OMRI HAYATII

13

by @asmybaliyu

OMRI HAYATII 

by....
Asmy b Aliyu 

13...

har washegarin ranar bai Kara magana da malaak ba haka ya jera mata kusan miss calls 3 ya tura mata saqo babu replay babu daga waya abunda ya dan Sosa masa rai kenan Shima ya shareta bai Kara nemanta ba,babu maccen da yake yiwa kira 3 a rayuwarsa bayaga mahaifiyarsa da malaak din ko kannensa Sun sansa Sun San tsarinsa baya kira biyu a waya.
suna dawo daga massalaci shida Abba,
Kai tsaye ya nufi bangaren maifiyarsa
bayan ya gaisheta ya koma bangarensa,
ya cire jallabiyyar jikinsa wacce take fara tas ya nufi bangaren motsa jikin dake cikin part dinsa.daga shi Sai farar vest wacce ta kamasa ta fito da halittarsa.

a hankali ya farar geaming cikin wata kwarewa nan take ya fara hada zufa
jijiyoyin jikinsa Suna miqewa da murdewa lokaci daya,Sai da ya kusan awa a haka
kafin ya dauki towel da aka jera acikin hangars masu tsananin taushi da tsafta
ya fara goge zufan dake tsiyaya ajikinsa,
Yana kammalawa ya wuce cikin bedroom dinsa ya dauki wayarsa dake aje kan bed,
yaga miss call daya daga malaak baibi takan misscall din ba yayi dialling lambar fareeda marafa.cikin bacci ta daga wayar
fareeda ki hadomun white coffee yanxu ki kawo mun a bangarena."

"Yayanmu!"ta fada cikin shagwaba
mintuna goma."ya fada Yana Kashe wayar,
tamkar fareeda xatayi kuka ta fara murza ido jiya bata kwanta da wuri ba har kusan 12 tana kallon wani movie jin take idan ta miqe tsaye Xata iya faduwa,Kai tsaye tayi dialling lambar Ayusherh marafa
tana fara ring ta dauka dan allah ki hadawa Yayanmu white coffee ki kai masa ki tausayawa baiwar Allah baccine a idona."
murmushi Ayusherh tayi tana katse Kiran,
ta miqe tsaye tana kallon kaaka da ta fara 
bacci itama tana zaune akan sallaya,
ta ninke carpet din hannunta.
da dogon hijab din dake jikinta ta nufi kitchen Wanda Yan aikinsu guda biyu har sun fara aikin breakfast nan ta gaishesu da girmamawa kafin ta dora ruwan
zafi ta bude drowers tana fito da kayan da Ake hadawa mu'azzam din coffee 
ta rasa kaunar yayan nasu da coffee.
bayan tagama ta hada komai cikin madaidaicin tray ta nufi bangaren mu'azzam marafa ,da sallama ta shiga 
cikin falonsa na biyu ta samesa zaune 
akan Coach ya axa laptop akan table
Yana dannata cikin kwarewa ,ya daga Kai 
Yana kallonta ya amsa gaisuwarta cikin natsuwa lokacin har yayi wanka 
yana cikin wasu tsadaddun designer short wears farare tas da sukayi masa mugun 
kyau .Sai kamshi ke tashi cikin falon,
a hankali Ayusherh taja wani side table 
ta dora tray din ta dauki cup ta tsiyaya masa ta mika masa tareda fadin"good morning yayanmu."
ya karba Yana fadin good morning 2 
Queen kin tashi lafia?"
ya fada still hankalinsa na akan laptop dinsa.
ta mike tsaye tana fadin"lafia kalau Alhmdullahi,gyada Kai yayi Yana cigaba da sipping hot coffee dinsa.
juyawa Ayusherh tayi ta fara tafia
kafin yace thank you queen.
murmushi tayi masa tana daga masa hannu alamar bye-bye Shima a natse 
yayi mata bye bye din cikin class da kamewa.
daman yasan yadda yaji muryar fareeda
bazata hadamasa wani coffee ba 
kwafa yayi alamar Zasu hadu ne.

da suka hadu wuraren qarfe 9
sunyi Shirin zuwa islamiyya kasancewar weekend ne ,Suna zaune a table sai da ya rankwasheta ihu ta fasa da sauri Mami
ta kallesa tana tambayar meya faru."anan ya fadawa Mamin murmushi kawai Mamin 
tayi ta kalli fareeda ki saki jiki ki gama
yayanku ya saukeku a islamiyyar 
tunda abbanku ya aiki driver,
shiya saukesu a islamiyya
kafin ya nufi clinic Shima bai jima a clinic din ba yabaro ya hadu da Anas Sai kusan 2 yabar gidansu Anas haka kawai 
ya Karya kan motarsa zuwa unguwar su malaak Sai da ya shiga da motarsa har cikin get din gidansu yayi parking wurin da aka tanada dan aje motoci.
saqo ya tura mata akan gashi a waje
sakon na shiga da sakan biyar sai ga kiranta ,aje wayar yayi dan bayajin zai iya dauka har tagama ring bai daga ba 
Sai bata sake Kiran ba baifi minti biyar ba ta bayyana a gabansa,dan tasan idan ta kira maigadi ta fadamasa ace ya shigo
ta kirawa kanta ruwa dan juyawa 
zaiyi ya koma bazai shiga ba. 
ta taba yimasa hakan bai shigo ba
kawai ya tada motar yabar gidan,
da taji shiru ta fito ta tambayi maigadi
ya fadamata ai ya tafi rufe maigadin
tayi da fada tamkar xata dakesa
bai fadamasa sakonta bane??
nan maigadin ya rika yimata rantsuwar
ya fadamasa ranta a bace ta kira 
mu'azzam Cike da rigima take tambayarsa meyasa ya tafi bayan ta bada sako a fadamasa ya shigo cikin falo....

"lower your voice miss Malaak!!!"
ya fada cikin bacin rai kafin ya dora da fadamata shi ba yaronta bane da Zata aiko a fadamasa sako,idan bazata iya fitowa tayi masa iso ba Kar ta Kara yimasa irin wannan ganganci yadda taji muryarsa
ta bude baki zatayi magana ya datse Kiran
da wani irin shock ta rika kallon wayarta.
akan wannan abun mu'azzam ya dauke
mata gaba daya Sai da tasha wahala kafin
ya sauko,ta karaso tana kallon cikin fuskarsa kamshinsa nan take ya cika mata hanci wata irin natsuwa taji tana shigarta,
hannu tasa ta bude kofar motar
kyawawan idanunsa ya zuba mata,
sanye take cikin wani maroon material Wanda akayi wa dinki boubou 
material din bakaramin kyau yayi mata ba Sai scarf dinda ta daura akanta 
kalar material din Sai wayarta da ta rika
a hannu kallon sama da kasa ya riqa yimata Yana kallon maikatan maxan dake yawo a harabar gidan Kuma ta zabi ta fito 
a haka su ganta,wani irin kishi 
yaji Yana saukar masa.
langabe Kai tayi tana kallonsa ganin yadda 
yake wani shan kamshi da alamar 
Yan miskilancin Sun motsa,
hannunta ta basa ya kalli hannun da take basa.sai ta ware masa ido
saka hannunsa yayi cikin nata ya fito daga cikin motar Yana jin zuciyarsa na tafasa,
a hankali ya xare hannunsa cikin nata hannun a haka suka jera suka nufi entrance din shiga gidan.....

suna isa a falon da ake saukesa idan 
yazo gidan ya zauna daya daga cikin kujerun da suka kawata falon .
Yana zama tayiwa kanta masauki akan kafafunsa a hankali ta sakala hannayenta cikin wuyansa fuskarsa tana dan gogar kirjinta lumshe ido yayi Yana furzar da numfashi mai zafi,hannu tasa tana shafa 
fuskarsa har zuwa kan kyakkyawan 
(quarter million)din da ya Kara kawata doguwar fuskarsa......

please........ta fada cikin sanyin murya 
Mai Jan hankali a hankali ya bude fararen idanunsa da suka fara canja Kala
ya saukesu a kanta,
"meyasa??"
ya fada da wani yanayi a muryarsa,
meyasa bakya saka Mayafi idan xaki fita
Bude ido tayi da mamaki tana kallon
rigimarsa,acikin gidansu zai ce Sai ta nemi wani mayafi .tsirin mu'azzam tsoro 
yake bata sai kace bai San a turai 
tayi rayuwarta ba.

"beb acikin gidanmu fane
akwai wani aibu acikin wannan shigar?
ta fada tana kallon cikin idanunsa
da ta hango wutar kishi na kamawa acikinsu,kokarin tashi yake tsaye ta Kara manne masa. bude baki yayi zaiyi 
magana da wani irin salo ta hade bakinsa
da nata lokaci daya tana Kara tallabo 
kansa wani irin tsotsa take yiwa harshensa 
tamkar ta samu sweet,kiss mai zurfi
tayi masa still dayan hannunta na cikin sumar kansa wacce take kwance luf
tamkar ta larabawa....yadda take shafa kansa yake Kara kunnasa Kara mannowa
tayi cikin jikinsa ya fara tayata kiss
din harshensa ya saka Yana zuko duk wasu yawu dake cikin bakinta 
Yana hadewa,hannunsa ya dora akan 
cinyarta Yana jin notukkan kansa na warware kansu,da Karfi ya kaiwa
cinyarta wata damkar da ya sakata 
runtse idonta da Karfi da wani irin slow 
ya fara shafa cinyoyinta Yana sauke 
Mata wani irin numfashi mai dumi,
a hankali ya xare bakinsa cikin nata
tana kallon yadda fuskarsa ta canja
tayi wani irin Ja idonsa suka kankance lokaci daya.

lumshe idonsa yayi Yana sauke numfashi
yana jin yadda jininsa yagama saki lokaci 
daya.sai da ta tabbatar ya samu natsuwa
Sai ta dagasa cikin gida ta nufa 
bata jimaba ta dawo dauke da tray
taja table ta dora tray ta tsiyaya juice na fivealive tazo ta Kara zama akan kafafunsa
ta nufi bakinsa dashi babu musu
ya bude bakin ya fara sha a hankali
Yana jin wani sanyi na sauka ajikinsa,
suna cikin wannan yanayin wayarsa 
dake cikin aljihun wandonsa ta fara ring
hannu malaak ta saka tana kokarin ciro masa wayar,sunan mami ta gani
Wanda ya rubuta da wasu irin heart red agaban sunan,wani irin motsawa zuciyarta tayi ganin yadda yake kallon wayar still wayar na 
ring ta miqa masa tana kokarin daidaita natsuwarta sunan da yagani ajikin screen din wayarsa ya shiga wani irin tari
lokaci daya ya sarqe da sauri
malaak din ta karbi cup din da ta mika masa da Zata ciro wayar,ajesa tayi akan tray tana mikewa daga jikinsa.sai famar sannu take jera masa tana dan shafa bayansa da hannunta.

da wani Kiran ya shigo Sai ya mike tsaye
da gaggawa yayiwa malaak din sallama.
ko minti daya bai qara ba ya fice daga cikin falon Yana jin zuciyarsa na tsananin bugawa,ganin yake idan ya dauki wannan Kiran Mamin Zata iya gane Yana wurin malaak.....da wani irin shock Mai dauke da bayannen mamaki malaak din tabi mu'azzam din dashi.daskarewa tayi a wurin tana jin kafafunta na kasa daukarta.


#OMRI HAYATII 
#LOVE/FATE
#BEST LOVE
#MU'AZZAM MARAFA
#MALAAK FAROOK RANO 
#ASMY B ALIYU 
#***