Page 16
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 16
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Da sauri na sunkuyar da kaina kasa ina wasa da ledar hannuna, kasa cigaba da tafiya nai na tsaya a bakin kofar toilet din.
Karasowa ciki yai sai da ya zauna akan kujera yace "dauki waccan ledar naki ne"
Bin hannun sa nai da kallo zuwa ga ledar daya ke nuna min tana ajiye akan table din, ban masa musu ba naje na dauko ledar budewa nai naga Meat pie da yogurt mai sanyi hadiyar yawu nai don dama yunwa nake ji, satar Kallonsa sa nai ganin bama ni yake kalla ba danne danne yake a system dinsa yasa ni zama a kan doguwar kujerar office din na juya masa baya na shiga shan yogurt dina Ina korawa da meat pie cikin kankanin lokaci na cinye duka sai kuma a lokacin naji kunyar yaga cewa na cinye komai.
Ina cikin tunanin yadda zan yi kawai naga hannun sa ya ajiye min kwalin magani da ruwa a Kan cinyata, bin maganin da kallo nai da mamaki ganin irin sa nake sha aduk lokacin da ciwon mara ya taso ni gaba, dauka nai na balla nasha.
Sai da na nutsu sosai sannan na sauke ajiyar zuciya na dakko waya ta dan duba tym ganin 5:40 hakan yasa na mike na dauki jaka ta, takowa nai na isa gaban table dinsa dan sassauta fuskata nai nace "Nagode Allah ya biya ka da gidan aljanna ya raba ka da iyayen ka lafia Sir, gobe insha Allah zan dawo ma da kayan"
Kallona yai yana kankance idonsa yace "me zanyi da kayan in kin dawo dashi, ko sawa zanyi?"
Sunkuyar da kaina nai nace "Sorry sir"
Tabe baki yai yace "u can go"
Ledar kayana na dauka na fita daga office din, ina fita na sauke ajiyar zuciya a hankali kuma hankalina ya dawo jikina sai na fara tunanin Mai zan cewa Umma ba in ta tambaye ni ina na samo kayan.
Kafin na isa gida Saida na samo amsar duk tambayar da nasan zata min don nasan in na fada mata Mr Wicked ne ya siya min Kaya kuma a office dinsa na chanja na mutu kawai.
Da sallama na shiga gidan da mimi na fara cin karo tana wasa da yar tsana a tsakar gida sai Umma da Aisha da alama aiki suke a kitchen, duk zuba min ido sukai suna kallona tun daga sama har kasa.
Murmushin yake nai ina hadiyar yawu cikin dauriya da kokarin saita kaina nace "Umma ina wuni ya aiki"
Karasowar kusa dani Umma tai tace "a ina kika samo kayan nan"
Dafe kaina nai nace "Umma ai yau Allah ne ya taimake ni da badan Asma'u ba da bansan yadda zanyi ba", ledar kayan nawa na bude nace "na manta ban tafi da extra pad ba gashi ina rushing wallahi Umma duk na bata kayana har hijabi na"
Hade rai Umma tai sosai tace "ba wannan na tambaye kiba ina kika samo kayan jikin ki"
Sosa gira ta nai nace "Asma'u ce ta bani sababbine ma a kayan lefen ta ta dakko sbd mamanta bata da lafia an kwantar da ita a asibiti sai ta taho da kayan ta wanda zata chanja don tana so ta kwana a gurin maman tata, sune ta bani tace sai ta koma gida ta dauko wasu"
Ganin kallon da Umma take min yasa ni marairaice wa nace "wallahi Umma ita ta bani kuma zan iya kiranta ma ki tambaye ta, nace mata ma zan tambayi Abba in ya barmu nida Aisha sai muje duba maman tata"
Ajiyar zuciya Umma ta sauke tace"Allah ya kara sauki, cire kayan toh ki wanke mata gobe ki mayar dasu"
Daga kai nai na shiga daki na chanja kaya nafito a gurin fanfo na zauna ina wanke wa ganin kayana dana wanke Wanda sukai staining sosai su suka sa Umma kwantar da hankalin ta.
Da daddare muna zaune nake tambayar Abba akan zuwa duba maman Asma'u da nake son yi bai musa min ba yace "Allah ya kaimu"
Duk da ina da lecture gobe amma karfe 2 zan dawo nasan tym din Aisha ma ta dawo daga school sai mu tafi tare gaba daya.
********
Azlan kuwa bayan barin ta office din mikewa yai yace bara yaje yaduba toilet dinsa ko ta masa kazanta a ciki, yana budewa yaji kamshin air freshener ya doki hancin sa, Dan tabe bakinsa yai har zai juya idonsa ya sauka akan sink nan yaga pant da pad da alama dai daya kawai aka taba aka bar ragowar.
Gyara tsayuwar sa yai ya dafe kansa cikin takaici yace "yanxu data bar min wannan kayan anan in wani yazo ya gani fa wani irin kallo xai min da mutuncina"
Dauko wa yai sai kuma ya samu kansa da bin pant din da kallo, sa sauri ya kauda tunanin dake neman bijiro masa ya fito hannun sa rike da pant da pad din, da sauri ya tsaya ganin Haidar tsaye a tsakiyar office din yana kallon sa.
Saurin kallon abin hannun Azlan haidar yai sai kuma ya maida duban sa gurin Azlan din da mamaki yace "Azlan mai xan gani haka meye kake yi da kayan mata"
Hade rai Azlan yai ya nufi kan table dinsa yana boye pant din a gefen rigar sa, haka kurin ya samu kansa da kin son haidar din ya ga pant din, janyo jakar sa yai ya sa pant da pad din sannan ya juyo gurin Haidar daya saki baki yana kallon sa.
Kara hade rai yai yace "taya zaka shigo min office ba tare da sanarwa ba"
Dan tsaki Haidar yai yace "me kake yi da kayan mata Azlan nidai a iya sanina baka hulda da Mata"
Lasar lip dinsa yai yana kankance ido yace "budurwa ta ce take jini shine na siyo mata ko da magana ne?"
Hangane baki Haidar yai yace "budurwa kuma yaushe kayi budurwa?"
***