MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 86

by @maimunabala209

*MATAR GIDA BOOK* 2



*SHUUKRAN*/023




P86



A wannan dare bacci ɓarawo ne ya dauki Hajiya Bilƙisu,kusan kwanan zaune ta yi tana tunani ta haɗa wannan ta kwance waccan,sosai ta shiga damuwa wanda hakan ya haifar mata da ciwon kai mai tsanani dake da alaƙa da cutar hawan jini da ta dauki tsawon shekaru tana fama da shi,har karfe uku na dare Hajiya Bilƙisu na zaune saman darduma tana addu'ar Allah ya rufa mata asiri,Allah ya sa Alhaji Babba ya janye zancen zuwa neman gafara wajen iyayen yaran da suka sa aka saka da kuma mazajensu,ina ma da Alhaji Babba zai ce ta kashe iya kungiya kawai amma banda batun zuwa niman gafara,tarwatsa kungiya bazai ɗaga mata hankali ba saboda ba ta da asarar komai,dukiyoyinsu da Alhaji Babah ya ce zai karɓa nan ma bata damuwa a kan wannan,amma har cikin zuciyarta tana jin kunya da tsoron zuwa neman gafara,ba ita ta samu bacci ba sai karfe huɗu da wasu mintina nan ma ba da saninta ba bacci ya dauke ta,karfe shidda da wasu mintina na safe ta tura saƙon gayyata zuwa group ɗin matan gida kamar yadda Alhaji Babah ya umurce ta,Mama ce kwance cikin ɗakinta zazzaɓi ya rufeta,yau kwanaki tara kenan  da faruwar haɗari,damuwa da yawan tunani tare da rashin cin abinci da kuma yawan kuka da Mama ke yi duk sanda babu hankali mutane a kanta musamman cikin dare su suka haifar wa Mama zzzaɓi mai zafi,tun daren jiya take kwance,hannunta manne da drip ga ledar magunguna gefenta,Babah Rabi ce zaune cikin dakin daga gefenta kowa wani yaron makwabciyar Mama ne mai suna Aliyu wanda ya yi karatun health zaune gefe Babah Rabi yadda yake nunawa Babah Rabi wasu magunguna da ya siyawa Mama ɗazu,sosai Aliyu yana da kokari da mayar da hankali kan karatu, wanda hakan yasa yake iya yiwa mutane treatment cikin unguwa,bayan ya  gama nunawa Babah Rabi magunguna ne ya yi masu sallama daga haka ya fita ɗakin,bayan fitowarsa da wasu ƴan mintina Baffah ya shigo ɗakin bakin dauke da sallama jin muryar Baffah yasa Mama share hawaye dake fuskarta da sauri,Babah rabi ce ta amsa sallamar Baffah,a hankali baffa ya tako har inda Mama ke kwance suka gaisa,sosai murya Mama ta yi  ƙasa dalilin ciwo da kuma yawan kuka da take a ɓoye ba tare da sanin Babah rabi da Baffa ba,bayan sun gama gaisawa ne Baffah ya kalle cikin idanun Mama sarai ya gane kuka take kafin ya shigo ɗakin,waje ya samo ya zauna cikin ɗakin inda yake fuskantar gadon da Mama ke kwance a kai,bayan ya zauna ne ya bude baki a hankali ya ce ''kuka ke yi ne yayah?" Mama ta yi shiru bata ce masa komai ba,Babah Rabi dake haɗawa Mama tea ta mayar da dubanta ga Mama ta ce ''kuka kuma?" ta ƙare magana fuskarta dauke da mamaki ita dai Mama bata tanka su ba,ɓoyayyar ajiyar zuciya Baffa ya sauke kafin ya ce ''addu'a suke bukata daga gareki yanzu,damu baki ɗaya wanna kukan bata da fa'idah,ki tuna Allah ne ya ba ki yaran nan kuma ya karɓi abinsa babu yadda muka iya da ikon Allah sai dai mu gode masa,duk sanda Ubangiji ya jarabce bayinsa abinda ake so dasu shine su gode masa, tabbas da ciwo rasa duka ƴaƴanka lokaci guda amma kuka ba mafita ba ce addu'a ce mafita,in muka dage da yi masu addu'a da yardar Allah zamu samu sauki cikin zuciyoyin mu''..daga haka ya yi shiru na wasu ƴan sakanni can ya ce ''rasuwar yaran nan ba iya ke kadai ya shafa ba rashi ne da ya shafemu duka,dan Allah ki yi hakuri da daina kukan haka'' Baffah ya dauki a ƙallah sama da mintina talatin yana yiwa Mama nasiha tare da rarrashi,bayan Baffah ya gama yiwa Mama nasiha ne Babah Rabi ta mayar da dubanta ga Mama sosai take tausayawa ƴar uwarta harda ita ma daurewa kawai take saboda tun daga ranar da aka yi haɗarin zuwa yau bata da wani nitsuwa duk abinda take daurewa kawai take yi,hannu take ta share hawaye da ya gangaro mata ba tare da saninta ba,Baffah ya gyara zama tare da kallonsu duka biyu ya ce ''ina son jibi na koma Gombe amma wannan koke koken da ku yi ba zai bani damar tafiya ba'' Mama ta kallesa shiru na wasu ƴan mintina saboda ba yaushe take fahimtar abinda ake faɗi ba,tun sanda akayi haɗari wata lalura ta sami Mama da ita kanta bata san da me zata kira wannan lalurar ba,sau da yawa in ana magana da ita ko ana hira a gefenta ta kan tsinci kanta da daina jin duk abinda ake faɗi,bata ji,bata gane komai ba,ga ta dai zaune tare da mutane amma sai a yi ta magana bata ji ba,yanzu ɗin ma hakan ne ya faru,duk nasiha da bayanai da Baffah ya mata ba duka ta ji ba,kawai ta yi ta kallonsa tun sanda ya fara magana har ya gama babu wani abinda ta fahimta,a hankali ta sauke numfashi tare da gyara kwanciya,a hankali ta buɗe baki ta ce ''dan Allah ina son da na samu lafiya zan tafi Niger zan dauki ƴaƴan Aisha Auwal tare da ƴaruwarsa zan tafi da su zan sama masu makaranta a can'' Babah Rabi da Baffah suka zubawa Mama ido basu ce komai ba hakan yasa Mama daura da ''bana jin zan iya cigaba da zama a wannan gidan da ma garin nan baki ɗaya,ina da yaƙini in na bar Nigeria zan samu sauƙin abinda yake damuna''daga haka ta mayar da dubanta ga Baffah ta ce ''ina tunanin sanya gidan nan a kasuwa in an samo masu siya ka yi min magana in Allah ya yarda da an siyar zan yi amfani da kuɗi na fara wata sana'a  a can Niger'' shiru Baffah ya yi na wasu ƴan mintina can ya ce ''in hakan ya yi maki babu damuwa zan nimi dillalai su yiwa gidan kuɗi'' a hankali Mama ta jinjina kai murya can ƙasa ta ce ''nagode''










Kamar yadda Alhaji Babah ya faɗa washegari misalin ƙarfe sha biyu na rana Alhaji Babah tare da Hajiya mahaifiyar su Hajiya Bilƙisu tare da Hajiya Zulfa'u da Hajiya Bilƙisu suka diro garin Kaduna, cikin motar Alhaji Babah suka zo wanda driver Alhaji Babah ya tuƙa su,a gidan Hajiya Bilƙisu suka sauka daman a gidan ta za a yi taro,tun kafin su taso Hajiya Bilƙisu ta kira ƴar aikinta ta ba umurni da ta yi masu girki,a babban parlourn baƙi Alhaji Babah ya yada zango,ita ko Hajiya mahaifiyar su Hajiya Bilƙisu tana can ɗakin Hajiya Bilƙisu kwance tana huta gajiyar hanya,a can wajen su Hajiya Bilƙisu kuwa babu wacce take cikin nitsuwa kowacce da kalan tunanin da take,kallo ɗaya zaka masu ka fahimci dukkaninsu suna cikin dimuwa da tashin hankali musamman Hajiya Biklisu,ita dai Hajiya Zulfa'u matsalarta kwara ɗaya ce sanin kanta ne in za a tafi niman gafara gidan iyayen yaran da suka sa aka saka dole da ita za a tafi,saboda duk abubuwan da Hajiya Bilƙisu ke yi da saninta kenan in Hajiya Biklisu zata bada hakuri dole tare zasu bada hakuri,hakan yana nufi harda ita cikin ɓarnar da aka yi,zaune take cikin parlour ta buga tagumi idanunta kan tv tana kallon shirin da ake haskawa cikin tv ta korawa tv ido amma ko kadan hankalin baya kan shirin da ake cikin tv yayin da Hajiya Biklisu na ɗaya dakin da babu kowa tana aikin tunani,suna cikin wannan yanayi ƴar aikin Hajiya Biklisu ta yi sarving ɗin su abinci da lemo inda ta kaiwa kowa nasa,bayan sun gama cin abinci duk suka yi wanka,Hajiya Bilkisu ce ta kaiwa Alhaji Babah abincinsa can parlourn baƙi,babu laifi Alhaji Babah ya ci abinci haka ma Hajiya sosai ta sake jiki ta ci abinci hankalinta kwance,Hajiya Biklisu tare da Hajiya Zulfa'u kowa basu wani ci abinci ba musamman Hajiya Bilƙisu tsakura abincin kawai suka yi,misalin ƙarfe ɗaya da wasu mintina wata babbar mota ce dauki da kujeru da canopy irin wanda ake amfani da su wajen bukukkuna ta yi parking kofar gidan Hajiya Bilƙisu,mai gadi ne ya buɗewa driver gate wanda hakan ya bawa driver babbar motar damar shigar da babbar mota harabar gidan,tare da taimakon mai gadi samari biyu da suke cikin mota tare da driver suka sauke kujerun da canopy,bayan sun gama sauke kujerun ne mai gadi ya koma bakin aikinsa yayinda  driver da samarin suka suka shiga aikin kafa canopy da jera kujeru,ba a yi decorating compound ɗin ba,saɓanin duk sanda za a yi taro matan kungiya ke kashe uban kuɗaɗe wajen dacoration,dalilin da yasa Hajiya Bilƙisu bata kashe kuɗi wajen yin dacoration ba wanna taro ba taro bace ta kungiya wacce suka saba yi,taro ce ta rufe kungiya,iya kujeru da canopy kadai aka kafa,girke girke da suka saba yi duk sanda za su yi taro nan ma Hajiya Bilƙisu ba ta yi order abinci ba iyaka order ruwa da lemo ta yi katan katan,karfe hudu da wasu mintina na yammacin wannan rana gidan Hajiya Biklisu ya cika maƙil da manyan mata, matan kungiyar matan gida,kamar dai yadda suka saba kowacce ta yi ado iya ado wasu sun saka tsadaddun lesses wasu kuma atamfuna masu mugun tsada,wa'inda suke aure masu kuɗi sun baza ƴan kunne da sarƙokin gold sai baza ƙhamshi suke., ya yinda wa'inda suke auren middle class sun yi ado da ƴan kunne da sarƙokin masu ɗan sauki kuɗi irin ƴan dubu ashirin haka zuwa dubu talatin,babu laifi duk cikin su babu wacce ta daura zanin ƙasa da dubu hamsin,wannan dalilin yasa sun fito rass abinsu sai baza  ƙhamshi suke kaman sun yi wanka da turare,duk wacce ka kalla cikin su zata katabbar lallai ba ƙananun mata bane,sun wuce raini,da yawa yawan su suna kasuwanci yayin da wasu daga cikin su suna aikin gwamnati,wasu kuma mazajen su ne ke da kuɗi Allah kuma ya daura su bisa kan mazajen sai yadda suka yi da mazajen nasu,wanda haka ya basu damar yin abinda suke so,sai dai duk wannan aji da izza da isa irin na matan gida hakan bai hana su halin ƙaranta ba,duk sanda suka ziyarci ɗaya daga cikin su duk abinda suka gani a gidanta ya burge su dauka suke ba tare da tambaya ba, duk abinda suka ga dama shi suke yi,haka zalikah duk abinda suka gani dauka suke walau sutura ko kayan abinci ko ma menene dauka suke ba tare da izini ba,wanda hakan ba komai bane a wajen su,sun dauke hakan normal ne 









*SHUUKRAN*