NURI

THE KINDNESS SHE NEVER EXPECTED

by @saddiqahhh



Last page nayi mistake na saka 67 instead of 68.

Suna kammala wayar ya duba mata idan akwai jirgin da zaizo kaduna from Abuja, Allah ya taimaketa akwai atake ya sai mata ticket ya tura mata suka sake maimaita maganar sannan suka yi sallama. Sai dai ya bar Ammi cikin burin son ganin yarinyar don ta tabbatar yarinyar deserves the pity da Abbie yake mata.

NURIYYA'S POV

Da safe Nabeela ta amsheta bayan ta kawo mata breakfast na awara da kunu. Da kallo ta bita duk da ta fara sakin jiki da Nabeela ammn akwai iya limit din da take son su tsaya. Sai dai ba zata iya mata musu ba don ko bakomai Nabeela shows she care. Godiya tayi mata ta amsa ta ajiye, iya kunun kawai ta iya sha. Kallon Inna dake bacci har sannan tayi bayan farkawar da tayi tsakar dare ta ishesu da wash wash cikinta likita ya sake mata wani allurar.

Can gidansu ta koma ta gyara dan dakin nasu taje ta wanke bandaki ta dibi ruwan sanyi tayi wanka. Bayan ta shirya ta dan dibarwa Inna abinda zata buqata na amfani duk da basu da wasu kaya masu yawa. Zama tayi tana jiran ayi kiran sallahn Zuhr sai baccin da ba tayi daren jiya ba yazo ya dauketa. Ba ita ta tashi ba sai around 3, a firgice ta tashi bayan ta fahimci kamar ta dade a baccin. Hannu ta kai ta murza idonta da kyau sannan ta miqe ta fita ta sake sabuwar alwala tazo ta tayar da sallar Zuhr. Addu'a sosai ta dade tana yiwa Inna da fatan nasara a aikin da za'a yi mata. Babu dadewa ta miqe ta fita zata tafi ba tare data kula kowa ba yadda ta saba sai jin muryar Maman Nabeela tayi a bayanta tana tambyarta "ya mai jiki Nuri?" Haka kawai taji wani irin kunya ya lullubeta na yadda ta shareta bayan kulawar da 'yarta ta nuna musu wanda da izninta akayi hakan.

A kunyace ta durqusa har qasa ta gaida ita wanda tunda suka shigo gidan babu wanda ta taba gaisarwa sai ranar. Da far'a sosai Mama ta amsa mata tana sake maimaita tambyar da tayi mata. Tana wasa da gefen maroon hijab dake jikinta ta amsa da "da sauqi Alhamdulillah."

"Masha Allah. Allah ya qara sauqi yasa kaffara ne.."

"Aameen Mama... Anjima za'a yi mata aiki ma." Ta samu kanta da fada duk don ta goge laifin share maman da tayi.

"Allah yasa ayi a sa'a Nuri. Qarfe nawa za'a yi sai nazo na tayaki zama..." Babu shiri ta dago tana kallon Mama, zuciyarta yayi mata wani iri kamar irin dama acikin gidan akwai wanda yake da irin wannan karar. Zuciyarta taji ya bata amsa da "kece baki bawa kowa dama ba, kin yiwa mutane jam'u kin kebance kanki daga garesu taya zaki gane mutanen ƙwarai?" Qasa tayi da kanta da sauri tana jin dama ba haka ta gina alaqar zaman da suka yi agidan ba.

"Qarfe hudu Mama bayan Asr.."

"Allah ya kaimu da rai da lafiya Nuri. Ga abinci to ki tafi muku dashi Allāh ya tsare zanyi qoqari na kammala aikin da nake da wuri sai nazo... " At this point, Nuri stood up from her crouched position. Daga jiya zuwa yau ta tabbatar akwai na Allah, akwai mutanen kirki. Matsalar daga ita ne, daga zuciyarta ne data dena yadda da kowa amman hakan ya samo asali ne daga Inna! Inna ce ta jawo ta dena yadda da mutane ganin ita da take jininta ga abinda tayi musu sannan Aunty Zakiya ma dake 'yar Inna ga abinda tayiwa Mamanta.

Nauyi taji bakinta yayi ga wani kunya daya lullubeta fiye da na dazu ta kasa budar baki tayi magana sai take ganin kamar Mama ba zata yadda da godiyar nata ba. Da kyar dai ta daure ta furta "nagode Mama... Allah ya saka da alkhairi.."

Kai Mama ta girgiza tana fara dakan yaji a turmi ta furta "Kai haba babu komai tashi ki wuce..." Dagowa tayi ta kalleta tana so ta bata haquri amman ta kasa haka tasa hannu ta dauki flask din data zuba mata abincin ta juya ta fita tana lura da yadda Maman Nusaiba take tabe baki tana hararta, yanzu ta gane Maman Nusaiba ce ta saka tayiwa mutanen gidan fahimta daya, yanzu ta gane ba duka aka taru aka zama daya ba.

Tana fita taji hawaye ya cika mata ido da sauri ta kai hannu ta goge. Ta rasa ya akayi ta zama brave ta dena kuka da. Idan akwai abinda za tace take so acikin halin data koya a past two years din ne bai wuce dauriyar dena kukan data koya ba and now, all of a sudden, she was back to being the girl who cried easily over the smallest things. It quietly occurred to her that being emotional was part of who she was, she had been born that way.

Sai data je can babban titi ta samu napep ya kaita asibitin zuciyarta cike fal da danasanin yadda ta sauya halayenta daga mai sanyin hali zuwa mai zafin hali da sam bai dace da ita ba, it didn't suit her at all. A bakin ward din ta hadu da Abbie dake waya shi da wata mace a tsaye gefensa sanye cikin wani sky blue din applique lace mai touches din blue black ta yafa metallic veil shima blue black, shigarta was very simple but yet elegant.

Qasa tayi da idanunta tana samun kanta da tafiya ahankali taji kamar an zare mata dan sauran kuzarin dake jikinta. Bata qarasa kusa dasu ba daga nesa ta samu kanta da tsugunnawa har qasa kanta a sunkuye ta bude baki da kyar ta iya cewa "Ina.. yini.." shima a rarrabe ta furta.

Tar Abbie da Ammi suka juyo suna kallonta. Lokaci daya wani irin murmushi ya wanzu kan fuskar Abbie wanda yasa Ammie fahimtar she was the girl. Wajenta Abbie ya qarasa yana cewa "oya tashi daughter tashi.." kasa miqewa tayi tana jin nauyinsa haka kawai babu dalili sai Ammi ce ta qaraso ta dagota tana cewa "zaki bata kayanki.." Bata iya kallon Ammi ba, don vividly take hango kamannin mutumin da take son mantawa dashi arayuwarta though her heart refused to cooperate with her.

"Muje ciki ko.." Abbie ya fadawa Ammi dake riqe da ita suka nufi cikin ward. Nuri dai ta rasa mene ya sameta don tafiyarta kamar me jan qafa taji jikinta duka a sanyaye. Zata so ace tana da kwarin gwiwa ta tambyeta ko ta sanshi ko kuma itace ta haifeshi amman ina, this was the last thing she could imagine herself doing. Har cikin dakin da Inna take suka qarasa, idonta biyu suka tarar da ita tare da Nabeela dake mata hira wai ya debe mata kewa. Idon Inna akansu har suka qaraso ciki tana qarewa Abbie kallo irin na tsaf dinnan. Miqewa Nabeela tayi tana basu waje don su zauna.

"Inna kin tashi?" Nuri ta tambyeta fuskarta a sake not like the way she's used to a da. Kai ta gyada mata tana kallonta muryar Ammi suka jiyo tana gaida Inna. Baki ta bude ta amsa mata haka ma Abbi daya gaisheta. Kallon Nuri tayi irin kallon nan na su waye su dinnan ta yarfe mata hannu alamar bata sani ba. Murmushi kawai Ammi dake kallonsu tayi hakama Abbie.

Suna tsaye anan sai ga nurses sunzo daukan Innar a stretcher zasu wuce da ita afara shirin surgery din. Da kallo ta bisu na mamaki kamin ta kalli Nuri tana cewa "Nuratu me za'a min?"

Bata kalleta ba don tasan Inna ta tsani harkar asibiti sam don haka tayi kamar ba taji abinda tace ba. Nurse din ta tmbya duk da tana jin jiki ammn fa ita kawai a tsorace take dasu saboda tana tunanin wancan aikin da akayi mata na koda shine duk mafarin wani ciwo dake tare da ita.

Gaba Abbi yayi ya fara fita Ammi tana kallonta tace "let's go.." Kai ta gyada mata suka rufa mata baya ita da Nabeela. Suna fita Maman Nabeela na qarasowa. Kallonta Nuri tayi ganin ashe da dagaske za tazo. Wallahi, at that moment, she felt loved. Nothing extraordinary had happened, yet she felt noticed because of the little care Maman Nabeela and Nabeela had shown her.

"Mama kinzo?" Ta tambyeta kamar irin mai neman tabbacin nan. Murmushi Mama tayi mata suna bin bayansu Abbi da nurses da suke tura Inna zuwa theater room ta furta "eh ya mai jiki da sauqi ko?"

"Alhamdulillah Mama. She's now talking ma.."

"Sannu da zuwa Mama." Nabeela ta gaida ita bayan ta basu dama sun gama magana. What she had never expected happened! She had thought she would be alone in the waiting area, waiting for Inna to come out! But here she was, surrounded by different people she barely knew. Abba and Ammi, whom she didn't know, sai Mama da Nabeela, wanda taqi bawa dama ko sau daya tun daga sanda suka zo Kaduna.Today they were all there with her as Inna underwent surgery, reassuring her and helping her to stay calm.

Ta tuna Maminta! She had never imagined that one could live in this world with their mother still alive and yet have no contact with her. Gaba daya hanyar da zasuyi communicating da Mami yanzu babu ita. Har gwara da suna dan samu shima sai afi sati biyu.

Ta tuna ranar da Mami ta basu tarihin ta, she clearly recalled Mami's statement when she said that she prayed Allah would never subject Nuri to the same fate she had endured, living all alone in the world without anyone to call her own. It was as though Nuri had inherited her mother's life. Tayi rayuwar Maminta though nata akwai banbanci, ita akwai Inna ammn her presence is not useful.

30 minutes passed, then an hour, then an hour and a half, and finally two hours, but there was still no sign of Inna. In fact, the surgery indicator light hadn't come on or given any signal even once. Hankalin Nuri yadan tashi, ta miqe tsaye tana jin wani iri kawai na dadewar da suka yi. Kamar ita suke jira sai ga blue light yayi lighting aka bude qofar suka fito kowa yana sharce gumi.

Kamin kowa yayi noticing Nuri ta nufi Inda suke "How's she doing Doctor?"

Kai ya jinjina mata yana mata murmushi yace "Your grandma is a fighter. She survived the surgery Alhamdulillah. It was successful..."

Murmushi tayi masa kawai tama kasa masa godiya sai Alhamdulillah da take ta furtawa, her face full with that hope na cigaba da rayuwa da wanda ta sani. Duk suma sauran qarasowa Inda take suka yi suna tayata murna including Ammi shi Abbi likitan yabi a baya don yaji sauran bayanan aikin da akayi.

Ammi ta riqo hannun Nuri ta zaunar da ita tana miqa mata bottle water dake hannunta tace "Take this. I've been observing you for a while. Oya, sha..." Wannan karan duk yanda bata son kallon fuskar Ammi sai data kalleta tana samun kanta da yi mata murmushi Ammi ta mayar mata da wanda yafi nata taushi mai sanyi wanda ya sake fito da zallar kamannin da take ta avoiding din gani. Qasa tayi da kanta tana assuring kanta yanzu ba time din da zata tsaya tunanin wani bane... Lokacinta yanzu na Inna ne!


To be continued...

Like, comment and share