LOKACI CHAPTER 25
by @fulani32
***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU FULANI
YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
FULANI ❣️
***
PAGE 2️⃣ 5️⃣
Tana jin yanda zuciyarta take bugawa kamar zata faso ƙirjinta ta fito.
"Besty"
Sosai kiran da ya mata ya ƙara mata bugun zuciya, saboda muryar da yayi amfani da ita wajen kiran nata, muryar da a da take iya gane halin da yake ciki, farin ciki ko akasin sa, kau da kanta tayi gefe.
"Zan tafi" ta ce ba tare da ta kallesa ba.
Gyara tsayuwarsa yayi, sannan ya bita da wani irin kallo mai tarin tambayoyi, a hankali ya kirata cikin taushin murya, duk da fuskarsa babu alamun fara'a.
"Falmata!"
Lumshe idonta tayi, ta daɗe ba taji sunan ba, suna ne da ya kasance shi kaɗai ne yake kiranta da shi, sunan yana ɗauke da wani irin sirri.
"Besty!!" Cikin wata iriyar murya ya kirata, ba ta san sanda ta ɗago ta zuba masa ido ba. Kallonsa take cikin wata iriyar shagwaɓa, da ita kanta batasan ta bayyana akan fuskarta ba, sosai ta kwaɓe masa fuska, ɗan ƙaramin bakinta ta turo masa, sai motsa bakin take a hankali, ta kasa tsaida idonta waje ɗaya sai faman ƙifƙifta su take.
Cak ya tsaya yana kallonta, sai dai ba wannan Zahran yake gani ba, Bestynsa yake kalla, saboda yanda ta koma masa ƴar yarinyar sak, a hankali ya matso kusa da ita, ya rage tazarar da ke tsakaninsu.
"Me ya sa kike guduna?"
Ya yi mata tambayar muryarsa a ƙasa sosai, amman hakan bai hanata jin zafi a cikinta ba, ƙasa ta ƙara yi da kanta.
"Ni ba gudunka nake ba"
Ɗage girarsa ya yi yana kallonta har lokacin.
"Oh really?"
Marairaice masa fuska tayi, dan ta rasa me zata ce masa.
"Tsoron me kike ne Besty?" Ya jefa mata tambayar yana murmushin gefen baki.
Ƙasa ta sauke idonta ta rasa abin da zata ce masa, wasa ta fara da zoben hannunta, kamar yadda ta saba a duk lokacin da take cikin damuwa.
Kai tsaye idonsa ya sauka akan hannunta, da take ta faman murzawa, bai san ya akai ba kawai ya ji hannunsa ya sauka akan nata.
Wani irin shock ne ya ratsa su duka biyun tare da baƙon yanayin da suka tsinci kansu a ciki, jikinta ne ya fara rawa, dan babu wani namiji da ya taɓa riƙe mata hannu, shi kuma idonsa yana kan zoben.
Ɗago kanta tayi a hankali ta kallesa, idonta taf da hawaye, shima kallonta yake ido cikin ido, ƙasa tayi da idonta dan ba zata iya jure kallon idonsa ba, sosai ya zuba mata ido yana kallon fuskarta, kamar wanda yake son gano wani abu a fuskar.
"Besty" ya kirata a hankali.
Lumshe idonta ta yi "ya rabb" ta ce a zuciyarta, jin yanda tsigar jikinta take tashi, da ƙarfi ta runtse idonta, jin yanda tattausan hannunsa yake shafa ɗan yatsanta.
"Best.. fri..end!!" Ta kira sunansa ba tare da ta shirya ba, cikin rawar murya.
"Uhmm" kawai ya iya ce mata.
Cikin sanyin murya ta ce "hannuna ka saki dan Allah" kallon hannun nasu yayi, sai kuma ya kalli fuskarta, ganin idonta ya cika da hawaye, a hankali ya buɗe hannunsa da nata yake ciki, ya ba ta damar janye nata, sai dai kafin ta kai ga janyewa, idonsa ya sake sauka a kan zoben, ƙara riƙe hannun nata yayi.
"Ka sake ni" ta ce cike da raunin murya.
"Har yanzu kina tare da shi?" Tambayar tasa ta daskarewa, kallon hannunta tayi, babu shiri ta saka ɗayan hannun nata ta rufe wajen zoben.
"Zahra!" Ya kira ta a dake.
"Kalle ni" maƙale masa kafaɗa tayi, hawayen da take ta faman riƙewa ya zubo mata. "Ni ka sake ni gida zan tafi"
"Ki kalle ni na ce" ya yi maganar a tsawace.
"Kinsan adadin shekarun da nayi ina neman ki? Kinsan yanda rashinki ya azabtar dani? Shine kike cewa na sake ki? Har abada bazan kuma barin ki ba, idan ma kina wannan tunanin kidena" dunƙule hannunsu yayi a nasa.
Cize leɓenta na ƙasa tayi, sosai take ƙoƙarin danne kukan da ya fara ta so mata, abin dai da take tsoron faruwar sa gashin nan yana shirin faruwa.
"Ka sake ni, dan Allah"
"Me?" Ya tambayeta dan shi ya ma manta hannunta yana cikin nasa.
"Nace ka sake min hannu ko" tayi maganar da ƙarfi tana ƙoƙarin zare hannunta.
A hankali ya saki hannunta, ba tare daya ɗauke idonsa a kanta ba, "toh na sake ki faɗamin meyasa kike guduna, me kuma kike tsoro?" Tana murza hannunta ta ce "babu wani dalili"
Maimaita abin da ta ce yayi, tare da wani irin murmushi da iya kacinsa fatar bakinsa, "naji kalleni toh" runtse idonta ta yi tare da saka hannu ta rufe fuskarta. "Ni ka rabu da ni"
"Me ya sa?" Kasa ce masa komai ta yi. "Ko kuma dai kina tsoron.."
"Muhan" ta katse sa da ƙarfi, shiru sukayi dukkansu, "to faɗa min meyasa?" Baya ta matsa, ta jingina da teburin bayanta, dan ta fara gajiya da tsayuwar, shi kuma irin halinsa da ta sani, tasan idan har ba amsa ta basa ba, ba zai taɓa ƙyaleta ba, kuma tasan yasan duk yanda zaiyi ya sakata ta faɗi abin da ba tayi niyya ba. Ji take kamar ta koma wannan ƙaramar yarinyar da take zama a aji kusa da shi, kamar su koma lokacin da take jin haushin yawan kallonta da yake, shi kuma ya dinga harararta akan ta karɓe masa matsayinsa a exam, sai dai wannan karon ba batun sakamakon jarabawa bane, batu ne na alƙawari, alƙawarin da ya yi mata shekaru da dama da suka wuce, alƙawarin da ya saka ta dariya a wancan lokacin, alƙawarin da a yanzu ya zama katanga a tsakanin ta da shi.
" Ba ka fahimta ba ne Muhan"
"Ina jinki fahimtar dani" yace bayan ya naɗe hannunsa a ƙirji.
Tas ta goge hawayen fuskarta, sannan ta tattaro jarumtarta ta fara masa magana "ka bar abubuwan da suka faru su wuce, ba gudunka nake ba, kuma ba tsoronka nake ba, kawai ina son nayi rayuwata anan kamar ko wace ma'aikaciya, ka manta dani Muhammad, ka manta da cewa kama ganni dan Allah ka fita da ga rayuwata! Ba dole bane sai mun koma yanda muke da ba, kaga dai yanzu mu ba yara bane"
Shiru yayi mata.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin yanda yayi, sai tayi tunanin ya amince da abin da tace, take taji wata nutsuwa ta sakko mata.
"Wa ya ce miki ina son mu koma yanda muke a da?"
Da mamaki ta kallesa jin abin da ya ce mata. Kusa da ita ya matso "sai na san me ya faru da bestyta, sai nasan abin da ya canja ki haka, ke a taƙaice ma kawai ki bar wannan maganar"
"Ni fa ba yarinyar da ka sani a da bace, babbace ni yanzu dan haka ka ajiye maganar Besty a gefe"
Cike da rainin hankali ya ce "nagani ai"
"Toh ka rabu da ni"
Kai tsaye ya ce "ba zan iya ba"
Cikin gajiya da maimaita maganar ta ce "me ya sa" murmushi ya yi wanda ya ƙara masa kyau "saboda har yanzu keɗin dai bestyna ce, sannan kuma..." Bai ƙarasa ba, sai murmushin da yake bin ta da shi.
Zuciyarta ce ta buga da ƙarfi, kawar da fuskarta gefe tayi, dan idan ta ci gaba da magana, tsaf zai sakata ta faɗi abin da ba tayi niyya ba.
"Falmata"
"Wai ba za ka rabu da ni ba Muhan?"
Wani murmushin ya ƙara sakar mata, zuciyarsa kuma cike da farin ciki, ganin yanda tayi masa maganar, kamar dai bestynsa, sai dai abin da ya saka shi murmushi, fahimtar ita kanta bata san abin da take a gabansa ba, abin da take ma ya daina bashi haushi, nishaɗi take basa, dan haka ya ci gaba daga inda ya tsaya.
"Besty!"
Harara ta watsa masa, ta juya ta bar inda ya ke. Take mata baya yayi, gaba ɗaya ta kasa tsayawa waje ɗaya, magana ce ta gaji da yi masa, shi kuma ta fahimci burinsa ayi ta jan maganar. Tsayawa ta yi ta kallesa na ƴan daƙiƙu, murmushin yaƙe tayi ta ce.
"Wanda zan aura yana da kishi sosai, shi ya sa nace ka rabu dani, idan ya samu labarin ina kula wani samu matsala da shi, ba zai duba cewa kaiɗin tsohon abokina bane"
Cak ya tsaya, a take murmushin fuskarsa ya ɗauke, sai ma wani irin kallo da yake jefa mata, tsoro ne ya fara kamata ganin yanda fuskarsa ta koma a lokaci ɗaya, amman ta dake ta ƙara bashi tabbacin mijinta yana da shi, shiyasa ta ce ya manta da ita.
"Zan baki mamaki Zahrah"
"Me za ka yi?" Ta tambayesa muryarta tana rawa.
"Kin tuna a duk lokacin da na miki zan yi wani abu, sai ki dinga dariya kina cewa ba zan iya, amman kuma idan lokacin yazo sai ki ga nayi haka ne?"
Tabbas da ya na kusa da ita da yaji yanda zuciyarta take bugawa da ƙarfi. Bai jira cewarta ba ya ci gaba.
"Yanzu daga gani na duk kin firgice, tun ma kafin na faɗa miki abin da zanyi"
Wannan karan bugun da zuciyarta tayi ta fi na farkon.
"Kina jin tsoron na cika wani alƙawari da nayi akan ki ne?"
A firgice ta ce "ba ka da wani alƙawari da ka yi a kaina" kallonta yake itama tana kallonsa, ya na ganin yanda tsoro ya bayyana ƙarara a idonta, shikenan ya zurmata, daman ta san dole sai ya saka ta, ta faɗi abin da ba tayi niyya ba. Hannayensa ya cire daga aljihu ya kuma kallonta.
"Alƙawari" ya maimaita kalmar a hankali. "Kin ji na ce ika da alƙawari a kanki ne?" Shiru tayi masa, dan idan ta ci gaba da magana ba tasan mai kuma zai sakata ta ce ba.
"Ni fa ina nesanta kai na daga wajenka ne saboda bana son abin da zai ɓatawa mijina rai Muhammad, ina sonsa bazan juri ganin ɓacin ransa ba, a kan ka, dan haka dan Allah ka rabu dani, idan ma dan kana ganina ne a wajenka, zan nemi transfer na koma inda nake aiki tun farko"
"A kan wani kike cewa na rabu da ke?" Ya tambayeta yana kallonta.
"Eh!"
Juyawa ya yi ya nufi hanyar fita daga kitchen ɗin, dan ba zai jure jin wata kalmar daga bakinta ba.
Bayansa tabi da kallo, zuciyarta na yi mata zafi akan abin da tayi masa, sai dai bata da wani zaɓi ne, kuka ne ya ƙwace mata, dan a idonsa taga yanda kalaman ta suka taɓa masa zuciya, jakarta ta ɗauka doguwar riga ta ɗora akan unifoam ɗinta tayi rolling ta fice daga restaurant ɗin, ba tare da ta bi ta kan masu tambayarta akan Zay'd ɗin ba.
Napep ta tare ta shiga, har taje gida tunani take, lokacin da ta koma babu kowa a tsakar gidan, kai tsaye ɗakinta ta shige ba tare da taje wajen Mahmah ba, da kayan jikinta ta kwanta ta zubawa sama ido, a hankali abin da ya faru a lokacin ya fara dawo mata.
Suna zaune lokacin sauran paper biyu suka gama exam ta jiniour candy, fuskarsa cike da murmushi ya ce.
"Falmata"
"Na'am Muhan" ta amsa masa tana mayar da hankalinta kansa.
"Wane irin miji kike son aure?"
Sosai tambayar tasa ta bata dariya "sirri ne Best friend ba zan faɗa maka ba" amsar da ta bashi kenan, amman ya takura mata akan sai ta faɗa masa.
"Bana son auren namiji yaro, na fi son auren babban mutum, wanda ya girmeni sosai"
Taɓe bakinsa ya yi ya ƙara tambayar ta "zaki aure ni?"
Tambayarsa sosai ta bata dariya, har sai da taga ya fara jin haushin dariyar da take sannan ta ce "Allah ya kiyaye na auri classmate ɗina, caɓ Muhan kai fa agemate ɗina ne ma, ta ya kake tunanin zan aureka shirme ma kenan"
"Wallahi Besty, idan har lokacin da na isa aure ya yi, ke ba ki yi ba, ko ta halin yaya sai na aure ki" wata dariyar ta ƙara masa ba tare da ta ce masa komai ba.
"Ki riƙe wannan Zahra alƙawari ne da na yi miki, kuma na yi wa kaina!"
A lokacin duka a shirme ta ɗauka, amman ranar da ta gansa a office ɗinsa, abu na farko da ta ji tsantsar mamaki, sai kuma ta ji wani irin farin ciki na ganinsa, sai dai kafin ta ce komai, alƙawarin da ya yi ya dawo mata, wannan shine dalilin da ya sa ta juya masa baya ta gudu, dan tana tsoron abin da zai je ya dawo, yana da taurin kai, a duk lokacin da ya ce zai yi abu sai ya yi shi, bare kuma ya ce alƙawari.
A lokacin da ya yi mata alƙawarin, Muhammad ne, amman a yanzu shiɗin Zay'd ne, mamallakin gidan abincin da duk Kano babu mai girmansa, daga ganinsa kuma tasan kuɗi ya zauna masa, duk da ma a wancan lokacin ma tasan iyayensa masu kuɗi ne.....
★★★
Khairiyya
Watanni uku sun shuɗe cikin sauri, watanni ukun da suka kasance sabon babi na rayuwarta, a cikin watanni ukun ta je makarantar ta, ta koyon girke girke, kuma alhamdullah ta samu abin da ta ke so, dan sosai ta mayar da hankali akan abin da ake koya musu, sosai ta jajirce har zuwa ranar da aka bata certificate na kammalawa.
A ranar da aka bata certificate ta ji wani irin farin ciki da ta daɗe ba ta jisa ba, tana riƙe da takardar fuskarta ɗauke da murmushi, ta na dawowa gida cikin farin ciki ta nuna wa Ummu, bata iya barinsa a hannunta ba, ta tafi da shi ɗakinta ta ajiye a inda duk sanda ta shigo ɗakin da shi zata fara cin karo.
"Alhamdullah" ta furta a bayyane. "Ya Allah na gode maka da ka nuna min wannan ranar, Allah ka sawa sana'ar da zan fara albarka" kamar yanda Aunty Maryam ta ce mata, wannan wata hanya ce da zata tsaya da ƙafafunta, sai ta fara tunanin ta ina ya kamata ta fara, da farko ta fara ne da dafa abinci, da wasu kayan ciye_ciye a gida, idan tayi sai ta ɗauki hotonsu masu kyau, ta ɗora a status ƴan gidansu ma su tayata, a hankali ta fara sana'ar cike da jin daɗi.
A hankali mutane suka fara saninta, sosai take samun order, abin da ta fara a matsayin ƙarami, sai gashi ya zamar mata abin da take samun kuɗi sosai, wani lokacin haka zata zauna tana lissafin kuɗin da ta samu, tayi ta kalla ta na jin daɗi.
Babban abin da yake damunta, yawan kawo mata maganar aure, gashi kai tsaye Alhajinsu ake nema da maganar, ko kuma Ummu, wani lokacin ma harda Aunty Maryam, duk sanda su ka yi mata maganar shiru take ta ƙi basu amsa, dan ita babu lissafinsa a tare da ita yanzu dai.
Ta na zaune a parlow ta na kallon video na abinci, Ummu ta shigo a kusa da ita ta zauna.
"Khairiyya ba ni hankalinki magana za mu yi" tana jin haka ta sha jinin jikinta.
"Tohm Ummu" ta ce bayan ta kashe wayar.
Gyara zamanta tayi sannan ta fara magana.
"Wani ɗan gidan ƙawata ne ya ce yana son ki, matarsa ɗaya da yara 4, dagaske yake dan kai tsaye maganar aure yake, kuma ya ce baya son a ɗauki lokaci mai tsayi"
Shiru tayi mata, ta mayar da kanta kan wayarta, saboda ta ɓoye wa Ummu sauyin da ya bayyana akan fuskarta.
"Kin yi shiru Khairiyya"
"Bansan me zan ce ba Ummu" ta ce ba tare da ta kalleta ba.
"Kin amince kenan?"
Ajiyar zuciya ta sauke, kanta ta ɗago ta kalli Ummu, "Ummu ni fa ba ƙib aure nake ba, kawai ina jin tsoro ne" ta yi maganar cikin sanyin murya.
Ido Ummu ta zuba mata, tana karantarta, ganin yanda damuwa ta bayyana akan fuskarta "Tsoron me?" Ta tambayeta duk da tasan tsoron me take ɗin.
"Tsoron abin da zai faru a bayan auren Ummu, ni kaɗai nasan abin da na fuskanta, Ummu zaki ga mutum kamilalle sai bayan anyi auren, halinsa zai bayyana, kinyi aure kina farin ciki, amma daga ƙarshe ki ƙare cikin baƙin ciki da rayuwar da baki taɓa zato ba, idan aka kawo min maganar namiji a yanzu, sai na fara tunanin abin da ya faru da ni, nayi ta tambayar kaina, shin wannan ma zai zama kamar sauran ne? Ko kuma zai kasance wanda nake burin samu" kuka ne yake ƙoƙarin zuwar mata, ta dakata da magana, mayar da shi ta yi sannan ta ci gaba. "Babbar damuwar Ummu, ba za ka gane asalin mutum ba, sai ka zauna da shi, tun da dai shi halin mutum ba a goshi ake rubuta shi ba"
Numfasawa Ummu ta yi a hankali tana kallon Khairiyyan cike da tausayi. "Na fahimce ki, na kuma san me kike jin tsoron, amma kada abin da ya faru da ke a baya ya sa ki yanke hukunci akan duk wanda zai zo wajenki a yanzu, kowa da halinsa"
Gyaɗa mata kanta tayi. " Na sani Ummu shi ya sa ban ce ba zan yi aure ba, kawia dai ina son na samu lokacin da zan fahimci mutum sosai, sannan inyi addu'a akan Allah ya zaɓa min wanda ya fi zama alkhairi, Ummu ba zan maimaita kuskuren da nayi a baya ba"
Hannunta Ummu ta riƙe, ta saka ɗayan hannunta ta share mata hawayen da ke zubo mata "ki ci gaba da addu'a, nima ba zan matsa miki ba, Allah ya zaɓa miki mafi alheri".
Murmushi ta yi, tana jin daɗin yanda yanzu Ummu take fahimtar ta, baya takurata kamar da, a take taji nauyin zuciyarta ya ragu, bayan Ummu ta fita, ta mayar da hankalinta kan wayarta, order a ka saka mata, reply tayi, sannan ta rubuta.
FULANI
***