi za ta sake komawa gun bokan ya ƙara wani aikin akan na da"
Gyara zamanta ta yi sannan ta ce
"Yeeeeh!!! You are the best Mom ever, Ina alfahari da samunki a matsayin uwata"
A can murmushi Hajiya Ramla ta yi sannan suka ci gaba da hira, sun kai kusan mintuna ashirin suna waya daga bisani suka yanke kiran. Kamar jira ake Tahseen ta kammala wayan sai ga wani kiran ya shigo cikin wayarta. Ganin My Pleasure a screen ɗin wayar lokaci guda ta saki murmushi tare da ɗaukan kiran tana cewa
"My Sakhiyya! My pleasure! "
A can Sakhiyya ta ce
"Haba my love wato daga dawowan Ya Arqam shi ne kika manta dani ko"
Kwanciyar rufda ciki Tahseen ta yi sannan ta ce
"Ummm Haba my Sakhiyya kin san bazan taɓa mantawa da ke ba, Mom ce ta ce na zo nan saboda birthday ɗin Ya Arqam amma zuwa gobe ana kammalawa zan dawo gida"
A can Sakhiyya ta ce
"Auu gobe ne birthday ɗinsa, ai kuwa zan zo, sannan akwai wani party da za a yi jibi, It's gonna be on fire, Ina fatan za ki zo daga nan sai mu yi making love ko, Kin san na yi missing ɗinki sosai don ma Allah yasa jiya na yi babban kamu a club"
"OK to sai kin zo, zuwa jibin zan zo partyn, nima nan wallahi a matse nake kawai ina daurewa ne, sai kin zo ɗin" cewar Tahseen tana rungume pillow tana lumshe ido
A can Sakhiyya ta ce
"Kin san Ya Akmal ya dawo kuwa? "
"Laaah wallahi ban sani ba, da yake kwana biyu mun rabu da chat"
A can Sakhiyya ta ce
"Ayya! Kin san Ya Khalil bai dawo ƙasar ba shi yasa bai zo gidansu Ya Arqam ba"
"Ban san meyasa basa jituwa da Ya Arqam ba, kamar ba ƴar uwa ba"
A can Sakhiyya ta taɓe baki sai ta ce
"Who knows for them mu dai mun haɗe kanmu, kuma muna ƙaunar junanmu"
Ci gaba da hirar suke suna dariya wanda yawanci akan ɓoyayyar alaƙarsu suke hirar akai wanda iyayansu babu wanda yasan da haka, don har da ƙungiya suke da ita ta ƴan lesbian.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A can part ɗin Hajiyan Sama, sosai Fauziyya take shiri don kai wa Arqam breakfast, don Tun a yau take son fara gwada sa a kafin a yi mai kankat wato Hajiyan Sama ta bijiro ma Alhaji da zancen auran nasu. Sanye take cikin doguwar riga straight gown amma bata matseta ba ta yafa gyale mai shigen kayan, saboda tana so ta yi shigan mutunci ƙila ya yaba don baya son shigar banza, tun suna yara idan sun saka riga da wando yake korasu ciki su saka hijab, da wannan dalilin yasa ta yi shigar mutunci. Bayan ta shirya sai ta shigo falon Hajiyan Sama wanda tasan tana ciki, babu sallama ta shiga ciki tana cewa
"Mom ya kika ganni"
Hajiyan Sama da ke zaune a kujerar mutum tana kallon TV sai ta juyo ta zuba mata ido, lokaci guda ta sakar mata da murmushi mai narkar da zuciya ta ce
"Yarinyar Mominta wannan kyau haka kamar ke kika yi kanki, dole Arqam ya so ki ko saboda kyau da Allah ya yi miki, Yanzu part ɗinsa kika nufa"
Fauziyya da ke jin kanta a sama saboda koɗatan da Hajiyan sama ta ce
"Eh Mom na shirya breakfast ɗin a basket"
Miƙewa Hajiya sama ta yi tana cewa
"Yawwa Ina zuwa"
Kai tsaye ta wuce bedroom ɗinta ta ɗauko wata kwalba ƙarama ta miƙa mata tana cewa
"Ga wannan kwalbar turare ne mai mugun ƙarfi na farin jini, Hajiya Zinatu ne ta kawomin,kina isa ƙofarsa sai ki buɗe turaran ki goga a jikinki sai ki shiga ciki, ki tabbata sai kin je ƙofarsa za ki goga turaran don yana da matuƙar ƙarfi sannan Arqam ɗin kawai ake so ya shaƙa kamshin turaran "
Rungume Hajiyan sama Fauziyya ta yi tana farin ciki, gyara gyalenta ta yi sannan ta ɗauki basket ɗin ta sauko zuwa ƙasa. Direct ta wuce part ɗin Hajiya momma kasancewar sai an wuce part ɗin Hajiya momma kafin a je part ɗin Arqam. Tana isa ƙofar ta tsaya, ajiye basket ɗin ta yi sannan ta waiga hagu da damanta ta duba kar wani yana kallonta. Da sauri ta goga turaran a kayanta sannan ta ƙwanƙwasa ƙofar, shiru babu alamun an ji, sai kawai ya murɗa handle ɗin ƙofar. Tana murɗawa sai ƙofar ta buɗe, shiga ta yi bakinta ɗauke da sallama. P.A ɗin Arqam ne mai suna Bilal wanda yake ɗan yaro ɗan uwa Alhaji ya amsa mata lokaci guda ya ja numfashinsa tare ta shaƙar turaran da ta shafa, ai nan take ya juyo yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce
"Wa'alaikissalammm!"
Murmushin yaƙe ta yi don ba haka ta so ba, ta so a ce da Arqam ta fara tozali amma kashhh! Ta yi rashin sa a. Gyara tsayuwansa ya yi yana kallonta sannan ya ce
"Fauziyya yarinyar Hajiyan sama ko"
Fuska a ɗaure Fauziyya ta ce
"Eh"
Lallausar murmushi ya sakar mata zai yi magana sai ga Arqam ya fito daga bedroom ɗinsa, Melonsa na biye dashi a baya sai ya samu kujerar mutum ɗaya ya zauna. Da sauri Bilal ya nufi wurinsa hannunsa riƙe da File da mini laptop. Ganin Arqam ya zauna sai Fauziyya ta matso kusa dasu ta dubi Arqam cike da kissa da karairaya ta ce
"Ya Arqam, ga breakfast nan Mom ta ce na kawo maka tare da coffee"
Shiru bai amsa mata ba kuma bai kalleta ba, idanunsa na akan wani File da Bilal ya miƙa masa. Da yake Bilal yasan mai gidansa ba tanka mata zai yi ba, sai dai ta daɗe a tsayan har ta gaji, sai ya dubeta bakin nan kamar mai tallar audiga ya ce
"Ammm ba damuwa My Fauzeey queen, Ki ajiye basket ɗin muna godiya sosai"
Wani malolan baƙin ciki ne ya ta so wa Fauziyya bai tsaya ko'ina ba sai a daidai wuyanta,ji take kamar ta je ta shaƙe wuyan Bilal ko za ta samu sassauci a cikin zuciyata, a ranta ta ce 'Shi kuma wannan mai yake nufi da Fauzeey queen, Sai wani murmushi yake yi kamar wanda aka yi masa bishara, Mts!'
A ƙufule ta dire basket ɗin tare da juyawa Fuuuu! Kamar za ta tashi sama tabar ɗakin. Tana fita ta ci karo da Tahseen za ta shigo ɗakin. Wani wawan tsaki Fauziyya ta ja ba tare da ta ce komai ba ta wuce. Taɓe baki Tahseen ta yi tare da cewa
"A sauka lafiya uwar snatching, halin nan na ki na nan baki bari ba ballagaza ta wani kwaso jiki kwasai-kwasai za ta min snatching miji, to ƙwlelanki hegiya"
Fasa shiga falon ta yi sai ta koma masaukinta tana jin daɗi saboda daga gani Arqam ya ɓata ma Fauziyya rai shi yasa ta fito a hasale.
Kai tsaye Fauziyya ta wuce garden don bata so ta je wurin Hajiyan sama a haka ta gane akwai matsala, ta fi so ta yi yaƙinta da karan kanta ba tare da taimakon kowa ba. A ranta ta ce 'Tun da Plan A ya rushe, bara na je ga plan B, wallahi Arqam ko kaƙi ko ka so saina mallake ka, kai ɗin nawa ne ni kaɗai, sai ka dawo a tafin hannuna ina juyaka yadda na so' Bayan yanayinta ya daidai sannan ta koma part ɗinsu tare da yi ma Hajiyan sama ƙarya wai aikin ya ci Arqam har yana mata murmushi tare da ce mata ya gode. Sosai Hajiyan sama ta shiga murnar nasara don haƙarta tana gab da cimma ruwa.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
Bayan fitar Fauziyya daga ɗakin sai Bilal ya gyara tsuyuwansa cike da girmamawa ta ce
"Yallabai ammm dama na ce"
Sai kuma ya yi shiru yana duƙar da kansa saboda abin da yake son yana da nauyi. A hankali Arqam ya ɗago oily eyes ɗinsa ya saukesu a kan Bilal, bai ce komai yana kallonsa, da yake yasan halayan ogan nasa ba zai yi magana ba sai dai ya yi nuni da idanunsa. Ganin haka sai Bilal ya tafi kai tsaye ya ce
"Ammm daman na ce idan ba a yi ma Fauziyya miji ba Ina..."
Bai ƙarasa abin da ya yi niyyar faɗa ba saboda yadda Arqam yake kallonsa. Sai can kuma ya janye idanunsa tare da sakin murmushi sai a sannan ne Bilal ya ji natsuwa ta ratsa zuciyarsa.
"Sai ka shirya tunkararta" kamar an yi masa dole ya yi maganar daga haka bai sake cewa komai ba, sai ci gaba da duba files. Sosai Bilal ya Shi farin ciki don lokaci guda so da ƙaunar Fauziyya ta ratsa jini da ɓargonsa har tabi jijiyoyinsa, ji yake idan bai aureta ba zai iya mutuwa. Wannan ke nan
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Washe gari*
*Da misalin ƙarfe 4:12pm na yamma*
Kowa ya hallara a babban ɗakin taron da yake a gidan Alhaji Imran kama daga Hajiya momma, Hajiyan sama, Hajiya Ramla, Hajiya Nafisa, su Nazima,, Zahriyya, Fauziyya, Sakhiyya da uwar gayya Tahseen kamar wata amarya saboda kwalliyar da ta sha da kuma kayan da ta saka. Razina da Hujayrah su ne gaba-gaba, Hujayrah ta saka baƙin tabarau saboda yanayin idnaunta. Kaya kala ɗaya suka saka ita da Razina, Abokan Arqam ba a barsu a baya suma sun yo gayya ƴan matansu saboda taron babba ne sosai. Arqam, Mas'ud, Mahmoud da Bilal suna a table ɗaya. Sun sha kyau kamar ka sace su ka gudu. Kasancewa ba iya birthday kaɗai ne ya tarasu ba, har da murnar dawowansa Nijeriya bayan ya ɗauki tsawan shekaru baya ƙasar .Sosai hall ɗin ya haɗu, ya sha decoration wanda ya ƙara ƙawata hall ɗin, a can sama aka ajiye cake mai hawa uku da champaigns. Bayan kowa ya hallara sai Mc ya buɗe taron da addu'a sannan ya fara koro bayanin maƙasudin abin da ya tara su. Bayan Mc ya faɗi maƙasudin Abin da ya tarasu sai ya ba Alhaji mic, shi ma ya yi nasa bayanin a matsayinsa na mahaifi, daga Alhaji aka ba Hajiya momma ita ma ta yi nata jawabin, a haka har kusan iyayen Arqam sun yi nasu jawabin daga bisani ma'aikata su kaita kai-kawo da abinci da abin sha wanda a lokacin kusan ana gab da kiran magrib. Su Alhaji da sauran iyaye suka bar hall ɗin kowa ya gidansa, sai aka bar yara saboda akwai party bayan sallar isha'i. Arqam da sauran abokansa suka tafi sallar wanda basu suka dawo ba sai da aka yi sallar isha'i.
Yanzu aka fara party, Dj ya saki wata duma mai saka liman rausaya, ɗaya bayan ɗaya ƴan mata da samari suka shigo fili, suna bin waƙar da rawan, Tahseen da Sakhiyya suna cikin filin sai taka rawa suke, daman ƴan son rawa ne ko a club, nan da nan suka fara rawa suna bin waƙar. Sosai Dj ya ƙura sauti baka jin komai sai muryoyin mutane suna bin waƙar wacce take trending a yanzu. Razina, Fauziyya, Zahriyya, Nazima har da su Mahmoud da Bilal sun shiga filin suna taka rawar. Arqam da Mas'ud kaɗai aka bari a kujerun suna kallon masu rawar, Hujayrah na zaune tana kallonsu tana dariya sai can ta miƙe zuwa wurin filin don yanzu ne daidai lokacin da ya dace ta aiwatar da ƙudirinta akan Tahseen, ba wai ta iya rawar ba ne amma don ta cika ƙudirinta ta shiga filin tana taka rawarta na hauka. Duk wanda ya ga Hujayrah a lokacin dole ya ce daga ƙauye ta fito domin rawar hauka kawai take tana daka tsalle tare da yarfa hannu tana cin baki, ita ala dole ta iya ta iya waƙar. Tun lokacin da Hujayrah ta miƙe zuwa filin Arqam ya kafeta da ido yana kallonta, yadda take rawar haukan ya sake jan ra'ayinsa ya koma babu wanda yake kallo sai ita kaɗai. Murmushi kawai yake dokawa a ransa yana faɗin 'Allah ya baki lafiya Hujayrah, don da alamu ƙwaƙwalwarki ta taɓu' Mas'ud ma ita yake kallo yana dariya har da riƙe ciki.
Suna cikin rawar Hujayrah ta ciro wata leda a cikin ƴar ƙaramar jakarta still bata fasa rawar ba ta kwance. Arqam da Mas'ud suna kallonta suga mai yake shirin yi. Kawai sai suka ga ta shiga tsakiyar filin daidai inda Tahseen take rawa, ganin hankalin Tahseen ya daɗe da barin gangan jikinta sai ta yi amfani da Wannan damar. Cikin rawa Tahseen ta ɗan duƙa tana karkaɗa duwawu, sai ta ji zuban abu a jikinta ta ko'ina. Kasancewar rigarta mai off shoulder ne har cikin bra ɗinta abin ya zuba. Da matuƙar sauri Hujayrah ta fito daga cikin filin Still tana rawarta na hauka. Babu wanda ya lura da abin da Hujayrah ta yi sai mutane uku, daga Arqam, Mas'ud sai Salame wacca shigowanta ke nan kamar Ance ta kalli tsakiyar filin sai taga Hujayrah na barbaɗama ma Tahseen garin magani a jiki. Ba a fi second ashirin da Hujayrah ta barbaɗama Tahseen garin maganin ba sai Tahseen ta fara jin ƙaiƙayi a jikinta. Daurewa ta yi ta ci gaba da rawar amma fa rawar ta canja salo don yanzu bil hakƙi da gaskiya take tiƙar rawar ko za ta samu sassaucin ƙaiƙayin da take ji a jikinta sai dai kamar ana ƙara mata ƙaiƙayin ne. Kowa matsawa ya yi daga tsakiyar filin aka bar Tahseen tana rawa wanda yanzu ya koma na hauka. Wasu har wayoyinsu suka ɗauko suna videoing ɗinta. Canja waƙa Dj ya yi sai ya samo wata waƙa wanda ta yi daidai da irin rawar da Tahseen take yi. Waƙar *Tekno mai suna OYA SHAKE BODY* habawa Ai tuna salon ya canja tana girgiza jikin tana susar jikinta musamman wurin ƙirjinta, ji take kamar ya ciro nonuwanta ta fara susa, gashi bayanta ma haka, ƙaiƙayin bala'i kawai yake mata, tuni zufa ta fara yi mata sallama babu ƙakƙauwa. Mutane babu abin da suke sai ma Tahseen tafi ji kake Raf! Raf! Raf! Kowa a tunaninsa duk cikin rawar ne.
A ɓangaren Hujayrah kuwa gefe ɗaya ta samu tana kalar rawar Tahseen tana dariya har da juyi tana girgiza kafaɗu irin yadda Tahseen take rawar har da soshe-soshe . Da sauri Mas'ud ya yi nufin miƙewa sai Arqam ya yi saurin maida shi ya zauna. Kallonsa Mas'ud ya yi alamar *Why* sai Arqam ya girgiza masa kai, cikin muryar nan tasa kamar wanda aka yi ma dole ya fara magana.
"Just leave her, Tahseen ce ke da laifi because without any offense ta wanka ma Hujayrah mari twice. So she deserve this. Ta yi min daidai da ta zuba mata karara a jiki, Next time she won't dare try that stupidity to her or to any body "
Mamaki ne ya cika Mas'ud jin abin da Arqam yake faɗa. Cike da ruɗu ya ce
"You mean in front of you ne Tahseen ta mari Hujayrah"
Gyaɗa masa kai ya yi, ƙara suka ji lokaci guda, da sauri Mas'ud ya miƙe zuwa cikin fili kowa ya ruɗe ganin Tahseen na susar jikinta tana ihu har da kuka, duk jikinta ya yi ja abin ka da Farar mace. Ba a maganar wurin nonuwanta don kamar Allah ya aikota haka take sosa rigar tana kuka. Hankali tashe Sakhiyya da Nazima suka yo kanta tare da taimaka mata. Jikin Sakhiyya na gogar inda Hujayrah ta baɗama Tahseen magani nan take ta fara susa kamar za ta cire fatar jikinta. Dole Dj ya tsaya da kiɗin, Fauziyya da Zahriyya sai dariya suke mata, har videon lokacin da take kuka sai da suka yi. Kai tsaye suka fita da ita daga hall ɗin tana ihu, jiki na rawa Nazima ta kira Hajiya momma take sanar mata da abinda ke faruwa, kasancewar akwai clinic a estate ɗin sai Mahmoud ya ja motar zuwa asibitin.
Mas'ud na dawowa daga filin sai ya kira Hujayrah, gogar kamar ba ita ba, saita je wurinsu fuskarta da fara'a, tana zuwa ta ce
"Ya Mas'ud ina wuni"
Bai amsa mata sai ya jefo mata tambaya da yayi
"Me kika saka ma Tahseen a jiki"
Turo baki Hujayrah ta yi sannan ta ce
"To to me yasa za ta mareni bayan ban mata komai ba"
Ɓata fuska Mas'ud ya yi yana cewa
"Shi ne tambayar da na yi miki? "
Zama ta yi kusa da Arqam dan tsokana sannan ta dubi Mas'ud ta ce
"Nifa Karara na saka mata a jiki ba komai ba, sannan wannan karkarar ta daban ce ko a garinmu, ban takaleta da faɗa ba ta takale ni. Ni kuma ban ga wanda a duniya zai shiga gonata ba ban girbesa ba. Don haka ba laifina ba ne. Idan ita ta iya zalunci da mugunta ni da shi aka haifeni, bana bari koda karcen susa ne"
Sosai Hujayrah taba Mas'ud mamaki, bai yi tunanin ƴar ƙauye za ta iya wannan abin ba, ko shi sai haka sannan babu wanda ya ankara da ita. Arqam dai yana zaune kamar babu shi a wurin, sai dai duk abubuwan da Hujayrah take faɗa yana ji, a ransa yana faɗin 'Great job! Haka nake son naga mutum baya ɗaukar raini' (Kai kai kai 🤭🤭🤭da alama Arqam shi ma mugu ne wallahi, kusan halinsu ɗaya da Hujayrah 😂😂😂)
Ɗan shiru Mas'ud ya yi sai can ya ce
"Yanzu Hujayrah baki tsoron iyayanta su ɗauki mummunar mataki akan ki"
Taɓe baki Hujayrah ta yi sannan ta ce
"Ko kuliya manta sabo za su kai ne ina jiransu, don bana tsoron kowa sannan ban ga abin da zai sa na ji tsoron mutum ba, ka ganni nan ko maciji da kunama ba tsoronsu nake ba"
Waro idanu Mas'ud ya yi waje, shi ma Arqam kallonta yake, jinjina musu kai ta yi sannan ta ce
"Sa wasa Ya Mas'ud, kar ka manta Hujayrah ce fa jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoran mutuwa" tana gama maganar tabar wurin
Girgiza kansa kawai ya yi, shi kuma Arqam ya bita da kallo. Taro dai ya watse tun lokacin da aka kai Tahseen asibiti, kowa ya tafi gidansa wanda a lokacin kusan 9:19pm na dare. Razina da Hujayrah suka wuce cikin gida,koda suka isa Hajiya momma bata nan ta tafi asibitin da aka kai Tahseen. Kwanciyarsu kawai suka yi.
A can asibiti a gigice Hajiya Ramla ta shigo asibitin, da yake Salame tun bayan da taga abinda da Hujayrah ta barbaɗama Tahseen sai ta tsaya taga mai zai faru, ganin Tahseen ta fara soshe-soshe sai fita tare da kiran Hajiya Ramla ta sanar mata da abin da Hujayrah ta yi ma Tahseen. Bayan ta katse kiran sai ga kiran Nazima ya shigo, tana ɗaukan kiran sai Nazima ta sanar mata da sun wuce da Tahseen asibiti. Nan fa hankalin Hajiya Ramla ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi, a cikin daren ta zo asibitin, bata daɗe da shigowa ba sai ga Hajiya momma ita ma ta shigo asibitin a gigice.
Lokacin da aka fito da Tahseen daga emergency room Bacci take yi, ga jikinta duk ya yi ja, kamar borin jini, musamman wurin nonuwanta. Kai tsaye aka wuce da ita wani ɗaki. Sosai Hajiya Ramla ta shiga masifa da bal-bali akan sai ta hallaka Hujayrah tun da ta taɓa mata tilon ɗiyarta. Sai a sannan ne suka san ashe Hujayrah ce ta yi mata wannan ɗayyan aikin. Da yake Hajiya momma tasan da marin da Tahseen ta yi ma Hujayrah jiya sai kawai ta yi tunani ramawa ta yi itama don taga alamun Hujayrah bata ɗaukar raini. Senata Hajiya Ramla ta kira da yake yau ya bar ƙasar zuwa England, sanar masa da abin da aka yi ma Tahseen ta yi. Shi ma sosai ya shiga faɗa yana faɗin sai ya maka yarinyar kotu. Hajiya momma ta kira Alhaji ta sanar masa duk abin da ke faruwa, sai ya ce gaya nan zuwa.
A kusan tare ya zo da Mas'ud don Arqam ya ce ba zai zo ba,sannan ya hana Bilal zuwa, daman Mahmoud ne ya ja motar. A nan dai Alhaji ya ce a bari Tahseen ta samu sauƙi sai a zauna a ji ta bakin kowa. Da yake babbar asibiti ce sun yi ma Tahseen treatment Mai kyau Don yanzu haka ta farka kuma ta ɗan rage jin ƙaiƙayin. Hajiya Ramla da Sakhiyya ne aka bari a asibitin da yake kusan 12:35am na dare da farka. Da kuka ta farka tana kiran Mominta, a nan mom ta ce Hujayrah ce ta yi mata wannan muguntar.Rantsuwa Tahseen ta shiga yi tana cewa
"Wallahi Mom sai na Kashe Hujayrah! Sai na illata rayuwarta kamar yadda ta jizgani a gaban mutane"
Kuka take tana maganar, Hajiya Ramla da Sakhiyya sai haƙuri suke bata, suna ƙara tabbatar mata da za a ɗauki mummunan mataki akan Hujayrah. Sai a sannan ne hankalinta ya kwanta har ta koma bacci. Suma sai suka kwanta.
A can ɓangarensu Fauziyya da Zahriyya labari da ɗumi-ɗuminsa suka kai ma Hajiyan Sama. Sosai ta yi farin ciki tana dariya don har da videon Fauziyya ta yi ma Tahseen lokacin da take rawa tana susar jiki ta nuna mata. Ba ƙaramin dariya Hajiyan sama ta yi,har da saka ma wanda ya yi aikin albarka tana ce da za ta ga mai aikin har da tukuici za ta bashi.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Washe gari*
Da sassafe aka sallamo Tahseen saboda ta ji sauƙi sosai sannan ta ce ita bazata zauna a asibiti ba. Haka aka sallamota suka dawo gida Alhaji, a lokacin ya kira Hajiya momma, Hajiyan sama, Hujayrah, har da Salame. Kowa ya hallara a falon, Hajiyan sama, Hajiya Ramla da Tahseen sai aika ma Hujayrah muguwar harara suka. Tana ankare da su, hankalinta kwance kamar ba wacca ake tuhuma dalaifi ba, sai murmushi kawai take abin ta. Wannan Karon Arqam ya zo falon Alhaji, saboda Alhaji da kansa ya kirasa a waya bayan kowa ya zo. Bayan Arqam ya zauna sai ɗakin ya yi shiru na ɗan wasu sakanni daga bisani Alhaji ya yi gyaran murya ya fara magana yana duban Hajiya Ramla
"Ramla kika ce Salame ta sanar miki da Hujayrah ce ta zuba ma Tahseen karkara a jiki"
Gyara zama Hajiya Ramla ta yi tana jifan Hujayrah da mugun kallo kamar idanunta za su faɗo ta ce
"Eh Yaya Salame ce ta kirani tare da sanar min Abin da Hujayrah ta yi ma Tahseen"
Jinjina kasan ya yi sai ya dubi Salame wacca take a zaune a gefe kamar mai roƙon gafara ya ce
"Salame ina so ki bamu labarin abin da ya faru"
Cike da tsoro Salame ta fara bada labarin abin da ya faru har da ƙara gishiri da Maggi,don bayan karkara har da cewa ta zuba mata wani baƙin abu daga cikin wata kwalba. Sosai kusan kowa ya shiga mamaki musamman Hajiya Ramla, Tahseen da Hajiyan Sama, ita Hajiyan sama so take a kori Hujayrah daga gidan shi yasa take salati don ta samu makamin da za ta saka dole a kori Hujayrah daga gidan. Hujayrah da Arqam sai kallon Salame suke don ba haka labarin yake ba. Bayan Salame ta ɗige aya, sai Alhaji ya dubi Hujayrah wacca hankalinta yake kan Salame tana ayyana yadda za ta ci ubanta dakyau-dakyau sai ya ce
"Hujayrah shin abin da Salame ta faɗa gaskiya ne"
Zama ta gyara tana duban Alhaji cike da girmamawa ta fara magana
"Abbu a maganar Salame abu ɗaya nasan tabbas ba ta yi ƙarya ba, amma sauran duk ƙanzon kurege n..."
Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba Hajiya Ramla ta daka mata wata uwar tsawa. Tana cewa
"Ubanki ne yake ƙarya! shegiya ƴar iska tsintsacciyar mage! Alhaji wannan yarinya ba mutum bace mayya ce kai baka ganin yanayin idanunta ne, wallahi sai kin fuskanci hukunci mai tsauri daga wurina, munafukar Allah Ta'ala, tsinanniya"
Sosai ran Hujayrah ta yi ƙololuwan ɓaci, kallon Hajiya Ramla take babu ko ƙyaftawa, can kawai ta saki murmushi har haƙuranta farare tasa na bayyana. Alhaji ne ya taka ma Hajiya Ramla burki da cewa
"Ramla ki shiga taitayinki, miye na zagin iyayanta ke za ki daɗi ana zagar miki iyayen"
A ƙufule Hajiya Ramla take don ji take kamar ta tashi ta janyo Hujayrah ta yi mata dukan tsiya. Cike da ɓacin rai Hajiya Ramla ta ce
"Amma Yaya kisa fa ta so yi fa, yanzu da ba don su Sakhiyya sun yi saurin kai ta asibiti da yanzu ana wani labarin ba wannan ba, don haka sai na kai ta kotu an kullemin shegiya a prison, don Nan gaba tasan mu ba ƙanwar lasa ba ne"
Wannan Karon Hujayrah ta dubi Alhaji ta ce
"Abbu ka bani daman inyi magana babu laifi?"
"Za ki iya magana Hujayrah"
Babu tsoro balle firgici da dubi Hajiya Ramla idon cikin ido ta ce
"Da farko Maman Tahseen ni ba maƙaryaciya ba ce, ban san me ake kira da ƙarya ba saboda a gidanmu ba a koyamin ƙarya ba, ita wacca kike tunanin gaskiya ta faɗa to kisani ita ce maƙaryaciyar bani ba, sannan koda Kaini kotun ƙoli na duniya za ki yi to kisani bazan fasa faɗin gaskiyar abin da ya faru ba, sannan ba tsoron kotu nake ba ko gidan yari. Ni Hujayrah ɗiyar Abdullahi jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoran mutuwa bana tsoro ko firgici akan gaskiyata domin ko za a kasheni bazan taɓa faɗin abin da ban sani ba balle na yi ƙari. Saboda kuna da kuɗi ne kike tunƙaho akan zaku Kaini kotu, Kaiiii!!!! Ashe kuwa allura tana gab da tuno bakin garma. Don bakina baya shiru indai akan gaskiyana ne. Abbu zan iya bada labarin asalin abin da ya rafu"
Kallonta Alhaji ya yi sannan ya ce
"Za ki iya Hujayrah"
Gyara zama ta yi sannan ta fara koro labari tun daga abinda ya faru a falon Arqam har marin da Tahseen ta yi mata har zuwa jiya da ta rama abin ta yi mata ta hanyar zuba mata karara. Sannan ta ƙara da ce
"Abbu ni bana ɗaukan mataki kai tsaye sai dai daga baya in na yi nazari akan abin da aka min sannan nasan abin da ya dace na yi ma mutum. Dalilin da yasa na zaɓi zuba mata karara a jiki ba rama marin da ta yi min ba shi ne;A musulunce fuskar mace ita ce mafi ƙololuwan daraja daga cikin jikinta domin idan mace bata da kyawun fuska to hakan zai iya shafan auranta. Haƙiƙa manzon Allah (S.A.W) ya yi gaskiya da ya ce Allah baya son namijin da yake dukan matarsa da fuska, don haka ko mari ne babu kyau, ganin manzon Allah ya haramta marin mace a fuska sai kawai ban rama marin da ta yi min ba, na nai mi abu mai sauƙin ramawa na yi mata saboda gaba kar ta yi tunani marin wani hakan nan bai yi mata komai ba. Salame ƙarya ta yi muku akan na zuba ma Tahseen wani abu a baya, tunda nasan akwai camera a gidan mai zai hana a duba a ga cikakkyan abin da ya rafu "
Ɗakin shiru ya ɗauka, kowa yana sauran Hujayrah tana koro wajabi daki-daki ba tare da gargada ba ko tangarɗa har sai da ta dire aya, sauke ajiyar zuciya Alhaji ya yi sannan ya dubi Arqam ya ce
" Arqam tunda a ɗakinks matsalar da afku me kake ganin ya dace a yi"
Sai a sannan ne ya cire idanunsa daga kan Hujayrah, ɗan murmushi ya saki sannan ya fara magana kamar wanda aka yi ma dole ya ce
"Abba abin da Hujayrah ta faɗa gaskiya ne, nothing is wrong sannan hukuncin da ta ɗauka shi ne daidai, next time Tahseen za ta koyi hankalin daina wulaƙanta mutane without any genuine reason"
Salati Hajiya Ramla ta shiga yi tana cewa
"Muhammadu dan Abdullahi ya Rasullalahi, Arqam haka ka koma yanzu ashe ban sani ba, a ce ka kasa goyan bayan ƴar uwarka sai tsintsacciyar mage wacca Hausawa suka ce ba za ta taɓa zamantowa mage ba, Yaya ka ji halin ɗanka ko, to wallahi idan ku baza ku iya ɗaukar mataki ba to ni da kaina zan ɗauki mataki, ta shi muje Tahseen "
Tana gama maganar ta miƙe, ita ma Tahseen ta miƙe suka bar falon. Sai da suka fito Hajiyan sama ta miƙe ba tare da ta ce komai ba tabar ɗakin, Hujayrah da salame Alhaji ya ce za su iya tafiya. A tare suka fito daga ɗakin Hujayrah da Salame, cike da izza salame ta dubi Hujayrah ta ce
"Ki guji ran da za ki shiga gonata yarinya domin ruwa ba sa'ar kwando ba"
Wani ƙasaitaccan murmushi Hujayrah ta saki sannan ta ce
"Ashe Kema a wurinki haka abun yake, so ai ga fili nan kuma ga doki mai ya rage miki yanzu Salame, sai ki hau ki yi ta sukuwa ko, hhhhhh lallai kina gab da kai kanki ramin kura, don karan-batta dani babu daɗi, domin buhun ƙaya nake nafi ƙarfin danna, sannan ni buhun barkono ne duk wanda ta taɓani sai ya fyace, so ki kula don duk randa kika kuskura kika shigo gonata ha ha haaaa! Za ki ci Ubanki lakada a waje, Ina sane da abubuwan da kuke aikatawa keda uwar ɗakinki, to kibi a hankali don wannan yarinyar ta dabance, na barki lafiya "
Bata jira me salame za ta ce ma sai ta yi tafiyarta. Sheƙeƙe Salame ta tsaya tana kallon hanyar da Hujayrah ta bi, don ita a tunaninta magananta za ta tsoratar da Hujayrah har ta koma bata haƙuri to amma me, reshe ne ya juye da mujiya,madadin Hujayrah ta ji tsoro sai ma ta yi matuƙar tsorata ta da kalaman. Ganin tana ɓata lokacinta ne a tsayan sai kawai ta yi sashensu.
A ɓangarensu Hajiya Ramla bayan sun bar ɗakin sai ta kira Hajiya momma tare da ce mata ya kamata ta yi ma Arqam maganar auransa da Tahseen yanzu. Jiki na rawa Hajiya momma ta amsa mata da yanzu-yanzun nan. Wai munafikin murmushi Hajiya Ramla ta saki sannan ta katse kiran sai ta ce Tahseen ta kwaso kayanta su koma gida, rai bai so ba haka Tahseen ta ɗauko jakarta suka shiga motar sai suka tafi.
A ɓangaren Hajiyan sama mamaki Hujayrah ne ya shiga ƙwaƙwalwarta, tana tunanin aya wannan yarinyar mutum ce kamar yadda Hajiya Ramla take kokwanto akai, kwata-kwata a rayuwarta bata da tsoro, kai tsaye take abunta, dole ta yi maganin yarinyar don taga alama za ta iya taka mata burki akan cikar ƙudirinta, don yadda ta lura Arqam yana mata wani irin kallo ya tabbatar mata anya babu wata a ƙasa kuwa, ko ma mene ne za ta gyara, dole ya auri Fauziyya saboda hakan kaɗai ne sai sa ta ci dukiyar Hajiya Mubina son ranta.
A can falon Hajiya bayan Hajiya momma ta yi waya da Hajiya Ramla sai ta dubi Arqam wanda yake shirin tashi ya fita sai ta ce
"Ina za ka ce kuma magana za mu yi"
Babu musu ya dawo inda yake ya zauna ba tare da ya ce komai ba. Hajiya momma ta dubi Alhaji sannan ta ce
"Ko za ka yi mishi maganar ne?"
Murmushi Alhaji ya yi sannan ya ce
"Ai waƙa a bakin mai ita tafi daɗi, bismillah"
Gyara zama ta yi da kyau sannan ta dubi Arqam ta ce
"Arqam maganar aure ne na o maka da shi, tun da kana da aikinka, sannan ka mallaki shekarun da ya dace a ce ka ajiye mata, ai sai ka yi aure, shin kana da wacca kake so ne? Kafin mu yanke namu hukuncin?"
Ɗan shiru Arqam ya yi sai ya ɗan ɗago kansa ya ce
" I don't her any Ammie amma ina nan Ina roƙon Allah akan haka"
Daɗi Hajiya momma ta ji a ranta sannan ta ce
"To shikenan idan kai baka da shi mu muna da shi, tun da ƴar uwarka Tahseen ta kammala makaranta sannan tun tana yarinya take sonka, to mai zai hana ka aureta, don ni banga wacca ta dace da kai ba illa Tahseen, don haka ita ce zaɓinmu amma fa idan ka ɗaukemu a matsayin iyayenka"
Da matuƙar ƙarfi ƙirjinsa ya bata sautin Dummmmmm! Cike da tashin hankali wanda ke bayyane a fuskarsa ya ɗago da sauri yana duban Hajiya momma, a sanyaye ya ce... ✍️
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***