Chapter 12
by @authorrukie
Na tashi da sassafe, tun kafin kowa ya farka. Na san aikin da ke jirana, don haka ban tsaya ɓata lokaci ba. A gidanmu, akwai ayyukan da na san dole ni ce zan yi su, ko da kuwa sauran mutanen gidan suna cikin barci.
Na nufi tsakar gida na fara sharewa, ina jin sanyin safiya yana ratsawa jikina. Bayan na gama, sai na ɗauki bokiti na debo ruwa, na ajiye shi a inda ya dace. Na gyara wasu abubuwa a cikin gida, sannan na koma kicin domin in fara shirya abin da za a ci da safe.
Duk wannan lokacin, gidan yana cikin shiru. Wasu suna barci cikin kwanciyar hankali, wasu kuma kamar ba su da wani aikin yi. Ni kaɗai nake ta kai da komowa, ina ƙoƙarin kammala komai kafin su farka.
Wani lokaci nakan tsaya ina kallon ƙofofin ɗakunan, ina tunanin yadda wasu suke da damar yin barci yadda suke so, alhali ni kuwa ba kasafai nake samun cikakken hutu ba.
Amma na saba. Na san cewa idan ban yi waɗannan ayyukan ba, babu wanda zai tashi ya yi su a madadina. Sai na ja dogon numfashi, na ci gaba da aikina, ina addu’ar Allah Ya ba ni ƙarfin jure rayuwar da nake ciki.
Bayan na gama sauran ayyukan, sai na dama koko domin abin sha na safe. Na auna garin kunu a tukunya, ina shirin haɗa shi yadda ya kamata. Tun da wuri nake son gamawa, saboda na san cewa kafin kowa ya farka, akwai sauran ayyukan da suke jirana.
A gidanmu, hatsin da Baba yake nomawa ya zama kamar shi ne babban abincin da muke dogaro da shi. Kusan kullum sai an yi wani abu da shi, ko koko, ko kunu, ko kuma a niƙa shi a yi tuwo. Wani lokaci ma nakan ji kamar hatsin ne kaɗai ya san hanyar shiga cikin tukwanen gidanmu.
Hatsin da ake samu daga gonar Baba yana taimaka wa iyalinmu sosai. Duk da haka, ni da sauran yaran gidan ba ma rayuwa iri ɗaya. Wasu suna samun lokacin hutawa da jin daɗinsu, ni kuwa tun da sassafe nake tashi domin in tabbatar da cewa komai ya tafi yadda ya kamata.
Ina cikin motsa kokon ne na ji motsin mutum daga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan. Na ɗaga kai ina sauraro, ina tunanin ko wani daga cikin matan gidan ne ya farka.
Na ci gaba da aikina, ina sa ran zan kammala kafin sauran mutanen gidan su fito. Ban san cewa ko da ranar ta fara ne cikin shiru ba, ba lallai ne sauran lokutan ranar su kasance haka ba.