005
Dawowa tayi bakin tap d'in tayi alwala shigewa d'akinta tayi ta gabatar da sallar magariba.
A kan katifarta ta kwanta tana mai rufe idanunta.
A haka soyayya ta kullu tsakanin falmata da Ibrahim.
Falmata ce yau tafe tana wak'e wak'en ta na zamani.
Can nesa ta hangi ibrahim a wajen mai shayi.
Murmushi tayi a ranta tana fad'in yau gani ga masoyina ni na dade ma bangansa ba.
K'arasawa tayi mai shayin, Ibrahim ne ya hangota hakan yasa shi mik'ewa ya bar wajen.
"me kika zo yi mini kuma anan, ni banason wannan shirmen naki fa.Ibrahim ya fad'a.
" Haba masoyina tin ranar da ka turo mini da takardar soyayya ban k'ara ganinka sai yau, me kake nufi kenan.
"Barinki nayi ki yarda ki amince saboda naga kamar baki amince ba.
" Wane bari kuma, ai baka sani ba tin ranar dana d'ora idanuna a kanka naji babu wanda nakeso sai kai, ba wanda nakeso na aura sai kai.
Murmushi ibrahim yayi yana kallonta, irin kallon so kenan.
" yawwa masoyi na to yaushe zakazo gidan mu yanzu.
" Gidan ku kuma ai na d'auka a hanya zamu na had'uwa.ibrahim ya fad'a
"Gaskiya a'a kawai anjima kazo gidan mu kaga sai mu dade muna hirar mu, cikin soyayya ko.
Murmushi khalil yayi.
" Shikenna zanzo ai maza kije aikenki idan nazo zan turo a kira mini ke.
Tafiya tayi cike da jin dadin zancen khalil.
Ko da taje gida ta kai aiken umma ta kalla wadda ke kok'arin d'ora sanwar girki.
" Umma bara na lek'a gidan su ummi yanzu zan dawo.
"Shikenan maza kije ki dawo kizo ki karb'i girkin nan, ta fad'a tana kallon falmata.
A gidan su kuwa fad'a mata abinda ibrahim yace mini nayi.
Ummi wadda ke kwance tai saurin tashi ta kalleni.
" Falmata karki fara haka, ki fara bari ki k'arasa karatunki sai kiyi soyayyar, ki tsaya ki Gina kanki karki biyewa ibrahim, ibrahim bashi da hali mai kyau, kinsak bazan ga wani abu dayake kok'arin cutar dake ba kuma ace na kyalesa.
Fincike hannunta tayi tai.
"Dallah cika ni, kuma wallahi sai na biye masa d'in, ke fa na fuskanci dan baki da saurayi shikenan nima sai na zauna bani da shi, to billahillazi sai nayi soyayya da ibrahim, kuma har muyi aure sai dai ki mutu, hannunta ta warce ta fita.
" Falmata! Falmata!! Haka ummi ke kwala mata kira amma ina ta bar ta anan.
Bayan sallar magariba, falmata na zaune sanye take da riga da wando na yadi, wani yaro ne ya shigo yace"wai ana sallama da falmata.
Umma wadda ke tsaye tana kok'arin dakko wani kaya a saman baranta tace"je kace tana zuwa.
"Sai ki fashi kije kiga wanene yake nemanki, fitt ta mik'e ta fice umma har tana ganin saurinta.
Ibrahim ne yazo shi da abba abokinsa, kallonta yayi yace" 'Yammatan ba.
"sannunku da zuwa.
" Yawwa amaryar abokina, fatan mun sameku lafiya.
Farrr tayi da ido kafin tce"lafiya louh.
Abba bayan sun gaiss gefe ya koma ya zauna yana danna wayarsa.
Malam yasir ne ta tuk' o kekensa ya taho gida, tin daga nesa ya hangi falmata.
K'arasawa yayi falmata wadda ke tsaye cike da jin tsoro tace"sannu da zuwa baba.
"yawwa ya amsa daidai lokacin da idanunsa suka sauka akan Ibrahim.
Sakkowa yayi daga kan keken yayi yace" kai meya kawoka gidana.
Ibrahim Wanda ke tsaye ya tab'e baki yace"kamar ya kenan baka ga ni dawa ka gani ba.
"kai karka kuskura ka mini rashin kunya, falmata ya kalla yace" huce gida ko na ballaki a wajen nan.
"Ka sani kar na sake ganin kafarka a kofar gidan nan, idan kuwa ka kuskura ba gani to billahillazi baka bina bashin rantsuwa, na lahira sai ya fika jin dad'i.
Abba ne ke jansa yahin da khalil ya tsaya.
" to me zaka iya, me kake nin zakayi, kuma soyayya ce yanzu na fara da 'yar taka, aikin banza kawai, mutum ya tsufa amma baisan ya tsufa ba, ai da nasan kaine mahaifinta take ka zanyi da machine d' in ka mutu kowa ya huta sai nazo naci kare na babu babbaka.
Dik wannan zancen da yake malam yasir bai tanka masa ba a ransa yace 'Dan kuka mai jawa uwarsa jifa, daga haka ya huce ciki.
Umma kallon ta tayi yadda take hawaye shabe shabe a fuskarta, "ke kuma ke dawa kike gudu da huci, ai kafin ta rufe bakin ta malam Yasir ya shigo yana fadin ashe yarinyar nan bata da mutunci har haka.
" me ya faru malam,malam yasir ne ya kalli falmata sai kuma ya kalli umma yace"ina yaron da nace miki ya kusa ture ni da machine har nayi masa magana ya kusa zagina bai kalli tsufa na ba,shi ne fa ta kawo min kofar gida jamila, ki duba min lamarin nan ki gani ya dace kenan.
"ai kasan ba lallai tasan abinda ya faru tinda lokacin da kazo kana maganar bata nan, kuma tin daga ranar ba'a kara ta da zancen ba,umma ce tai maganar tana kallon falmata wadda ke gefe a tsugunne.
Tsaki malam yasir yaja sannan ya kalli falmata yace" na saka Miki doka falmata daga yau kar na kuskura na kara ganin ki da wannan yaron.
Falmata ce tace"to a fili yayin da zuciyarta ke fad'in wallahi bazan iya rayuwa ba khalil ba, baba bazan iya rabuwa da shi ba.