BAUTAR ZUCI

002

by @queenwaleedah51

Falmata wadda ke tsaye kamar tabarya ta kalli ibrahim tace"dan allah ibrahim ka taimake ni ka taimaki zuciyata wallahi bazan iya daina sonka ba,wallahi zuciya ta ta riga data kamu da sonka kuma banga rananr da zata daina sonka ba, yayin da hawaye ke fita daga idanunta.Ibrahim ne ya kalli lungun ganin ba kowa yasa shi fadin"to ya kikeso nayi falmata iyayenki sun ce kar na kuskura na k'ara zuwar musu kofar hida, sun ce bani ba ke, to ya zanyi ko da inasonki dole na hakura saboda girmama maganar manya.

Falmata ce ta kallesa a karo na biyu ta tsugunna a gabansa gwiwa bibbiyu tace"dan allah Ibrahim karka barni bazan iya rayuwa babu kai ba wallahi, na riga na kamu da matsananciyar soyayyarka, kuma bazan iya daina sonka ba, karka barni."naji bazan barki ba, yanzu ki tashi ki tafi makaranta domin kuwa lokaci yana tafiya anjima idan zakije islamiyya kizo ki sameni kinji, zan san yadda zanyi.
Mikewa tayi tana mai share hawayen fuskarta ta kallesa a hankali ta furta" sure, saurin daga mata kai yayi sannan ta tafi.Tana tafiya ya bita da kallo hadi da kallon mugunta yace"uhmm yarinya baki sanni ba amma ki biyewa zuciyarki tabbas zakiga abinda zai biyo baya, daga nan ya juya ya koma d'aki.A school kuwa class ta shiga yayin da ummi ko kallonta batayi ba dik da gata ga ummin.

Falmata jin bazata kulata bane yasata fadin"ummi kiyi hakuri dan allah nasan ban kyauta miki ba, amma akan ibrahim wallahi komai zan iyayi, ke ko wuta yace na fada banga wanda ya isa ya hanani ba.

Ummi da mamaki ta kalli falmata tace"ashe falmata baki da hankali bansani ba, ashe girman banza ne ba kwakwalwa, yo ba kwakwalwa mana,yanzu ke har wani d'a namiji zai iya cewa kiyi abu kuma kiyi, shi ba yaynki ba, ba babanki ba, ba dan uwanki ba, ba dangin iya ba na baba, ba sidi ba sadada kawai dan yace ki shiga wuta sai ki shiga saboda allah ya cire miki hankali koo.

Falmata ce ta kalleta tace"dallah malama karki b'atan rai aikin banza kawai, dan kinga ina baki hakuri ina ruwanki da rayuwata, daga yau karki sake shiga sabgata ki barni nida ibrahim, shi na gani kuma shi nakeso akan ibrahim na fadamiki babu abinda bazan iya yi ba, matukar zai faranta ran masoyi na.Falmata ce ta tattara jakarta da sauran kayanta ta canja wuri, ummi kallonta tayi kawai tana mamakin halin falmata domin soyayya ta rufe mata idi bata gane daidai ko akasin hakan.

Ummi ce ta furzar da numfashi ta kalli inda ta koma, wato cikin 'yan. Iskan class din su wanda basajin kunya kuma babu mai fada musu suji,ummibtayi niyyar yi mata magana amma sai ta share hakan saboda tasan yanzu idan tayi mata magana komai zai iya faruwa.

Ko da aka tashi daga makaranta ummi ta riga fitowa daga school a bakin gate ta tsaya jiran falmata, amma da mamakin ta sai hango falmata tayi cikin dabar k'awayenta suna tafi suna tafi da shewa.

Ummi da sauri ta karasa hadi da fizgar hannunta tace"ke falmata kizo mu tafi gida tin dazu nake jiranki fa.
Wani wawan kallo falmata tayi mata tace"ke dallah malama sakarni da kike min wannan haushin da tare mukazo ne.

Ummi da mamaki tace"ni kike gayawa wannan maganar falmata, ni nake miki haushin,tsaki falmata taja tace"sai me kenan, me zaki iya naga ai ba ubanda zaki iya ko.

Ummi ce tai murmushi tace"laifina ne da har nake shisshige miki, rayuwarki ce amma salon yadda kika d'auki rayuwa ina mai tabbatar miki da cewa zata koya miki darasi, zaki dawo kina neman yadda zakiyi ki gyara kuskurenki, a wannan lokaci kuma baki da damar hakan, dag haka ta huce ta barta a tsaye.

Falmata wadda jikinta yayi sanyi da kalaman ummi tayi shiru.

Jamcy ce tace"wai falmata kardai kice kalaman waccan figigiyar yarinyar yayi tasiri a kanki.

Firgigit ta dawo tace"haba hauka kenan ai bazan taba bari wani abu yayi min shamaki da buri na ba jamcy, ina nan akan baka na na neman na mallaki ibrahim ta kowacce hanya.

"Yawwa ko kefa fad'in jamcy wadda ke gyara jakarta.

Ummi kuwa tafiyarta tayi tana k'ara jinjina wauta irin ta falmata, akan namiji zata zama Haka, wai soyayya a fili ta furta" allah ya rabamu da son wani wanda baisan darajar mu ba.

Falmata kuwa sai da ta biyewa sabbin k'awayenta su jamcy sannan ta k'arasa gida da sallama ta shigo tana kalle kallen tsakar gidan.

Can wajen baranda ta hango umma a kishingide, karasawa tayi tana fadin"umma sannu da gida,umma ce ta d'ago sannu dai falmata.

D'aki ta shiga bata dade ba ta fito sanye da doguwar riga 'yar yaloluwa wadda bazatayi zafi ba, sanann ta zauna kusa da umma.

"kije ki zubo abincinki,kamar jira take ta mike tana kallon kitchen d'in.

 Sadiq ne yayi sallama yana kallon falmata wadda ke kokarin zuba abinci, a fili yace"aunty falmata ki zubo dani dan wallahi yunwa nakeji.

Umma ce ta dubesa tace"sadeeq ina ka baro usman, yana waje shi da abokinsa ni yunwa nakeji shisa nagaji na shigo daga haka bai k'ara cewa uffan ba.

Abincin suke ci yayin da gaba d'aya tinanin falmata ya karkata ne a kan ibrahim wanda yace tazo anjima, ta rasa mai zai bata, amma idan ta tuna da hudubar k'awayenta sai taji dik wani tsoro nata ya gushe.

 Tana gama cin abincin sallah tayi tashiga wanka, komai cikin hanzari take yinsa, umma ta lura da hakan amma tayi tinanin tanayin sauri ne saboda karta makara.

A gurguje ta fito da uniform dinta,katon hijab ne coffee brown sai nikab da jaka a hannunta ta kalli umma wadda har yanzu tana kishingide tace"umma na tafi sai na dawo, bata jira mai ummar zata ce ba tai ficewarta.

 Tana fitowa ko ta kan gidan su ummi bata nufa ba tai hanyar gidan su ibrahim, tana tafe tana tina abinda suka tattauna tsakaninsu da jamcy.

Flash Back

Tafe suke yayin da jamcy ta kalli falmata tace"haba mana falmata dubeki kyakkyawa san kowa kin wanda ya rasa, na tabbatar da cewa ibrahim na mugun sonki kuma zai iya komai saboda ke,ki dube ki, ki dubi surarki, abinda zan fad'amiki a matsayi na na kawarki shi ne ko mai ibrahim zai nema a wajen ki bashi hadin kai, domin indai kina masa abinda yakeso to ki sani ba wadda zai so sai ke.

Falmata ce tace"seriously, farida ce ta cabe zancen da cewa sai kiyi ai ke ana nuna miki gabas kinayin yamma, ke fa falmata gaki dai da suffar wayayyu amma har yanzu ke ciki ce, ba ubanda kika sani sai shiririta da hauka.

 Da wannan tinanin ta karasa har bakin shagon ibrahim, zuwanta yayi daidai ta fitowar wata kwailar yarinyar wadda falmata a kalla ta bata shekara biyar haka, da mamaki falmata ta dubi yarinyar ta kuma kallon ibrahim.

"huce ki tafi ibrahim ya fad'a yana mai kallon yarinyar.

Falmata ce ta d'age nikabin ta tace"dama ibrahim dik abinda ake fad'a akan cewa kana kawo mata ashe da gaske ne, banza yayi mata ya juya ya shige d'akinsa,bin bayan sa tayi juyowa yayi ya dubeta yace" indai kinsan b'ata min rai zakiyi to ki fita anan bana buqatar ganinki, akin banza kawai.