Chapter 19
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*Ba ni da Madogara*
(Sai Allah...)
019
Kamar wacca aka tsikara ta yi wuff! Ta miƙe ta shiga cikin garden ɗin kasancewar babba ne sosai ga kayan marmari da dama an shuka a ciki, tafiya take yi tana tsinkan duk kayan marmarin ya yi mata ba tare da ta wanke ba take sha. Kamar ance ta juyo gefen hagunta, waro dara-daran idanunta ta yi waje ganin Salame tana haƙon rami a gefanta kuma wata ɓaƙar leda ne a ƙulle. Nan da nan Hujayrah ta ɗaure fuska ta nufi inda Salamen take gadan-gadan. Tana zuwa wurin ta tsaya cak! Hannunta riƙe a ƙugu ta ce
"Kutumar uban me kike yi a nan wurin munafuka?"
Da matuƙar tsoro Salame da ɗago daga duƙyen da ta ke tana kallon Hujayrah gabanta sai lugudan bugu yake. Wata uwar tsawa Hujayrah ta daka ma Salame tana cewa
"Ba da ke nake ba ne! Ko halin da kike ce a baya za ki nunamin, shi yanzu kike shirin nunamin?"
Gyara tsayuwa Salame ta yi don a yanzu ta cire tsoron da ya ɗarsu a zuciyarta lokacin da ta yi arba da Hujayrah. Wani munafikin murmushi Salame ta saki sannan ta dubi Hujayrah ta ce
" Ƙwarai kuwa halin nawa zan nunam..."
Bata ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ba ta ji saukan nushi a hanci da bakinta kamar walƙiya, ai babu shiri Salame ta saki ƙara ita a tunaninta murmujejen dutse ne Hujayrah ta maka mata. Ta yi taga-taga za ta faɗi sai ta yi saurin daidai tsayuwanta don babu ƙarya nushin ya shigeta sosai. Fitar wani abu mai ruwa-ruwa daga hancinta sannan ɗanɗanon miyon bakinta ya canja ta yi saurin saka hannunta ta taɓa hancinta, tana duba hannunta ta waro idanunta waje ganin jini kwance yana bin hannunta, ƙarin mamaki sai sanda ta zubda miyon bakinta taga jini ne, da sauri da kalli Hujayrah kafin ta ce wani abu Hujayrah ta cakumo wuyan riganta tana mata wata iriyar jijjiga mai saka kayan cikin mutum rayar Naira Marley, tayi-tayi ta ƙwace kanta amma hakan ya faskara, daga bayansu suka ji an ce
"Meke faruwa ne?" cikin sanyin murya ya yi maganar
Juyowa Hujayrah ta yi tare da sakin Salame, kamar jira Salame take yi, da gudu ta koma bayan Arqam tana faɗin
"Yallabai ka yi min rai Hujayrah za ta kasheni! Wayyo Allah!"
Bai ce da ita komai ba sai ya juyo yana kallon Hujayrah alamun neman ƙarin bayani, kamar jira Hujayrah take yi tana haki ta ce
"Ya Raqam qam barni da wannan shegiyar, maciyiya amana, cin amanar Mammi take yi a gidan nan, kalla abin da aka aikota ta birne don a illata Mammi! Ai wallahi yau sai Kinci ubanki da dani, sai kin gwammaci kiɗi akan karatu"
Bata jira mai Arqam zai ce ba tayo kukan kura ta damƙi Salame ta wurgar da ita a ƙasa sai ta haye saman cikinta tare da kai mata nushi da ko'ina a fuskarta, ihu kawai Salame take yi tana neman mai kawo mata ɗauki. Cikin zafin nama Arqam ya yi kan Hujayrah yana jawota daga jikin Salame, duk yanda yaso Hujayrah ta tashi daga kan Salame abun ya faskara don bada wasa take dukan Salame ba. Ganin lallai Hujayrah za ta illata Salame idan bai yakiceta daga jikin Salaman ba, sai ya yi amfani da ƙarfinsa na namiji ya finciko Hujayrah daga jikin Salame, sai tirjiya Hujayrah take yi ma Arqam tana ihun rana cewa
"Kasakeni Ya Raqam qam!!! Wallahi sai na illata shegiya mai cin amanar mutanan da suka yarda da ita tsawon shekaru! Kasakeniiiiiii!!!"
A bayansu Mas'ud wanda yanzu ya shigo garden ɗin saboda Arqam ya kira shi ya ce ya sameshi a garden zai nuna mishi wani abu, sai yaji ihun mace a garden ɗin kai tsaye ya ƙarasa inda yake jib ihun na tashi, cike da mamaki ya ce
" Subhanallah Hujayrah meke faruwa ne?"
Da sauri Hujayrah ta fizge kanta daga riƙon da Arqam ya yi mata, ɗaukar baƙar ledar da Salame ta ajiye ta yi ta buɗe, tana huci kamar wata zakanya ta cire abin da ke ciki ta nuna ma Arqam da Mas'ud tana cewa
"Ya Mas'ud wannan matar bata da zuciya mai kyau domin za ta iya kisa wallahi, ita ce fa wacca na ce maka na ganta da Maman Tahseen a wani lungu a babban falo suna ƙus-ƙus, idan baka manta ba Ya Mas'ud na faɗa maka akwai wani mugun sihiri da ke yawo a jikin Mammi, bana tantama ko kokwanto wannan shaiɗaniyar matar ce ta birne sihirin sai dai bansan inda ta saka ba balle na cire, kin yi asara wallahi "
Tana ƙarashe maganar ta kai mata wani Chinese a tsakiyar ƙirjinta, wani razananniyar ƙara Salame ta saki tana riƙe cikinta tana kuka, ga fuskarta ta kumbura, idanu ne, labɓanta ne balle uwa-uba kumatunta kamar fanƙen da aka cika masa yeast. Da sauri Mas'ud ya riƙeta don wani Chinese ɗin take niyyar kaima Salame. Arqam riƙe ƙugu ya yi yana kallon Salame, matar da ta yi shekara da shekaru tana aikin a part ɗin Ammiensa, tsabar yardar da Ammie ta yi mata har bedroom ɗinta take shiga kai tsaye, lallai ɗan Adam ba abin yarda ba ne. Cike da ɓacin rai ya dubi Salame da ke dirzar kuka ya ce
"Wa ya turoki?"
Wani Sabon kukan Salame ta saki tana zubewa a ƙasa tana cewa
"Yallabai ka yi min rai don girman Allah, sharrin shaiɗan ne amma ba halina ba ne wallahi ka yarda dani"
"Dallah yi mana shiru makira, tambayarki ake yi wa ya turo, ba roƙo muka ce ki yi ba, don dole kibar gidan nan a yau ba sai gobe ba" cewar Mas'ud bayan ya saki Hujayrah.
Cike da da na sani Salame ta ce
"Yallaɓai Hajiya Ramla ce ta turo ni, amma na roƙeka da Allah da Annabi dan binta ya Rasulallahi kar ku koreni, wallahi banda kowa sai Allah, da aikin nan na dogara nake taimaka wa iyayena da yarana"
"Lallai matar nan kin san da haka kika ci amanar da aka baki shegiya! Ai daman tunda zuciyata ta ƙi yarda da ke to tabbas muguwa ce ke tun ranar da na ganki" cewar Hujayrah tana cilla mata wata uwar harara, ji take kamar ta fizgo Salame ta yi ta bugu kamar Allah ya aikota.
"Na baki nan da awa daya ki tattara komai naki ki bar gidan nan" cewar Arqam yana mata binta da ugun kallo. Jiki babu ƙwari Salame ta wuce tana tafiya kamar wata ƴar maye tabar garden ɗin. Juyowa Hujayrah ta yi tare da ɗaukar ledar za ta wuce Mas'ud ya ce
"Ƙonawa za ki yi ne?"
"Mammi zan nuna ma wa daga bisani sai na ƙona" tana maganar tana ƙulle bakin ledar. Waro ido Arqam da Mas'ud suka yi waje don akwai babbar matsala idan Ammie ta ji wannan maganar saboda tana da ciwon zuciya wanda tun bayan haihuwar Razina Allah ya jarabceta da shi. Arqam ne ya yi saurin cewa
"A'a Hujayrah karki faɗa mata komai akan wannan batu"
Sheƙeƙe ta tsaya tana kallonsa, cike da mamaki ta ce
"Saboda me?"
Gumi ya Share sannan ya ce
"There is problem but please don't let her know about this"
"A'a fa Ya Raqam qam nifa ba jin wannan yaran na masu jajayan kunne nake yi ba, wai dwan diar ko abuwat disa ne ka ce ko miye oho"
"Karki faɗa mata don Allah" cewar Mas'ud
Taɓe baki Hujayrah ta yi sannan ta ce
"Da sharaɗi" A ɗaure ta yi maganar ta kallonsu da manyan idanunta.
Shiru suka yi don mamaki wai da sharaɗi, ko sharaɗin mene ne oho. Mas'ud ne ya ce
"Wani sharaɗi kuma Hujayrah ana zaune ƙalau?"
Gyara tsayuwa Hujayrah ta yi da kyau sannan ta ce
"Da sharaɗi Ya Raqam qam zai bani kyautar magensa sannan zan ƙi faɗa mata, don wallahi duk ranar da Mammi ta yi maganar ina ƴar aikinta to saina faɗa mata komai, kai ni wallahi ban ƙi in kwance mata biri har wutsiya ba, don ba a ƙarya a gabana sannan bana yin ta ahtoo "
Waro ido Arqam ya yi don mamaki, wai Melonsa zai bata kai! Amma wannan yarinyar ƴar hau ce wallahi.
" Ki faɗi wani abu daban amma banda Melona " A sanyaye ya yi maganar.
" To ni kuma Melonka nake so, idan ba ita ba to yanzu zan je na faɗama Mammi, Ni kunga tafiyata"
Juyawa ta yi abinta za ta wuce da sauri Mas'ud ya ce
"Zoo! Hujayrah an baki Melon shikenan"
Ɗan murmushi ta sakar masa sannan ta ce
"Yawwa babban yaya, zuwa anjima za a bani amma ko, don ya wuce yau gobe da sassafe zan faɗa ma Mammi"
"Eh yanzu jeki abin ki"
Cike da murna Hujayrah ta juya tana ƴan waƙe-waƙen da ta saba tabar garden ɗin. Sauke ajiyar zuciya kowannansu ya yi sannan Mas'ud ya juyo daga inda yake kallo ya dubi Arqam ya ce
"kaga abin da nake faɗa maka a zahiri ko"
Jinjina masa kai ya yi sannan ya ce
"Nagani kuwa, washhh Allah na wallahi duk na gaji, ga kaina wani azababban ciwo yake min saboda rikicin yarinyar nan" Yana maganar yana dafe kansa.
Ɗan dariya Mas'ud ya yi sannan ya ce
"Ga rikicin nata ya zama alkhairi, who knows wani mugunta aka shiryawa Ammie"
"Hakane, let's go to my part don sai na watsa ruwa kafin mu yi maganar" yana gama maganar suka fito daga garden ɗin bayan ya ɗauki laptop ɗinsa da wasu takardu.
A ɓangaren Salame da kuka ta shiga sashensu, bata samu kowa ba saboda kowa na can yana aikinsa a ɓangaren da yake, tattaro ƴan komatsan kayanta ta yi sa ta fito tana kuka. Tana fita daga sashen ta ci karo da Talatu ta kammala aikinta za ta koma ciki. Cike da mamaki Talatu ta ce
"Lafiya Salame? Mai ya samu fuskarki haka ba kyan gani"
Cikin gunjin kuka Salame ta labarta mata duk abin da ya faru tun daga kiran da Hajiya Ramla ta yi mata a yau da sassafe ta amso asirin da za a birne a cikin garden har zuwa yanzu da Arqam ya koreta daga gidan. Salati da salallami Talatu ta yi har tana tafi da hannayanta saboda mamaki, cike da takaici ta ce
"Yanzu saboda ɗan wannan abun Arqam ya koreki, wato wannan shegiyar yarinyar har ta samu fada a wurin Arqam, lallai kuwa" Tana maganar tana mamaki don kusan halinsu ɗaya sai dai wacca Talatu take yi ma aiki wato Hajiyan Sama a sashensa Hajiya momma bata taɓa bata wani abu makamancin asiri da saka koda a abinci ba ne, kasancewa Talatu tana ɗaya daga cikin masu yi ma Hajiya Momma girki a yanzu.
Sai dai Hajiyan sama takan ce mata ta saka ido a komai na sashen Hajiya momma sannan kome aka yi ta sanar mata. Kafin Salame ta ce wani abu sai ga Hujayrah ta fito za ta wuce part ɗinsu, cak! Hujayrah ta tsaya tana ma Salame mugun kallo, sai yanzu ta tuna dole Salame ta sanar mata inda ta birne asirin da ke jikin Mammi kafin ta bar gidan. Kai tsaye Hujayrah ta taho wurinsu, Salame da ta ga haka a tunaninta wani dukan Hujayrah za ta yi mata, ai nan take Salame ta saki jakar da ta riƙe tare da jan skirt ɗinta sama ta falla aguje tana ihu, Hujayrah da taga Salame ta falla a guje sai ita ma ta biyota a sittin tana cewa
"Ki tsaya Salameeee! Idan baki tsaya ba har kika bari na kamaki wallahi sai na yi miki dukan tsiyaaa!"
Salame kamar ƙara wa ƙafarta mai ake yi, don gudu take yi sosai da iya ƙarfinta bata ma sauraron abin da Hujayrah take cewa, ita ma ihun take yi tana cewa
"Jama'aaaaaaa! A kawo min ɗauki don ya Rasulallahi!!! Za ta kasheni jama'a ku ceceni don Allah!!! Wayyyo Baabataaaa! Na shiga uku na lalace ceeeee, yeeeeee Jama'aaaaaaa a taimaka min!" da ƙarfi take maganar tana kuka, duk da azabar da take ji a jikinta bai hanata gudu ba, domin ta tabbata Hujayrah ba mutum bace aljana ce. Su Arqam sun fito daga garden za su wuce ciki, sai suka hangi Hujayrah da Salame suna gudun mage da ɓera, ga bakin Salame yaƙi shiru duk da a kumbure yake. Da sauri Mas'ud ya dubi Arqam ya ce
"Man bari nabi Hujayrah kar ta illata matar can"
Shima binsu ya yi da gudu yana ƙwalla wa Hujayrah kira. Tana jinsa ta yi banza da shi don bata so ya ɓata mata plan ɗinta. Kasancewar gate biyu ne a gidan sannan tsakanin gate na farko dana biyu akwai ɗan tazara, har sun fito daga gate ɗin farko suna gab da kaiwa na biyu, Salame ta yi matuƙar sa a ƙofar gate ɗin a buɗe take wani ya fita yanzu, da gudu ta fita daga gidan kafin Hujayrah ta fita Mas'ud ya ƙwalla wa mai gadin kira akan ya yi maza ya kulle gate ɗin kafin ta fita. Unluckily kafin Hujayrah ta kai gate ɗin mai gadi ya yi saurin kulle ƙofar har da saka key. Wani wawan birki Hujayrah ta ja ta tsaya sai faman haki take, gaban mai gadin ta je ta tsaya tana cewa
"Malam buɗe min ƙofar kafin mu sami matsala? "
Kafin mai gadi ya ce wani abu har Mas'ud ya ƙaraso inda suke, shi ma hakin yake yi. Sai da ya ɗan lafa masa kafin ya dubi Hujayrah wacca ta kafe mai gadi da manyan idanunta ya ce
" Hujayrah me yasa ke baki jin magana ne don Allah? Ba mu ce ki ƙyaleta ba!"
A ɗan zafafe ya yi maganar yana kallonta. Turo bakinta ya yi waje ta ce
"Ya Mas'ud nifa babu abin da zan yi mata, kawai dai ta tsorata ne, tambayarta fa kawai zan yi ina ta ɓoye ɗaya aikin da aka turota, shikenan fa ko wurinta ba je ba ta fara gudu tana ihu, ina kiranta amma kamar ƙara ruɗar da ita nake yi, gashi yanzu ta gudu ban san a ina ta ɓoye ɗayan ba, Mts! "
Cike da takaicin guduwar Salame Hujayrah ta cije yatsa tana wani jijjiga kai bata so Salame ta gudu ba tare da ta faɗa mata inda ta birne asirin ba.
" Oh God! I thought dukanta za ki yi shiyasa na ce a rufe ƙofar, by the way in sha Allah za ki gani karki damu , yanzu juya mu koma ciki don na gaji wallahi"
Sai da ta tokari gate ɗin da ƙafarta kafin tabar wajen suka koma ciki. Kamar jira ake su wuce sai Talatu ta fito daga inda ta ɓoye ba tare da sun ganta ba ta saka mai gadi ya buɗe gate ɗin ta fita daga gidan. A wajen wata gindin bishiya ta samu Salame tana dirzar kuka miƙa mata ƴan kayanta ta juya da sauri kar a kamata. Haka Salame tabar estate ba tare da tasan inda ya dace ta dosa ba.
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangaren Hajiya Ramla suna falo ita da Tahseen har da Hajiya Lubna suna hira kasancewar Hajiya Lubna bata tafi gida ba saboda sai ta jira Salame ta kira waya sun ji ta kammala aikin tukunna, wayar Hajiya Ramla na kusa da ita, bini-bini sai ta duba ko Salame ta kirata bata ji ba, don ta yi matuƙar ƙagara Salame ta kira ta ce komai angama, saura jiran sakamako.
*Waiwaye*
Da sassafe Hajiya Lubna ta iso gidan ƙawarta Hajiya Ramla da yake da daddare ta dawo daga wurin bokan nasu. Bayan sun gaisa sai Hajiya lubna ta ciro wata leda baƙa daga jakarta ta kwance. Layu ne mabambanta guda biyu sai wata farar kwalba mai ɗauke da wani baƙin ice ɗan ƙarami an nannaɗe shi da jan zare.Matsowa kusa da Hajiya Ramla ta yi sannan ta miƙa mata kwalbar tana cewa
"Ammmm kinga wannan kwalbar?"
Jinjina mata kai Hajiya Ramla ta yi sai ta ci gaba da cewa
"Kamar yadda boka ya faɗamin, ita ce wanda ruhin Arqam ke ciki, za a birne a gidan inda babu wanda zai sani, da zarar an birne to nan take za ta fara aiki, a cewarsa Arqam da kansa zai zo gidan nan wurin Tahseen, sannan zai takura iyayensa su aura masa Tahseen, koda sunyi auran asirin ba zai taɓa karyewa ba har abada inda ba an haƙo asirin daga inda aka birne ba ne. Sannan ba a so wani yaga lokacin da mai birne asirin "
Wani ƙasaitaccan murmushi Hajiya Ramla ta saki har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana murmushi, Tahseen kowa tsallan murya ta fara yi a ɗakin tana rawa har da girgiza ƙugu tana cewa
" Yesss! Yessss! Soon to be the wife of multi billionaire Arqam Imran Abdulfatah Gaɗau, ha ha haaaa zan yi yadda nake so a garin nan, hhhhhh"
Babu abin da su Hajiya Ramla suke yi sai dariya don rawa take yi sosai tana murna. Sosai Hajiya Ramla ta shiga farin ciki mara misaltuwa ganin sanyin idaniyar cikin farin ciki da walwala, wannan kawai ya isheta a rayuwa, bata ƙi duk abin da ta mallaka ya ƙare in har hakan zai samar ma tilon ɗiyarta farin ciki. Hajiya Lubna ta katse Tahseen da cewa
"Bari na kammala bayanin sai ki ji daɗin yin rawar da kyau"
Wuri Tahseen ta samu a ƙasa kusa da Hajiya Lubna ta zauna, sai hakan ya saka su Hajiya Ramla dariya. Ci gaba da magana ta yi tare da miƙa ma Hajiya Ramla ɗaya daga cikin layun.
"Kinga wannan layar? Kamar yadda a baya wacca take yi miki aiki ta saka a cikin katifarta to wannan karon ba a katifarta za ta saka ba, pillow Wanda tasan tafi kwanciya a kansa, shi ake so a yanka a saka layar sai a ɗinke, daga haka kuwa angama da wannan babin domin da zarar ta saka kanta a saman pillow, shi kenan kun mallaketa sai abin da kuka ce za ta yi har da Tahseen domin wannan asirin mai mugun ƙarfi ne, shi yasa nace ki sake turo wasu kuɗaɗan don wannan na daban ne. Bayan haka za ta dawo tana mutuwar son Tahseen har ma son da take mata yafi wanda take yi ma yaranta. Sai kuma wannan"
Miƙa wa Hajiya Ramla ɗaya layar ta yi wanda ta kasance ta bambanta da ɗayan layan, bayan Hajiya Ramla ta amsa sai Hajiya Lubna ta ci gaba da cewa
"Sai wannan na shegiyar yarinyar nan ce ta gidan, duk yadda za a yi a tabbatar an saka layar nan a cikin katifar da take kwana, ita wannan layar ba kamar sauran layu da kika sani ba ne,tana da matuƙar hatsarin gaske, da zarar ta kwanta a saman layar to kwananta ya ƙare da yardar boka"
( *Ya Rahman duk wuya duk rintsi karka bari zuciyarmu tafi ƙarfinmu, ka bamu Ikon aikata alkhairi sannan ka nisanta mu daga aikata sharri komai ƙanƙantarsa,ka tsarkake mana zukatanmu baki ɗaya* )
Nan take Hajiya Ramla ta kira Salame ta sanar mata ta zo gidanta yanzu. Bata wani ɓata lokaci ba ta iso gidan, ledar Hajiya Ramla ta miƙa mata sai Hajiya Lubna ta yi mata bayanin yadda za ta birne kwalbar da kuma yadda za ta saka layun, tare da yi mata gargaɗi akan kar wani ya ganta, sosai Salame take gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa. Bayan ta yi mata bayani sai Hajiya Ramla ya miƙa mata bandir ɗin ƴan dubu-dubu guda uku tare da ce mata
"Ga dubu ɗari uku kyauta na baki don ki ji daɗin aikin da kyau, ki yi duk iya yinki kar a samu matsala, don na kashe kuɗi sosai a wannan karon, bana fatan a samu matsala na yi asarar kuɗina domin miliyoyi na kashe"
"Angama ranki shi daɗe, zan yi yadda kuka ce ba tare da an samu wata matsala ba, da na kammala aikin zan kiraki" Tana maganar tana tura kuɗaɗan cikin jakarta jikinta har wani rawa yake, tun da uwarta ta haifeta bata taɓa riƙe dubu ɗari koda kuwa na aro ne balle a kai ga nata na karan kanta, sosai ta shiga farin ciki mara misaltuwa. Sai godiya take yi kamar za ta yi musu sujjada.
Bayan Salame ta dawo gidan kai tsaye ta nufi garden can ciki saboda tasan babu mai zuwa can cikin sai idan za a cire kayan marmari idan sun nuna. Ganin a wannan lokaci duk wani ma'aikaci yana ɓangaren da yake aiki, sannan ba shi da dawowa ba sai kusan 12:00pm shi yasa ta yi amfani da Wannan damar, sai dai Kasshh! Kamar yanda Hausawa suke cewa *Rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya cak! Ta mai kaya* dubun Salame ya cika, domin dumu-dumu Hujayrah ta kamar Salame tana b haƙa rai za ta birne kwalbar wanda a ƙarshe taci dukan tsiya hannun Hujayrah ga kuma koran da Arqam ya yi mata nan take. Wannan ke nan.
*Cikin Labari*
Su Hajiya Ramla na tsaka da hira kamar walƙiya suka tsinci muryar Salame tana faɗin
"Hajiya ki taimakeni na shiga uku na lalace"
Da sauri suka miƙe suna kallonta don zuwa yanzu fuskar Salame ta canja kwata-kwata, ko'ina a gumbure yake, idanunta sun shige can ciki,ƙofofin hancinta sun ƙara girma ga uwa-uba labɓanta sun yi suntum! Sai sheƙi suke yi. Cike da tsoro gami da ɗumbin mamaki Hajiya Ramla ta ce
"Salame meya sameki? Ko hatsari kika yi ne?"
"A'a Hajiya, wannan shaiɗaniyar yarinyar ce ta yi min haka"
Waro idanu suka yi waje don mamaki, kafin suke wani abu sai ga Senata ya shigo falo babu ko sallama don hakan na ɗaya daga cikin ɗabi'arsa.
"Meke faruwa ne naga kun tsaya kun yi cirko-cirko?"
Hajiya Ramla bata tsaya wani ɓata lokaci ba, ta sanar masa duk abin da ke faruwa kama daga tafiya Hajiya Lubna zuwa wurin boka da kuɗaɗan da ta kashe har zuwa yanzu da Salame ta zo musu da mummuna labari wai Hujayrah ta kamata. Kasancewar halin Hajiya Ramla da mijin duk ɗaya ne shiyasa bata ji tsoron faɗa masa komai don tasan shi ma zai iya taimaka mata a wani ɓangare har su samu cikan burinsu. Cike da mamaki ya dubi Salame ya ce
"Faɗa ma duk abin da ya faru don mu san abin da ya dace mu yi"
Salame bata ɓata lokaci ba ta sanar musu duk abin da ya faru duk daga dukan data sha wurin Hujayrah zuwa koranta da Arqam ya yi, sai biyota da Hujayrah ta yi har gate don ta sake bugunts duk ta sanar musu. Shiru ɗakin ya yi baka jin motsin komai sai ƙarar A.C wanda ke sanyaya ɗakin. Wani tsaki mai ƙarfi Tahseen ta ja sannan ta dubi Salame ta ce
"Shikenan za ki iya tafiya Madam don yanzu bama muƙatarki"
Mamaki ne ya cika Salame, a tunaninta za su ɗauke aiki a nan tunda a sanadinsu ne ta rasa nata aikin. Cike da ƙwarin gwiwa Salame ta dubi Hajiya Ramla ta ce
"Hajiya zan iya samun aiki a nan tunda na rasa aikin..."
Wani mugun kallo Hajiya Ramla ta jefi Salame da shi wanda ya sanya Salame kasa ƙarasa maganar da ta yi niyyar faɗa. Cike da ɓacin rai da hargagi ta fara maganar tana nuna Salame
"Ke dan ubanki har kina na bakin da za ki ce na ɗauke ki aiki!!! Ehhhh lallai kuwa na yarda talaka shege ne bashi da kunya!!! Bayan kinsa na yi asarar maƙudan kuɗi sannan ki zo da yamutsattsan fuskarki ki dubi tsabar idanuna ki ce na baki aiki, to da ke da aikin kunci kutumar ubanki, maza tashi kibari min gida kafin nasa a ƙara saka wa a lallasaki munafukar banza, makira wa yasani ke kika lalata mana aiki don nasan talaka ɗan baƙin ciki ne a duk inda yake ya tsani yaga mai kuɗi a rayuwarsa"
Da sauri Salame ta fita daga falon tana kuka mai ratsa zuciya gwanin ban tausayi. Daman duk wanda ya ce tukunyar wani bazata taɓa tafasa ba to kuwa nashi ko zafi baza ta yi ba. Ga dai Salame tana cikin kogin nadama dumu-dumu wanda son zuciyarta da neman abin duniya ya kaita ga haka.
A can falon kuwa Senata ne ya dubi matarsa Hajiya Ramla ya ce
"Me yasa tun farko baki nemi shawarata ba, kika tafi kai tsaye ba tare da kin ji ta bakina ba? "
Ɗan shiru Hajiya Ramla ta yi sai can ta ce
"Ai naga kamar baza mu samu matsala ba ne shi yasa tun farko ban nemi shawararka ba"
Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce
"Baku biyo tsarin da ya dace ba, don ba asiri ya dace ki yi wa yarinyar ba, kamata ya yi ayi kidnapping ɗinta, kamar yadda ya saka hannu ta illata min yarinya haka nake so Tahseen ta saka hannu ta kasheta da hannunta kuma kisan wulaƙanci, kamar yadda ta wulaƙanta min yarinya a gaban mutane haka nike so ta yi mata kisan wulaƙanci sannan a jefar da gawanta a titi"
Wani farin ciki mara misaltuwa ya ɗarsu a ran Tahseen, rungume daddynta ta yi tana murna, shi ma murmushin ya yi.
"A gaskiya kuwa tun farko mun yi kuskure, wannan hanya ai tafi sauƙi wallahi, gashi yanzu na yi asarar kuɗaɗe na a banza tun da haƙar mu ta gaza cimma ruwa, to yanzu daddyn Tahseen what's the way out?"
Gyara zamansa ya yi sannan ya ce
"Ku bari a ɗaura auranta da Arqam tunda Alhaji Imran ya yi min magana cikin satin nan za su zo maganar auran Tahseen da Arqam, kinga idan an yi auran daga bisani sai mu cika ƙudirin mu akan yarinyar. I will like to see that bastard gurl that touch my princess, sai ta gwammace ba a haifeta ba"
"I'm so lucky to her you Dad, da hannunta zan kashe shegiya, yadda ta wukaƙantani a cikin mutane sai na yi daga-daga da zuciyarta" cewar Tahseen tana nuna musu yadda za ta yi wa zuciyar Hujayrah. (My Esteem fans na ce wani abu ko mubarta da Hujayrah 🤭🤭🤭🤭).
"Da kyau my Angel kyawun ɗiya ta gaji ubanta, karki ragewa kowa a garin nan koda kuwa da farce susa ne"
Haka suka ci gaba da hirarsu wanda kusan akan Hujayrah ne da yadda za su yi kidnapping ɗinta bayan bikin Tahseen da Arqam. Da bisani Senata ya fita abunsa, ya barsu Hajiya Ramla da jimami matsalar da aka samu.(Da alama Senata bai san yarinya da ƙungiyarsu take nema ruwa ijallo bace Hujayrah, Hmmmm akwai ƙura, koya kuka ce My Esteem fans 🤭🤭🤭) Wannan ke nan... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*BAYAN KWANA TAKWAS*
*Legacy Housing Estate, Bulunkutu, Maiduguri, Borno State. Nijeriya*
A yau ne Abdul da mahaifiyarsa suka iso gidan Sheikh Munnir akan batun auran Halima. Bayan sun gaisa sun sha ruwa sai ɗakin ya yi shiru, can Abdul ya dubi Sheikhul Munnir wanda su yake jira ya ji abin da ke tafe da su ya ce
"Sheikh mun zo maganar auran Halima ne"
Da ɗan mamaki ya dubi Abdul don bai fahimci inda ya dosa ba.
"Ban fahimceka ba Abdul na kun zo maganar auran Halima, na ga ban riga da na saka ranar ba balle na shaida muku"
"Eh mun san da haka, dalilin da ya kayomu shi ne a gaskiya mijin da kake so Halima ta aura ba mutumin kirki ba ne kuma ɗan shaye-shaye ne mai hurɗa da ma..."
Bai ƙarasa abin da ya yi niyyar faɗa ba Sheikh Munnir ya daka masa wata uwar tsawa yana faɗin
"Kai waye da har za ka yi jayayya dani! who are you!!! Halima ƴata ce ni nake da right ɗin zaɓa mata miji ko tana so ko bata so, kuma dole ta aure shi"
"Sheikh Munnir ba faɗa ya kawo mu nan gidan ba, Ina so ka fahimce ni kamar yadda Abdul ya faɗa ya kamata a duba ne, ba muna nufin ka yi ba daidai ba ne, sai dai shi wanda kake so Halima da aura maida hali, tun da tana da wanda take so kuma yana da aikinsa zai iya ciyar da ita, mai zai hana ka aura mata shi tunda bata son shi wanda kake so ta aura. Alhaji ya so zuwa ku yi maganar sai kuwa kwatsam! Aka kira shi a London meeting haka nan ya tafi. Don girman Allah ka fahimcemu" cewar mahaifiyar Abdul don tasan halin Sheikh Munnir wani birkitaccan mutum ne mai ganesa sai Allah wanda ya hallicesa. Wani mugun kallo Sheikh Munnir ya jefi Mahaifiyar Abdul, a fusace ya ce
"Kun ga ku tashi kubar min gida don abin da kuke so kar a yi bazan fasa ba, Halima ƴata ce kuma ni nake da iko da ita baku ba, sannan maganar auran da kuke cewa baku so ayi da wanda na zaɓar mata to kusani zuwa nan da kwana biyar za a ɗaura mata aure da shi, na fasa wata ɗaya da na saka, sai ku yi duk abin da za ku yi"
A matuƙar fusace Abdul ya daga masa wata uwar tsawa har jijiyoyin kansa sun tashi sun yi raɗo-raɗo, cike da ɓakin rai ya fara magana yana kallon Sheikh Munnir ba tare da ya ji tsoransa ba
"Baka isa ba wallahi Sheikh Munnir!!! Kamar yadda kake da iko da Halima haka muke da iko da ita!!! Don kaga marainiya ce shi yasa kake son wulaƙanta ta, to kasani mu ba za mu yarda ka aura mata wanda bata so ba, sannan da kake cewa zuwa nan da kwana biyar za ka yi mata aure, Hmmmm ai sai mugani!!! Ina maka kallon malami wada yasan ya kamata amma ashe ba haka kake ba"
Wani mugun kallo Sheikh Munnir yake jifan Abdul, idanunsa sun kaɗai sun yi ja sosai maganganun Abdul suka ɓata masa rai, ganin yaro ƙarami wanda bai wuce sa'an ɗansa Haladu ba yake faɗa masa baƙaƙyen maganganu son ransa, da alama bai san ko shi waye ba ne, idan da yasan ko shi waye to da lallai bai yi gigin koda kuwa kallon sa ne balle gasa masa baƙaƙyen maganganu. Tsam! Sheikh Munnir ya miƙe ba tare da ya ce musu wani abu ba ya fita daga falon ya barsu da mamakinsa. Abdul ne ya ce su zo su wuce tunda abin nasan haka ne, babu musu mahaifiyarsa ta miƙe suka fita, sun samu Halima a waje tana jiransu, koda suka iso sai Abdul ya yi mata raɗa a kunne, da sauri ta juyo ta kallesa fuskarta ɗauke da damuwa. Sai ya ce
"Halima za mu yi waya kin ji, ki kwantar da hankalinki everything will be alright OK"
Gyaɗa masa kai ta yi sai mahaifiyarsa ta yi mata ɗan nasihu akan haƙuri da juriya daga bisani suka bar gidan. Bayan ta koma cikin falo sai ta tarar da Sheikh Munnir na kai kawo a ɗakin yana masifa matarsa na ta yi shi, tana isa tsakiyar falon babu zato babu tsammani Sheikh Munnir ya ɗauketa ta matuka hagu da dama, nan take Halima ta zube ƙasa tana kuka, bai barta ba sai ya yi mata dukan tsiya madadin Mom ta ceceta sai ma ƙara zuga shi take yi. A nan take ya amshe wayarta ya haura sashensa yana huci. Mom kuwa wani daɗi ne ya ratsata ganin yau Sheikh Munnir ya dubi ƴar da yafi so duk a cikin yaransa. Miƙewa ta yi tabar falon tana yi mata dariya har da gwalo kamar wata yarinya ƙarama. Jiki babu ƙwari Halima ta miƙe zuwa sama, kai tsaye ta wuce bayi tana kuka ta yi wanka ta gasa jikinta saboda kusan ko'ina na jikinta ya yi ja kasancewarta fara sosai. Bayan ta fito sai ta saka kaya sai ta duba cikin wani ɗan ƙaramin akwatinta ta ɗauko wata ƴar siririyar waya ta koma bayin, kai tsaye ta kunna wayar tare da saka numban Abdul ta kira. Yana picking ta fashe masa da kuka tare da sanar masa dukan da Papynta ya yi mata wai duk laifinta ne data faɗa musu. Sosai hankalin Abdul ya tashi da yake sai zuwa gobe za su koma gida kasancewar mahaifin Abdul yana da ɗan uwa a nan Maiduguri. Ce mata ya yi karki damu idan ta kama gudowa za ki yi ki zo wurinmu ba matsala ba ne, don ba za ki aure wanda yake so ki aura ba tun da bakya sonshi. Sosai yaci gaba da lallashinta daga bisani mahaifiyarsa ta amshi wayar ta lallasheta sai suka yi sallama... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Kwanar Faru ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*
A waɗannan kwanakin abubuwa da dama sun faru daga ciki akwai auran Zaliha da Alhaji Zakari har da tarewanta gidan da kuma kitumumurar da Zaliha ta haɗa wanda hakan ya jawo Alhaji Zakari ya saki Hannatu saki ɗaya, tare da autanta Faisal suka tafi Giwa. Sannan a cikin kwanakin Murja ta yi yawo gidajen bokaye da malamai har kusan biyar amma duka abu ɗaya suke ce mata kamar haɗin baki, a ɗan daudu ɗanta zai ƙare rayuwarsa don aljanun da suke kanta hatsabibai ne sosai sannan ɗaukar fansa suke yi akan abin da ake yi musu ( *A lokacin da suke jikin Jamilu yaron Hannatu, an yi amfani da ayoyin Al Qur'ani ya raunata su, wasu kuma an ƙona su, hakan yasa suka ɗauki fansarsu akan Jabiru ɗan Murja* ).
Haka Murja ta haƙura har sai lokacin da Kawunta ya kira waya idan malamin da yake yi masa aiki ya dawo wanda yanzu haka shiri take yi don a jiya Kawunta ya kira waya akan ta shirya yau Zaliha ta rakota Maraba don tare za su je har da shi.
A ɓangaren Zaliha kuwa bayan shigowanta gidan Alhaji Zakari sai ta fara tsula tsiyarta yadda take so tunda ta mallake Alhaji Zakari, komai ta ce masa da sauri yake yi babu jayayya, wulaƙanci da cin mutuncin kawai take zubawa a gidan har ta Kakulle bata bari ba, kowa yi masa take yi tunda tana da wanda za ta juya tare da basa umarnin wanda take so ya wulaƙanta. Kasancewar da sassafe za su je wurin malamin kamar yadda Murja ta sanar mata, sai ta shirya tsaf! Bayan sun kammala shan roman soyayyarsu ita da Alhaji Zakari. Suna kammala karyawa sai ta shirya tare da yi ma yaranta wanka kasancewar da yaranta duka ta zo gidan bata bar ma innarta ko ɗaya ba, a cewar gwara suma su zo su dangwali arziƙi. Yaran Zaliha Huɗu ne maza biyu mata biyu, namiji ne babban ɗanta Ɗahiru wanda yake sa'an Faisal autan Hannatu sai kuma mace mai suna Baraka wacca take bi masa sai Iliyasu da Ruƙayya ƙaramarsu.
Bayan Zaliha ta shirya sai ta fito suka tafi Maraba tare da Murja daga can ko sauka daga mashin ɗin da ya kawosu basu yi ba sai suka ɗauki hanya wanda mashin ɗin Kawu na gaba nasu yana bisa har suka isa bukkar da malamin Kawu yake. Bayan sun sauka sai suka bi layi kasancewar akwai layi sosai kama daga talakawa har da masu kuɗi mazansu da matansu. Bayan layi ya zo kansu sai suka shiga ciki su ukun.
Bayan Murja ta faɗa masa maƙasudin Abi nda ke tafe dasu, madadin ya bata amsa sai ya yi shiru yana kallonta ba tare da ya ce komai. Kasancewar idanun Murja na kallon ƙasa bata san irin kallon da yake mata. Jin shirun ya yi sai Kawu ya dubi malaminsa ya ce
"Malam Dubu mun ji ka yi shiru ko akwai matsala ne?"
Sai a sannan ne Murja ta ɗago da idanunta ta ga yadda yake mata wani irin kallo wanda ta kasa fassara ko na mene ne. Sosai gabanta ya yanke ya faɗi lokaci guda tsoransa ya ɗarsu a zuciyarta, da sauri ta maida idanunta ƙasa. Sai da ya lumfasa kafin ya juya ya dubi Kawu ya ce
"A gaskiya banzan ɓoye muku ba wannan aikin ba mai yiyuwa ba ne saboda aljanun da ke jikin yaron sun fusata babu abin da zan iya musu wanda za su fita daga jikinsa, don ɗaukar fansa suka zo yi a kan ɗan matar da ta yi sanadiyyar wulaƙantarsu, ko ba haka ba ne? "
Yana duban Murja ya ƙarashe zancen. Da mamaki ta kallesa ji abin da yake faɗi.
" Ni fa malam bangane abin da kake nufi ba? "Ta yi maganar tsakaninta da Allah don ta kasa gane laifin da ta yi har ya shafi ɗanta.
" Au kin manta ke kika lalata asalin asirin da aka yi, ko bake bace? "
A ɗan zafafa ya yi maganar yana watsa mata muguwar harara. Duƙar da kanta ta yi ba tare da tace komai ba. Gyara zama Kawu ya yi yana duban malamin Dubu ya ce
"Yanzu malam Dubu baka da wani ɗan taimako ko ya yake da zai saka ya rage haukan da yake yi, har ta auransa an fasa don iyayen matar sunce bazasu aura wa ɗan daudu ƴarsu ba, malam ka taimaka"
Shiru malam Dubu ya yi yana zanari sai can ya kalli zama tare da girgiza kai kamar wanda ake yi wa wahayi. Juyowa ya yi yana duban Kawu sai ya ce
"A gaskiya ban da taimakon da zan iya yi muku a yanzu, ku yi haƙuri kawai"
Gwiwa a saɓule suka bar bukkar, Murja kuwa ta kasa tsaida hawayen da ke zuba a idanunta. A ranta sai ayyana mugayen abubuwa take yi akan yadda za ta illata rayukan yaransu Hannatu da Zaytuna, tabbas kamar yadda yaronta zai dawwama a ɗan daudu to babu shakka balle kokwanto sai ta illata musu yara illa mai munin gaske wanda har su mutu illar nan na a tattare dasu. Ta ɗaukar wa kanta alwashin sai ta bar wa su Hannatu da Zaytuna miki a cikin zukatansu wanda har su mutu suna jin raɗaɗi da zafinsa. Har suka iso gidan Kawu Murja bata bar saƙa da warwarar da take yi a cikin zuciyarta ba.
Kamar dai kullum Jabiru na nan yana surutan da ya saba marasa kangado don da alamu ba ɗan daudun kaɗai suka barsa ba har da zautar dashi suka yi. Su Murja na shiga gidan suka tarar da Jabiru na tiƙar rawa a tsakar gidan, yara sai dariya suke yi, matan gidan kuwa kamar TV haka suka ɗauki Jabiru, sai zufa yake yi kasancewar har rana ta fito. Kawu ne ya daka ma Jabiru tsawa ganin abin nashi kullum ƙaruwa yake yi ba raguwa ba. Cak! Jabiru ya tsaya daga rawar da yake yi yana kallon Kawu,can kuma ya tako daga inda yake yana tafiya iri na riƙakƙun karuwai kamar ya saka takalmi mai tsinci zuwa inda su Kawu suke.
"Haba mana! Ina cashewata a bikin babbar ƙawata Gimbiya Yalisa za ka tsayar dani! Haba kalli fa" nuna musu inda ya taso ya yi sannan ya ci gaba da cewa
"Duk ƙawayena ne ga kuma gimbiya Yalisa can tana jira na zo mu ci gaba da rawarmu"
Sakin baki Zaliha da Kawu suka yi, ita kuwa uwar gayya Murja ai kawai ta fashe da kuka har da shassheƙa don a yanzu ta tabbatar da ba kai ɗan daudu suka mayar mata da ɗa ba har da hautashi suka yi.Juyawa kawai ta yi ba tare da ta yi sallama da Kawu ba tabar gidan tana rusar kuka,biyota Zaliha ta yi a baya lokacin ta yi sallama da Kawu. Kai tsaye suka samu mashin biyu suka hau. A hanya ma sai kuka take yi kamar wata yarinyar goye har mai mashin ɗin ya gaji da kukan nata ya tambayi ko lafiya.Bata ce masa komai ba sai ta rage kukan da take yi har suka shigo layinsu. Mashin ɗinsu Zaliha ne a gaba na su Murja ba biye har cikin layin. Mamaki ne ya cikasu ganin mutane da matuƙar yawa a ƙofar gidansu har da mai unguwa da sarkin kasuwa garin da manyan mutane, ba a ma maganar mata masu leƙe ta katanga. Nan ta nan suka ce wa masu mashina su sauke, bayan sun saukesu sai suka sallamesu sannan suka ƙarasa wurin. Gaban kowa sai faɗuwa yake yi suna tunanin meke faruwa ne haka da za a tara manyan mutane da kuma ƴar gari, wani tashin hankali daya matuƙar gigita ƙwaƙwalansu shi ne *Gawawwaki* ne har biyu a kwance an rufesu da zani da alamu gawawwakin na yara ne. Kafin su ƙarasa sai yarinyar Zaliha ta rugo da gudu ta faɗa a jikin Zaliha tana matsanancin kuka duk da ƙara cin shekarun, jijjigata Zaliha take yi hankali a matuƙar tashe yana faɗin
"Baraka! Baraka lafiya waya rasu? meke faruwa ne?"
Cikin kuka Baraka ta ce... ✍️
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***