BOOK ONE CHAPTER 20
*ZAINAB*
"Aunty...! Aunty....!! Aunty.....!!!"
Tafaɗi da iya ƙarfinta, tana miƙewa zumbur ta zauna a tsakiyar gadon.
Jikinta ko ina kyarma yake yi. Wani irin zufa na keto mata tun daga maɗigarta har tafin ƙafarta.
Auty Sahura dake kwance kusada Ramlat tana rikeda ita tun sanda aka sanya mata ƙarin ruwa ta mike zaune tana tofa mata addu'oi.
Zainab dake zaune akan sallahya tana ma Khadijah addu'a a sallar nafilar da tayi yanzu ta mike tana share hawayen dake kan fuskarta.
Idanuwanta dake ɗauke da tarin abubuwa da dama ta sauke akan Ramlat dake rungume da Aunty Sahura ƙam ajikinta.
Tunda suka dawo daga asibiti Ramlat ta suma, da zaran an yayyafa mata ruwa ta farfaɗo zata hau kiran sunan Khadija sai ta koma suma.
Tun ana ɗaukan abin da sauki harse daga ƙarshe Yaya Yusha'u da Aunty Sahura suka ɗauketa itada Anis suka kaisu asibiti.
Shi aka bashi magunguna, ita kuma aka
hadota da nurse tazo ta sanya mata dreep.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo mata zuciyar ta na matsewa da wani irin ciwo mara misaltuwa.
ƊACIN MUTUWA
Kalmace da take da sauƙin faɗa a fatar baki, amma nauyin sa, raɗaɗinsa, dama ɗacin gabadaya abace da babu wata jimla da zatai bayaninta.
Jiki da zuciya su kaɗai ne suke fahimta, se kuma mutumin da yaɗan ɗana kamar su.
Idan har bata makara ba to tana miƙa ta'azaiyya ga duk wanda yataɓa rasa wani mafi soyuwa arayuwarsa.
Don ita a'unin yau kaɗai jinta take yi kamar wata butun butumi. Tamkar tana tsaye awajen duniyar mutane tana hango cikin sa daga waje.
Jiki ba ƙwari ta juya ta fita daga ɗakin. Tana fitowa tsakar gida kunnuwanta suka jiyo mata sautin kukan Anis.
Ɗakinsu Khalid ta shiga.
A tsaye taga Khalid ya jingina kansa da garu. Anis na zaune a tsakiyar gadon yana rera kuka cikin disashshiyar muryansa.
Ƙarisawa tayi ta zauna agadon. Ta jawo Anis jikinta. Hannunta taɗora goshinsa se taji zafi rau alamar zazzaɓin bai sauka ba.
Ta kalli Khalid tana tambayar sa"Anis yasha maganinsa kuwa?"
Ahankali yagirgiza mata kansa dake mai ciwo kamar zerabe gida biyu.
Zainab ta mike. Ta buɗe bedside drawer ɗinda taga Yaya Yusha'u yasaka maganin sanda aka siyo.
Batare da Khalid yayi maganaba ya dauko mata ruwa ya kawo mata.
Magungunan ta ɓallo, ta ɗago Anis ta basa. Amsa yayi, yasha, ya maida kansa yaɗora akan cinyar Zainab yana sauke ajiyar zuciya.
"Kai zoka kwanta...!"
"No Mami kona kwanta bazan iya bacci ba."
Yai maganar gaskiyarsa na fitowa ta cikin rikitacciyar muryansa.
Zuciyar Zainab ta karye. Ƙwalla masu zafi suka ciko idanuwanta. Ta daure daƙyar ta furta:
"Ko baza kai bacci ba kazo ka kwanta."
Ba musu Khalid ya tako yahayo kan gadon ya kwanta.
Cikeda tausayawa Zainab ke kallonsa, hannunta na yawo ajikin Anis dake kwance yana bacci cikin sauke zuciya.
______
Kamar yanda kowani gidan mutuwa yake, kwanaki bakwai aka ɗauka ana zuwa gidan gaisuwa.
Masu ta'azaiyya nayi, masu kawo salaka nayi both kudi da kayan abinci kala-kala.
Aƴan kwanakinnan action din da Ahmed ya nuna yayi matuƙar karya mata zuciya fiyeda kodayaushe.
Zuciyar ta taƙara hakura da zama dashi amatsayin miji, yayinda soyayyarsa ke danƙare awani killataccen wuri da duk yanda rayuwa zata garata da kaddara, wannan soyayyar bazata taɓa rugujewa ba.
Abinda ya faru atsakanin ta da Alhaji Haruna yasan yata haƙura da aiki awurin su. Ko giyan wake tasha bata fatan ƙafafunta sujata zuwa good and best.
Tarigada tayi making decisions akan zatai using kudaden data samu ta soma sana'a acikin gidanta. Idan har Allah ya tai maketa sai ta sami mafita.
Sedai me!ayanzu samun sana'ar da zakayi mai riba batareda mutane sun karya kaba aiki ne. Wannan yasan yata yin zurfin tinani akai amma tarasa wani sana'a zatayi.
*KHALID*
Zaune yake aƙasan bishiya. Daga inda yake yana hango Oga Joshua da sauran abokan aikinsa na aiki.
Idanuwansa da sukai mai nauyi ya lumshe kansa na kuma sarawa akaro na ba adadi.
A idanuwan mutane Khadija ce kawai ta mutu. Yayinda agaresa rayuka biyu ne suka mutu. Aka birne ɗaya a maƙabarta, ɗayan kuma aka barshi aduniya zuciyanshi na bugawa, idanuwansa abuɗe.
Tunda Khadija ta mutu ko rintsa idanunsa bayayi. Da duk iskan daze shaƙa da yanda ciwon mutuwanta ke ƙara samun wuri yana zama a ko'ina na jikinshi.
A kwanaki bakwai kacal yai wata iriyar rama mai ban tsoro. Ya fice a hayyacin shi gabadaya. Hatta Mami seda tai mai magana da wa'azi gamida tinatarwa agaresa kan mutuwa.
Shiyasa ma ayau ya daurema zuciyar sa ya fito wurin aiki saboda ya rage mata damuwa.
Akil ne yatako zuwa inda yake, ya zauna akusa dashi yana tambayar sa "Mr man lafiya kake zaune anan? Oga nacan yanata masifa akanka."
Kallonshi yayi yana bashi amsa daƙyar "Bana jin daɗi ne."
"No kamar akwai abinda yafi ƙarfin haka atare da kai. Idanunka sun yi jaa, jijiyoyin kanka sun mimmiƙe, I think kamar rashin bacci ne yake damunka."
Khalid ya ɗanyi shiru kamar bazai amsa ba yace"bana samun bacci ne."
"Hakan na faruwa idan muka rasa wasu makusantanmu. Like me da Mama ta tarasu seda na daina bacci amma mai chemist din anguwanmu na haɗa min wasu ƴan magunguna na soma amfani dasu shikenan."
Khalid ya kallesa da rinannun idanunsa. Yasan shan magani ba bisa ka'ida ba sunanshi shaye-shaye. Amma Akil yace a chemist kenan pharmacist ne mutumin. Be bar tambayar acikin shiba seda ya amayar dashi agaresa.
"Educated ne guy din?"
"Yeah master's degree gareshi a pharmacy."
Khalid ya ɗanyi shiru yana tinani. Shi bayada kuɗi ayanzu balle yabi Akil pharmacy su siyo maganin don yana matukar bukatar ta ko don Mami, ko don ya rage mata damuwar daya gani acikin idanunta sanda take mishi nasiha.
Kamar Akil yasan abinda yake ƙasan ranshi sai yaciro kudi a aljihun shi yana cewa"muje na rakaka asiyo."
Miƙewa Khalid yayi yana mai godiya. Sukai taking excuse awurin Oga Joshua suka nufi cikin road din su Akil.
Sukai sa'a chemist ɗin abuɗe. Gashi guy din ya iya treating mutane sosai, ayanda Khalid yalura ma akwai sabo mai girma atsakanin shi da Akil.
Daga nan wurin mai chemist sukai sallama da Akil. Ya kamo hanyar gida yana addu'ar Allah yasa karyaga Mami a tsakar gida.
Aikam yai sa'a. Addu'ar sa ya karɓu,tsakar gidan babu kuwwa. Ɗakinsu yashige. Ya ɗauki kwayoyin guda biyar ya watsa abakinshi ya korada ruwa. Ya hau kan gado. Ya lumshe idanunsa, magungunan na soma aikin su.
*JAMILA*
Zaune take akan gadonta taƙura ma wuri ɗaya ido.
Inda kuka na maganin damuwar zuciya da ayau hawayen data zubar sun wanke mata dukkan damuwarta.
Ta runtse idanunta kalaman Raihan na mata ciwo a wuraren data san har abada bazasu taɓa warkewa ba.
Rayuwa kenan sauyi akodayaushe. Baicin haka ina ita Jamila zata kasance awannan halin da take ciki.
Itace mace ɗaya tilo da ko wani namiji yake fatan mallaka arayuwar sa. Itace tauraruwar data disashe kowace mace dake cikin anguwarsu dama kewayenta. Itace mace ɗaya tilo da namiji ke mallaka mata zuciyar sa akallo guda daye mata.
Amma ayau itace abar sharewa, itace wacce namiji ya jingine agida yai tafiyarsa yabarta kamar babu ita arayuwarsa.
Itace wacce namiji yace ma ta manta ta taɓa kasancewa dashi.
Hawaye masu zafi suka sauko mata. Zuciyar ta ciwo take mata. Bana iya abinda ya faru ba, harda na kalaman Raihan agareta.
Tinaninta ya tariyo mata wani lokaci can baya daya shuɗe
*
Tsaye take agaban wadrope tana ciro kayanta tana zubesu acikin akwatin ta.
Turo ɗakin yayi da sallama cikin muryansa mai taushi da tai ƙasa saboda damuwa da tashin hankali.
Bai damu da rashin amsawanta taba ya ƙariso inda take yana kallon kayan da fadin
"tafiya zakiyi ki bar Ni?!."
Wani duban wulaƙanci tai masa. Ta yamutse fuskanta tace "tunda kaƙi sakina zanje wurin waɗanda suka ɗaura auren su sanya ka karabu da Ni."
Zubewa yayi akan guiwoyinsa. Kuka yake yi sosai yana sheshsheƙa da roƙonta.
"Kada ki min haka don Allah. Kece mahaɗin rayuwata. idan kika barni komai na duniya zai barni. banada ikon maida kaina yanda ki keso saboda Allah shine mai azirtawa. amma zanyi iya ƙoƙarina naga na baki dukkan wani rayuwar farin ciki data danganci soyayya, kulawa, ta...."
"Shin waɗannan abubuwan da kake faɗi zasu bani farin cikin duniya?! Zasu cika min account dina?!!...zasu..."
"Zasu cika miki zuciyar Ki. walla...
Itama ta katse shi "zuciyata ta rigada ta cika. ayanzu bana buƙatar ƙari."
Tana gama faɗin haka ta soma zuge akwatin ta.
Ya taso jikinsa na ɓari ya riƙo ta. Kamar wacce wuta yataɓa haka ta fizge jikinta tana fadin
"Idan har ka haifu ɗaa acikin Safina kabar Ni natafi gidan ubana."
Tana gama faɗin haka ta jawo akwatin ta. Bata damu da yanayin da yake ciki ba ta buɗe ɗakin ta fita.
Tarwatsewan zuciyar ta da abinda tayi yasan yata dawowa hayyacinta. Ta fashe da kuka mai sauti tana jan numfashi mai ciwo.