ƊAURIN ZUCI

Chapter 39

by @maryamstar248

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 39.
    "Bansani ba ko akwai me shigen ƙaddarata, amma dai tawa ƙaddarar me nauyi ce, babbar jarabawar dana fara fuskanta tun lokacin dana san kaina ita ce rashin mahaifa, ƴan uwa da dangi, na tashi bani da mahaifa Allah yayi musu rasuwa su duka, kuma bani da yaya ko ƙanwa, ni kaɗai suka haifa kafin Allah yayi musu rasuwa.

Ni cikakkiyar balarabiyar Dubai ca, Dubai tana daga cikin wuraren da kasuwanci ya fi ƙarfi a duniyar Larabawa.
    Na ci gaba da rayuwata a inda na tsinci kaina, na tsayu ta hanyar gina kaina da ɗan ƙaramin kasuwanci ban dogara da kowa ba sai Ubangijina, ban azawa dangina nauyi ba, ni kaɗai keda kaina kamar yanda ni kaɗai nike rayuwata, ban yarda dangi da ƴan uwana ba, ina leƙa su lokaci zuwa lokaci muyi zuminci, amma hatta da karatu ban yi shi ba, nadai yi karatu akan kasuwanci, du shekara muna zuwa sauke farali domin hakan al'adar family na ne, komi ƙanƙantar yaro ana zuwa da shi gaban Ka'aba yayi ibada a lokacin azumin ramadan da kuma ƙarshen shekara lokacin aikin hajji.

A canma ban yi sake da damata ba naci gaba da kasuwancina ka'in da na'in ina nemo abunda keda sauƙi a can, wanda zaiyi wahala ko tsada a Dubai insara in tafi da shi, abin da kuma ke tsada anan ina shigo musu da shi idan na sake zuwa.
    Haka rayuwata taci gaba da tafiya, dayawa daga ƴan kasuwa sun san sunan matashiyar balarabiyar busurwa wato Rimsha Abdullah musamman mutanen Nigeria dakan shiga ƙasar Dubai domin kasuwanci, kasancewar tako ina ana damawa da ni.
    A wannan yawon nawa na kasuwanci ne Allah ya haɗa ni da wani mutum guda, wanda lokaci ɗaya ya zaunar da ni, yayi min nuni da abin da ya fi dacewa da rayuwata a matsayina na ƴa mace kuma me rauni.
   Sunan wannan mutumin Abubukar Muhammad Saminaka, na kwashe tsayin shekaru biyar ina haɗuwa da shi a aabgogin kasuwanci mabambanta amam magana bata  taɓa haɗamu ba, duda muna gane juna a yawan lokuta, maganar data fara haɗa ni da shi, wacce ta zama tsanin takawarmu har muka hau katangar da ƙaddara ta gina mana.
    Ya yi siyayya ba irin wacce ya saba yi ba, ya sayi rings na gold wanda nice wacce zan buga ma shi stam da hannuna akan receipt, a lokacin na buga stam na ɗago fuskata ƙunche da murmushi bayan na ɗage liƙabi na.
    "Muna godiya ranka ya daɗe Allah ya haɗa mu da alkairi." na faɗa da harshen larabci, da mamakina sai shima ya amsa min da yaren idon shi ƙur a kan fuskata.
   Ware idanuwana na yi a lokacin ina ƴar dariya na ce da shi.
   "Wow ma sha Allah ashe kana jin yare na, nima ina jin naka yaren amma kaɗan." na faɗa ba tare da nasan firar tamu zata yi tsayin da har alaƙa zata shiga tsakanina da shi a ranar ba.
    Daga wannan zance fira me cike da nutsuwa ta ɓarke a tsakanina da shi, yana nan a tsaye har aka bashi wajen zama ya zauna, ina aikina muna fira firar data zarce daga yarena da nashi ya shiga bani labarin al'adun ƴan Nigeria da kuma yarukan su wanda ya lissafa min wanda yake ji sosai kuma ya iya, bamu muka rabu da sai da lokacin sallah ya gabato.
   Daga wannan ranar alaƙar da banida masaniya akan sahihin lokacin ƙulluwarta ta ƙullu a tsakanina da shi, muddin yana ƙasar tofa zai kasance atare da ni na tsayin wuni, duda shima da nashi sabgogin da suka kawo shi haka ya ke jingine su gefe har sai lokacin tashina yayi daga aiki, sannan muke rabuwa.

     Cikin ƙasa da watanni biyu wata iriyar zazzafar soyayya da shaƙuwa ta shiga tsakanina da Abubakar Saminaka, har takai ga yana zuwa takanas domin ni, ya ganni muyi fira ya faɗa min ya da ya yi kewata nima na faɗa masa, ya jadadda min yanda ya ke ƙainata nima na maida martani, domin kuwa bansan wani abu wai shi ɓoye-ɓoye ba kai tsaye nike nuna zallar ƙaunar da nike yi ma shi.
       A tsarin rayuwata gaba ɗaya ban tsara yin aure nan kusa ba, amma a ranar ɗaya da Saminaka ya zaunar da ni ya fayyace min zallar ƙaunar da yake yi min, ya kuma haska min irin rayuwar daya tanadar mana nan take na kwaɗaitu da kasancewa a ƙarƙashin innuwar aurensa, musamman dana gaji da walagigi sakaka a gari, banja da nisa ba nan take na amince ma shi na kuma bashi damar ya sadu da dangina ya nemi aurena a wajen su.
    Ba tare dana sani ba ashe ƙaddarata ce da ke ƙasar Nigeria ke kirana tana yimin tuni da lokacin wanzuwarta ya gabato....

Ɗan Allah kuyi haƙuri yau update ɗin babu yawa, naso ace cikin two pages muka gama labarin nan amma Allah bai nufa, amma in sha Allah gobe zan baku da yawa, sai kun dinga yimin uzuri wallahi hidima ta gabato yanzu banda cikakkiyar nutsuwar yin typing kullum ammadai zan ƙoƙarta in sha Allahu.

Nice taku har kullum.

MARYAM STAR AMANAR BILYN-ABDUL