EP_________ 4️⃣
by @swrites22
🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️
*HAUSA EDITION*
🕊️ QADDARARREN AURE🕊️
SWRITES
A-K-A
YOUNG WRITER✍🏻
EP_________ 4️⃣
Saida suka zauna sannan Shenal ta ce, "Masha Allah! Allah ya sanya alheri Faryal. Gsky na taya ki farin ciki whl".
Manira ta katse ta da cewa, "Ai ba ki ga komai ba sai kin ziyarci Faryal's Touch of Elegance, wannan shi ne ma na ƙarfen, Brand ɗin ta ne na event planning and decorations".
"Kaii, Faryal ɗin dai?". Shenal ta tambaya cike da mamaki.
“Kina wasa, wannan yarinyar da kike gani ba ƙaramar attajira bace. Umm, ni kin ma tuna min wani abu. Faryal, wai ya batun Company furnitures ɗin da kika ce za ki kafa? Har yanzu baki kammala shirye shiryen ba ne? Dan whl na fara gajiya da kitchen ɗin nan".
Faryal ta yi dariya cikin sigar tsokana ta ce, "Madam Chef, Madam Chef tamu. Bari ku ga dai. Tunda na gama duk abinda zanyi a nan. Ku tashi mu je restaurants ɗin su Madam Chef, dan nayi missing ɗin girkin nan nata me daɗi".
"A'a, ita ma Manira aiki take a restaurant?". Shenal ta tambaya.
"A'a, restaurant ɗin Ammy ne, but ita take dafo abincin daga gida sai a kai can. Kin san ita anan tafi ƙwarewa".
"Kai ni ku tsaya. Sai Maganar aiki kuke, Aure fa? Har yanzu ba wanda ta fidda miji ne?".
Manira ta kalli Faryal, ita ma Faryal ta kalli Manira. Maniran ce ta fara cewa, "Tana nan tana fama da wani zauna gari banza, yana ɓata mata lokaci ina zata bawa wasu dama har aje ga batun aure".
"Eh, na ji ni zauna gari banza ne dani, amma wasu tsabar bakin hali ko zauna gari banzan ma basu ajje ba". Faryal ta faɗa tana harararta.
"Ai wallahi kin san da hankali na, ba zan zauna jiran namiji har tsawon wannan lokacin ba. Shekaru biyar fa, haba Faryal! Shekaru biyar kina jiran namijin da ba ki da tabbas akansa, namiji da ba'a shaidar sa. Ke baki ganshi bane Shenal, kwata kwata basu dace ba, ni bansan ma me ta gani a tare dashi ba taqi rabuwa dashi. Baki ga kansa ba shul kamar zakara zaiyi kera".
A fusace Faryal ta yi ƙoƙarin damqar Manira tana faɗin, "Dan qaniyar ki! Hamdan ɗin ne mai kai shul. A gabana kike faɗar haka".
Shenal kuwa in banda dariya ba abinda takeyi, har da hawaye. Yayin da su kuma suka shiga zagaye cikin office ɗin Faryal na son riqe Manira amma ta kasa, sai kawai ta ja ta tsaya tana cizon yatsa haɗi da kallon Manira data riƙe ƙugu tana mata gwalo.
Kwafa Faryal taja, ta sake haɗe gira, sannan ta ƙarasa ta fara tattare kayayyakinta kafin tayi kira ta landline din office ɗin.
Ana ɗagawa tace, "Aysah, ki kula da sauran abubuwan da suka rage. I'm off today, Idan akwai wani abu kya gabatar min da shi ranar Monday, Okay?".
Daga ɗaya ɓangaren, Aysah ta amsa, "Okay Ma'am".
Ajje wayar tayi sannan ta juyo tana faɗin, "Bestie, mu je ko". Ta faɗa ba tare data kalli inda Manira take ba.
"Hajiya Faryal Mrs Hamdan, sai Ina kuma?". Manira ta faɗa tana dariya ƙasa ƙasa.
Faryal ta watsa mata wata harara, kafin ta ce, "Idan kika sake min Magana whl in na haɗa miki wata mahangurba, sai kin fita ta window can, munafuka kawai".
Manira ta yi dariya ta ce, "Ai kin san idan faɗa ne, nafi ƙarfin ki whl".
Faryal ta ja tsaki ta nufi ƙofa inda Shenal ke tsaye tana jiransu. Suka fice, da gudu Manira ta biyo bayansu tana dariya, domin ta san ta tabo zuciyar Faryal ɗin tunda ta tabo Hamdan.
Wani ma'aikacinsu ta hango, dan haka ta kira shi, yana ƙarasowa ta bashi key motarta tare da faɗin, "Shehu, ai ka san gidanmu ko?".
Shehu wanda yake durƙushe a ƙasa tunda ya gaishe su ya amsa da, "Eh Hajiya. Zan iya gane gidan".
"To, da Allah mota ta zaka kai min gida".
Karɓar makullin yayi da hannu biyu kafin ya amsa da, "To, Hajiya".
"Ga wannan sai ka biya kuɗin keke in zaka dawo". Ta faɗa tana miƙa masa dubu uku.
Karba yayi yana zuba mata godiya, su kuma suka wuce Faryal na tambayar Shenal, "Shenal, ina motar da kuka zo da ita?".
"Ga ta can". Ta bata amsa. Wurin motar suka nufa. Shenal ta shiga mazaunin driver, Faryal ta shiga passenger front seat, yayin da Manira kuma ta shiga gidan baya. Suka ɗauki hanya.
"Ina muka nufa ne Hajiyar mu?". Shenal ta tambaya, hankalinta akan tuƙin da take.
"Africana Bite". Faryal ta amsa, tana mata kwatancen wurin.
Manira ce ta ce, "Ke Shenal yanzu yaushe za ki fara aiki?".
Shenal ta ɗan yi shiru na wasu lokuta kafin ta ce, "A gaskiya Manira, aure nake son in fara yi. Idan dai har na samu wanda nake so yake so na. Kin san fa babu wani jin daɗin da ya fi mutual love. Amma ina samun wanda na gamsu da halayensa, tuni zan shige daga ciki. Idan ya yarje min sai in nemi aiki in fara bayan auran. Idan kuma bai yarda ba, shi ma ba ni da matsala da hakan. Dan kuwa ni ma ba ni da wani ra'ayin aiki bayan aure. Nafi so in mayar da hankalina wajen kula da gidana da kaina, saboda idan ina aiki dole hankalina zai rabu biyu".
Faryal, wadda ta faɗa cikin kogin tunani tun lokacin da Shenal ta ambaci mutual love, ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce, "Yanzu dai in na fahimta kin samu wanda kuka daidaita kenan?".
"Eh to, ba nace ba, kinsan yadda samarin wannan zamanin suke, rimi rimi za'a fara soyayya, predict futures together, plan everything, daga ƙarshe kuma aci masarauta da yaqi kowa ya kama gabansa. Shiyasa kabi komai a hankali kawai, ka jira kuma kaga wanda Allah zai zaba ma. Dan ko da mun yi namu zaɓin, zaɓin Allah ne shi ne mafi alheri a gare mu". Shenal ɗin ta faɗa.
Cikin tsokana Manira tace, "Ke dai bar wani kame kame kawai kice kina jiran 💯 perfect gentleman".
Faryal ta yi dariya kafin ta ce, "Amma kafin ki samu dream guy ɗin naki, ya kamata ki fara wani abu. Zaman gidan haka bashi da daɗi ko kaɗan".
"Bestie, wasu mazan fa tsoron tunkarar macen da take Financially independent suke, saboda gani suke irin waɗannan matan kamar sun fi ƙarfinsu, ko kuma sun fi ƙarfin aljihunsu. Ko da namiji yana son mace, idan ya ji tana cin gashin kanta, zai ji tsoron bayyana mata soyayyarsa, musamman idan shi ɗin ba mai ƙarfi bane sosai".
"Waya gaya miki? jar uba". Manira ta faɗa, kafin ta ƙara da faɗin, "Ai yanzu aure ya koma kamar kasuwanci a zamanin nan. Men marry for financial security and women do too. Da yawa sunfi son mace data kasance financial stable saboda sauƙin nauye nauye. Dan idan namiji ya san you are financially independent, ba zai kalle ki a matsayin burdens ba, domin yasan ke ma za ki iya yin wasu yan kananun bukatunki ba tare da kin dame shi da bani bani ba. Sai kiga yama fi tarairayarki".
"Amma dai kinsan a Musulunci, nauyin ciyarwa, sutura, da matsuguni ga mace ya rataya ne a wuyan mijinta ko, kamar yadda Suratun Nisa'i (Aya ta 34) Allah ya fada karara cewa maza ne masu tsayuwa a kan al'amuran mata saboda abin da Allah ya fifita sashensu akai da kuma abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu. Haka kuma a cikin Huɗubar Bankwana (Hajjatul Wada'i), Manzon Allah (SAW) ya tabbatar cewa hakkin mata ne a ciyar da su, a tufatar da su gwargwadon iko. Dukiyar mace ta musamman ce, kuma ba ta da wajabcin kashe ko kwabo a gidan miji ko da tana da shi. Duk wani taimako da ta ba mijinta a matsayin tallafi yana da lada a matsayin sadaka, kuma hakan haƙƙinta ne na shari'a ba roƙo ba". Shenal ta bata amsa.
Daidai lokacin wayar Faryal ta fara ringing. Tana dubawa ta ga sunan Fayyad, "Manira ga abokin faɗanki na kira". Faryal ta faɗa.
"Waye?". Manira ta tambaya.
"Fayyad". Faryal ta amsa, tana answering call ɗin da ya kusa katsewa da sallama.
Fayyad ya amsa da, "Wa alaikis salam". Kafin ya ɗora da, "Driver learner, ya kike?".
Faryal ta ɗan yi dariya kafin ta ce, "Lafiya lau Fayyad. Wby?".
"Same here. Jiya ban kira naji yadda kuka isa gida ba, na ɗan shiga rububi ne. Ina fatan dai yau ba wanda ya sake blocking ɗin ku". Ya tambaya cikin barkwanci.
Faryal tayi murmushi kafin tace, "Eyyerh bakomai whl. Yau kam ba wanda yayi blocking namu, amma Maybe ma in anyi Manira za ta iya fito da mu".
"Haba wane ita. Wannan aikin ai na tsoffin driver ne". Fayyad ya faɗa cike da alfahari.
Wayar da take a handsfree Faryal ta miqawa Manira, wadda ta ce, "Stop bragging man. Sa'a ce kawai, kuma kowa zai iya samun irin wannan sa'ar".
Fayyad ya yi dariya kafin ya ce, "Ashe kina kusa?".
"Eh, ina nan. Kuma na ji duk abin da ka faɗa".
"And so? Ai kinsan gsky na faɗa, ko nayi karya? Idan da na bar miki motar nan jiya, za ki iya fito da ita ne daga inda take?".
"A big fat lie ma kuwa. Kai dai kawai ka yi saurin karɓar key ɗin ne, amma ai da ni zan gwada".
"Ba za ki taɓa saduda ba. Kinga bawa me wayar wayarta abeg".
"To Alhamdulillah, tunda bani nace ta ba ni ba wayar ba". Ta faɗa tana miƙa wa Faryal wayar, wadda take ta dariyar dramar tasu.
"Hello Fayyad". Faryal ta faɗa.
"Faryal, wannan yar uwar taki fa bakinta ba ya rufuwa ko kaɗan". Fayyad ya faɗa.
"Kamar ka sani whl Fayyad. Ni kaina kullum sai ta sani ciwon baki". Faryal ta amsa tana dariya a hankali.
"Ba zan miki musu ba. She can from all indications. Amma duk lokacin da ta dame ki, ki kira ni, zan yi miki maganinta". Fayyad ya faɗa.
"Hey, Mr Man! Karka manta ni fa ba mota ba ce". Manira ta faɗa ta yadda zai iya ji.
Fayyad ya yi dariya kafin ya ce, "You will be easy to deal with more than a car".
"Ai kuwa idan ka yi haka, to ka biyani". Faryal ta faɗa. Haka suka cigaba da hira cikin barkwanci har na tsawon 15 minutes kafin daga bisani suyi sallama ta kashe.
"Shi kuma wannan ɗin waye?". Shenal ta tambaya bayan Faryal ta ajje wayar.
Nan Faryal ta bata labarin haɗuwarsu ta jiyan. Shenal ta dinga dariya, kafin ta ce, "Kaii dama ina wurin, daga gani bashi da matsala".
Faryal ta amsa, "Indeed whl". Nan suka ci gaba da hirar Fayyad har suka isa Africana bite ɗin.
Bayan sun sanya order abinda suke so suka nemi wuri suka zauna. Ba jimawa order su ta iso, kowanne ya ja plate ɗin sa ya fara ci yana jijjiga kai haɗi da lumshe idanu saboda yadda daɗin abincin ya shiga ratsa su.
Ba tare da sun sani ba Manira ta zaro wayarta ta shiga ɗaukarsu video tana dariya, su kuwa sun zage sai santi suke zubawa. "To ko dai a ƙaro muku da wasu nau'ikan abincin namu ne?". Thumb kawai Shenal ta mata tana kai lomar chicken biryani, ta ma kasa magana.
Daga bayansu, suka jiyo sallama, wadda tasa su dagowa dukkansu, idonsu ya sauka akan wani saurayi dake tsaye. "Heyy ladies".
"Hello". Manira ta amsa, hankalinta a kan wayarta da take saving videon su Shenal da ta ɗauka.
"May I?". Ya tambaya, yana kallon kujerar da ta rage ba kowa akai.
Faryal, wadda take kallonsa, ta amsa da, "Why not".
Zama yayi yana faɗin, "Good evening ladies". Hankalinsa a kan Manira, wadda tun dagowar farko bata sake ɗagowa ba.
Da ƙafa Faryal ta ɗan zungureta, hakan ya sa ta ɗago kai. Suka haɗa ido da shi, gajeren Murmushi tayi kafin tace, "Sannu".
"Sannu". Faryal ta kwaikwaye ta, making a funny face kafin ta daɗa da faɗin. "Ce miki akayi ɗan caburos ne, kamar ke".
Dariya sukayi, ban da Faryal da ta ce, "Umm, mutum dai bai ji daɗin halinsa ba".
Da ragowar dariyar da bata gama gushewa akan fuskarsa ba yace, "Haka yan mata masu aji suke ai ƙawarmu. Well, My name is Aminullah, amma ana kirana Amin. Ban san ko zan iya sanin naku sunayen ba?".
Faryal ta nuna Manira kafin ta ce, "Shes Manira by name, the CEO of this restaurant".
Waro fararen idanunsa yayi cike da mamaki ya ce, "It's really her place?".
Manira ta juya ga Faryal tana faɗin, "Oh, Allah na gode maka! Wai wani tsautsayin ne yasa na yarda muka taho dake nan wurin Faryal?".
"Auu, dama da yardarki ne ma nazo nan ɗin?".
Da sauri Shenal ta ce, "Kun ga ku rufa mana asiri! Kada ku jawo mana hankalin mutane. Ku bari sai kunje gida sai ku ɗaura daga inda kuka tsaya, in ma rataye kanku zakuyi sai kuyi".
"Ki ma barta. Ta dai san ba zan daku ba whl". Manira ta faɗa cike da tsiwa. Faryal ta ja kwafa.
Haka suka cigaba da shan chapter har da Amin da ya sake sosai a cikinsu as if they had known each other for a long time, with a warm and friendly demeanor. Amin ya kasance perfect gentleman, courteous and respectful towards ladies, hakan ya sake armasa shi a wurinsu.
A haka suka kammala cin abincin har Amin ma da Shenal tasa aka kawo masa. Ko da suka gama, ƙara gyara zaman hira suka yi aka cigaba daga inda aka tsaya, sun ɗan jima kafin su tashi dan zuwa biyan kuɗin.
Faryal tace a buga mata total harda na Amin duk zata biya. Manira tayi dariya tace, "Shenal gafa mutumiyar, omoo rich kids, kice yau spoiling ɗin mu aka zo yi kawai".
Amin ne yace, "A'a ba za'ayi haka ba Aunty Faryal, kiyi haƙuri ki bari na biya".
"Ka barta ta biya Amin, raba arne da makami ai ibada ne". Manira ta faɗa cikin sigar tsokana. Shi kuma Amin ya dage saidai Faryal ta bari ya biya, daƙyar ya haɗa ta da Allah da Annabi ta hakura ta barshi ya biya.
Haka suka fito harabar wurin Shenal na masa godiya kafin suyi sallama, bayan ya karɓi number Manira a wurin Faryal.
Ko da suka ɗauki hanyar gida haka suka sako Manira a gaba da tsokana iri iri wai tayi kamun babban kifi a tsakiyar Teku.
A gidan su Faryal suka yada zango, sai da sukayi sallar Magriba sannan Shenal ta yiwa su Faryal sallama bayan sun mata alqawarin zuwa gidansu ran sunday. Daga nan suka fito tare da Manira, Shenal ɗin zata sauketa a gidansu ne sai ta wuce.
Bayan sun wuce, Faryal ta koma ciki ta watsa ruwa, sannan ta kwanta tana ɗan hutawa har aka kira sallah isha, tashi tayi ta gabatar kafin ta ɗauki wayarta ta fita zuwa falo, inda ta tarar da yan gidan nasu zaune. Da alama ba su daɗe da haɗuwa a falon ba.
Tana shigowa falon Beta ta nufeta da gudu ta maqale ta. Faryal ta riqe ta tana murmushi kafin ta ce, "Beta zamu faɗi fa, sakeni in gyara".
"Bahan(Sister) abu zan faɗa miki, ki tsaya kiji". Beta ta fada tana ƙoƙarin tsalle ta kama kunnen Faryal.
Ɗan rage tsawonta Faryal ɗin tayi, yayinda Beta ta kama kunnenta ta shiga raɗa mata wani abu, tana yi tana kallon Daadee.
Sai da ta gama sannan Faryal ta gyara tsayuwarta, tana dariya ta riqo kafaɗun Beta ɗin suka ƙarasa shiga cikin falon.
Daadee ta ce, "Kun ga mun wannan ƙaramar kwaron, Ita ma wai ta iya kai tsurku".
Faryal ta sake yin dariya ta zauna tana faɗin, "Kai Daadee! Beta ɗina fa ba ta gulma. Labari kawai ta ba ni".
Hadiyyah, wadda take yanka guava, ta amsa da, "To, idan da gaske ne, me ya sa baza ta faɗa da babbar murya ba? Daadee, ki rabu dasu, dama ai Faryal ɗin ce ta koya mata kai tsurkun".
Kafin Faryal tayi Magana Nasar ya shigo da wireless headphone a kunnensa.
Fasa faɗin abinda tayi niyya ta yi ta juya ga Maama tare da faɗin, "Yauwa Maama, key mota ta yana wurin waye ne?".
"Motarki? Dama ba da motarki kuka zo ba?". Maama ta tambaya da mamaki.
Faryal ta gyara zamanta, in a serious tone tace, "A'aa? Maama. Ai na turo wani daga cikin ma'aikatanmu ya kawo min ita gida tun lokacin da Manira da Shenal suka same ni a Office, lokacin zamu fita ne a motar Shenal ɗin sai naga gwara kawai a dawo da tawan gida".
Kafin Maama tace wani abu, Nasar da ya nemi wuri ya zauna ya cire wireless headphone ɗin ya tsinci last sentence ɗin nata. "Tana wurina. Da ya zo ne ya same ni a compound, sai ya ba ni key ɗin".
"Nasar, Hope my car is safe?". Faryal said, looking curious.
Nasar ya ɗan susa kunnensa kamar marar gsky, kafin ya ce, "Eh". Ya faɗa yana miƙo mata Key da ya ciro daga aljihunsa.
Maama, wadda ta ƙure shi da ido tace, "Nasar, kar ka ce min da motarta ka fita?".
"Aa Maama". Ya amsa, ba tare da ya bari sun haɗa ido ba.
"Sa idon ka cikin nawa idan har da gaske kake". Ɗagowa yayi yana kallon Maama sai kuma dariya ta kubce masa.
Daadee ta ce, "To kai a yaushe ma ka koyi tuƙi da har ka fara ɗaukar mota ka fita kai kaɗai?".
"Idan wani abu ya lalace a motata ko, you'd be responsible for it". Faryal ta faɗa tana maida masa da key tace, "Je ka ɗauko min wasu takardu a ciki".
"Nawa za ki biya". Nasar ya tambaya yana dage mata gira.
"Mtwee! Idan na haɗa ma wani mari ko? Zaka tashi kaje ka ɗauko min ko sai na tashi kaga tsayi na".
Wartar Key ɗin yayi ya tashi ya nufi waje yana gunguni.
Kusan mintuna uku sai gashi ya dawo. Faryal ta ɗauke idanunta daga kan tv, ta kalle shi da niyyar tambayar ina takardun, ganinsa empty handed.
Sai ya nuna mata wallet yana faɗin, "Ke kuma yaushe kika fara amfani da wallet ɗin maza?".
"Ohhh!". Faryal ta faɗa tana dafe goshinta, kafin ta karɓi wallet ɗin ta ajiye a kan cinyarta. Ta ce, "Ina takardun suke?".
"Ni fa ban ga wasu takardu a ciki ba in banda wannan wallet ɗin dana baki". ya amsa yana haɗe rai dan ma kar tace ya koma ya sake dubawa.
Faryal ta yi ɗan shiru tana tunani kafin ta ce, "In dai basa mota to na barsu a Office kenan".
"Ita wannan wallet ɗin ta waye?". Daadee ta tambaya hankalinta akan Faryal ɗin.
Faryal ta ɗago idanunta ta saci kallon Maama, wadda hankalinta yake kan wayarta. Kafin tayi saurin maida kallonta kan Daadee tace, "Maybe ta ma'aikacin mu ne da na aiko ya kawo motar, shi ne ya mantata a ciki. Amma ranar Monday zan mayar masa da ita, in sha Allah".
Tana rufe bakinta, wayarta na ɗaukan ruri, ko bata duba ba tasan waye saboda ringing ɗin sa dabanne dan haka ta miqe kawai riqe da wallet ɗin ta bar falon.
Tana ƙoƙarin shiga ɗakinsu ta amsa wayar ganin tana ƙoƙarin katsewa. Muryar hamdan ce ta daki dodon kunnenta, "Assalamu alaikum".
"Wa alaikas salam wa rahmatullahi wa barakatuhu". Faryal ta amsa da wata irin sassanyar murya, kafin ta daɗa da faɗin, "How's my Man doing?".
"Lafiya lau Alhamdulillah. Wby?". Ya tambaya shi ma cike da kulawa.
"Same here. How's everything?".
"Everything's dry fa"
"Haba dai? Babban mutum kamar ka". Faryal ta faɗa da sigar tsokana. Bai bata amsa ba sai muryarsa data tsinto a background yan shiga Magana da yan gidan su.
"Childhood friend ɗi na fa ta dawo". Faryal ta katse masa surutun da yake zubawa a background ɗin.
"Haba, wacece?".
"I want you to guess".
"Ummm, Shenal ko?".
"Ummm, yeah! Finally you guessed right".Ta faɗa tana murmushi, kafin ta shiga bashi labarin yadda ranarsu ta kasance.
"Kice min dai yau an sha gulma kawai". Ya faɗa yana yar dariya.
"Maybe ita da Manira, ni ai bana gulma". Ta faɗa tana dan murmushi.
"Ba wani nan. Ke dai faɗi gaskiya dan nasan har dake. Maybe ma kece leader ɗin". Faryal ta yi dariyar yaqe, dan ba ta ji daɗin amsar da ya bata ba. Amma in da sabo zuwa yanzu yaci ace ta saba da yadda Hamdan yake magana da ita kai tsaye. He never minces his words, kuma ko tunanin maybe kalamansa na iya sawa taji ba daɗi ba yayi.
Wani lokacin sai tayi tunanin ko dan irin yadda suka saba da juna ne kamar wasu abokai yasa yake mata haka. Amma idan ta kalli abun ta fuskar soyayya, sai taga sam hakan bai bada wata ma'ana ba, saidai kuma bata taɓa masa magana akan haka ba ko ta nuna masa rashin jin daɗinta.
Haka dai ta ɗaure suka cigaba da hirar, wadda ba wani armashi a cikinta dan daga labaran ball sai na dramar da suke kwasa shi da mahaifinsa, haka dai take biye masa har ya gama surutun nasa ya saki ya tafi hira da wasu Cousins din sa da suka shigo a lokacin da suke wayar, wadda duk hirar suma akan match ɗin ranar ne. Shuru kawai ta yi tana saurarensu kafin taji muryarsa na faɗin, "Ina zuwa Faryal. Barin shiga in ga Mom in dawo".
"In jira ka ne a online ɗin?".
"Eh, ki jira ni, in sha Allah. Da zarar na fito daga wajenta, zaki ganni".
"Alryt to sai na ganka, ka gaishe ta". Daga haka sukayi sallama ya kashe.
Tana shirin miƙewa sai ga wani kiran ya shigo. Tana dubawa ta ga Barr. Hashim ne, ɗagawa tayi suka gaisa kafin tace, "Ya aikin naku Barr?".
"Aiki gashi nan so stressful and annoying most times".
"But it's a very good work fa". Faryal ta faɗa.......