BAUTAR ZUCI

008

by @queenwaleedah51



"Kasan abinda ya faru kuwa, da niyyar auren ta yaje, amma ubanta da yake allah yayi shi da kafar kai, ga shegen son girma k'ememe ya nuna bazan auri 'yarsa ba, ni kuwa yanzun nan da ka ganni dama kawai nakeso na samu wallahi sai na k' untata masa a duniyar nan.

"Amma wannan wane irin uba ne, shi da zai murna 'yar sa ta samu miji sai kuma yazo yana cewa ba haka ba.

" Kai dallah rabu da shi ajawo ne, amma fa sai na nuna masa bai isa akan falmata ba, ni na isa da ita, da wannan hirar suka cigana da cin abincin su.

_____

Falmata ce ta fito, nafef ta samu ta hau ta shige zuwa asibitin da aka kwantar da ummi.

Bata sha wuya ba taga d'akin.

Da sallama a bak'inta ta shiga d'akin, umma wadda ita ce a kanta ta amsa ta juyo.

Da fara'arta ta kalleta tace"aa ashe 'yammatan umma ne, shigo lale marhaban falmata.

Waje ta samu ta zauna bayan sun gaisa tayi mata ya mai jiki.

Juyawa tayi ta kalli ummi wadda ta kasance' yar gayu da ita. Tabbas ta tausayawa ummi.

Bata dade ba ta taso ta taho tana k'ara tuno yadda ta ganta, tabbas d'an adam ba abakin komai yake ba.

Wunin ranar ko abincin kirki bata ci ba, tana can tinanin khalil da wannan shegiyar yarinyar amira.

Bayan sallar magariba, usman ne ya shigo da sallama a bakinsa, ita da umma suna zaune a babbar tabarmar da take tsakar gidan.

"Ke falmata kije inji wani a waje.

" Waye shi d'in falmata ta tambaya.

Umma wadda ke gefe ce tace"gidanku tashi ki tafi karki tsaya tinanin waye.

Ba dan taso ba ta tashi tana zara mayafinta, ita dai a ranta tace"Jaraba ni ga wanda nakeso amma kunce ba shi zaku bani ba, kuma kun hanashi zuwa gidan nan.

Fita tayi wanda tayi tsammani shi ta gani, wato Auwalu saurayi wanda yake matukar sonta amma tana raina masa wayau, so yake mata na hakika tsawon shekara 3 kenan yanzu yana bibiyarta, amma taki basa dama.

Kusan kullin sai yazo amma sam bata kulasa, zata tsaya wataran ta gaggaya masa magana, wani lokacin kuma ta huce ta tafi wajen khalil.

"Salamu alaikum! Ta fad'a tana buntsuro baki.

"Wa alaikissalam.

" Malama falmata, fatan mu sameku lafiya.

"Lafiya ta bashi amsa tana kallon gefe.

" Kwana biyu bamu gaisa ba, naje abuja ne, kuma ke ba waya a hannunki bare nace ko na kiraki.

"Ohhh ta fad'a kawai.

Baba ne ya turo kekensa zai shige.

Auwal har k'asa ya tsugunna ya gaisheshi.

Baba ne ya dubesa yace" idan ka samu lokaci kamin magana idan kun gama.

"to baba nagode ya fad'a yana rissinawa.

Falmata tab'e baki tayi ta kallo gefe.

Wata leda ce ya mik'a mata yace" ga wannan falmata nasan bazaki rasa abubuwan buqata ba.

"kai in banda ka raina mini hankali, me nake buqata a wajenka, bar shi idan ma ina buqata na rasa a wajen wanda zan nema sai a wajenka, to ka tattara abubuwan nan ka tafi dasu dan bana buqata ni kuwa.

" Kasshhhh amma falmata kin yi mini mummunar fahimta ba haka bane wallahi kawai 'yar tsaraba ce na kawo miki.

" to bana buqata ta bashi amsa ta huce.

Yaro ya samu ya bita da kayan sannan ya tsaya.

Can ba dadewa baba ne ya fito.

"Malam auwa ya fad' a, har k'asa auwal ya tsugunna yana sosa kai.

Ba yadda baba baiyi ba akan ya taso amma yaki tasowa.

" to dama auwal ba wani abu ne, naga ka dade kana zuwa, shi ne nace mai zai hana ka aiko da iyayenka azo ayi magana, kowa kawai ya huta ko kuwa.

Auwal washe baki yayi domin kuwa damar kawai yake jira a basa.

" to baba insha allahu ba matsala, nagode sosai allah ya saka da alkhairi ya k'ara lafiya da imani.

" Ameen ameen auwalu, idan kaje ka gaishe mini da mahaifin naka, nagode sai na jika.

"to baba insha allahu kuwa zaka jini nan kusa, kuma ai ni ke da godiya, baba ne ya huce ya barsa a tsugunne.

Hucewar baba yasaka shi sakin murmushi ya d'aga hannu sama yana godewa allah da ya bashi wannan damar.

Baba gida ya shige, bai wa kowa magana ba ya huce d'akinsa, da wata zabgegiyar dorina ya fito ya ajiye ta gefe.

Falmata wadda ke d'akinta ya fara kwalawa kira.

Da sauri ta fito ta tsugunna tana fad'in gani baba.

"wato falmata ban isa na saka doka a gidan nan ba abi ko,ban isa na saka ki ba ban kuma isa na hanaki ba, ban isa nace karkiyi abu ki kiyi ba, ban isa kuma nace kiyi kiyi ba ko falmata.

Shiru tayi tana zazzare idanu.