015
Ummi ce ta mik'e ganin hasken rana ya bayyana sosai mutane sun fara shigowa, dan har an d'aura shinkafar biki.
D'akina ta shigo da sallama da mamaki take kallon dakin gashinan a bude take amma wayam bana ciki, bata damu ba domin tunanin ta ina band'aki, haka ta zauna tai ta jirana, ganin bazan fito ba yasa ummi mikvewa ta nufi dubani ko zata ganni.
Haka tai ta dube dube ita ce har gidan su khalik, har k'ofar d'akinsa amma bata ganni ba, hakan yasa kirjinta yaci gaba da dukan da yakeyi.
Da sauri ta dawo gida, aunty sanah wadda ke tsaye tana tunani.
"Aunty sanah zo Kiji ummi ta fad'a tana kallonta.
Bin ta tayi suka nufi d'akin umma wanda ba kowa," aunty sanah banga falmata ba, ba inda ban duba ba banganta ba.
Murmushi aunty sanah tayi tace"to ke ummi ke da b'ata zatayi ba, bare naje na duba ke ma ki dudduba.
Haka suka ci gaba da neman amma babu ni babu alamu na, a k'alla sun d'auki rabin awa amma babu ni.
D'akin suka dawo yayin da ummi hawaye ke fita a idanunta take kallon umma wadda take a zaune kan gado ta had'a kai da gwiwa.
Baba ne ya shigo yace"wai kuna nufin ta gudu.
"yo ta gudu mana malam, gaskiya falmata bata kyauta mini ba, ba tab'a bani kunya ba sai yau, sai taje idan tana tinanin zata ga daidai, daga yau na cireta daga sahun 'ya' yana, kuma wallahi bazan tab'a.... Saurin rufe bakin ta sanah tayi tana jijjiga kai yayin da hawaye ke fita daga idanun sanah.
Baba yaji maganar guduwar nan ta falmata, kallon ummi yayi wadda ita ma durkushe take, a fiki ya furta tinda har na hadva mutane to billahillazi falmata bazata sakani jin kunya ba, ficewarsa yayi daga gidan.
A kofar gida naga ya tsaya ya kalli gidan su ummi, mahaifinta wanda ya fito cikin babbar riga fara yajasa gefe, bansan dai me suke tattauna wa ba nidai.
A ciki kuwa da kyar aunty sanah ta lallashi umma ta daina kukan sai dai kukan zuci wanda shi taketi tin daga lokacin da falmata ta bijirewa umarninsu.
'yan uwanta kuwa kowa so yake yaga amarya falmata yayin da babu ita babu alamunta.
Karfe 12:00 aka sanar da daurin auren wanda aka d'aura sa a masallacin da yake kusa da su, baba yana can shi da baki, angwaye suka shigo gaishe da umma.
Umma mamaki ne fal ranta, kenan yanzu haka malam ya d'aura auren nan bayan ba falmata, to me yake nufi, tambayoyi ne fall ranta amma ta rasa mai bata amsa.
Bayan taro ta ragu wajen karfe d'aya har yanzu ummi tana d'akin umma tana kuka, ban tab'a tunanin haka ummi ke k'aunar ahalin mu sai a ranar nan.
Baba ne ya shigo d'akin, hango ummi tana kuka yasashi k'arasowa yace"ummi sai kuma ya juyo yace"sanah ki shirya ta kawai da kayan falmata na amarci.
Warrrr ta waro idanunta, ta kasa gane mai yake nufi, tambayoyi ne fal cikin ranta, bude baki tayi da niyyar tayi masa magana sai kuma yayi murmushi.
"ummi nasan bazaki bijire wa umarnin mu ba, haka kuma nasan ki kina da hakuri da kuma kawaici, na samu iyayenki mun yanke hukuncin d'aura aurenki da auwal.
Zabura tayi ta tashi tana d'aga hannu ta dora a ka.
" Na shiga uku na lalace, baba taya zaka yanke mini wannan hukuncin, baba ban cancanci haka ba daga gareka.
" Kin cancanci haka ummi, dan haka sanah huce da ita ki shirya ta, mahaifiyar ummi ta fad'a wadda ta shigo yanzu.
"umma ban tab'a muku musu ba, ko na d'aga muku murya amma yau na muku musu, wallahi umma bana son auwal bazan iya zama da shi a matsayin miji ba, hawaye ne ke zuba daga idanun ta yayin da numfashinta ya fara sama da k'asa.
"Ummi ki tsaya ki saurareni ko, idan baki sauraremu ba wa zaki saurara ummi.
Hawaye ne ke zarya a idanun kowanne a cikinsu banda iyayen maza.
Da kyar aka samu ummi ta nutsu tayi shiru tana zubar da hawaye cikin sanyin murya tace" Umma meyasa kuka aikata mini haka.
"amma naga ummi ai bazamu aikata miki abinda ba daidai ba ko.
To fahhhhh..........
Alk'alamina dai anan zai dakata dan haka kuyi sauri ku mallaki naku domin ku k'arasa karatu cikin kwanciyar hankali a farashi mai sauki na ₦300kacal.
Ga tulin tambayoyi babu mai bada amsar su, sai fa idan kun karanta.
Dan nidai nasan sam khalil bayason falmata.
Abu d'aya ne ke bani mamaki ni fa, shin falmata da tabi khalil suka gudu shin zai aureta, ko kuwa zai ajiyeta ne, ko kuwa zai wullar da ita ne? Ko kuma siyar da ita zaiyi ya amshi kud'inta?
Ummi zata yadda da auren auwal kuwa, k'addara ta yadda da auren shi auwal zai yadda da ummi bayan irin mutuwar da yayi a kan son falmata.
Yaya iyayen falmata zasu tsinci kansa bayan maganar nan ta fasu cewa falmata ta gudu a daren d'aurin aurenta.
Kaiii jama'a Rikici ne kawai a wannan littafi, domin kuwa rikicin ya b'aci.
Dika zaku sami wannan littafi a kan naira 300 kacal.
Mai buqata yayi mini magana direct ta wannan number *** whatsapp/call.
Ko kuma ka tura kud'in ta wannan account
***
Aisha Sunusi Muhammad
O pay
*BAUTAR ZUCI🥹😭💔*