ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER 21

by @hindatuauwal

*ALIYA*

Kwance take akan cinyar Ustaz. Wayanshi na hannun ta, tana buga game ahankali. Jikinta duk amace saboda yanda Ustaz ke yawo da hannun shi acikin gashin kanta yana yamutsa shi tare da sura yatsun shi sosai aciki kamar mai mata masage.




Duk yanda taso ta daurema yanayin ta kasa. Jikinta ya soma kyarma daye da ban dana zazzaɓi, wannan na zallan feelings ne dake tasowa daga jiki yana kaima zuciya.



Kanta ta ɗaga daga jikinsa.


Yaɗago ya kalleta idanunsa ɗauke da tambayar meyafaru.



"Na ga ji."


Ta furta daƙyar tana haki.


Hannu yasa zai jawota jikinsa ta kauce. Ya ƙara kai hannunsa, ta miƙe zumbur akan ƙafafuwanta. 



Shima miƙewan yayi yana kallon cikin ƙwayannin idanunta.



Haka kawai taji bazata iya jurema kallon cikin nasa idanun ba. Sai ta sunkuyar da kanta ƙasa tana haɗe yatsunta wuri guda ta soma matsasu kamar mai yi musu tausa.



Ɗumin tafukan hannayen sa taji a side by side na fuskarta. Ya duƙo fuskansa ya saita ta danashi har tana jin ɗumin numfashin shi dake sauka afuskarta.


Murya can ƙasa ya jefa mata tambaya "dame kika gaji."



Jikinta ya mutu muruss. ta lumshe idanunta zuciyar ta na dokawa. batasan iya adadin lokacin da suka ɓata ahaka ba. ta dai tabbatarma kanta ta samu natsuwar daze bata damar yin masa magana.




"Da komai."



Batasan ko ya fahimci abinda take nufi ba, tunda itama da tai maganar ba zata ce ga ma'anar maganan nata ba.



Akaro na ba adadi ta runtse idanunta. Taja numfashi da ƙarfi tana fatan ya ratsa cikin huhunta ya kaima zuciyarta daya dakata na wucin gadi.



Anatse da takunsa mai sanyi yabar wurin. Ta silale ta zauna akan kujera, ta jingina bayanta tana ɗora kanta asaman kujeran.



Tananan azaune sai gashi ya dawo hannunsa riƙeda hijjab ɗinta ya matso ya sanya mata. Seda ya gama tana kallonsa da mamaki. Ya kama tamiƙe, ganin yana shirin fita da ita yasan yata yin masa magana.



"Ustaz ina zamu je.?"



Sanda ze bata amsa har sun fito tsakar gida.


"Shan iska zamu je."


"Wani irin shan iska.?!"
 

Ta tambaya kanta na kullewa.



"Idan muka je zaki gani."



Ya zata yi da Ustaz hakanan ya gunguro mashin din zuwa ƙofar gida ta hau.




Tafiya suke yi ahankali cikin natsuwa. Tunma kafin ya kaita inda yake muradi taji ta sami gamsuwar da take buƙata. Kasancewar damina tayi nisa da yamma hadari ya haɗu ruwa bai sauka ba sai garin yai sanyi mai daɗi.




Hannunta ta ziro ta ƙugunsa. Ta kwantarda kanta a kafaɗarsa. Wannan dai dai ton ya isheta. Ji takeyi inama su dawwama ahaka suna zagaye duniya dashi. Yanayine na musamman daze zauna atare da ita har fitan numfashinta na ƙarshe.





____Domin gina alaƙa ta gaskiya da aminci tsakanin zuciyar ka dana wani baka buƙatar manyan kuɗaɗe, tsadaddun motoci ko takura kanka da wasu abubuwa na daban.



Amfani da abinda ke hannunka zuciyar ka abuɗe da soyayya kaɗai ya wadatar.




Abakin wani shop mai kyau sukai packing suka shiga.

Abakin entrance suka tsaya. Ɗaya daga cikin masu kula da customers ya taresu da fara'ansa yana cewa"barkan ku da zuwa."



Da fara'a Ustaz ya amsa masa. Ya tambayi mai suke so Ustaz yace "mai zaki sha.?"



"Ice cream." Ta fadi dasauri don ita aduniya ba abinda ke burgeta samada ice cream.



Mai shop yace"wani kala kike so.?"



Idanunta ta kaɗa alamar tinani tana murmushi. Shima guy din da murmushin sa yake lissafo mata kalolin ice cream ɗin da suke dashi.



Jiyayi kamar yasaka hannu aka ya fasa ihunda duk duniya zasu ji shi, suzo su taru suima wannan ɗan iskan mutumin dake tsaye agabansa dukan tsiya.



Ya kalli Aliya da idanuwansa da suka sauya kala se yaga duk duniya bata taɓa murmushi mai kyau da tsari irin wanda take yi yanzu ba.


Ya cije leɓensa da ƙarfi batareda yaji zafin abinda yayi ba kamar yanda yake jin zuciyarsa na tafarfasa.




Mai ice cream ya ajiye vanilla ice cream guda uku agabanta yana murmushi yace


"zakiji daɗin wannan sosai."


Aliya ta faɗaɗa murmushin ta tana amsa masa da"dagaske!"



Jiyayi kamar ya managreta. Duk se yaji haushinta ya kamasa. Suna zaman zamansu ta miƙe da sabon salo na banza da wofi, harda wani cewa ta gaji, shi kuma ya biye mata. gayinan ai wani yazo abanza yana kalleta. Bai san wani dogon tsakin takaici ya kufce masa ba seda sautinsa ya shiga cikin kunnuwansa.




Mai shop ya kallesa shida Aliya yana tambayar"Alhaji lafiya."



"Guda biyar zaka bata. Gayinan ka cire kudin ka "



Ya fadi yana miƙa mai A.T.M ɗinsa yana wani hararansa ƙasa ƙasa.



Duk sai mai shop yasha jinin jikinsa. Ya karɓa ya cire kuɗaɗensa. Aliya ta ɗauki ledan yana cemata "sai anjima."



Ganin yanda ya haɗe fuska ya dawo mata ainihin Rayyan ɗinsa data sani ya sanyata kame kanta. Ita babu ma abinda ya tsorata ta irin ganin yanda idanunsa sukai jaa. To meyasa haka? Ta tambayi kanta. Tunda ita dai lafiya ƙalau suka fito dashi. Shigansu wurinnan ne yasauya. Ta buɗe baki zatai magana se tai shiru ganin suna kan hanya. Gashi ko tayi magana bazai jitaba saboda yanda yake jan mashin din da gudun gaske.




Suna isowa cikin gida yayi packing ta sauko. Tai tsaye tana jiransa, ya kashe mashin din amma ko kallonta bai yiba yabude falon yai shigewansa ciki.




Dasauri tabi bayansa tana kiran sunansa yayi banza da ita.



"Don Allah kada ka tafi ka gaya min meyafaru?!."



Dakatawa yayi da tafiyar. Sedai bai juyo gareta ba.



"Idan nice nai maka laifi don Allah ka ya haƙuri, kada kai fushi da Ni."



Tafaɗi cikin muryan kuka hawaye na saukar mata.


Nan take ƙafafuwansa suka sage. Kamar wanda aka zare ma lakar jiki haka jikinsa ya mutu muruss! Duk yanda yaso hana kansa dubanta sai ya kasa. Zafin kukanta ayanzu yafi ƙarfin abinda yake ji. Da duk numfashin kukan da take ja da yanda zuciyarsa ke matsewa da ciwon gaske. Wannan kawai azaba take gana masa, tana rama abinda yai mata.




Ya jada baya. Ya rungumeta ajikinsa yana bubbuga bayanta ahankali cikin rarrashi.



Aliya ta ruƙunƙumesa tana sauke ajiyar zuciya taji muryansa mai taushi akunninta.




"Kukan ya isa haka."



Kanta ta ɗago. Tana share hawayenta tace "gayamin mai ya faru."



Yayi shiru yana kallonta batareda yasan amasar daze bata ba. Tom yace mata me! Yayi fushi saboda kawai wani yayi mata magana?koko ze ce mata zuciyarsa ta kusa fashewa saboda tayi ma mai shop murmushin data saba yinma kuwwa. shi kuma idanunsa suka ce duk ba haka ba? Tom shi kansa se yanzu ya fahimci yayi shirme.





Ganin Aliya ta tsare shi da idanunta tana niman ƙarin bayani yasashi cewa"muje kisha ice cream ɗin ki."




Kai ta gyaɗa masa. A zuciyarta tana deciding barin maganar tunda baya son faɗa.



Hannunta ya kamo cikin nasa suka taka atare suka je suka zauna. 



Ice cream ɗin ta ta buɗe ta kama sha ita kaɗai. Shi kuma yayi zaune yana kallonta because kayan sanyi basu dame shiba.



Duk yanda yake hango kyawun Aliya sai yaga tafi haka ayanzu da tai zaune tana shan ice cream ɗin nan sai ta fito a cutie babe abinta.



Ya karkatar da kansa gareta, yana kallonta babu ko ƙiftawa zuciyarsa na doka mata.



Seda ta gama tass sannan ta miƙe ta saka raguwar guda hudu a fridge. Ita ta tafi ɗakinta shima ya tafi nasa ɗakin.



Sedai me! Bayan suduka sun kwanta da niyyan bacci sai baccin ya ƙaurace musu. Tunanin juna da baza'a kirashi da kewa ba ya mamaye su. Suka dingi juyi lokaci na tafiya.



Duk yanda yaso danne zuciyarsa da tunanin Aliya da tai mai tsaye aƙirji ya kasa. Bayada zaɓin da ya wuce ya tafi ɗakin Aliya.




Tana kwance tana juyi taji anturo ƙofa anshigo. Ƙamshin tirarensa mai sanyi ta shaƙa.



Kai tsaye ya hayo kan gadon. Sosai tai mamakin yanda ya iya kamota ya rungume don ɗakin babu wani wadataccen haske ta rigada ta kashe light. hasken farin wata ne kawai ke haska ɗakin.




Duk surutunta da tambayoyin ta sai taji ta kasa tambayarsa abinda ya barosa da ɗakinsa yazo nata ɗakin.




Tabar komai ayanda yake. Ta ƙara shigewa jikinsa tana lumshe idanunta da shaƙan ƙamshinsa mai bada natsuwa na musamman. Wanda ba iya ita kaɗai bane ga Ustaz Rayyan ma haka lamarin yake.




Baccin da suke nema da juyi zuciyarsu na dokawa yazo ya ɗaukesu anutse.