Page 17
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 17
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Jakar sa ya dauka yace "tunda ga zubairu komai sai na fada muku”, ya karashe yana dage girar sa guda daya.
Girgiza kai Haidar yai yasan karya Azlan ke masa ba wata budurwa da yai amma kuma mai pant da pad suke a office dinsa.
Zama Haidar yai yace "biyo wa nai ta hanyar shine nace bara nazo mu gaisa Naga yadda Azlan yake lecturing".
Dan tsaki yai yana sosa girar sa ya lashi jajayen lips dinsa yace "bari kawai na gaji so nake nayi na bar aikin amma hakan baxai yiwu ba don nayi ma Baffa alkawarin ban barin aikin sai da yaddar Abie", ajiyar zuciya ya sauke yace "kuma kasan Abie baxai taba yadda na bar shi ba ga aikin company nidai an maida ni kamar engine."
Dariya Haidar yai yace "hakuri zakai mutumin, Ka ki fito da mata daka fito da ita da duk ba haka ba"
Kankance ido yai yace "ban shirya rabuwa da budurci naba, kai nifa ba wannan ba kunya ma nake ji ace inyi aure ina aure kowa yasan Mai zan dinga yi."
Kalkalewa da dariya Haidar yai har yana rike cikin sa yace "na shiga uku ni Haidar dama da abinda Oga Azlan yake jin kunyar sa."
Dan hade rai yai kadan yana kokarin hana kansa murmushi yace "eh mana gashi Ka gani kuwa, wai dama wa yace muku bani da kunya ni ko hannun mace kunyar rike wa nake."
Sai da suka gama Wasa da dariya sannan Haidar yace "kar na manta mutumina maganar aurena kasan saura wata daya, mai dame kake tunanin zamuyi su dai tace min zasuyi kamu da walima ni kuma ina son muyi dinner da."
Karkada kafa Azlan yai yana yamutsa fuska yace "meye kuma dinner?"
Harara Haidar ya watsa masa yace "baka da kirki wallahi Azlan don Allah ni Ka maida hankali muyi magana kasan kaine amini na da kai kawai nake shawara kuma nasan halin ka zan iya hadawa kace baxa kaba."
Kafadar sa ya daga yace "kadan daga aikin kenan, amma zanje ai taka ce mune a gaba gaba gurin cin cake."
Yadda yai maganar yasa Haidar dariya, sun dade suna tattauna sai da aka Kira magriba sannan suka fito kowa ya shiga motar sa ya tafi gida.
Gidan Baffa ya nufa don ya dade bai je ba, a Palour ya same sa yana zaune yana Jan carbi idonsa akan Sunna TV, shigowa yai bakinsa dauke da sallama.
Dagowa Baffa yai ya sakar masa murmushi yace "sannu da zuwa Zaki"
Shima dan gajeran murmushin ya saki ya zauna a kasa kusa da kafar Baffa yace "barka da dare tsoho"
Murmushi shinfide akan fuskar Baffa yace "barka kadai gauro mai tsoron Mata"
Wani miskilin murmushi yai yana shafa gashin bakinsa yace "Uhmm tsoho kenan bara dai nai shiru kar kace Banda kunya amma da nace wani abu"
Dariya Baffa yai yace "Zaki Allah ya shirye ka, amma ya kamata Ka duba kaga kullum girma kake ko baka so na dauki gudan jinin kane kafin na mutu."
Yamutsa fuska yai yace "tsoho meye kuma haka ana magana zaka kawo zancen mutuwa."
Murmushi Baffa yai yace "mutuwa dole ce ai Zaki, kuma tunata wajibi ne ga duk mai Imani."
Shiru yai kawai ya lumshe idonsa sai kuma ya shiga tunanin wannan mara kunyar yarinyar yadda bakin ta ya mutu, baiyi tunanin wani Abu zai iya sata ta shiga hankalin taba sai gashi ta nutsu ko harara batai masa ba.
Baffa daya zuba masa ido yana ganin yadda yake ta murmushi yace "lafia Zaki tunanin wa kake haka yau"
Mikewa yai daga kishingiden da yake yace "sirri ne tsoho, in na fada ma zaka ce na zama Dan iska toh gwanda nai Shiru."
Binsa da kallo Baffa yai ganin ya koma kan kujera ya kwanta, da mamaki yace "anan zaka kwana ne?"
Daga masa kai kawai yai ya lumshe idonsa fahimtar hakan yasa Baffa sanin cewa Yan miskilancin ne suka motsa knn, shima Shiru yai amma yana cikin tunanin mafita akan maganar da Mummy tazo masa da shi.
Tazo masa da maganar auren Zainab da Azlan dinne daya nuna mata kin hadin sbd abinda Azlan yace sai ta sa masa kuka tace taga kamar baya so ayi auren ne kuma gashi zainab din kullum cikin kuka take sbd son da take ma shi Azlan din, shiyasa duk ya rasa yadda zaiyi yana bukatar tunani sosai tunda Azlan yace baya so yasan ya fada ne har cikin ransa kuma shi ya fada mata baxai ma Azlan dole ba in har ya Kara tuntubar sa akan maganar yace baya so toh Zainab dn tayi hakuri ta fidda miji a cikin masu sonta.
************
Tafawa sukai kamar kawaye cikin farin ciki Zainab tace "Mummy naji dadi amma sosai wallahi ba ta biyun ki Mummy, ni nasan dama tunda kika ce na kwantar da hankalina kamar na gama Zama matar Ya Azlan ce kawai."
Murmushi Mummy tai itama tana sa kazar data yaga a baki tace "ai sai da na tabbatar na fada masa yadda jikin sa zaiyi sanyi sannan na tafi, haka kurin"
Saudat ce kanwar Zainab da ta zuba musu ido tace "wallahi Ya Zainab da nice ke hakura zanyi da shi, ya Azlan yace baya sonki Amma kin dage ke dole sai kin tusa kanki rayuwar sa a haka zai soki ana cusa masa ke"
Wurga mata jarkar ruwa Mummy tai tace "rufemin baki munafukar banxa ke na rasa wani irin Hali ne dake maimakon ki taya yar uwar ki neman abinda take so Amma so kike ki sanyaya mata gwiwa"
Tsaki Zainab tai tace "wallahi Mummy wannan Yarinyar kamar bake kika haife taba kwatakwata bata hawa hanyar abinda kike dorata akai shegia kawai"
Mikewa saudat tai tana turo baki ta fita daga palourn tana musu fatan shirya don tana jin Mummy na dada fadawa Zainab in Azlan din yaki yadda ma gurin malamai zasu Kaisa.
********
Mun fito daga lecture kenan kafin mu shiga wata na yi sauri na nufi office dinsa hannuna rike da ledar kayan sa dana saka aciki, a hankali nayi knocking sai da nayi knocking sau uku sannan naji ance "come in"
Tura kofar nai na shiga da sallama yana zaune akan kujera hankalin sa na kan laptop din kan table dinsa da yake sarrafawa sai kuma wadannan da suka taba tareni ahanya su uku ne amma ynxu da alama assignment suka zo submitting don naga papers a hannun dayar.
Dauke kaina nai daga kansu na nufi table din gaba na Yana faduwa.
Su Zuby kuwa zuba mata ido sukai cike da bakin ciki, ji take kamar ta janyo ta ta shake, tun dazu suka zo submitting assignment din da ya basu tunda yace su ajiye a gurin bai Kara daga kai ya kalle suba, ita kuma zuby sai tambaya take masa akan course din wani zai bata ansa ne wani kuma banxa yake mata.
Cikin nutsuwa da saurin maganar da nake yi nace "Good Morning Sir"
Dagowa yai daga aikin da yake yi ya kalle ta tana sanye da doguwar riga mai budewa sai mayafi data yafa a kanta ta rufe sosai har kirjin ta.
Hade rai yai haka kurin ya soma tunanin haka ta shigo school da wannan shigar duk da rigar budaddadiya ce amma sam ransa bai masa dadi ba ganin ta a haka ba hijab.
Kara hade rai yai yace "mai yasa baki sa Hijab ba yau"
Dan ware ido nai na kalli jikina sai na kalle sa da mamakin Jin tambayar sa.
Ganin yadda tai ne yasa shi kara hade rai kawai samun kansa yai wani bacin rai yana lullube sa.
Ni kuwa duk da maganar sa ta ban mamaki amma haka na kanne a raina ina fadin ji wata gulma kuma meye hadin sa da Hijab dina.
Ledar na ajiye akan table din nace “sir ga kayan na gode Allah ya saka da alkhairi”.
Dan kallon ta yai ya kalli ledar sai kuma yayi baya da jikin sa akan kujerar kafin ya mike cikin takunsa na cikakken namiji kuma lafiyayye ya karasa gaban ta ya tura hannun sa cikin aljihun wandon jikin sa.
Dan baya nai gaba na Yana faduwa sbd kusancin mu dayai yawa, hade rai ya sake yi cikin muryar sa mai zurfi yace "ce miki nai ki dawo min da su"
Kamar zanyi kuka nace "Sir toh ai ba nawa bane kuma cema Umma nai friend dita ce ta bani in na ce mata kaine kaban kashe ni zatai inaga"
Tsayuwar sa ya gyara yace "dauki ki mayar dasu na ki ne ai ko so kike na dinga sawa ne ina yawo, haka kika bar min kayan kazantar ki a toilet ynxu da wani ya gani fa"
Da sauri na sunkuyar da kaina kasa cikin kunyar maganar sa, cikin lallashi nace "sir toh gashi na dawo dasu"
Daga kafada yai yace "baxan karba ba in nayi kyauta bana karba ragowar kayan naki ma suna jaka ta," juyawa yau ya bude jakar ya fito da pant da pad din tsirara ya miko min
Kallon hannun sa nai ganin abinda yake miko min yasa ni juya masa baya da sauri nace "na shiga uku"
Wani murmushi ne ya subuce masa da bai shirya masa ba.
Su Zuby da dukkan su suka hangame baki suna kallon ikon Allah da sauri Nana ta tabo Zuby ganin hawaye na zubo Mata, ajiye papers din Tai kawai na nufi kofa tana fashewa da kuka, suna su Nanan baya suka mara Mata da sauri.
Suna fita na juyo kamar zanyi kuka nace "sir ynxu me zasuyi tunani kace na bar kayana a toilet kuma Ka dakko wannan abun"
Kankance ido yai yace "ke me kike tunani badai kina tunanin wasu manyan abubuwa ba kwaila da ke har kin iya wannan tunanin"
Zaro ido nai ina kama baki na nace "sir" sai kuma na ajiye masa ledar na juya cikin sauri na fita.
Shima idonsa ya zaro ganin yadda mazaunai suke rawa sbd sassarfar datai, cikin mamaki yace badai yarinyar nan ciko take ba, Tabe baki yai yana fadin kai kuma meye naka Azlan.
Komawa yai ya zauna amma sai ya kasa aikin masa kawai tunanin yadda take yawo a school ba Hijab yake Maza suna kallon ta.
************
Uku saura na karasa gida a gajiye nai wanka naci abinci Sannan na shirya cikin riga da skirt simple style na yafa babban mayafi na rufe jikina, Aisha ma data sa irn kayana itama mayafin ta yafa.
Mimi nake sawa takalmi data dage akan sai ta rakani hadda birguma a akasa dole na shirya ta itama.
Mikewa bai bayan na gama samata takalmin na kalli Umma da take cewa kar mu manta mu tsaya mu siya mata fruits na dubiya daga Kai nai nace "Insha Allah Umma baxa mu manta ba"
Muna fitowa daga gidan mukai kicibus da cilla a daidaita zai wuce, tsayawa yai ya sakko yace "uwar dakina barka da wannan lokacin"
Murmushi nai don Allah ya sani kwana biyu nayi missing cilla don ma kusan kullum sai munyi magana ta WhatsApp, daga kai nai ina kallon sa yana ma Mimi magana suna dariya.
Kallon adaidaitar nai nace "ina Ka sami adaidaita cilla"
Dariya yai yace "ta Nasiru ce ya ban nadan yawata Nima a ciki ynxu xan fita ma mu gwada sa'ar mu"
Murmushi nai cilla yana burgeni sam bashi da matacciyar zuciya yana da zuciyar nema sosai, cikin Raha nace "toh muje mu zaka fara dauka asibiti muka nufa duba maman Asma'u"
Adaidaitar ya shiga yace "Bismillah uwar dakina shigo muje Allah sarki Nima na samu na duba ta"
Ciki muka shiga muna hira har muka isa asibitun bayan mun tsaya na sai musu kayan fruits na 2k din da Abba ya bayar.
Cikin asibitin muka nufa cilla na rike da ledar ni kuma ina rike da hannun Mimi, kasancewar Asma'u ta fada min number din dakin yasa bamu sha wuya ba gurin Nemo dakin.
Knocking mukai aka bamu izinin shiga muka shiga cilla kuma ya tsaya a waje tukun, ba mutane da yawa a dakin daga maman tasu dake zaune akan gado sai Asma'u sai wani namiji da kallo daya zaka mai kasan yayan Asma'u ne.
Cikin girmamawa muka tsugunna har kasa muka gaishe da maman Asma'u da tambayar ta ya jiki, cikin sakin fuska ta amsa mana.
Kallon Asma'u nai wacce tun shigowar mu ta kafe Mimi da ido cike da al'ajabi murmushi na sakar mata nace "Asma'u ya mai jikin ALLAH ya Kara sauki"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "da sauki Batul jikin Alhamdulillah anjima ma za'a sallame mu"
Masha Allah na fada ina gyara zamana don duk a takure nake sbd kallon da Yayan Asma'u yake min, Mimi ce dake Kan cinyata tace "Maa mun bar uncle a waje fah"
Dan bude baki nai na kalli Asma'u da kanta ya Kara daurewa Jin sunan da Mimi ta cemin nace "Asma'u tare muke da cilla shima yace zai duba jikin mama yana waje"
Ita ta shigo dashi shima yai mata ya jiki sannan muka mike bayan na ajiye mata ledar kayan Fruits din, sallama mukai wa Maman tasu ita kuma ta rako mu waje.
Rike hannun Mimi tai tace "wannan ma kanwar kice amma bakwa kama sam ni wallahi da Mr Azlan ma take min kama sosai kamar an tsaga Kara"
Duk da gabana ya fadi Jin sunan Wanda ta ambata amma hakan daure nace "Yata ce fa ni na haife ta"
Wani ja tai ta tsaya tana kallona sai kuma ta kalli Mimi tace "yar kice bana son wasa don Allah"
Murmushi nai ina cigaba da tafiya nace "wallahi yata ce kinji ma na rantse"
Da mamaki sosai tace "dama kin taba aure"
Shiru nai kawai ban mata magana ba ina kokarin controling mood dina har muka karasa gurin adaidaitan, shiga mukai nayi Mata sallama mukai gaba.
Har kofar gida cilla ya maida mu sannan na basa kudin motar, dakyar ya karba da yace baxai karba ba sai da na bata rai sannan ya Karba yana dariya.
Washe gari da wuri na tashi don karfe 9 muke da lecture, amma sai Mimi ta tashi da rigima itama akan sai ta bini tunda an musu hutun boko da islamiyya duk yadda na rarrashe ta kin yadda tai hadda birgima akasa tana ihun wayyo Maaa ta daina sonta.
Kamar zanyi kuka na kalli Umma da tai kamar bata San muna yi ba, dole na shirya ta cikin doguwar rigar atampa na sa Mata baby hijab ba karamin kyau tai ba kamar ka saceta bama baby hijab din daya kasance dark blue sai ya haska fatar ta sosai.
Kudin kashewa na kara tunda da Mimi zanje ai nasan dole na tafi da kudi don Mimi bata shiri da yunwa.
Sallama mukai wa Umma da take dariya a ranta kuma tausayin Batul ne fal, murmushi tai tana binsu da addu'a.
A adaidaita sai da na gama ja Mata kunne akan Banda suruta kuma ban yarda ta yiwa kowa magana ba ba ruwan ta da mutane ita dai daga min kai kawai take bakin ta kamar zai tsage sbd murnar zan tafi da ita school dinmu itama.
Lokacin da muka isa har 9 ta kusa hakan yasa ni sauri ina rike hannun Mimi, sakin hannu na tai tana dariya tai gaba tana fadin "Nima zan iya MAA mu tafi toh"
Mun kusa zuwa hall dinmu sbd lecture din Mr Wicked ne shiyasa nake saurin zuwa don kar ya rigani shiga, da sauri na juyi Jin Mimi ta saki Kara a razane na kalli wanda ta bangaja din ina baya kamar zan fadi gabana yana tsanan ta bugawa.
Sir Azlan da yake tahowa hankali sa na kan wayar sa sbd wani sako da yake dubawa yasa bai San da mutum a gaban sa ba kawai sai ihun yarinya yai, da sauri ya sa wayar a aljihun sa yana sa hannu ya dago Yarinyar data sunkuya tana duba hannun ta data bige san da shi, wani irin bugawa kirjin sa yai da karfi sanadin arba da fuskar yarinyar da yai............
***