Chapter 13
by @authorrukie
Na gama aikin da nake yi, na nufi komawa ɗaki, sai ga Baba ya fito daga ɗakinsa, riƙe da buta a hannunsa, yana asuwaki irin na tsofaffin mutanen ƙauye.
Na tsaya na kalle shi, sannan na gaida shi cikin girmamawa.
“Ina kwana, Baba?”
“Lafiya,” ya amsa a taƙaice, ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Ya ci gaba da asuwakin da yake yi, yana riƙe da butar a hannunsa.
Na saba da halinsa, don haka ban damu ba. Na ci gaba da tafiya zuwa ɗakinmu
Na shiga ɗakin, na zauna a kan katifa, sannan na ɗan kwanta domin in huta. Tun da safe nake ta kai-komo da ayyukan gida, don haka jikina ya fara nuna alamun gajiya.
Lokacin kuwa har ƙarfe goma na safe ta yi.
Na lumshe idanuna, ina jin hayaniyar da take tashi daga tsakar gida. A gidanmu, da zarar gari ya waye sosai, kowa yana fitowa ya kama hidimarsa. Wasu yaran suna kai-komo, wasu suna Taya eyayen su hada kayan sana a
Hayaniyar yaran gida ta gauraya da ta matan gida, har gidan ya ɗauki wani irin ƙara. Wani yana kiran wani, wani yana neman kayan aikinsa, yayin da wasu kuma suke ta hira a tsakaninsu.
Ni kuwa ina kwance a ɗakinmu, ina ƙoƙarin samun ɗan hutun da ban samu ba tun da sassafe.
Amma ai gidanmu ba gidan da za ka kwanta ka huta yadda kake so ba ne. Kullum akwai wani aiki da zai taso, kuma ko da ka gama ɗaya, wani zai biyo baya.
Ina cikin wannan tunanin ne na ji muryar Aisha
daga tsakar gida tana magana da ƙanwarta.
Ke Lubabatu, ba za ki zo mu haɗa abincin nan ba? Kin san fa ƙarfe biyu za mu fita bakin kasuwa da shi. Yanzu har goma ta yi, amma ba mu fara komai ba!”
Lubabatu ta amsa daga ɗakin da suke ajiye kayan girki.
“To, ga ni nan zuwa mana! Ai ba ni kaɗai ce a gidan ba.”
“Ke dai kullum sai kin yi magana! Maimakon ki zo ki taimaka, sai ki tsaya kina mayar da amsa.”
Na lumshe idanuna, ina sauraron yadda suke saɓani. Na san sana'arsu ta dafa abinci a bakin kasuwa tana buƙatar shiri sosai. Dole ne su gama girki, su zuba abincin a cikin tukwane, sannan su shirya komai kafin lokacin fita ya yi.
Ni kuwa, duk da gajiyar da nake ji, ban samu damar hutawa yadda nake so ba.
Ina kwance kenan, sai na ji muryar Gwaggo ta tashi daga tsakar gida.
“Rammu! Ina kika shiga?”
Na buɗe idanuna a hankali. Na san wannan kiran ba zai kasance na tambayar lafiyata ba.
“Ga ni nan, Gwaggo,” na amsa, ina miƙewa daga kan katifa.
“Ki fito ki taimaka wa Aisha wajen gyara kayan girki. Ba kya ganin lokaci yana tafiya? Sai an gama girkin kafin ƙarfe biyu.”
Na sauke ajiyar zuciya, na miƙe tsaye duk da yadda jikina yake yi mini nauyi. Na gyara ɗankwalina, na fito daga ɗakinmu.
Da na isa wurin girkin, sai na tarar da Aisha tana ware wake, yayin da Lubabatu take wanke tukwane. A gefe kuma, akwai albasa, barkono da sauran kayan miya da aka tanada domin girkin.
Aisha ta kalle ni.
“Rammu, ki taimaka min ki bare albasa ki yanka ta. Da zarar kin gama, sai ki taimaka wajen gyara sauran kayan.”
Na zauna a gabanta, na fara aikin ba tare da na ce komai ba.
Gaskiya na gaji, amma wa zan faɗa wa? Tun da safe nake ta hidima, kuma da alama har sai sun gama shirya abincin zan ci gaba da aikin.
Aisha da Lubabatu kuwa suna ta shirye-shiryen sana'arsu, domin sun san idan suka makara zuwa kasuwa, za su iya rasa wasu kwastomominsu.
Na sunkuyar da kaina, na ci gaba da yanka albasar, hawaye na ɗan zubo min saboda tsananin ƙamshinta.
A raina kuwa, tambaya ɗaya ce take ta yawo.
Shin akwai ranar da wani zai lura da wahalar da nake sha, ya bar ni in huta ko da na ɗan lokaci ne?