Chapter 32
by @umsar
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 32
Nihla ba su shiga Kano ba sai wajen ƙarfe uku na yamma. Tana kwance a bayan mota kamar mai bacci, amma a zahiri idonta biyu. Tana cikin tunani, tana ta tufka da warwara, yayin da kalaman Irfan suka ƙi barin zuciyarta.
Aliyu ma ya fara tunanin ko ba ta da lafiya, saboda yadda ta yi shiru tun suna kan hanya.
Da suka isa kano, Fatima suka fara saukewa, sannan suka taho gida.
Wannan karon Nihla ba ta ga Baba Idi ba. Wani sabon mutum ta gani daban. Mutumin ya gaisa da Aliyu, ita ma ta gaida shi, ya amsa mata cikin fara'a. Yana da ɗan kama da Baba Idi, sai dai bai kai shi shekaru ba.
"Baba Ado, taimaka ka shigar mana da kayanmu," Aliyu ya faɗa yana kallon mutumin.
Nihla dai ta wuce gaba ta shige cikin gidan.
Falon babu kowa. Gidan ya yi shiru kamar babu mutane a cikinsa.
Kai tsaye ɗakin Hajiya mama ta shiga, amma ba ta same ta ba. Ta dawo falon, ta nufi kitchen, amma Hajiya ba ta nan. Sai Baba Jummai da Baba Asabe kawai ta tarar.
"Ya na ji gidan shiru haka? Ko masu gidan ba su nan?"
Baba Jummai ta kalleta da fara'a.
" har Kun Karaso kenan,Ba kowa a gidan nan. Sun tafi Bebeji. Abokin babanku ne ya rasu, shi ne suka tafi gaba ɗaya."
Nihla ta gyada kai, sannan ta koma ɗakinta.
Ta shiga wanka, ta sauya kayanta zuwa na gida, sannan ta zauna a gefen gadonta.
Bayan ɗan lokaci, Baba Jummai ta leƙo ta tambayeta:
"Nihla, a kawo miki abinci ko sai anjima?"
"Baba Jummai, sai anjima zan ci. Kafin nan na san su ma sun dawo."
"Madalla."
Daga haka Baba Jummai ta juya ta fice, ta ci gaba da aikinta.
Nihla kuwa ta ɗauko wayarta, ta shiga TikTok, tana kallon wasu abubuwa ko zai ɗan rage mata tunanin da ya cika mata kai.
Ta fara kallon bidiyoyin da ke gabanta. Wani lokaci tana murmushi kaɗan, wani lokacin kuma ta tsallake bidiyon ba tare da kalle shi sosai ba.
Amma duk ƙoƙarinta na kawar da tunanin Irfan bai yi tasiri ba. Kamar dai tunanin ya zauna ne a wani wuri na musamman a zuciyarta.
Ta kashe TikTok ɗin, ta koma WhatsApp.
Nan take idonta ya sauka kan sunan IRFAN.
Ta ɗan tsaya.
Yatsarta ta kai kan sunan, amma sai ta janye ta.
"Me nake shirin yi kuma?"
Ta ajiye wayar a gefenta, ta kwanta tana kallon silin ɗakin.
Sai dai bayan ƴan mintuna, ta kasa jurewa. Ta sake ɗaukar wayar, ta shiga chat ɗinsa.
Saƙon da ta tura masa da safe yana nan a ƙarshe, babu wata amsa daga gare shi.
Zuciyarta ta ɗan motsa.
"Har yanzu bai gani ba?"
Ta sake duba lokacin da aka aika saƙon, sannan ta lumshe idanunta.
A wannan karon, abin da ya fi damunta shi ne rashin jin ta bakinsa tun safiyar yau.
Ba ta san me ya faru da shi ba, amma wani irin rashin natsuwa ya fara mamaye ta.
Ta sake ajiye wayar, tana ƙoƙarin Hana tunaninshi tasirii.
Amma zuciyarta ta ƙi Bata hadin kai.
Su Hajiya Mama ba su dawo ba sai bayan sallar Magariba.
Nihla tana kwance a ɗakinta lokacin da ta ji ƙarar horn ɗin motarsu. Nan take ta miƙe ta nufi falo cikin sauri har tana hadawa da Dan gudu.
Hafiz ne mutum na farko da ta fara cin karo da shi. Cikin murna suka rungume juna.
Jafar ya ƙaraso, yana kallon ta cikin murmushi.
"Ga manyan ɗalibai, ƴan matan jami'a!"
Dariya Nihla ta yi, sannan ta saki Hafiz ta koma wajen Jafar ɗin.
Hajiya ce karshen fitowa daga motar, sai Yaya Babba ya biyo bayanta.
Nihla ta kalli Hajiya.
"Amma Hajiya, kun san zan dawo yau. Me ya sa gaba ɗaya kuka fita?"
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa.
Kafin Hajiya ta samu damar amsa mata, Aminu ya ce:
"Sorry, Auta. Laifin Babban Yaya ne. Shi ne ya ce sai an yi tafiyar Nan yau."
Nihla ta saci kallon Yaya Babba, sannan ta risina tana gaida shi.
Ya amsa mata tare da tambayarta karatunta. cikin gidan ya shige.
"Wato mu kika raina kenan? Ba za ki iya gaishe da mu ba ko?"
Jafar ya faɗa cikin zolaya.
Dariya Nihla ta yi, ta kai masa ɗan duka.
Daga nan gaba ɗayansu suka dunƙuma suka shiga cikin gidan.
alwala suka yi. Yaya Babba ya jagorance su wajen yin sallar Magariba a falon gidan, domin ba su samu damar yin ta a hanya ba.
Suna idar da sallar, Yaya Babba ya miƙe ya fice, yayin da sauran suka zauna a falon suka buɗe babin hira da labaran makaranta.
Kowa yana ba da nasa labarin, har lokaci ya yi nisa ba tare da sun ankara ba.
Har ƙarfe goma sha ɗaya na dare suka Kai, sallar Isha ma a falon sukayi ta, Basu samu zuwa masallaci ba.
Zaman da Nihla ta yi tare da ƴan uwanta ya taimaka mata ta ɗan manta da damuwar da take ciki. Da ta shiga ɗakinta, ta kwanta a kan gadonta.
Gajiyar da ta kwaso da Kuma zaman mota shi yasa bacci ya dauketa da wuri.
Umsar ✍️