Chapter 37
https://www.arewapen.com/book?id=6ab251c3cb0cfb2373811a7f
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 37.
Wata mata ta gani tsugunne tana ta faman kelaya wani irin amai, da hanzari ta matsa kusa da ita tana ambatar sunan Allah a ranta.
Tsugunnawa ta yi tare da saka hannayenta duka biyu ta riƙo kafaɗun matar gam, cigaba da zazzago amanta ta yi kamar me amaye hanjin cikinta.
"Ruwa, dan Allah."
Ta faɗa cikin fisashiyar muryar da ta fito a galabaice.
Har Maryam ta tashi da zummar ɗauko mata ruwan, sai taji bata iya barin matar a nan ita kaɗai sai ta tsugunna tare da faɗin.
"Wajen nan bashi da kyau, ko zaki daure muje can inbaki ruwan?."
Jinjina ta yi a wahale sannan ta ce.
"Bazan iya tafiya ba jikina rawa yake, ko zaki taimaka min please."
Durƙusawa Maryam ta yi tare da tallafar matar ta miƙar da ita tsaye, suna soma takawa sannu da ahankali har zuwa wajen da take zaune.
Bayan sun zauna ne Maryam ta bata ruwan data buƙata, sai da ta kuskure bakinta sannan ta shanye gora ɗaya, kallon Maryam ta yi tare da faɗin.
"Dan Allah yata kiɗan ƙaramin ina jin ƙishi sosai." da sauri Maryam taja mata duka sauran ruwan.
Jiki na ɓari ta shiga balle murafin tana shanye ruwan sai da tasha roba biyar sannan ta dakata ahakanma badan sun wadaceta ba gani ta yi ruwan ya ƙare saura gora biyu.
"Idan basu ishe ki ba ki shanye sauran, zan je inƙaro wani."
Maryam ta faɗa tausayin matar na lulluɓeta.
Wani busashen murmushi matar ta saki tare da faɗin.
"A'a ya ishe ni, dan Allah zan iya kwanciya a nan inɗan huta kaina yana ciwo sosai?."
Ta faɗa tana rintse idanuwanta.
Da sauri Maryam ta ce "Ih za ki iya yin dukkanin abin da kike so a nan ɗin."
Kwanciya ta yi a ƙasan wajen tana maida numfarfashi a wahale, ga wani irin zazzafan zazzaɓi daya soma rifar mata.
Ci gaba da tazbihi Maryam ta yi, tana jin yanda har lokacin tsikar jikinta ke mimmiƙewa.
Sun ɗauki lokaci a haka, kafin numfashin matar ya fara sauyawa, ta fara wani irin nishi haɗi da gurnanai, jikinta ya soma rawa daga kwancen da take, wani irin tururi na fitowa daga fatarta.
Da sauri Maryam ta matsa kusa da ita sosai tare da riƙe hannunta da yayi zafi jau a cikin nata hannun aɗan rikice, cikin hasken zobenta take ƙarewa fuskar matar kallon, wani abu na hawa da sauka acan ƙasan zuciyarta.
Jin matar taci gaba da jijjiga tana wani kalar gurnani, kuma zafin cikinta sai daɗa ƙaruwa yake ya saka Maryam sake ruɗewa, ta tallafi fuskar matar a cikin hannayenta ta soma yi mata tofi tana shafe daza kan fuskarta har zuwa wajen ƙirjinta.
A hankali ta soma rage kyarmar numfashinta ya daidaita taci gaba da wani iri wahalalen numfashi har firgita take yi tare da sambatu a cikin barcin.
Sosai matar ta bawa Maryam tausayi, yanayin da ta ganta ciki kawai abin a tausaya mata ne.
Sun kwashi lokaci me tsayi a haka, yayinda kanta ya koma kan cinyoyin maryam, ita kuma bata jinkirta da yi mata tofi ba har sai da itama barcin yaci ƙarfinya.
Zuciyarta ta kwashe shekaru tana zullumi da firgici a koda yaushe, amma a yau da ta yi nasarar barin wajen kuma ta tsira wani yanki daga sashen zuciyarta ta samu salama, salamar da ta bata damar yin barci cikin salama, babu wannan tsoron, babu wannan zullumi da tashin hankalin data jiya tana barci a cikinsu, yanzun fresh ta ke kamar wata sabuwa....
***
JUNAID.
Da taimakon Uncle ya samu ya bawa Abeey wannan ruwa maganin da suka je amsowa, duda ba duka ya shanye ba amma yasha babu laifi, kuma yana gama sha yaci gaba da barcinsa, barcin da ya ke basu nutsuwa domin kuwa sun san yana cikin aminci da samun salama.
Yayinsa Fahad ya ke zaune a gefe ya zabga uban tagumi ya gagara koda furta kalma ɗaya, hasalima shi kan shi baaya cikin nutsuwar shi.
"Fahad follow me."
Junaid ya faɗa bagan ya dafe kafaɗar shi ta haggu.
A razane Fahad yaja da baya, tashin hankali da tsoro na bayyana a fuskar shi, kafin kuma ya saki ajiyar zuciya me ƙarfi ganin da ya yi Junaid ne.
Da kallon ƙurulla Uncle yabi Fahad ɗin, yana saƙawa da warwarewa a cikin kan shi.
Ta shi ya yi tare da bin bayan Junaid ɗin kamar yanda Fahad ɗin shima ya bi bayan shi.
A wani ƙaramin ɗaki da aka ake kujeru ƙanana tare sa table guda ɗaya suka shiga tare da zama.
Fuskar Junaid na kallon gefe ya soma magana.
"Zan tambayeka a karo na ƙarshe Fahad, wannan gaskiyar wacce na sanka da ita tun muna yara ita nike da buƙatar ji daga bakinka, karka damu da ɗacin da zata yi maka wajen fitowa, muma wannan ɗacin shi zamu ji a yayin jinta, karkuma kace zaka ɓoye mana komi, domin kuwa komin muke da buƙatan sani domin mu samawa kanmu mafita."
Jinjina kai Uncle ya yi tare kallon fuskar Fahad ɗin da ya soma tsatsafo da gumi sannan ya ce.
"Damuwarka damuwarmu ce Fahad, hankakinmu bazai taɓa kwanciya ba bayan munsan baka da cikakkiyar nutsuwa."
A tsawace Fahad ya ce da su yana zazzare idanuwa.
"So kuke insanar da ku ɗanyan aikin dana kama mahaifiyata tana aikatawa, koko so kuke insanar da ku abin da idanuwana suka gane min da har na kasa walwala da sukuni???." ya yi maganar yana zazzare idanuwan shi, sai kuma ya koma ya zauna tare da fashewa da ƙaƙƙarfan kuka.
"Na kasa amincewa da lallai Mommy na gani da idanuwana, na kasa yadda ita din ce na kama tana aikata ɓarna da hannayenta." ya faɗa yana buɗe tafukan hannayensa duka yana ƙoƙatin kwatanta musu.
"Calm down my brother, I am with you, tell me abin da ya faru da muna hospital." Junaid ya faɗa yana shafa bayan shi.
Sake zabura Fahad ya yi yana zare idonshi da suka cika tab da hawaye kamar zararre ya soma faɗin.
"In faɗa muku ku ƙata tsanarta, koko infaɗa maku ku koreta daga gidan bayan nasan dukanku babu wanda yake sonta."
"Ba zamu koreta bama zamuyi komi ba muna son sanin abin da ta aikata ne kawai domin musan ta inda zamu warware bakin zaren." Junaid ya faɗa a gaggauce domin kuwa ƙage ya ke da sanin abin da Mommy ɗin ta aikata.
Share hawayen idon shi Fahad ya yi tare da komawa ya zauna.
"Ina son Mommy kamar yanda kuma nike tsananin sonku, kuma kamar yanda nike tsananin son Mahaifina abin alfaharina, amma bazan iya ɓoye wannan gaskiyar ba kamar yanda bana jin zan iya bayyanata da kaina."
Yana gama faɗin hakan ya tashi ya fice a guje yana kuka me sauti.
"Oh mu god, wannan yaron yana so ya caza mana kai wallahi, please miye abin yi yanzun."
Uncle ya faɗa yana kallon sashen sa Junaid ya ke.
"Na fara gano wani haske akan lamarin nan, ya ce Mommy kuma ya ce Daddy kenan abin ya dangance su.
And yanayin da muka taradda Abeey da kuma Fahad, sannan kiran sunan Mommy da ya yi kafin ya suma da kuma dubawa da muka yi bamu ganta a gidan nan ba, bayan driver da security sun tabbatar mana da ta dawo kuma ita ta aike su, wannan kaɗai ya isa hujjar da zan zargeta, sannan idan baka manta ba akwai wanan abun, wannan abin da ya sake bani tabbaci abin da muka samu a ɗakin Abeey, amma dai bazan yu gaugawa ba zanci gaba da bin komi a sannu har na cimma nasara, na gyara komi da aka lalata, na haɗe ahalina da aka tarwatsa sannan in gyara rayuwata da aka nakasta." Ya faɗi yana runtse idanuwan shi, yana sauraron yanda zuciyar shi ke suya akan rashin kawo ƙarshen abubuwan da ke faruwa....
Da daddare bayan Junaid da Uncle sun sake bawa Saminaka magani, suka tabbatar da baya da wata damuwa, komi yana tafiya daidai, Junaid ya yiwa Uncle sallama ya nufi ɗakin shi, yayinda shi kuma Uncle ɗin zai kwana tare da Saminaka.
A gajiye ya ƙarasa bakin gadon tare da zama ya dafe kan shi da yayi ma shi nauyi, yanajin yanda ya ke barazanar tarwatsewa muddin bai sarara daga cunkusa ma kan shi wasu tunanika ba.
Takalmin ƙafar shi ya fara zarewa, sannan ya cire safar data saka ƙafar ta shi tayi ɗumi sosai, ya jefar a ƙasa tare sa yunƙurawa ya soma rage kayan jikin shi yana jefarwa a wurare mabanbanta, har ya isa ƙofar toilet, babban fari ƙar ɗin towel ya ɗauka tare da buɗe ƙofar ya shiga ciki bakin shi ɗauke da addu'ar shiga bayi....
Kwanciya ya yi akan makeken royal bed ɗin shi yana juyi tako ina, jikin shi na ƙwanƙwatsar gajiya da zirga-zirgar da yake yawan yi a kwanakin, da kuma ƙananun aiyuka waɗanda bai saba da su ba sai zuwan shi ƙasar nan.
Gam ya runtse idanuwansa da lokaci guda ganinsu ya ɗauke daga kan komi ya lula can yana hasko ma shi abin da ya faru bayan futar shi ta farko.
' "Ruwa zaka bani please." '
Muryarta ta dawo ma shi a dodon kunnen shi, suffarta na bayyana a cikin idanuwan shi, numfashin shi ya soma shiga da fita cike da wani yanayi da akanta kaɗai ya soma jin shi, a hankali ba cikin hayaniya ko gaugawa ba tarin damuwoyin shi da kuma tunanikan da suka ɗaure kan shi suka shiga warwarewa, zuciyar shi ta bashi sararin yin tunani akanta ita kaɗai.
Wani sanyi ne ya soma lulluɓe shi bayan na AC ɗin daya ƙure a ɗakin, take shauƙi ya ɗebe shi ya lula da shi wata duniyar ta daban, fuskarta da ɗan ƙaramin bakinta me ɗauke da laɓɓa masu tudu kaɗan wanda suka fizgi nutsuwarsa.
Sannu a hankali wata ƙofa da baisan da ita ba a zuciyar shi ta soma buɗewa, tana zuba memories ɗin shi da ita da kuma yanayin da yake ciki tana ajewa a cikinta.
Rintse hannun shi ya yi kamar me ƙoƙarin kama wani abu yana jin yanda ɗumin jikinta ke ratsa gashi da ɓargon shi yana jin kamar yanzun ne take a jikin shi.
"Special." ya furta kalmar yana jin ta dace da sunan da ya bata, daga haka wani irin daddaɗan barci me cike da nutsuwar ruhi da gangar jiki ya sace shi, cike da kewar gangar jiki da ruhin d bai san inda zai sake yin arba da su ba....
MAKAFA.
A daidai lokacin da mutum ke kan ganiyar aikata son ran shi, lokacin daya shashantar da komi yayi butulci da ni'imar Ubangiji, sautari a lokacin ne jarabta ke samun bawa, wacce ke banbance manshi daidai da rashin daidai.
Ƙur ya ƙure ƙafafuwan shi guda biyu da jajayen idanuwan shi da suka sake turewa saboda azabar da raɗaɗin da suke karɓa.
A karo na babu adadi ya yi ƙoƙarin tashi da kalmomin da yake amfani da su wajen kiran tsafinsa, amma abun yaci tura ya kasa komi, ya gaga aikata komi, ikon mallaka ya suɓuce daga gare shi a daidai lokacin da yake tsananin buƙatar Ikon, ya kasa gasgata tunanin da hargitsatsiyr kwanyar shi ke son bijiro ma shi da shi akan Ƙwaro, Ƙwaro daya kasance kamar innuwar da shi Makafa ke fakewa a cikinta yana murza kambun iko, ya gagara yin tunanin me kyau saboda hayaniya da kuma surutan da suke ƙara yawaita a saman kan shi wanda suka kuma birkita lissafinsa.
Kai hannun shi ya yi akaro na babu adadi tare da rintse idanuwan shu cikin ƙarfin hali ya taɓa glashin kariyar da Kanzul ya yi wanda sillar rusheta ne wannan abib ya faru da shi.
Nan take hannunshi ya soye wani baƙin jini ya soma ɓulɓulowa daga cikin hannun, amma bai saki ba sai da yayi nasarar janyo ƙafar shi ɗaya cike da azaba, da ƙyar ya janye ɗayar itama sannan ya saki abar yana kurnanin azabar da ke ratsa shi tako ina.
Sandar shi ya ɗauka data rabe gida biyu, ya dogara da ita ya soma ƙoƙarin tashi sama, ya yi nasarar ta shi jikin shi ya rabu da ƙasa amam kuma bai tashi sama sosai ba kamar yanda ya saba ɓacewa cikin iska.
Hakanan ya lallaɓa ya soma ɓacewa sai dw kuma kasancewar ya yi ƙasa sosai sai ya dinga cin karo da bishiyu harma da wasu abubuwan a kan hanyar shi, dabara da yayi a maimakon ya koma gidan shi na cikin daji, sai ya koma na cikin gari a mugun gajiye, da ƙyar ya iya ɗagawa ya hau ta saman katangar ya shiga ta samab iska ya isa ɗakin shi....
Alhamdulillahi bayan tsayin kwanaki huɗu zuwa biyar yau Allah yayi na dawo naci gaba da typing, da fatan zakuci gaba sa kasance tare da ni a cikin wannan ƙayataccen labarin domin kuwa wannan karon da zafina na dawo.
Kukasance tare da ni domin jin yanda zata kaya nice taju har ƙullum.
Maryam Star Amanar Bilyn Abdul.