KADDARAR ZUCIYA

BACK TO ABUJA

by @jiddaahbarkum

KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER THIRTY-EIGHT: 38
BACK TO ABUJA
JIDDAAH BARKUM

Safiyar ranar ta kasance mai cike da hazo da tsananin sanyi, gidan Alhaji Kabeeru ya tashi cikin wani irin shiru na daban, domin yau ce ranar da Princess ɗinsu za ta koma Abuja, manyan akwatunanta guda biyu suna ajiye a tsakiyar falo, tamkar suna tunatar da kowa cewa lokacin tafiya ya yi, Inteesar ta fito daga ɗakinta sanye da doguwar ash abaya wadda aka yi wa ado da zare mai kyau, fuskarta babu ko ɗigon kwalliya, idanunta kuma sun ɗan yi luhu-luhu saboda rashin isasshen barci da kuma fargabar rabuwa da gida, ta tarar da Daddy da Mommy Haleema zaune a falo, a hankali ta ƙaraso, ta zame ta zauna a ƙasa, sannan ta ɗora kanta a kan cinyar Daddy, Daddy ya shafa gashinta a hankali, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Princess ɗina, kukan me kike yi kuma? Karatun fa na ’yan watanni kaɗan ne ya rage miki kafin ki dawo gida gaba ɗaya,” Inteesar ta shagwaɓe fuska, hawaye suka fara zuba mata a kumatu, “Daddy, zan yi kewarku sosai, gaba ɗaya jikina ba ya ba ni daɗin tafiyar nan,” Mommy Haleema ta matso ta zauna kusa da su, sannan ta yi amfani da gefen mayafinta ta goge wa Inteesar hawaye, “Haba, Inteesar, addu’a za ki riƙa yi, kin ji? Karatunki shi ne babban abin da kowa yake kallo yanzu, ki tafi lafiya, Allah Ya tsare miki mutuncinki da mutuncin gidanmu,” cikin kuka, Inteesar ta rungume Mommy, sannan ta juya ta rungume Daddy sosai, tamkar ba za ta sake ganinsu ba, bankwana da iyayenta ya raunana zuciyarta, har sai da Yaya Abubakar ya shigo ya tunatar da su cewa lokaci yana tafiya, don haka su hanzarta kafin ta rasa jirginta, a daidai lokacin ne Aliyu ya yi ƙaho a ƙofar gida, ya zo da motarsa domin ɗaukar akwatunan Inteesar da kuma raka ta zuwa filin jirgin sama, Yaya Khalil ma yana tare da shi, da suka shiga falon, Aliyu ya gaishe da Daddy, Mommy Haleema da kuma Yaya Abubakar cikin girmamawa, bayan sun amsa masa, sai suka fara shirya yadda za a ɗauki kayanta, ganin Aliyu ya zo ne ya sa Yaya Abubakar ya yanke shawarar barin shi ya raka Inteesar zuwa airport, tare da Yaya Khalil domin ya kasance tare da su, Aliyu ya lura da yadda idanun Inteesar suka yi ja saboda kuka, sai ya ji wani irin abu ya tokare masa zuciya, amma dole ya dake, musamman kasancewar iyayenta suna nan, bayan an gama saka akwatunan a boot ɗin mota, aka yi addu’ar tafiya, tare da addu’o’i da fatan alheri daga iyayenta.

Aliyu ne ke tuƙi, Yaya Khalil kuma yana zaune a kujerar gaba, yayin da Inteesar take zaune ita kaɗai a kujerar baya, ta shagwaɓe fuska tana kallon titin ta tagar mota, lokaci-lokaci tana share hawayen da suka ƙi tsayawa, Khalil ya juyo ta madubin gaba yana kallonta, sannan ya ce, “Wai ke kuwa, Princess, kukan nan ba zai ƙare ba? To, wallahi idan kika isa Abuja kika ci gaba da kuka, Yaya Umar zai ɗauka cewa mu ne muka yi miki laifi,” Inteesar ta turo baki, ta share hawayenta, sannan ta yi banza da shi, Aliyu kuwa, ta madubin tsakiyar mota yake kallonta, kowane ɗigon hawaye da yake gani yana ratsa zuciyarsa, amma ya kasa samun kalaman da za su kwantar mata da hankali, a ƙarshe, sai ya yi shiru yana tuƙi, lokaci-lokaci yana kallonta ta madubin, har suka isa filin jirgin sama na Aminu Kano International Airport (MAKIA), wurin ya cika da mutane masu zirga-zirga, Aliyu ya yi parking, suka fito gaba ɗaya, bayan sun sauke akwatunan, suka nufi cikin babban falon jiran shiga jirgi, wato departure hall, lokacin da sanarwar fara shiga jirgin Abuja ta amsa kuwwa a cikin falon, zuciyar Inteesar ta buga da ƙarfi, da gaske tafiyar ta yi kusa, Khalil ya matso kusa da ita, ya ɗora hannu a kafaɗarta, muryarsa ta sauya, ta zama mai cike da taushin soyayyar ɗan’uwa, “Princess, ki kula da kanki sosai, karatu za ki je yi, kuma kowa yana miki addu’a a gida, idan wani abu ya taso, kada ki ɓoye mini, kin ji?” Inteesar ta kasa daurewa, ta jefa kanta a ƙirjin Yaya Khalil, ta fashe da kuka mai taɓa zuciya, kamar a yau ne karon farko da za ta baro gida domin zuwa karatu a Abuja, Khalil ya rungume ta sosai yana bubbuga bayanta a hankali, duk da ƙoƙarinsa na nuna jarumta, shi ma idanunsa sun cika da hawaye, “Kin ji ko, Princess? Ki kula da kanki,” ya sake faɗa cikin sanyin murya, Inteesar ta gyaɗa kai tana kuka, bayan ta ɗan lafa, Khalil ya janye ta a hankali, ya kalli Aliyu, ya yi masa murmushin yaƙe, sannan ya ce, “Bari na ɗan matsa na ba ku mintuna biyu ku yi sallama,” ya juya ya ba su sarari.

Inteesar da Aliyu suka kasance su kaɗai a tsaye, Aliyu ya matso kusa da ita, ya zuba mata idanuwansa waɗanda ƙauna da damuwa suka cika, ya ga yadda take ƙoƙarin danne kukanta, amma hakan ya ƙara sa shi jin tausayinta, muryarsa ta yi ƙasa sosai, cike da rarrashi da ɗacin rabuwa, “Babygirl…” Ya kira ta a hankali, Inteesar ta ɗago idanunta da suka yi ja saboda kuka, ta kalle shi, Aliyu ya numfasa, yana kallon fuskarta cike da ƙauna, “Kukan ya isa haka, Babygirl, kin karya mini zuciya gaba ɗaya tun ɗazu a mota, idan kika ci gaba da kuka, ya kike so in juya in koma gida ni kaɗai?” Ta ciza leɓenta na ƙasa, muryarta tana rawa lokacin da ta amsa, “Zan yi missing ɗinka ne sosai, gaba ɗaya nake jin kamar kada in tafi,” Aliyu ya yi mata murmushi mai taushi, wanda ya nuna yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali, “Na yi miki alƙawari, distance ba zai rage komai a tsakaninmu ba, zuwa ƙarshen satin nan zan zo Abuja in duba ki, zan riƙa kiranki a waya bayan kin sauka, kuma za mu riƙa magana duk lokacin da muka samu dama, amma ki yi mini alƙawari za ki kula da kanki, sannan ki mayar da hankali a karatunki,” ta gyaɗa kai da sauri, “Na maka alƙawari, Mi Amor, I love you,” idanun Aliyu suka haskaka da farin ciki, ya yi murmushi, sannan ya amsa, “I love you more, Babygirl, jeki abinki kafin jirgi ya tashi,” Inteesar ta kalle shi na ɗan lokaci, kamar tana son ta riƙe wannan lokacin a zuciyarta kafin ta tafi, daga nan ta juya da ƙyar, ta nufi inda jami’an filin jirgin suke binciken fasinjoji kafin shiga wurin jirgi, ta miƙa musu tikitinta, amma kafin ta shiga gaba ɗaya, sai ta tsaya ta waiwaya, fuskarta na ɗauke da murmushin yaƙe, ta ɗaga musu hannu, Aliyu ma ya ɗaga mata hannu yana murmushi, duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar an cire wani sashe na rayuwarsa, Inteesar ta sake juyawa ta shiga ciki, yayin da zuciyarta ta bar wani babban ɓangare na rayuwarta a Katsina.

Jirgin Inteesar ya sauka lafiya a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport da ke Abuja, bayan ta fito daga cikin jirgin, ta karɓi akwatunanta, sannan ta ɗora su a kan trolley ta nufi wajen da ake jiran fasinjojin da suka sauka, gabanta yana ta dukan sauri-sauri saboda rashin sanin wanda za ta tarar yana jiranta, ashe, Nana ce da kanta ta zo ɗaukarta, tana tsaye sanye da farar abaya, fuskarta ɗauke da murmushi mai taushi na tarbar ƙanwarta, da Inteesar ta hango ta, sai ta saki wani nannauyan numfashi na nutsuwa, ta ƙaraso da sauri, ta bar trolley ɗin a gefe, sannan ta rungume Nana sosai, “Yayaa Nanaa!” ta kira cikin muryar wadda ta yi kewarta, Nana ta ƙara matse ta a jikinta tana dariya, “Barka da zuwa, Princess ɗin Daddy, wallahi mun yi kewarki sosai, Yaya Umar ma yana so ya zo da kansa, amma wani taron gaggawa ya tsayar da shi a office, shi ya sa na ce bari na taho da kaina,” da aka ambaci sunan Yaya Umar, Inteesar ta ji wani irin sauƙi a ranta, a ɓoye, ta yi farin cikin cewa taron ya hana shi zuwa ɗaukarta, amma ta ɓoye hakan a ƙarƙashin murmushi, “Na gode sosai, Yaya Nana,” bayan sun gama gaisawa, suka sanya akwatunan a mota, sannan suka ɗauki hanyar cikin gari.

Suna isa gidan Yaya Umar da ke Maitama, Inteesar ta ji gidan ya yi mata wani sabon yanayi na daban, ba kamar yadda ta bar shi kwanakin baya ba, ma’aikatan gidan sun riga sun kai kayanta ɗakinta na dā cikin girmamawa, amma shiru da sanyin gidan sun sa ta ji wani irin yanayi a jikinta, bayan ta yi wanka ta sauya kaya zuwa doguwar riga ta kanti mai sauƙi, ta sauko ƙasa domin cin abinci, Nana ta shimfiɗa mata abinci mai kyau a kan dining table, suna zaune suna cin abincin, Nana tana ta yi mata hira cikin kulawa, tana tambayarta jikin Daddy da kuma yadda ta baro mutanen Katsina, Inteesar tana ba ta amsoshi cikin natsuwa, tana jin daɗin kasancewarta tare da Nana bayan doguwar tafiya, a daidai lokacin ne suka ji ƙarar motar Yaya Umar tana shigowa harabar gidan, cikin ’yan daƙiƙu, sautin takun takalmansa ya gauraye cikin shirun babban falon, Umar ya shigo sanye da babban suit ɗinsa na aiki, riƙe da briefcase a hannunsa, gabanta ya faɗi lokacin da idanunsu suka haɗu, ta ɗan tsaya tana kallonsa, tana jiran ganin irin yanayin da zai nuna mata, amma fuskar Umar ba ta ɗauke da wata alama ta fushi ko rashin jin daɗi, babu tsantsar haɗe rai, babu kuma fara’ar da ta saba gani a wajensa, sai dai akwai wani irin nauyi da natsuwa a idanunsa, tamkar mutumin da ya riga ya sadaukar da wani abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwarsa, “Sannu da zuwa, Yaya, ina wuni?” ta gaishe shi cikin girmamawa, tare da ɗan fargaba a muryarta, “Lafiya lau, kin dawo lafiya?” ya tambaya a taƙaice, “Lafiya lau, Alhamdulillah,” Umar ya juya ya kalli Nana, sannan ya yi mata murmushi mai kyau, Nana ma ta mayar masa da murmushin kafin ta ce, “Sannu da zuwa, babe,” ya sake kallonta cikin kulawa, sannan ya ce, “Bari na shiga ciki in rage nauyin jikina, sai na fito,” yana juyawa ya nufi bene, Inteesar ta bi shi da kallo har ya ɓace daga ganinta, ta lura cewa Yaya Umar ya sauya sosai, ya zama wani mutum mai cike da natsuwa, natsuwar da take nuna kamar ya fara karɓar ƙaddarar da ba zai iya sauya ta ba, a karon farko tun dawowarta gidan, Inteesar ta ji wani irin sauƙi a zuciyarta, wataƙila zaman gidan ba zai zo da wani tashin hankali ba kamar yadda ta yi tsammani, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ci gaba da cin abincinta, ba tare da sanin cewa a bayan wannan natsuwar ta Umar akwai abubuwan da yake ƙoƙarin binne su a cikin zuciyarsa ba.