BIYU A ƊAYA

Chapter 40

by @barista

BIYU A ƊAYA 
     ( Don't judge a book by its cover)



Page 40
Sayyada barrister 
YOTA 13 
The five ink legends


A hankali yake jujjuya wayar dake hannunsa, yana mamaki a ce lokaci guda ya rasa number ta da kuma text message da suke yi wa juna, waye ya yi masa haka? Wa ya ɗauki wayar sa? Ai babu wanda ya san da labarin mon ange balantana ya goge, a hankali ya koma ya kwanta yana kallon siling ya lumshe idanunsa yana tunowa yadda aka yi har aka ɗauki wayar sa aka goge.

Ajiyar zuciya ya sauke da ƙarfi yana jin kewar kyakkyawar Aunty, ko ya take yanzu?..

Yana cikin wannan tunanin ne bacci ya ɗauke shi...

Washegari ya tashi jiki a sanyaye, baya jin daɗin komai, ya shirya cikin farin suit ya yi kyau, sai ƙamshi yake yi kai tsaye ya wuce ɗakin Mamie riƙe da side baga nasa, ya yi nocking ta ba shi izinin shigowa, ya tura ƙofar ya shigo yaga Daddy zaune yana shan tea, ya zauna tare da cewa 

"Barka da safiya Daddy"

"Abdulwahab barka, har ka fito?"

"Eh Daddy, Mamie ina kwana"

"Lafiya Babangida, ya gajiya"

Ya yi murmushi ya ce

"Alhamdulillah ba gajiya"

Daddy ya zuba masa tea ya ɗauka ya sha, ya tuna da shayin gargajiyan da Bilqees take dafa masa, ya yi kewarsa..

"Son mommie nka fa sun kusa dawowa"

"Allah ya dawo da su lafiya, yaushe ne za su dawo"

"Amin, nan da kwanaki 5 haka"

"Ai jikinta kam ya warware jiya da daddare ma mun yi fira a waya"

Cewar Mamie, Dr Waahab ya ce

"Ma sha Allah me za a fara shirya wa?"

Gobe weekend ko, baka da aiki sai mu yi magana"

"Ok Dad Allah ya kai mu"

"Amin"

Dr Waahab ya sha tea sannan ya yi musu sai ya dawo, Mamie ta yi masa addu'a kamar yadda take yi, cikin farin ciki ya fito ya haɗu da Ammie tana tsaye kusa da kitchen, ya gaishe ta, ta amsa tare da cewa 

"Likita ba dai za ka wuce wajen aiki ba?"

"Eh Ammie na kusa makara ma"

"To ga shi ƙannenka ma basu gama girka breakfast ba"

"Ba komai zan ci a office"

"To sai ka dawo"

Yana ƙoƙarin buɗe motar sa, Ashfat ta fito ta iso gurin tare da cewa 

"Barka da safiya Ya Waahab?"

A hankali ya juyo ya amsa

"Yawwa barka, kin fito?"

"Eh Ya Waahab in zai yu ka sauke ni a wajen aiki"

Ya ɗan yi jim sannan ya ce

"Ina motar ki?"

"Bana jin daɗi ba zan iya tuki ba"

Bai ce komai ba ya shiga ya zauna ya tada motar ita ma ta shiga, kira'ar karatun Alqur'ani ne ya ke tashi na ASheikh Maheer, yana yin waya lokaci zuwa lokaci tana kallon sa, komansa a nutse ya ke yi. Ta tuna jiya da ta saka yarinyar da take so tayi mata katanga da farin cikin ta a black list, har suka iso ya sauke ta, ya juya kai tsaye sai TH...

********************

Kasancewar weekend ne, ranar ƙarshen sati babu aiki, yasa KIRAWA'S FAMILY ya yi shiru ba hayani, kowa yana hutun gajiya da yara da manya. Dr Waahab yana kwance kan bed nasa ya kasa baccin safe, yana tunanin Angel, ya yi mamaki da bata nemeshi ba, ga shi kuma ya yi losing contact nata, da ƙyar yake iya runtsa idanunsa, ya rasa yadda zai yi.

Ya sauko daga kan bed ya zura jallabiya akan boxer da vest dake jikin sa, ya ɗauki wayar sa ya fito ya wuce filin wasa, yana isowa ya tadda Abdullahi KIRAWA da Abdullahi KIRAWA da team nasu suna wasan ƙwallon ƙafa, ya zauna daga gefe yana kallon su, ya yi kewar Sa'eed da yana nan za su buga ƙwallon hannu. Ya dannawa Sa'eed kira, bugu biyu ya ɗauka yana cewa

"Likita bokan Turai"

"Sa'eed how fah, gani zaune a side ba abokin buga wasan"

"Ai ina nan tahowa saura kwanaki uku ko huɗu mu diro Nigeria, za mu ɗaura daga in da muka tsaya"

"Daddy ya sanar dani dawowarku, ya me jikin?"

"Da sauƙi fa, ka samo mata ne ko sai na riga ka?"

"Ai sai ka dawo za mu tattauna"

"Ok to ni kam na samu"

"To acen Egypt ɗin"

"A'a Suhaima ce na shawo kanta"

"To ya yi maka kyau, wato ba jinyan mara lafiya bane ya kai ku"

"A'a kawai dai soyayya ta kullu"

"To ya yi kyau"

"Ina mutuniyar ce?"

"Wacce?"

"Ashfat ma"

"Ban sani ba, maybe tana ciki"

"To ta hakura kenan?"

"Da mene ne?"

"Da soyayyar da take yi maka"

"Oh yarinta ce dama, yanzu ta girma tana ma aiki"

Dariya Sa'eed ya yi, Dr Waahab ya sauya hirar sun jima suna yi sannan ya dawo ɗakinsa, ganin wasan da ƙannensa ke yi bana ƙarewa bane..


************

"Teemah daman na san ba ki goyon baya na akan Ya Waahab"

Cewar Ashfat cikin ɓacin rai, kowacce na kwance a kan katifarta, suna dandanna waya, Ashfat ta zubawa hoton Dr Waahab idanu...

"Ya Ashfat ba batun bana goyon bayan ki bane, don Allah ki daina rawan jiki akan sa, ai sai ki zubda class"

Hauwa ta ce

"Ita da mijinta ba za ta yi rawan jiki ba, ai gwanda ta yi kamin ayi mata kwace"

"Kin ga ƙanwar miji, kyale Teemah har yanzu yarinya ce, da Suhaima tana nan hirar za tafi daɗi"

Teemah ta ce

"Ko ɗaya ba wai bana sonta da Ya Waahab bane, ta kama kanta kamin ya watsa mata ƙasa a ido"

"Kin san Allah Teemah ki iya bakin ki, ai banga ranan da zai yi min haka ba, ke dai bari Mommie ta dawo"

"Matar Yaya ki kyale ta, ni ina bayan ki, kuma duk wacce ta ce za ta shiga sakaninku sai in da ƙarfina ya ƙare"

Cewar Hauwa, Ashfat ya tashi ta zauna ta ce

"Uhm ai ban gaya miki ba, cikin kwanaki biyun nan da dawowarsa, wata ta ishe shi da kira, wai oga me waye, na kasa riƙe sunan"

"Ya wahaab ɗin?"

"Eh amma na goge number ta, ke blocking ma na yi me gaba ɗaya"

Teemah ta tashi da mamaki ta ce

"Aunty Ashfat kika goge number ta?"

"Eh na goge"

Ta maida mata, Hauwa ta ce

"Kin yi min daidai"

Teemah ta ce

"Amma ba ki kyauta ba, kika sani ko abu me muhimmanci suke tattaunawa, ko kuma wani aiki ya haɗa su"

"And so what! Ni dai na goge"

"Uhm kin manta da Ya wahaab ko, wato kin ga ya yi sanyi"

"Teemah in bakya team nawa shikenan"

"A'a ina team naki amma dole na faɗa miki gaskiya"

"Riƙe ta bana so"

Ammie ta turo ƙofa ta shigo tare da cewa 

"Wai ku kam ba za ku iya tashi ku ɗaura breakfast ba kullum sai an yi muku tini, naga yadda za ku yi in kun yi aure"

"Ammie barka da safiya, yanzu za mu wuce kitchen"

Cewar Hauwa, Ammie cikin ɓacin rai ta ce

"Kada Allah yasa ku yi, kun san Daddynku suna karyawa da wuri shine ku ka yi shaɓe² a kwance"

"Ayi hakuri Ammie yanzu za mu fito"

Cewar Teemah, Ammie ta fice, Ashfat ta ce

"Uhm ni fah in nayi aure ƴar aiki zan ɗauka"

"Wa! Uhm ki ma cire a ranki, in dai a wannan family ne ba ke ba ƴar aiki"

Cewar Teemah, Hauwa ta ce

"Shi yasa nake sha'awar auren bare, don ba zan iya aiki da yawa ba"

"To ku tashi mu je kitchen"

Suka taso zuwa kitchen, su uku Farida ta shigo nan suka soma aiki basu ɗau lokaci ba, suka kammala, Ashfat ta shiryawa Ya Waahab ta kai masa ɗakinsa...

Yana zaune kan stool ya kunna system nasa dake kan tebur yana aiki, ta yi nocking ya bada izinin shigowa, ta shigo ɗauke da madaidaicin tray ta ajiye tare da cewa 

"Ya Waahab, barka da safiya"

Bai ɗago ba yana ci gaba da aikin ya amsa da 

"Yawwa Ashfat"

Ta sauke numfashi a hankali ta juyo za ta fito ya ce

"Ashfat"

"Na'am"

Ba tare da ya daina abin da yake yi ba ya ce

"Ki haɗa kan ku yaran ku gyara ɗakin Mommie"

Wasu hawaye suka ciko idanunta, sune yaran, shiru da ta yi ne yasa ya ɗago ya dube ta tare da cewa 

"Kin ji?"

"Eh"

Ta fito tare da rufe masa ƙofa, ta shigo ɗakin ta zauna bakin bed ta ce

"Ni fah gaskiya Ya Waahab baya kyauta min"

Hauwa ta ce 

"Matar Yaya me ya faru?"

"Kirana da yarinya ya yi, bayan yanzu na girma har aikin kaina nake yi"

Teemah ta ce

"Yarinya ne mana, ai gaskiya ya faɗa tun da ya girme ki"

"Ke amma gaba nake da ke"

"Allah ba ki hakuri"

Suna cin abinci ban da ita, da ƙyar ta saka hannu ta ce

"Ɗakin Mommie za mu gyara"

"To mu ci mu ƙoshi mu samu ƙarfin yin aiki"

Cewar Hauwa, suna kammalawa suka wuce side na Mommie don gyarawa...

Dr Waahab ya gama abin da yake yi, ya shige toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya, ya buɗe breakfast da Ashfat ta kawo masa kunun gyaɗa kawai ya sha, ya fito zuwa wajen Daddy.

Ya tadda su sun gama karyawa suna hira ya zauna, ya gaishe su, suka amsa nan suka hau tattaunawa akan zuwan Mommie, ya jima a cen sannan ya dawo side na Mamie, nan ma ya jima sannan ya koma ɗakinsa...


*******************************

Gida ya kauraye da hayaniya sai aiki ake yi, yau ce ranar da su Mommie za su iso Maiduguri, tun jiya jirgin da ya ɗauko su daga Egypt ya sauke su a Abuja sun kwana yau hau jirgin da zai kawo su Maiduguri.

Side nata an gyara shi tsaf kamar ba shi ba, sannan aka yi girke girke, Dr Waahab ya wuce ɗauko su shi da Umar KIRAWA da Abdullahi KIRAWA, suna zuwa suka tadda su suke jira, cike da farin ciki Dr Waahab ya iso inda Mommie take tsaye cike da mamaki ganinsa ya ce

"Ma sha Allah Mommie sannu da dawowa, Alhamdulillah jiki ya yi kyau"

Ta yi murmushi ta ce

"Doctor haka ka girma"

Ya ɗan jure bai zubda ƙwalla ba, don kusan shekaru ashirin kenan bata hayyacinta, ya ce

"Mommie mu je gida ki huta ko"

Ya dube Sa'eed da ya zuba masa na mujiya ya ce

"Ya dai Sa'eed baka gane ni bane?"

Ya iso ya rungume shi tare da cewa 

"Likita ka girma"

Hararar shi ya yi ya ce

"Amma na girme ka"

"Da watanni kawai"

"Koma da kwanaki ne"

"Ya Waahab barka da safiya"

Cewar Suhaima, ya dube ta tare da cewa 

"Sannu Suhaima kun dawo lafiya"

"Alhamdulillah"

Suka shige mota kai tsaye suka dawo KIRAWA'S FAMILY...

Suna shiga abin ka da babban family aka cika sakar gida, Mommie tana fitowa masu kuka nayi masu yi mata barka da zuwa na yi, masu rungume ta suna yi, da ƙyar aka barta ta shigo side nata, aka ce a kyale su kada a zo yi musu barka har sai sun nutsu, Suhaima tuni ta wuce wajen ƴan'uwanta suka rungume ta suna yi mata sannu da dawowa...

*******

Da yamma Dr Waahab ya shigo side na Mommie tana zaune kan dardumar sallah hannunta riƙe da casbi tana lazimi kamar yadda take yi a cen baya, ya yi murmushin farin ciki, Mommie is back, ta dawo kamar yanda take a cen baya...

Ya zauna har ta idar ta juyo tare da cewa 

"Yarona sannu"

"Yawwa sannu Mommie ya gajiya?"

"Alhamdulillah bacci na yi sai yanzu na tashi"

"Hakan yana da kyau wa lafiyar ki"

Suhaima ta shigo, ta ajiye yankakkun fruits, ta ce

"Ya Waahab barka da yammaci"

"Suhaima sannu da ƙoƙari Allah ya bada ladar jinyan Mommie da ki ka yi"

"Amin Ya Waahab"

Ta fice, yana mikawa Mommi tana ci suna hira, Mamie ta shigo tana ganin Dr Waahab ya ta 

"Ashe nan kayo, ai shikenan yanzu kam za a fara kus³ ba tare da na san komai ba"

Murmushi ya yi Mommie ta ce

"Ke da kika sani, babu me jin sakaninmu da yarona"

"Ah ni ma ban ce zan shiga ba"

"Don ma matar da na ba shi an raba ni da ita, da yanzu sirkina ne"

Shiru su ka yi, jikin Dr Waahab ya yi sanyi, da wuya da man ta mantar da abin, a hankali ya sauke numfashi 

"Mommie kin ga yanzu kika fara samun sauƙi, jiki ya yi kyau, ki nesantar da komai daga brain na ki da zuciyarki, yawan tunani zai sake haifi miki da matsala"

"Hajjiya sannu ya gajiya"

Cewar Mamie, Mommie ta ɗan sauke ajiyar zuciya ta ce

"Hajjiya Balkisu Alhamdulillah na same ku lafiya?"

"Kowa lafiya kalau, ai kwanan nan ma za ki aurar da ɗanki"

"Ai ko naga alama, ya girma"

Ya yi murmushi ya mik'e ya yi musu sai anjima, ya dawo side nasa ya tadda Sa'eed ya shigo, yana zaune, shi ma zaman ya yi ya ce

"Ina cen side na Mommie"

"Na yi tunanin haka, ina Suhaima?"

"Ina na sani"

"Au matar tawa ce ma kake cewa ina ka sani"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Da alamu idanunka sun rufe"

Ya yi murmushi ya ce

"Wai har yanzu baka zaɓi matar da za ka aura bane a family"

"Ɗan'uwa a waje na zaɓo ta"

"Kai ƴar wacce unguwa? Kai da ba wasu abokai ko yawo kake yi ba"

"Ƴar cen ƙasar Ghana ce"

"What?"

"Kamar yadda ka ji"

"To waye zai je ya nemo maka auranta?"

"Ku mana"

"Tab to ka sanar da su Daddy"

"A'a tukuna"

"Gaskiya ina ga da wuya su amince"

"Saboda menene?"

"Kana ɗaya daga cikin waɗan da za su aure ƴar wannan ahali"

"Na faɗa maka, ni bana sha'awar auren ƴar family"

"To nuna min ita a waya na ganta, what i mean her picture, wacece wannan wacce ta yi sa'ar sace zuciyar zinari?"

"Bani da photonta and even her contact"

"Ban gane ba, kamar yaya bakwa waya ne? Ko ba ka sanar da ita kana sonta ba?"

"Abin nima ya ɗaure min kai, muna waya, kuma ina kiranta, ita ma tana kira na, kawai rana ɗaya na rasa number ta, ba ki ɗaya a waya na, an goge min"

Sa'eed ya tashi ya zauna ya ce

"Akwai wanda yake da labarin ta ne?"

"A'a babu"

"Akwai"

Cewar Sa'eed, Dr Waahab ya sauke numfashi ya ce

"Waye?"...





_____________________________

Ayi hakuri da typing errors 






Comments and share fisabilillah