FreeArewaPen original
BAUTAR ZUCI
- 1views
- 10chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciya
Sample · 002
Falmata wadda ke tsaye kamar tabarya ta kalli ibrahim tace"dan allah ibrahim ka taimake ni ka taimaki zuciyata wallahi bazan iya daina sonka ba,wallahi zuciya ta ta riga data kamu da sonka kuma banga rananr da zata daina sonka ba, yayin da hawaye ke fita daga idanunta.Ibrahim ne ya kalli lungun ganin ba kowa yasa shi fadin"to ya kikeso nayi falmata iyayenki sun ce kar na kuskura na k'ara zuwar musu kofar hida, sun ce bani ba ke, to ya zanyi ko da inasonki dole na hakura saboda girmama maganar manya.Falmata ce ta kallesa a karo na biyu ta tsugunna a gabansa gwiwa bibbiyu tace"dan allah Ibrahim karka barni bazan iya rayuwa babu kai ba wallahi, na riga na kamu da matsananciyar soyayyarka, kuma bazan iya daina sonka ba, karka barni."naji bazan barki ba, yanzu ki tashi ki tafi makaranta domin kuwa lokaci yana tafiya anjima idan zakije islamiyya kizo ki sameni kinji, zan san yadda zanyi.Mikewa tayi tana mai share hawayen fuskarta ta kallesa a hankali ta furta" sure, saurin daga mata kai yayi sannan ta tafi.Tana tafiya ya bita da kallo hadi da kallon mugunta yace"uhmm yarinya baki sanni ba amma ki biyewa zuciyarki tabbas zakiga abinda zai biyo baya, daga nan ya juya ya koma d'aki.A school kuwa class ta shiga yayin da ummi ko kallonta batayi ba dik da gata ga ummin.Falmata jin bazata kulata bane yasata fadin"ummi kiyi hakuri dan allah nasan ban kyauta miki ba, amma akan ibrahim wallahi komai zan iyayi, ke ko wuta yace na fada banga wanda ya isa ya hanani ba.Ummi da mamaki ta kalli falmata tace"ashe falmata baki da hankali bansani ba, ashe girman banza ne ba kwakwalwa, yo ba kwakwalwa mana,yanzu ke har wani d'a namiji zai iya cewa kiyi abu kuma kiyi, shi ba yaynki ba, ba babanki ba, ba dan uwanki ba, ba dangin iya ba na baba, ba sidi ba sadada kawai dan yace ki shiga wuta sai ki shiga saboda allah ya cire miki hankali koo.Falmata ce ta kalleta tace"dallah malama karki b'atan rai aikin banza kawai, dan kinga ina baki hakuri ina ruwanki da rayuwata, daga yau karki sake shiga sabgata ki barni nida ibrahim, shi na gani kuma shi nakeso akan ibrahim na fadamiki babu abinda bazan iya yi ba, matukar zai faranta ran masoyi na.Falmata ce ta tattara jakarta da sauran kayanta ta canja wuri, ummi kallonta tayi kawai tana mamakin halin falmata domin soyayya ta rufe mata idi bata gane daidai ko akasin hakan.Ummi ce ta furzar da numfashi ta kalli inda ta koma, wato cikin 'yan. Iskan class din su wanda basajin kunya kuma babu mai fada musu suji,ummibtayi niyyar yi mata magana amma sai ta share hakan saboda tasan yanzu idan tayi mata magana komai zai iya faruwa.Ko da aka tashi daga makaranta ummi ta riga fitowa daga school a bakin gate ta tsaya jiran falmata, amma da mamakin ta sai hango falmata tayi cikin dabar k'awayenta suna tafi suna tafi da shewa.Ummi da sauri ta karasa h...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.