RU'UYAA (The dreams we never lived)

40. ..The weight of crushed dreams...🖊️

by @autum17




Wayarsa ce tayi ringing ya miƙe tsaye yaja gefe yana amsawa. wasa nake da yatsuna ina tsananin jin kunyar kaina meye wannan? 


'' daga yanzu tare da Sofia zaki dinga zama, bazaki sake komawa wancan sashen ba UHM?" Ya zauna gefe na. gyaɗa kaina nayi batareda na ɗago ba,ya ƙara riƙo hannuna

 '' Abeedah!" Ya kira gently da yasa zuciya ta narkewa haka ma idona suka ɗuri ruwa


juyo da fuska ta yayi towards him slowly yace '' I'm sorry...da ace nazo da wuri this wouldn't have happened'' girgiza kaina nayi idona a ƙasa.

Ƙwanƙwasa ƙofar da akayi yasa ya sake ni ya tafi ya buɗe ƙofar. batareda naga ko waye ba,Khalil ya karɓi wani abu daga hannun shi ya rufe ƙofar ya dawo.


ɗakin da nake zama ciki ya shiga ina mamakin mai zaiyi,bayan mintuna ya fito '' Kiyi amfani da wancan ki wanke kanki,idan akwai sauran abu a ciki zai mutu duka!" gyaɗa kaina nayi na miƙe na shiga ɗakin,da ƙyar na daure na kalli madubi.. mutanen nan sun min illa...da sauri na ɗauke idona baƙin ciki ya mamaye Zuciyata jiki ba ƙwari na shiga bayen


Wani farin abu daban san meye shiba na gani a cikin bowl ya jiƙa. slowly na fara cire kayana na shiga wurin wanka na zuba ruwa a kaina ruwan na sauka tare da kuka na da hawayena na fara wanke kaina. gashina...ya tafi...


Na daɗe a bayen kafin nayi wanka na fito ɗaure da towel...kayan dake saman gado na sa...nayi zaune ina kallon ƙasa nayi nisa cikin tunani


Bayan lokaci mai tsawo Khalil ya shigo,ban dena kallon inda nake kallo ba...ban kalle shiba..bana so inyi magana ƙila ya fahimci hakan yasa bai ce komai ba...


Ranar ta wuce a wani irin slow...naji duk duniyar ta isheni,kwanakin da suka biyo baya ba masu daɗi bane a gare ni,har an dawo min da komai nawa zuwa ɗakin Diyaam,hakan yasa ma'aikatan harda wa'yanda basu damu dani ba yanzu sun mayar dani maƙiyyiya..yan gidan ma kullum sai sun ɓata min rai...wai 'kai' suke kirana dashi duk da ina sa hula..suma ma'aikatan duk an musu aski banda su Aina'u amma hakan bai sa naji sauƙi ba,ga jarabawar mu data shamin kai...idan fa nima ina cikin waya'nda basu ciba? na sake faɗawa cikin ramin damuwa da koya nayi ƙoƙarin fita kasawa nake... Allah yasa kwanakin nan na mayar da hankali sosai wurin addu'a,tashin dare da kuma sadaƙa...duk idan na samu kuɗi a sadaƙa suke ƙarewa...


Har sati ya sake zagayowa saura kwanaki kaɗan mu gama jarabawar waec... Khalil da kanshi ya dawo dani gida wai kada in ɓace...


Bayan ya sauke ni ya sake fita ban san inda ya tafi ba...da ƙarfe biyu na dawo daga waje na tarar da duk mutanen gidan na zaune a parlor...kallona sukayi wasu na dariya harda Mukhtar dana daɗe ban gani ba...yanayi min wani banzan kallo


suka fara ƙus ƙus a tsakanin su

'' ke zonan!" Ayaan ya kira ni..kai ƙasa na nufi inda yake '' kawo min juice daga kitchen!" Ya faɗa da izza..juyawa nayi na shiga kitchen na ɗauko juice...dana kawo mashi wai bashi yake so ba...


 Na Shanye abinda ya tokare min maƙoshi na koma kitchen ɗin na ɗauko wani daban,nan ma yace bashi yake so ba...


Sauran da alamu suna jin daɗin wulaƙancin da nake fuskanta...a fusace na kwaso duk juice ɗin dake fridge ɗin '' gashi sai ka zaɓi duk wanda kake so!"

'' keni zaki yiwa rashin kunya? Sai inyi ƙasa ƙasa dake a wurin nan"

.hawaye na zuba daga idona nace '' Bismillah ka daɗe bakayi ba!" ƙirjina na sama da ƙasa 

'' haba Ayaan ba girman ka bane faɗa da mace!" Imam ya faɗa..hakan yasa sauran kwashewa da dariya...



Seraphina ta ƙaraso kusa ta jaye min hijabi dama ranar bansa hula a ƙasa ba...zirrr!!! Hawaye suka wanke Fuskata '' taya zaka hanashi gwada ƙwanji da ɗan uwanshi?" 

Sai duka suka tuntsire da dariya...nayi tsaye a wurin na kasa komai...ƙafafuna sun kasa motsawa bare in bar wurin...rauni ya mamaye ni...kawai inaso ƙasa ta buɗe in shiga ciki...


gani nayi Mukhtar ya taso hannunshi riƙe da juice yayo kaina yana min kallon rashin ɗa'a

'' I must admit...you look hotter like this!" Ya furta yana ƙoƙarin riƙe Fuskata da ɗan iskan murmushi a fuskar shi..naso matsawa baya amma akwai pillar a wurin,bayana ya haɗu da sanyayyar tiles ɗin,na runtse idona ganin yana ƙara matso ni...bakina na rawa....zuciyata na tuƙuƙi..

'' Hotter my foot!" Mufeedah ta furta tana juya idonta

Juyawa yayi '' da gaske nake fa... yarinyar I have to admit...'' ya matso da fuskarshi gefen wuyana da yasa na ɓare baki ina kuka

'' is really hoooot!!" yaja hot ɗin...once more yayi ƙoƙarin shafa fuskata. sai dai hannun bai sauka ba. wurin yayi tsit...


 ƙamshin sane ya mamaye duka parlorn...kafin na fara buɗe idona ɗaya bayan ɗaya harna buɗe su duka a kan kyakkyawar fuskarshi dake sakaye da Mask....his gaze was chilly...

'' then you should be careful..kada ka ƙone...we wouldn't want that do we?"yayi maganar yana murɗe hannun Mukhtar...take fuskar Mukhtar tayi ja,dan dama ya'yan Hajiya Wareesha farare ne dukansu,abu kamar basu da halittar uban a jikinsu...


'' Ya Rom...''

'' any problem?" Roman ya katse Seraphina batareda ya kalleta ba,sauran sukayi shiru tsoro ya bayyana a fuskokinsu...Mukhtar ya saki ƙara yana billiƙe billiƙe kamar ba gabjejen na miji ba...

'' now say sorry to her!" Roman yayi maganar kamar raɗa a kunnen Mukhtar..waye wannan mutumin?one minute ya barni cikin ruwa the nexy minute he's saving me from this low graded pervert, akwai ranar da zan taɓa fahimtar shi kuwa?

''.kiyi haƙuri Abeedaaaah!!!"ya faɗa a wahale idon shi sunyi ja...tunkuɗe shi Roman yayi..ya faɗi saman tiles ɗin yana murje murje yana kukan daba hawaye


Oh..ashe hawayena da kansu suma sun tsaya kallon dramar...matsowa yayi kusa dani har inajin ɗumin jikinshi badan jikinmu ya haɗu ba, batareda ya taɓani ba yajawo min hijabina ya rufe min kaina... Bai kalleni ba yabar wurin,idona suka bi kowane taku nashk


 na turo baki na raka bayan shi da harara...


su Seraphina kamar wa'yanda akayi ma wanka da ƙanƙara...sai ga Khalil ya shigo directly wurina yazo

 '' kitten...wani yayi maki wani abu ne?" Ya tambaya yana kallon Mukhtar dake ƙasa kafin sauran


Na fashe da kuka banko ɓoye abinda ya faru ba,sannan matakin daya ɗauka yaban mamaki...nan yasa aka tattaro mashi ma'aikatan gida harda shugar duka..yace '' daga yau,bana so inga kowa daga cikin ku ya shigo gidan nan da sunan aiki...'' ya nuna su Seraphina ya cigaba da faɗin '' they will do it for the entire week!" 


Shock ɗin dake fuskokinsu was worth billions...masu aikin ma haka sunyi mamaki.. saboda abinda akayi min ne ya ɗauki wannan matakin

'' kunji?" Ya tambaya suka shiga gyaɗa kai!

Riƙo hannuna yayi muka bar wurin su Seraphina suka faɗi zaune a tare,su Ayaan kuwa bakin su sai buɗewa yake yana rufewa...kuma basu isa suce bazasu yiba...Khalil yana da sauƙin kai amma shima sheɗanin kanshi ne...

Babu abinda mutanen parlorn suke tunani sai abinda Abeedah tayi amfani dashi tasa maxan gidan haukacewa akanta har haka...

Ɗakin Diyaam ya rakani yana share min hawaye...ya zaunar dani bakin gado yana lallashina...saida na dena kuka sannan ya fita...


'' Hamma yana sonki fa!" Diyaam data fito daga baye ta faɗa da murmushi 

'' nasani ko...''

'' ina nufin so na soyayya!" Ta zauna kusa dani,dawo da kallona nayi akanta cikin rashin fahimta '' baki ga yanda yake dake ba? Ƙila shima kanshi bai sani ba...'' tamin bayani...nayi ƙoƙarin haɗa pieces ɗin amma ni banga inda duk wani abu da yake min yayi kama dana soyayya ba

'' hmm...kawai dai yana min mutunci ne...'' taɓe baki tayi '' ke kina son shi to?'' da sauri na girgiza kai na '' bashi nake so ba wallahi!" Na faɗa da sauri

'' to wa kike so? nafa ga yanda kike kallon shi kema!" 

'' Ni? rufamin asiri..Roman nake s...'' da sauri na dafe bakina... fuskar Diyaam tayi haske da murmushi mai faɗi tana zolaya ta tace '' awwn...gaske koda yaushe kike maƙale mashi...''

'' wai ma! Ba wani maƙale mashi da nake kuma na dena sonshi!"

'' kin tabbata?" ta sake tambaya

'' eh mana....'' 

'' hmm! zamu gani ai,gashi har fuskarki tayi ja daga kiran sunan shi!" Ta iyarda hayewa saman gado ta jawo wani littafi...taune leɓena nayi ina shafa cinyoyina...

Ƙwanƙwasa ƙofa akayi na tashi na buɗe Roman ne tsaye a wurin saye da baƙar riga da wando brown..doguwar sumar nan ya yanke ta...naga kamar ya ƙara kyau... zuciya ta tashiga bugu har ina tsoro kada ace yana ji


'' kin gama kallona ko in haɗa da poses?" 

'' that sounds like a good idea...bari in ɗauko waya ta... wai kai kullum dole sai ka haɗa da sarcasm'' ƙanƙantar da idonshi yayi,na juya nawa

Wata farar jaka ɗauke da mayuka ya miƙo min,naɗe hannayena nayi a ƙirji,'' baka bani haƙurin abinda kayi min ba last...'' ɗage gira yayi '' Kuma idan ban baki haƙurin ba bazaki karɓa ba?"

'' eh bazan karɓa ba!"

'' then I should take back my creams!" Ya juya zai bar wurin,da sauri na riƙo gefen rigar shi..na karɓe ledar daya tsaya '' oh ashe fa na manta kai kyautar taka ba har zuci bane!" Ƙwafa yayi baice komai ba ya bar wurin..na tabbatar Khalil ya turo shi...


Jakar sai ƙamshin turaren shi take...ƙasa nayi da kaina ina ƙara shinshinar ƙamshin

'' someone's in love...'' da sauri na juyo naga Diyaam tsaye hannu a ƙirji

Raɓa ta nayi na wuce ciki...ina mamakin meyasa bayan duk abinda yayi min yanzu dana ganshi nake jin abinda ya kwanta yana sake yunƙurowa?... Kai! Romo ɗin nan sihri yayi min!


Diyaam tazo ta karɓi ledar daga hannu na wai tana so taga tsarabar da masoyina ya kawo min...wannan Diyaam ɗin

Baye na wuce nayi wanka na shirya cikin wata doguwar rigar material nasa farin hijabi harda shafa kwalli da man baki

'' ina zaki haka?" ta tambaya da tagumi a fuskarta 

'' wurin Roman!" Na bata amsa 

Dariya tayi kamar mahaukaciya kafin ta sauko riƙe da turare a hannunta tazo ta fesa min,kawai na bita da kallo 


'' what's a woman without scent?'' na jinjina kaina sannan na fita

ina tafiya slowly a hallway ɗin zuciya ta na bugu da ƙarfi kamar zata fito ta ƙirjina 

har na kawo gaban ɗakin shi sai kuma na tsaya bayan na tuna duk abinda yayi min...why should I go to his place?

Haushin kaina naji ya kamani kawai sai na wuce lambu


Nayi mamakin ganin Farzan a wurin da camera a hannun shi saye da kayan masu ɗaukar hoto yana ta ɗaukar hotuna

Ga wasu da yayi printing,da alamu shi bai ma gan ni ba

ƙarasawa nayi na ɗauki hotunan ina kallo da murmushi a fuskata 

 sai na matsa bayan shi '' sun yi kyau!"a mugun razane ya juyi har Camera ta suɓuce daga hannun shi kafin ta kai ƙasa nayi saurin kamawa

Fuskarshi kamar wanda aka kama yana wani mugun aiki,har ina ganin yanda zuciyarsa ke bugu da ƙarfi

nake kallon shi cike da rashin fahimta meye najin tsoro dan na kama shi yana hoto?

Ina tsaka da tunanin ya wasge camerar shi daga hannu na yana hararata 

'' toh me nayi kuma?" na tambaya tareda zagayo gaban shi 

'' bar wurin nan!" yayi maganar yana ɓoye camerar shi 


'' oh okay!" sai na juya na fara barin wurin ina mamakin meyake damun shine


'' da gaske sun yi kyau?" na tsinkayo muryarshi daga bayana yana tambaya

koda na juyo bani yake kallo ba,idon shi na akan wani wuri daban a lambun 

'' wallahi ban taɓa ganin hotunan da sukayi min kyau kamar wa'yannan ba!" 

Na dawo gaban shi,sai ya kalle ni da murmushi a fuskar shi '' thanks fluffy;" ya furta yana jan kumatuna cike da farin ciki


'' kina so in ɗauke ki hoto?" ya tambaya 

da sauri na gyaɗa kaina,ya nuna min yanda zan zauna da kuma styles..sai daya fara tafiya ya rufo ƙofar lambun sannan ya dawo 

Guda biyar yayi printing ya miƙo min,bakina kamar zai taɓo ƙasa tsabar murmushi 

'' wow you're really good at this..kana so ka zama photo grapher ne?" na tambaye shi ina kallon jajayen idonshi 

Ya gyaɗa kai '' ai ko zakayi cikini kai..wata rana sai dai mugan ka a Bill board...best photo graphing award goes to Farzan the red eyed guy!"  

Nayi maganar dramatically tareda tsayawa saman pond dake wurin ina kallon shi


Dariya yayi sosai har sai da haƙoranshi suka fito 

'' that is a dream that will never be lived'' yayi maganar da sadness a muryarshi yana shafa camerar 


'' meyasa?" Na dawo na zauna gefen shi, ya sauke ajiyar zuciya batareda ya kalle ni ba

'' cuz some ppl are never meant to have dreams...wasu mutanen basu da ikon burin zama wani abu kuma nima ina cikin su!" sosai na shiga ƙifta idona 

'' ban gane ba,gaka dai kai babba ne yanzu kaga babu wanda zai hana ka abinda kake so...'' 

Ya tsare ni da ido na tsawon lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya '' kin san abinda ake nufi da marionette?" 

'' obviously saboda kalmar daga yaren mu ne ai dole in sani!" na juya idona ganin yanda ya kafe ni da ido 

'' it won't kill you to say you don't know what it means Abeedah...'' yayi maganar a sanyaye har sai da naji yaban tausayi

'' I'm a marionette... that's all I'm '' ya furta ciki ciki kamar yana gudun kada inji yana wasa da igiyar camerar


'' me hakan ke nufi?" Na tambaye shi daga baya

'' ki tambayi wancan mutumin...''

na kalli inda yake kallo naga Roman ne ke wucewa ta zuwa top floor da kayan paintin shi,naji kamar in bishi amma babu inda zanje 

'' ko dai...kada ki tambaye shi...'' sai ya matso da bakin shi saitin kunne na

'' he hates that word,idan kika tambaye shi haukacewa zai yi...'' sai ya gyara zaman shi ganin ina kallon shi baki sake

'' toh meyasa?" Na tambaya da mamaki 

'' nima...babu ruwana..but just know that he hates that word... ranar dana ke ƙoƙarin bashi haushi nace marionette..''

Tashi tsaye yayi yaja rigar shi ya nuna min wani dogon tabo daga gefen kafaɗar shi ta hagu har zuwa gefen ƙugun shi na dama in a straight horizontal line 

'' kin ga abinda yayi min!" Ya sauke rigar shi,da sauri na rufe bakina da hannuna...ashe abun yayi ƙamari 


Ya sake zama '' but it wasn't his fault..in fact he's the most strongest person dana taɓa gani..idan da nine abubuwan da suka faru dashi suka faru dani,dana mutu kona haukace da gaske!" 

Yayi maganar da alhini kamar yasan wani gagarumin abu game da Roman wanda ni ban sani ba


'' we weren't always enemies...we used to be best friends..mu uku dani dashi da kuma Bray... abubuwa sun canja sosai'' yayi maganar yana kallon nesa

'' toh meyasa? na tambaya,bai amsa ba a maimakon haka sai ya canja topic ɗin 


'' you're so lively Abeedah and I like liveliness.. never ever lose it . Idan kin samu dama ki cika burin ki. Never waste time...''

'' kai ma ka cika naka burin '' nayi maganar idona a nashi 

'' some dreams are never meant to be lived'' na gyaɗa kaina ina jin baƙin cikin shi 


'' let me take you out!'' ya furta,cike da farin ciki na miƙe,ya miƙo camerar shi murya ƙasa yace '' ki ɓoye cikin hijabin ki kada ki bari kowa ya gani ki jirani a parking lot!" na shiga gyaɗa kaina da sauri na bar wurin cike da murna 


Farzan yayi tsaye a wurin hannayen shi zube cikin aljihu yana ƙoƙarin ajiye facial expression ɗinsa blank amma ya kasa ya sauke ajiyar zuciya yana haɗiye ɗacin daya tokare mashi maƙoshi 


The weight of crushed dreams hanging on his shoulders '' will I ever be?" yayi ma kanshi tambayar murya ƙasa


badaɗewa ba Farzan ya fito daga gidan ya shigo motarshi muka bar gidan 

Duk na kasa zama sai mutsu mutsu nake tsabar murna,shima yana tuƙi fuskarshi ɗauke da murmushi 

Bayan wani lokaci muka kawo wurin wani fun fair kusa da teku,akwai mutane da yawa manya da yara

ticket ya siya mana yasa face mask kafin muka fito 

Ya karɓi camerar shi muka shiga cikin mutanen...muna tafe yana ɗaukar hoto ta every chance

Mutane ganin ya iya sosai sukayi tururuwa akan shi suna roƙon ya ɗauke su hoto 

Naja baya ina wasa shi kuma ya fara aikin shi,har ina ganin wani irin farin cikin da ban taɓa gani tattare dashi ba


'' that's right...kowa yayi farin ciki'' na faɗa daga saman lilon da nake zaune


Can ya jani muka tafi wani wuri mai hakukuwa da flowers kamar meadow ya shiga ɗauka ta hoto 

sai kuma ya kira wani ya bashi camerar ya ɗauki mu biyun...

sosai Farzan yake farin ciki kamar wanda ya samu wani babban achievement,ya kaini wurin masu sayarda abubuwa a wurin sai dai shi duk yanda nayi dashi yaƙi ya ci kuma fa yana so...meyake damun shi da Roman ne? ka basu abu suna so sai suƙi karɓa

Duk da gara shi Farzan yana cewa '' I'm not allowed '' kona tambaye shi waya hanashi bazai amsa ba


'' thank you Fluffy;" ya furta yana Kallona sanda muka zauna kusa da tekun a ƙasa muna kallon faɗuwar rana


'' Are You kidding me?ai ni ya kamata nayi maka godiya...kamar kada ranar ta ƙare!".


'' nima haka nake ji!" Ya amsa min yana kallon rana nayi murmushi... shi ɗin ba mutumin banza bane ko mugu ashe

Kallon gefen fuskar shi da rana ta sauka akai yasa naji yaban tausayi, idonshi kamar wuta 

'' wai kai meyasa idon ka suke ja kamar ƙyanƙyashen garwashi,idan kayi fushi sai suyi kama da ƙyanƙyashen garwashin da iska ke hurawa...red eyes...'' 

Dariya yayi yana gyara camerar shi '' shine yasa ake kiran su ember eyes. '' na gyaɗa kaina

'' gashin ka shima color kasa dan yayi matching da idon ka?" ya girgiza kanshi 

'' haka gashina yake kona aske irin shi zai sake fitowa...'' sai ya juyo idon na ya sauka cikin nashi 

'' i told you your eyes have silver in them,daga ƙarshe dai mayya zaki koma kamar yanda yake faruwa a cikin littafi..your hair will turn white'' 

Nayi dariya jin abinda ya faɗa '' babu wani silver a idona wallahi ''

ɗaya daga cikin hotunan ta ɗauka ya nuna min 

 '' look at how your eyes are glinting... Abeedah the witch!" Yayi min bayani,wannan Farzan ɗin...ɗauke kaina nayi gefe ina murmushi 


Da ƙarfe shida muka dawo gida,..yayi gyaran murya na juyo sashen shi 

Da wani irin murya kamar ba shine ya gama yaƙe min baki ba yace '' kada ki kuskura inji maganar nan a baki wani..wai nayi amfani da camera na ɗauki hoto kona kai ki fun fair a beach or anything we did together today kin gane?" 

yayi maganar with so much emphasis kamar yana yima wata daƙila bayani 

'' meyasa?" Matsowa yayi ya haɗe ni da elevator yayi min rumfa,his eyes raging mad '' saboda na faɗa!" Ya amsa min 

Yana goga haƙoranshi,yaban tsoro sosai '' toh na gane..babu wanda zai ji '' nayi maganar da sauri


'' good!" Ya matsa baya yana gyara kayan shi '' batare muke ba kinji ni ko? tafiyar ki daban tawa daban..You and I didn't go out or do anything together!"

Nan ma kaina kawai na gyaɗa.. what's with the secrecy?




  🌹 ❤️📖✨



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin ***..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️