SAWU BIYU

PAGE 26

by @khadijahsulaiman406

SAWU BIYU 
Khadijah Sulaiman 
Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1

Page 26

Bayan sallar magrib ya tafi gidan Mami saboda baccin da ya ɗauke shi bayan ya sha magunguna.
A harabar gidan ya tsaya ganin mutane sai kai kawo suke,ya ciro waya yayi dailing number Mami.
Tana ɗauka ta ce"Faruq har yanzu dai bamu ganka ba".
"Gani a compound Mami,na ga akwai mutane sosai a gidan".
"Ka shigo kawai,babu kowa a parlourn".
Ya amsa da toh ya kashe wayar ya taka a nutse ya tura ƙofar parlourn ya shiga.
Bayan ya zauna ya kwantar da kanshi jikin kujerar,sanyin AC da tasirin maganin da bai gama sakin jikinsa ba ya sa bacci ya ɗauke shi a haka.
Zarah ta turo ƙofar ta shigo,har za tayi sallama ganin kamar mutum na bacci ya sa ta dakata ta zuba mishi ido, taɓe baki tayi ta haura sama inda nan ake shirin tafiya dinner.
Mami ta sauko ƙasan sanye da lace sea green,da mamaki take kallon shi.
Ta ƙaraso ta zauna kan kujera amma ko motsi bai yi ba.
"Faruq lafiya kuwa?"
Ya gyara zama da sauri ya ce"lafiya Mami".
"Ban yarda ba Faruq,bacci ƙarfe takwas saura?"
"Mami gajiyar aiki ne kawai".
"To ai shikenan,Umman ku na second room ɗin can shiga ku gaisa".
Ya shafa kai ya miƙe ya nufi ɗakin Mami ta bishi da kallo don ita ba ta yarda da abinda ya ce ba.
Da sallama ya shiga,tana zaune saman gado sanye da irin kayan Mami,ya zauna kan carpet ya ajiye wayar sa a ƙasa ya ce"sannu da zuwa Umma?"
Idonta kafe a kan shi ta ce"ba ka da lafiya ne?"
Da sauri ya ɗago jin abinda tace,ya girgiza kai ya ce"lafiyata ƙalau Umma,kawai gajiyar aiki ne".
"To Allah ya sa da gaske ka ke,Allah ya cigaba da tsare ku ya kare ku a duk inda kuke".
A hankali ya amsa da Amin.
Tana kallon shi ta ce"Tun da nake a rayuwata ban taɓa ganin mutum mai karamci kamar wannan baiwar Allah nan ba,ta riƙe ka tamkar ɗan da ta haifa,babu ƙyashi babu mugunta,bamu da abin da zamu saka mata dashi sai dai addu'a,ka cigaba da yi mata biyayya kamar yadda zaka min Sadauki".
"In Sha Allahu Umma".
Jin an fara kiran sallar Isha ya sa shi miƙewa tsaye ya ce"bari in tafi masallaci Umma".
"Ga banɗaki nan ka shiga kayi alwala a nan mana".
Bai yi mata musu ba ya cire agogon hannun shi ya ajiye kusa da wayar dake kan Carpet ya shiga toilet,tana ƙokarin ta da nata sallar ya fito,fita kawai yayi ya ja mata ƙofar.
Bayan kaman minti biyar Zarah ta shigo ɗakin,ganin Umma na sallah ta juya za ta fita,da sauri ta ɗaga ƙafarta jin ta taka abu.
Ta durƙusa ƙasa ta sa hannu ta ɗauko agogon,sosai agogon ya mata kyau duk da ya kasance na maza,da gani ka san agogo ne mai tsada,lokaci ɗaya ta fahimci mai agogon don gabaɗaya ƙamshin turaren shi ya gauraye ɗakin.
Ta juya ta ga har lokacin Umma sallah take, ta cusa cikin rigarta ta fita.
Da sallama ya shigo dakin,ya zauna inda ya tashi ya ɗauko wayar shi ya duba time.
Ganin babu wristwatch a wurin ya sa ya ɗan kafe wurin da ido.
Umma dake ninke darduma ta ce"ya dai?"
"Umma kin ga agogo a nan?"
"Agogo kuma,anya,ko dai ka manta inda ka bar sa?"
"Babu wanda ya shigo ɗakin nan?"
"Ina Sallah na ji an buɗe ƙofa,ban san waye ba dai,amma a gidan nan waye zai saci wani agogo".
Bai sake cewa komai ba ya hau danna wayarsa.
Mami ta turo kofar ɗakin ta shigo,ta zauna bakin gado ta ce"Faruq kana nan ashe,dinner za'a tafi yanzu,idan kana tare da mota sai ka ajiye mu".
A hankali ya ce"to Mami".
A waje suka tarar amare sun tafi tare da ƙawaye,da biyu Zarah ta ɓoye a ciki saboda sun gama shiri da Sudais shi zai kaita,Mami har ta fita sai kuma ta koma ta turo ƙofar ɗakin su sanin halin autarta,ƙaramin aikinta ne ta ce bacci za tayi.
Kwance ta tarar da ita tana danna waya,ta wangale ƙofar ɗakin ta ce"zo ki fita".
Ta miƙe da sauri kar ta sha mari ta ɗauki mayafinta ta fita tana turo baki.
Ganin ta nufi hanyar gate ta ce"dawo nan,babu wani mota da zai zauna zaman jiran ki har ki gama abinda ki ke ki fito".
Sadauki na zaune a driver seat ya bita da kallo,pink gown ɗinta sai jan ƙasa yake,ta sa hannu ɗaya ta riƙe rigar ta dawo wurin motar.
Mami ta nuna mata front seat ta ce"ki shiga kar ki ɓata mana lokaci".
Umma dake zaune kusa da Mami ta ce"an takurawa takwarata a gidan nan gaskiya".
Mami ta ce"wannan takwarar taki sai addu'a wallahi,yarinya kamar wacce ba'a yiwa faɗa".
Umma ta ce"za ta daina in sha Allah,lokaci ne".
Mami ta ce"to ai shikenan".
A gaban event center ya samu gefe ɗaya ya ajiye motar,Mami ta buɗe kofar suka fita,Zarah na ƙoƙarin fita ya hango agogon shi ɗaure a hannunta,da mamaki yake bin hannun da kallo.
Maganar Mami ya sa ya ɗauke kai ya ce"na'am Mami".
"Ba dai tafiya za ka yi ba?"
"A'a zan shigo Mami".
"To shikenan".
Ya sake bin Zarah da kallo ganin har ta shiga ciki,sosai abin ya basa dariya, wannan shine ƙarfin hali ɓarawo da sallama,ya shafa kai ya sauko daga motar ya shiga ciki.
Amare sun sha kyau kowacce zaune kusa da mijinta,kusa da Zeenah Zarah ta zauna ta riƙe hannunta.
Can baya ya zauna yana bin wurin da kallo,in banda Mami tayi magana babu abinda zai sa ya shigo wannan wurin.
Tsaki kawai yake ja ganin abin ya ƙi karewa har bayan awa biyu,ya ɗago da niyyar duba su Mami idon shi ya faɗa kan wani dake zaune can gefe sanye da baƙaƙen kaya, face cap da nosemask.
Ya harɗe hannun shi a ƙirji ya cigaba da ƙare masa kallo,ko sau ɗaya ya kasa daina kallon shi.
Kamar ance ya ɗago ya sauke idon shi kan Sadauki,da sauri ya ɗauke kai ya sake gyara hular kansa.
Sadauki ya miƙe da sauri ya nufi inda yake,yana hango shi ya miƙe da wani mugun sauri ya fita.
Cinkoson mutane ya hana Sadauki fita da wuri,yana isa waje ya hau waige waige amma ko alamar sa babu,cike da takaici ya naushi iska.
Ya koma ciki ya nemi gefe ɗaya ya tsaya ya fara bin kowa da kallo.
Har aka gama taron kusan sha biyu saura bai zauna ba,sai da aka gama fita daga hall ɗin sannan ya fita.
A gaban mota ya tarar dasu Mami,ya buɗe ƙofa ya shiga yana sake bin parking space ɗin da kallo.
Yana ajiye su Mami ya wuce gida,Bilal na kwance a parlour yana kallo ya shigo,ya kwanta kan kujera ya lumshe ido.
Bilal ya gyara zama ya ce"ina ka shiga sai kiran ka nake network na min tsiya,ko ka fara zuwa club ne?"
"Daga nan nake,ba ka ji warin giya ba?"
"Giya kawai? ashe naka da sauki".
Sadauki ya watsa mishi wani banzan kallo ya ce"anya babu abinda ka ke ɗan kurɓa Bilal?ban yarda da kai ba gaskiya".
Bilal ya fashe da dariya har da riƙe ciki,Sadauki yayi murmushi ya miƙe ya shiga ɗaki.

**********

Washegari sai da ya jira Bilal ya wuce aiki sannan ya shirya ya fito,direct asibitin da aka kai matar ola ya nufa.
Bayan sun gaisa da Dr ya nuna mishi ID card ya ce"sunana Captain Umar Sadauki,dan Allah wasu tambayoyi nake son maka a kan Mrs Olatunji".
Dr ya gyaɗa kai ya ce"Please go on".
Ya fuskance shi da kyau ya ce"Doctor,a bisa binciken da kayi,ko zan iya sanin dalilin mutuwar wannan family ɗin?"
Dr ya ce"eh to, preliminary findings ɗin mu ya nuna mana poisoning ne,Sir".
Sadauki ya ce"Kuma ka tabbata poisoning ne?"
Dr ya ce"Akwai ninety five percent assurance,amma dole sai mun jira toxicology analysis saboda mu san wani irin poison ne".
Sadauki ya ce"kana ganin cikin abinci kenan ko abin sha suka sami poison ɗin?".
"Eh zai iya yiwuwa,duk da bamu samu komai da ya nuna mana hakan ba".
Sadauki ya ce"akwai alamar physical struggle kamar kokuwa haka?"
Dr ya girgiza kai ya ce"babu gaskiya,ko ƙwarzane babu a jikin ko wannen su".
Sadauki ya ce"abinda ke cikin su kafin su rasu,kun yi bincike kuma baku lura da wani abu daban ba?"
"Eh,an karɓi stomach content daga duk su ukun,mun sami traces na abinda suka ci ko sha,amma ba mu da tabbacin a ciki poison ɗin ya ke sai result ya fito".
"Ko za ka iya estimating lokacin mutuwar?"
"Duk da babu tabbaci amma kamar misalin goma ne haka zuwa cikin dare".
Sadauki ya kalle shi ido jajir ya ce"zuwa yaushe final result zai fito?"
"Eh to,anytime soon zai zama available in Sha Allah,idan ya fito zan tura can Headquarter".
Yayi shiru kamar mai tunani sannan ya ce"amma zamu iya sanin abinda suka ci na ƙarshe kafin rasuwar?"
"Zamu iya sani,amma sai laboratory results ya fito".
Ya sake bashi hannu ya ce"Nagode Doctor,dan Allah idan ka fahimci wani abu so unusual ka sanar dani".
Yayi maganar tare da ajiye mishi wani ƙaramin card a gaban shi.
"Babu damuwa Captain,zan yi ƙoƙari in Sha Allah".
Cike da damuwa ya isa Headquarter,tsirarun officers ke kai komo saboda ana dab da tafiya sallar juma'a.
Ya isa office ɗin Brigadier ya ƙwanƙwasa a nutse.
Sai da aka bashi izinin shiga sannan ya tura ƙofar.
Yayi saluting ɗin shi with so much respect ya ce"Captain Umar Sadauki Sir".
Ya ajiye biron hannun shi ya ɗago ya ce"kai da ba ka da lafiya Captain,hope all is well?"
Ya sauke hannun shi ya ce"Sir, I would like to request permission to personally investigate the death of Olatunji's family."
Brigadier ya ce"personally?"
"Yes Sir,Ina tunanin kamar akwai wani abu a ƙasa da ya kamata a ce mun sani,daga asibitin nake, preliminary findings ya nuna duk sun mutu kusan lokaci ɗaya kuma ana kyautata zaton it was poisoning".
Brigadier ya gyaɗa kai ya ce"Colonel Barau yayi insisting zai yi investigating akan case ɗin".
Sadauki ya sake sunkuyar da kai ya ce"Sir,with due respect,a min wannan alfarmar Please".
Brigadier ya ce"alright Captain Sadauki,you may proceed,amma tunda Colonel Barau na da interest a kan case ɗin,sai kuyi aikin tare,Ina fatan hakan is okay?"
Ya gyaɗa kai ya ce"Yes Sir,i really appreciate".
Da yamma wani officer yayi knocking ƙofar Colonel Barau,bayan kusan minti biyu ya bashi izinin shiga.
Yayi saluting ɗin shi cike da girmamawa ya ce"Sir, Captain Sadauki has been authorized to investigate Olatunji's case."
Da mamaki ya ce"Captain Sadauki,waye ya bashi wannan damar?"
"The Brigadier,Sir".
Ya gyaɗa kai ya ce"I see".
Ya bi officern da kallo har ya kulle mishi ƙofa,ya miƙe da sauri ya dafa table ɗin gaban sa ya ce"Captain Sadauki".
Sadauki na fita daga office ɗin Brigadier yayi dailing numbern Bilal,bai jira yayi magana ba ya ce"turo min number Idayat".
Bilal ya waro ido ya ce"soyayya ya tashi kenan".
Ya yatsine fuska ya ce"eh,shine".
Yana tsaye number ya shigo,nan take yayi dailing.
Tana ɗauka ya ce"kina ina?"
Authoritative voice ɗin shi kaɗai ya sanar da ita waye,da sauri ta ce"ina office Sir".
"Ki same ni a waje".
Da sauri ta gwalalo ido ta bi wayar da kallo,sai kuma ta miƙe da sauri ta fita.
Har ta isa inda yake tsaye kallon shi kawai take cike da mugun soyayyar sa da ya dabaibaye ta,bai ma san ta nayi ba don danna wayarsa kawai yake.
Motsin da ya ji ya sa ya ɗan juyo,ya bi fuskarta da kallo ya ɗauke kai ya ce "come with me".
Da sauri ta bi bayan shi,ya buɗe driver seat ya shiga ta buɗe na kusa dashi ta zauna ta rufe kofar.
Tafiya kawai suke babu mai cewa komai,dai dai wani masallacin juma'a ya tsaya,ya ɗan juyo ya kalleta briefly ya ce"zan shiga in yi sallah,akwai na mata za ki iya shiga kafin in fito".
A nutse ta ce"ka shiga zan jira ka".
Ya ɗauke kai ya buɗe kofar ya fita ta bishi da kallo.
Bayan kusan minti sha biyar ya dawo,bayan ya kunna motar yayi gyaran murya ba tare da ya kalleta ba ya ce"I'll be investigating Olatunji's family death issue,na yarda da ke shi yasa zan yi wannan aikin tare da ke,it should be confidential".
Ta sunkuyar da kai ta ce"Yes Sir".
A gaban gidan yayi parking,ya dinga bin unguwar da kallo ganin mutane ba kamar ranar da ya fara zuwa ba.
Ya ƙarasa gaban gidan dake kusa da na Ola ganin mutane a wurin ya ce"sannun ku".
Da sauri su kayi shiru daga hirar da suke,ya ce "dan Allah ku yi haƙuri,ni jam'i ne daga ofishin wannan maƙocin na ku,ina son muku wasu ƴan tambayoyi idan ba za ku damu ba".
Ɗayar ta ɗauke kai da sauri alamar babu abinda za'a ji daga bakinta.
Ɗayar ta ce"oga,i dey hear you"
Ya ce"thank you,na san kun san da abinda ya faru da neighbor ɗinku right,daren da abin ya faru shin kun ji wani motsi ko ƙara haka daga gidan?"
Ta girgiza kai ta ce"not really Sir,amma misalin ƙarfe goma na ji tsayuwar mota a waje".
Da sauri ya ce"kin ga motar?"
"A'a,da yake a wannan lokacin babu wuta sai hasken farin wata kawai,amma kamar baƙi ne motar".
"Akwai wanda ya fita a motar ne?"
Ta gyaɗa kai ta ce"eh,wani ya fito daga motar ya shiga gidan,amma gaskiya ban ga fuskarsa ba don ya ɗora hula a kansa gabaɗaya".
Ya sauke numfashi ya ce"thank you".
Har ya bar wurin ta ƙwala mishi kira da ƙarfi ta ce"oga !".
Da sauri ya koma inda take.
"Akwai ranar na fito zan yi shanya,sai na hango wani baƙin mota parke a can".
Tayi maganar tare da nuna mishi dai dai inda ta hango motar.
"Zai kai kamar kwana nawa?"
Ta ɗan yi jim alamar tunani sannan ta ce"zai kai sati ɗaya".
"Kuma kin tabbata motar ce kika sake gani?"
Ta girgiza kai ta ce"ban tabbatar ba,saboda wancan cikin dare ne amma kamar kalan su ɗaya".



Na kusa gama Book 1,Book 2 na kuɗi ne.
Pay 1k into ***, Khadijah Sulaiman Opay.
Evidence of Payment via ***.
Thank you.




***