BAUTAR ZUCI

006

by @queenwaleedah51


"khalil meke damunka ne kai,karka manta shi din fa sirikinka ne tinda kana son 'yar sa ko,wani kallo ya wulla masa yace"kamar ya kenan an gaya maka ni inason' yar sa ne, to kasani ban taba son ta ba, kawai ina amfani da ita ne wajen fita raini.

Abba da mamaki yace"meye hakan khalil karka manta zakai aure, zaka haihu shin idan aka yiwa 'yar ka haka zakaji dadi kenan.

Khalil wani kallo ya wulla masa sanann yace"wace maganar banza ce haka abba, abba murmushi yayi yace"ai gaskiya ce na fada maka, ko kai aiki da ita ko kuma ka barta tsaki yaja ya huce ya barsa anan.

Tashi nai zan huce umma ce ta kalleta ta jinjina kai, domin inda tasan wannan yaron ne ba abinda zai sa ta barta ta fita.

Kallon fuskarta umma ta karayi a karo na biyu taga yadda take hade haden rai, ga hawayen da bai gama fitowa daga idanun nata ba,umma dai batayi magana ba ta tsaya tana kallonta.

Jinjina kai tayi a zuciyarta tana k'ara jinjina lamari na 'yammatan yanzu, ita yanzu.

A haka wannan ranaku suka huce amma abinda baku sani ba kullun sai falmata taje wajen khalil, rashin mutuncin yau daban na gobe daban ya gama raina ta.

Da kyar ta samu ta shawo kansa yaci gaba da kulata, ita dai a duniya bata da wanda takeso sai khalil, batajin zata iya rayuwa babu khalil.

Juyawa tayi akan tsummar katifan ta yayin da hankalinta na kan yadda zatayi wa umma karya gobe taje wannan birthdayn da khalil yace zasuje.

Ta rasa tayaya zata yi karyar, idan tace makaranta ga ummi 'yar makoftansu,bata da madafa hakan yasa ta jira sai gobe, addu'a tayi ta juya ta kwanta.

Washe gari yau da wuri ta shirya karfe 7 da rabi ta fice daga gida, ko kallon gidan su ummi batayi ba tayi hanyar makaranta, kamar kullun sai da tayi yanke taje dakin khalil wanda ke kwance yana sharar bacci.

Karar bude kofa ne ya tashe sa, falmata cire hijabinta tayi ta fara gyara dakin yayin da shi kuwa ya tsaya ya kurawa surar jikinta ido yana kallon yadda take aiki, a haka kamar tana sane take jijjiga jikinta, nan kuwa ba tana sane bane, sai da ta gama gyara dakin sanann ta je kusa dashi tana mai murmushi.

Murmushin yayi mata yace"baby kinyi kyau, hannunta ya kama yana murzawa a hankali, cikin salo na bariki yake kwallon kwayar idanunta,falmata zare hannunta tayi tace"ba da ban ummi ba da ba inda zanje ina nan tare da kai sahibina, amma ka bari zan dawo da wuri anan ma zanyi shirin birthday party, murmushi khalil yayi yana kallonta tana saka hijab, yahin da yake kiccifa abubuwa da yawa a ransa.

_____sannu ummi, mamanta ta fad'a ummi wadda ke kwance lullube da bargo tana makyarkyata, kallo daya na mata nasan ba lafiya ne da ita.

Mahaifin ummi ne ya shigo yace"to taso ta mu tafi asibitin na samu mai nafef.

Maman ummi janyo hijabin ummi tayi ta saka mata da kyar ta kamata, har zata shiga tace"malam bara na sanarwa maman falmata saboda kar taji bama nan,malam jinjina kai yayi, bata dade ba ta fito suka tafi asibiti.

A class kuwa falmata na tsakiyar kawayenta.

Jamcy ce tace"nikam wai bazaki gayyace mu partyn ba mu ma mu rakashe, murmushi falmata tayi tace"za'a barku kuje ne, murmushi sukayi su dika ukun.

Farida ce ta dubeta tace"to angaya miki kowa irinki ne wanda yake jin tsoran gidan su, ai falmata idan zaki bude kunnenki ki bude, ki sani ke din ba kalar wadda za'a na kullewa bace ana hanaki shakatawa,karki bari kanki yayi murfi.

Jamcy murmushi tayi sannan tace"barta farida ai ita kam bata waye ba, malama ki san yadda zakiyi ki shirya anjima kawai mu huce, shiru falmata tayi tana nazarin maganar su, kuma fa sun fada mata gaskiya indai hakane.

Juyawa tayi ganin bata ga ummi hakan kuw ayayi mata dad'i sosai a rai ko banza ta samu hanyar da zatayi k'arya a barta taje birthday.

Tinda aka tashi daga makaranta, tafiya take tana waiwaye kamar wata mara gaskiya, daidai kofar gidan su ummi ta tsaya tana kallon gidan, sai kuma naga taja tsaki tayi murmushi.

Da sallama a bakin ta ta shiga gidan su, umma ce ke tsaye da alama shigowarta take jira.

"Yawwa falmata ki kuka da gidan nan zanje asibiti ne yanzu.

" Umma wa aka kwantar a asibiti kuma,falmata ta tambaya.

"Ummi ce ba lafiya jikin kuma ya matsa sosai, idan su sadeeq sun dawo kya fad'a musu, fita umma tayi.

Tana fita falmata ta rangad'a gud'a, sai kuma naga ta hau rawa.

Abinci taci ta k'oshi ta kwanta ta fara bacci, ba ita ta farka ba sai wajen magariba a lokacin umma ta dawo.

D'aki ta shiga ta d'akko jakar makarantarta, wardrobe ta bude ta debi kaya ta zuba sannan ta fito ta samu umma a zaune a falo tana jan carbi.

Tsugunnawa tayi Tace"umma zanje gidan su farida, an bamu wani group assignment ne.

Umma kallonta tayi, sai kuma tace"shikenan sai kin dawo amma karki isha'i, daga haka bata k'ara magana ba, mik'ewa tayi ta fice daga gidan