007
Murmushi ta saki bayan ta fito daga cikin gidan.
Hanyar shagon ibrahim tayi tana tafe tana sauri domin kuwa ta san da cewa yanzu ya gaji ma da jiranta shi da yace tazo tin shida na yamma gashi ta kai bakwai.
A kofar Shagon ta tsaya tana kallon shagon a rufe, zama tayi a wajen ta rafka tagumi ta fili tace"Nashiga uku na lallace.
Tayi zama a k'alla na kusan rabin awa shiru babu shi babu labarinsa, sai can ta hangosa, da sauri ta mik'e ta biyosa tana fad'in"Ina kaje sai nemanka nakeyi fa.
Kallonta yayi sai kuma yaja tsaki ya hankadeta.
"Ke dallah matsa, tin yaushe nake jiranki, kinsan adadin awannin dana d'auka ina jiranki amma sai yanzu zakizo to ki huce ki tafi na fad'a miki dai.
Sororo tayi sai kuma ta fashe da kuka, ko juyawa baiyi ba ya huce shagonsa, jakar ta d'auka ta bisa tana sharar kwallah.
Shagon ta shiga ta fara canja kaya, shi kuma ya shiga band'akin shagin, dandanan ta canja kaya ta saka wata matsattsiyar doguwar riga ta atamfa, mudubi ta duba bayan ta tabbatar kanta da tayi kyau.
Yana fito bai mata magana ba ya juya ya fita binsa tayi ta bar jakar anan.
Tafiya yake tana binsa, sai da ya fita daga lungun, motar da ta kawo shi ya shiga ita kuma ta tsaya daga nesa, kallonta khalil yayi bayan ta shiga motar ya wurga mata wani kallo aurin zuwa tayi ta bude motar ta shiga suka tafi.
Wajen Birthday ya k'awatu domin kuwa ya k'awatu da kayan alatu, tun daga kofar hall d'in kake jin k'arar kid'a.
Shigarsu ke da wuya wata kodaddiyar yarinya ta taso ta tana rungume khalil wanda ke tsaye sank'ank'an kamar gunki.
Falmata ce ta tsaya tana kallon yarinyar, ganun bashi da niyyar tureta yasa falmta zuwa ta hankad'eta.
"ke dallah matsa dabba kawai kinzo kin wani nanikewa mijin da zan aura.
"Falmata ya fad'i sunan ta a fusace, hannu ya d'aga ya wanketa da mari.
K'ara d'agawa yayi ya sake wanka mata mari a karo na biyu.
"Ashe ke mahaukaciya ce bansani ba, ki rasa wa zaki ture sai Amira, kin san wacece ita a wajena, to ki tabbatar kin fitar mini daga hall d'in nan tin kafin dare yayi miki.
Dafe kunci tayi hawaye na zuba a idanunta, ta juya tsawar d aya dakamata ne yasa ta ficewa, daidai bakin kofar ta tsaya tana kallon yadda khalil ke rarrashinta ita kuwa tana masa wulakanci.
Tahowa tayi tana tafiya, tana zancen zuci.
"Me waccan ta fini da har zai mare ni a kan ta, me ta fini da shi, kodan kawai naga tafi iyayena kud'i, ba kyau ta fini ba, ba k'iba ba, ba haske ba bare a ce amma a gabanta ya zabga mini mari hagu da dama.
Daidai titi taji horn tsayawa tayi tana kallon yadda motocin wajen ke ficewa.
Nafef ta samu ta shiga, cikin murya wadda ta dashe tace"Dorayi suka taho, can nesa da gida ta tsaya, sai da ta biya gidan su farida ta karb'o hijabi kalar nata wanda ta fita dashi sanann ta taho gidansu.
Da sallama ta shiga gidan, baba wanda ke zaune akan sallaya gefe kuma umma ce suna tattauana maganganun su.
"Daga ina kike? Taji muryar baba.
Cikin inda inda ta fara magana, umma ce ta katsesa da fad'in ban gaya maka taje gidan su k'awarta ba karatu shi ne ai.
" Ke yaushe zakije asibiti ki dubo ummi? Ta k'ara jin maganarsa a karo na biyu.
"gobe ta bashi amsa cike da tsoro.
" Allah ya kaimu tashi kije, daga haka ta bar wajen tana dafe kirji.
A gurguje ta huce d'akinta, kwanciya tayi ta fashe da kuka, tana tino abinda khalil yayi mata a bainar nasi, hawaye take sharewa tanayi tana k'ara wani.
A can asibitin kuwa ummi ce kwance, kallo d'aya na mata na tabbatar tana jin jiki, yau d'aya ta rame baiwar allah kai bazaka ce ita ce ba ma.
Mamanta ce ke zaune tana mata sannu.
_Washe gari_
Kasancewar yau saturday ya saka falmata fitowa ta gama ayyukam gidan ta koma ta kwanta, tana kwance har yanzu tana tinanin abinda khalil yayi mata, ga kuma zuciyarta na k'ara azalzalalta da son khalil wanda shi a yanzu ma yana d'akin abokinsa.
Khalil wanda suke breakfast ne ke danna wayarsa kirar redmi.
"Man abinda kayi fa baka kyau ta ba tsakani da allah, kai ka sani yarinyar nan ba kalar duka bace amma ka zabga mata maruka har biyu dama da hagh, baka tsoran ta gujeka.
Wani murmushi khalil yayi sai kuma yace" ai kai bazaka gane ba, yarinyar nan tana mugun so na, dik abinda nace tayi shi takeyi, kai wallahi n arantse maka ko wuta nace ta fad'a sai ta fad'a.
"Amma bro kayi dace gaskiya, kayi dacen yarinyar da take sonka, amma dai ina fatan zaka aure ta ko.
Cakk ya tsaya da cin abincin sannan ya d'ago ya kalli abokin.