BAUTAR ZUCI

004

by @queenwaleedah51



Heheheheeeheeee kun d'auka asirin falmata ya tonu ne, a'a abinda nake hasashe zai faru ne sai kuma naga ba shi ke shirin faruwa ba.

Falmata tin da ta taho hanya take tinanin wacce karya zatayiwa iyayenta domin su barta taje wannan birthday'n, sam bata ta ummi tinda har tasan halin ummi ta riga tasan bazata k'ara kula ta ba, ita ma kuma tana sane tai mata hakan domin ta sama mata lafiya.

A haka har ta shigo layin su, da ummi suka had'u wadda har ta cire uniform da alama aikenta akayi domin da leda a hannunta,wani kallo falmata ta bita da shi yayin da ita yarinyar kuwa ko kallon ta batayi ba.

Da sallama ta shiga gida, a bakin tap ta samu umma tana shirin wanke wanke, jin sallamar falmata yasaka umma fadin yawwa falmata dan wanke min kwanikan nan,turo baki tayi kasa kasa a zuciyarta ta furta daga shigowa ta ko hutawa banyi ba, wai wanke wanke a fili kuwa da to ta amsa tashige d'aki, bata dade ba naga ta fito daga falo sanye da rigar d'azu ta huce bakin tap din.

Wanke wanken take yayin da ta lula duniyar tinan. Bara na leqa cikin tinanin nata.

FLASH BACK

Tafe suke su biyu kowaccen su da jakar makaranta a hannunsu, sanye suke da uniform na jss. Wasu samari ne da suke gefensu suka huce su, wani matashin saurayi ne yabini da kallo yayin da abokinsa ya janyo sa yace"haba wai kai khalil a duniya indai kaga mce sai ka juya, sanann ka. Dubesu da kyau wadannan ai kwailaye ne, murmushi khalil yayi yace"ai kai abba bazaka gane ba, bakasan da cewa kwailayen sunfi dadin soyayya ba, tsaki abba yaja suka huce.

Tin daga wannan lokacin indai zamu huce muna yawan ganinsu, tin bamu kula ba har muka fara kulawa da su wani lokacin khalil na mganar a dawo lafiya shi kuwa abba ko kallo, mun rasa da sassafe me sukeyi a wannan hanyar, ummi ita ce babbar kawata 'yar makociyar mu ce, ta girmeni amma kamar yadda na gaya muku cewa na fita girman jiki mutane da yawa sun dauka ni ce babba. 

Ummi wadda yau muke tafe da ita tin kafin mu karo wajen su khalil ta dubeni tace"gaskiya falmata abinda kikeyi sam baida kyau, taya za'ai baki san mutane ba kina tsayawa dasu har kusan mintu biyar bayan kinsan makaranta zamuje.

Murmushi nayi nace"ke ai dama ummi baki waue ba, ke bakisan ibrahim ba dan gidan alhaji auwalu mai garri shi ne fa wancan, tsaki ummi tayi tace"to ni nagaji gaskiya.

Falmata hucewa tayi tana mamakin hali na kawarta ummi,a ranta tce"ita fa wannan na lura da ita cewa batason gani na da saurayi india ta ganni da namiji sai tasan yadda tayi ta rabani dashi hankalinta ke kwanciya, tabe baki tayi ta huce.

Kamar kullun yau ma falmata ta tsaya amma bata dade ba, sun d'an fara tafiya kenan sai wani yaro ya shawo gabansu ya kalli falmata yace"kece falmata ko.

Falmata gyada kai tayi, da murmushi yaron ya zaro takarda a aljihunsa yace"gashi inji khalil daga nan ya tafi.

Falmata baje hakora tayi tace"laaa ummi kalli khalil ne ya turo min da wasika, allah yasa ta soyayya ce,kallon ta ummi tayi tace"ke wai falmata har kinsan wata aba soyayya dika fa jss3 muke amma kike wanann zumudin, falmata ki daina haka, ki daina haka, karki bawa khalil damar shigowa cikin rayuwarki, dik da bakisan mai takardar ta kunsa ba amma har kin yanke cewa ta soyayya ce.

Kallon sororo falmata tayi mata har ta fara bude takardar, da manyan baki aka rubuta I LOVE YOU MY FALMATA,wani tsalle falmata tayi tace"to da kike cewa bansan me takardar ta kunsa ba kalli kigani, ummi wadda ta juyar da kanta ci gaba tayi da tafiya, a haka har suka huce makarantar.

A b'angaren ibrahim kuwa abba ne ya dubesa yace"dan allah khalil karka cutar da rayuwar wanann yarinyar dan allah, kadubeta fa yarinya ce karama batasan komai ba amma zaka lalata zuciyarta da sonka ko.

Murmushi Ibrahim yayi yace"ai wallahi tinda na ganta tayi min ai kasan sai na d'ana ko, dan haka ka sakamin ido kawai.

_firgigit na dawo hayyaci na jin maganar baba nafad'in"ke wacce irin shashasha ce baki da hankali wasu na neman ruwa shi ne kika bar ruwan na zubewa a banza, tinanin me kike.

Saurin kashe famfon nayi na fara tattara kayan wanke wanken ina kaisu kitchen, tsaki baba yaja ya huce ya dakko buta yayi waje.

Dawowa tayi wajen famfon ta kunna ruwan tana alwala, a ranta tace"ohh shi kuma ba damar yaga ruwa na zuba sai yayi ta fada, dole fa yayi hakuri tinda ya saka wanann famfon, ni ya hanani wanda nakeso yazo yana fada da ruwa. 

A fili na furta falmata ina zakiga daidai kuwa kina wanann ta'asar.