BAUTAR ZUCI

009

by @queenwaleedah51



"Ba magana nake miki ba.

" ba.. Ba.... Bani... 

"Yi mini shiru munafukar allah.

Dorinar ya d'aga ya lafta mata a gadon baya, cikin k'araji ta saki ihu ta shasshekar kuka.

" idan baki rufe mini baki ba a gidan nan sai na kasheki na binne ba wanda yaji ba wanda ya gani.

Difff tayi da bakinta.

"yanzu falmata kin kyauta kenan, abinda kikeyi kenan, jiya da kikace min gidan k'awarki ashe abinda kika tafi yi kenan, kinyi kanki adalci, saurayin da baya ganin mutuncin iyayenki shi ne zaki zab'a har da zuwa shagonsa.

Umma ce ke wannan maganar tana sharar kwallah.

Falamata hawaye take zubarwa daga idanunta.

"Amma falmata kin bani mamaki, har yana hanaki xuwa makaranta saboda ga ubanki ko, yanzu har ki biyewa *BAUTAR ZUCI*Akan wani namiji.

" Shikenan kije mataki ne na riga da na d'auka, aurenku ne ke da auwal ba makawa, bazakije ki janyo mini abin kunya ba, kuma wallahi na kuskura na sake ganin k'afarki a kofar gida sai na b'allaki, karatun a hakura haka ai ba dole bane.

Wani hawaye ne ya gangaro mata, ta rasa ya zatayi budar baki tai.

"Dan allah karku rabani da khalil, wallahi inason khalil, banajin zan iya zama da wani idan ba khalil, bazan tab'a son wani ba sai khalil, umma ina son khalil, bazsn iya rayuwa ba ba tare da khalil a kusa da ni ba.

" Allah yaji kanki baba ya fad'a yana binta da wani mugun kallo.

" Inalillahi wa inna ilaihi rajiun, yanzu ke falmata har anyi lalacewar da zakizo gabanmu kina fad'in kina fad'in idan ba wani ba zaki iya rayuwa ba.

"Gafaracan shashashar yarinya mara kan gado, wadda bata san ciwon kanta ba.

Baba mikewa yayi zai huce, saurin rik'o k'afarsa tayi ta rike.

" Baba dan allah kayi hakuri, kayi hakuri ka aura mini khalil, wallahi ina son khalil idan ba Khalil ba wani namiji da zan aura.

" Hanb'are ta yayi ya fice ya barta a tsaye tana share hawaye.

"Amma falmata sai yau na tabbatar baki da hankali, sakin fuskar da ake muku ba wani dan anajin tsoranku bane, kawai dan ku san cewa an baku 'yanci ne.

" Wannan ne' yanci, wallahi wannan ba 'yanci bane, wannan tauye hakki ne, ni a gurina wannan hana abinda zuciya take so ne, na fad' a muku ina son khalil kun k'i yadda ko.

Baba a fuskace ya zabga mata bulalar, dukanta yayi sosai sai da ya gaji dan kansa, sannan ya tashi ya bar wajen, umma ma anan ta barta, in banda usman da sadeeq da suke zaune.

"na shiga uku na lalace, yau ga iyaye sun hana 'yarsu abinda takeso, nace muku khalil nakeso, khalil nakeso kunk' i yadda,ohhh ni falmata dame kukeso naji da wulakancin da ibrahim yayi mini jiya ko kuwa da hana ni fita da kukayi.

Haka tai ta rusa ihu, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru, can dare ya gama yi ta tashi ta tafi katifarta.

A ranar kwana tayi batayi bacci ba, asuba alwala tayi ta koma d'aki ta saka sakata sallah tayi tai kwanciyarta.

Bacci ne ya d'auketa, a kalla ta kai 11 na safe tana bacci, umma ko kallon hanyar d'akin batayi ba, domin ita haushin falmatar ma takeji.

Fitowa tayi tana turo baki, kitchen ta huce ta samu abincin karin kumallon ta ta d'auka ta koma falon.

Umma dai ko kallonta batayi ba, sai ma tsaki da taja domin ita falmata ta fice mata yanzu, wai yanzu falmata ake gani a shagon wani saurayi amma dik fad'in unguwar nan an sani amma babu wanda ya tab'a zuwa ya gaya mata domin ta d'auki mataki.

Lallai mutane sai dai a barsu da halinsu, yanzu da ace d'an wani ne da tuni yanzu an dameni da zancen banza.

Tsaki taja taci gaba da aikinta.

Bangaren auwal kuwa ya samu mahaifin sa akan maganar auren sa da falmata, mahaifin yayi na'am da zancen nasa.

Inda yace auwal ya sanar musu zasu zo ranar litinin wato jibi sai a tsayar da maganar auren kawai.

Auwal har gida yazo ya fad'awa baba, inda baba yaji dad'i matuka sosai, shi kuwa auwal yana cikin farin ciki domin ya samu abinda yake da muradi da buri a cikin rayuwar sa.

Umma yanzu bata shiga harkar falmata, inda ita yanzu takeyiwa kanta kulle, idan ta fito da safe bazata k'ara fitowa ba sai yamma daga nan kuma sai washe gari, hatta wanka yanzu falmata ta daina yi, b ruwanta da kowa batawa kowa magana, ba abinda take tunani sai soyayyar khalil wadda ta rufe mata ido.