KADDARAR ZUCIYA

THE FIRST WOUND

by @jiddaahbarkum

KADDARAR ZUCIYA

CHAPTER FORTY-ONE: 41

THE FIRST WOUND!

JIDDAAH BARKUM

———

Umar yana bin bangon a hankali yayin da yake nisa daga ƙofar kitchen ɗin, amma zuciyarsa tana nan a wajen, kowane kuka da roƙon da Nana take yi wa Inteesar yana ratsawa har cikin ƙasusuwansa, kalaman Nana na cewa, “Ki haifa mana yara da za su faranta wa Umar rai… tunda ni har yanzu shiru nake ji,” sun daki ƙirjinsa da wani irin ƙarfi da ya sa ya ji kamar an ɗora masa dutse a zuciya, he felt a deep sense of pain, ya rasa abin da zai yi da kansa, bai taɓa tunanin Nana za ta kai ga wannan matsayi ba, har ta roƙi inteesar da ta haifa mata yara domin ta faranta wa mijinta rai, yana jin alamar Inteesar za ta fito daga kitchen ɗin saboda yadda shirun ya yi yawa, Umar bai tsaya ba, to avoid any awkward confrontation, ya juya da sauri, ya nufi babban ɗakin karatunsa (study room) da ke ƙasan gidan, ya tura ƙofar ya shiga, sannan ya rufe ta a hankali, bayan haka, ya jingina da ƙofar yana sauke numfashi mai nauyi, idanunsa a lumshe, a wannan lokacin, zuciyarsa cike take da raɗaɗin da bai san yadda zai bayyana shi ba.

Gaba ɗaya jikin Inteesar ya yi sanyi, tamkar an tsiyaye mata jini, ba ta iya cewa uffan ba ga Nana, kuma ta kasa jurewa irin wannan babban roƙon da aka yi mata, a hankali ta janye hannunta, sannan ta fito daga kitchen ɗin da sauri, tana nufar sama kai tsaye zuwa ɗakinta, saboda saurin da take yi, tare da ƙwallar da ta cika idanunta, ba ta ankara cewa Umar yana gidan ba, balle ta san cewa ya riga ya shige study room, Nana kuwa ba ta iya jure ganin Inteesar ta gudu tana kuka ba, ta bi bayanta da sauri har zuwa saman bene, sannan ta tura ƙofar ɗakin Inteesar ta shiga a hankali, ta tarar da Inteesar ta faɗa kan gado, tana kuka sosai cikin tsantsar raɗaɗi, ganin haka ya sa zuciyar Nana ta ƙara karyewa, ta ƙaraso cikin sanyin murya, ta zauna a gefen gadon, tana ƙoƙarin taɓa kafaɗar ƙanwar tata domin rarrashinta, “Inteesar, ki yi haƙuri don Allah, ba don na ɓata miki rai na faɗi haka ba, tsantsar ƙauna ce da kuma yarda da nake da ita a tsakaninmu,” nan take, Inteesar ta tashi zaune da sauri, ta goge hawayen fuskarta, sannan ta dubi Nana kai tsaye, idanunta sun yi jajir, yayin da muryarta ke rawa saboda ɓacin rai, “Yaya Nana, don Allah ya isa haka! Idan har kika sake yi mini irin wannan maganar, ko kika ƙara kawo batun Yaya Umar a tsakanina da ke, wallahi zan kwashe kayana na bar miki gidan nan gaba ɗaya!” Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta, kafin ta ci gaba cikin tsananin damuwa, “Ta yaya ma za ki riƙa tunanin zan auri Yaya Umar? Don Allah, kada ki sake yi mini wannan maganar! Kamar yadda kika san babu aure tsakanina da Khalil, ina tabbatar miki cewa ni da Yaya Umar ma babu aure a tsakaninmu har abada! Shi ɗayan yayana ne, kuma mijin yayata, don Allah, ya isa haka!” Nana ta tsaya cak, kalaman Inteesar sun same ta a inda ba ta zata ba, ta dubi ƙanwar tata, tana kallon yadda ƙirjinta ke bugawa saboda tsananin ɓacin rai, a wannan lokacin, Nana ta fahimci cewa ta wuce iyaka, ganin irin tashin hankalin da Inteesar ta shiga ya sa jikinta ya yi sanyi, ta gane cewa ci gaba da wannan magana zai iya jawo babbar matsala a tsakaninsu, ta matso a hankali, ta zauna sosai a gefen gadon, sannan ta janyo Inteesar jikinta ta rungume ta, “Haba, Intee, ki yi haƙuri don Allah, shikenan, na daina, ba zan sake yi miki irin wannan maganar ba har abada, ki yi haƙuri ki bar fushin nan haka, kin san ba na son ganin ki cikin damuwa,” Nana ta faɗa cikin muryar lallashi mai sanyaya rai, Inteesar ta ɗan saki jikinta a hankali, kukan da take yi ya fara tsagaitawa yayin da dumin rungumar Nana da kalamanta na rarrashi suka fara sanyaya mata zuciya, Nana ta ƙara matse ta a jikinta, tana shafa bayanta a hankali har sai da ta ji numfashin ƙanwar tata ya fara dawowa daidai, “Shikenan, Princess, komai ya wuce,” Nana ta faɗa cikin muryar lallashi, “Yanzu tashi mu koma kitchen mu ƙarasa haɗa breakfast ɗinmu, ko?” Inteesar ta ɗaga kanta a hankali, alamar ta amince, ta goge sauran hawayen da ke fuskarta, sannan suka tashi tare, Nana ta riƙe hannunta yayin da suka sauko zuwa falon ƙasa, suna shigowa falon, sai suka tarar da Yaya Umar zaune a kan kujera, yana riƙe da wayarsa a hannu, fuskarsa cike take da natsuwa, tamkar bai san an yi wata rigima ko kaɗan a gidan ba, he acted completely oblivious to the intense argument that had just taken place, kamar an umarce shi, Umar ya ɗaga idanunsa a hankali lokacin da ya ji takun takalmansu, ya bi su da wani irin kallo mai zurfi da bincike, yana lura da yadda idanun Inteesar suka yi jawur, da kuma yadda Nana ke manne da ita, kallon ya ɗauki daƙiƙu kaɗan kafin ya janye idanunsa a hankali, ba tare da ya ce uffan ba, ya sake mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan wayarsa, wani irin silent tension ne ya ratsa falon, Nana da Inteesar kuwa ba su tsaya ba, suka wuce kai tsaye zuwa kitchen domin ƙarasa abin da suka bari.

Bayan sun kammala haɗa abincin safe, suka fito da shi zuwa falon ƙasa, suka jera komai a kan dining table, sannan Inteesar ta dubi Nana cikin sanyin murya, “Yaya Nana, zan koma ɗaki na ɗan kwanta,” ba ta jira amsar kowa ba, ta juya ta yi sama, domin a wannan lokacin tana buƙatar samun sarari ita kaɗai, Nana ba ta ce mata uffan ba, ba ta son sake takura mata bayan abin da ya faru, don haka ta kyale ta ta tafi, sai dai bayan ɗan lokaci, ta haɗa wa Inteesar abincinta daban a cikin tray, sannan ta ɗauka ta bi bayanta zuwa sama domin tabbatar da cewa ta ci wani abu, a duk wannan lokacin, Umar yana zaune a wurin yana kallon kowane motsinsu ba tare da ya ce uffan ba, idanunsa kawai ke binsu tun daga fitowarsu daga kitchen, zuwa lokacin da Inteesar ta hau sama, har zuwa lokacin da Nana ta ɗauki tray ta bi bayanta, bayan sun ɓace daga ganinsa, ya mayar da hankalinsa kan wayarsa, amma zuciyarsa ba ta samun natsuwa, kalaman da ya ji a kitchen ɗin sun ci gaba da yawo a cikin kansa.

Bayan Nana ta ajiye mata abinci ta fita, Inteesar ta tsinci kanta cikin tsantsar kewar Aliyu, a wannan lokacin, tana buƙatar jin muryarsa fiye da komai, tana son ta ji yadda yake kiranta da sunayen soyayyarsa, watakila hakan zai taimaka wajen rage nauyin da ke ƙirjinta, ta lallaba ta ɗauki wayarta, sannan ta danna lambarsa, tana jiran ya ɗaga, zuciyarta na cike da wani irin fata na samun kwanciyar hankali daga gare shi, wayar tana fara ringing, sai aka ɗaga cikin sauri, ba ta jira komai ba, ta canza muryarta zuwa ta shagwaɓa, tana nuna tsantsar ƙaunar da take masa, “Mi Amor…” Maimakon ta ji muryarsa mai daɗi, sai ta ji sautin muryar wata mace daga ɗayan ɓangaren wayar, matar ta saki wani ɗan gajeren murmushi mai nuna nutsuwa, sannan ta ce cikin sanyin murya, “Sorry fa… ya shiga wankan Sunnah ne yanzu, ki jira ya fito, ko?” Nan da nan, Inteesar ta ji wani abu mai nauyi da zafi ya daki ƙirjinta, jikinta ya ɗauki rawa, numfashinta ya tsaya na ɗan lokaci saboda tsananin kaɗuwa da ɓacin rai, ba tare da ta iya cewa uffan ba, ta katse wayar, ta jefa wayar a kan gado, sannan ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya, tana ƙoƙarin fahimtar abin da ta ji, gaba ɗaya duniyarta ta rikice, ta yi shiru, idanunta a zare, tana kallon wayar da ta ajiye kamar za ta sake magana da kanta, wankan Sunnah? Kalaman matar suka sake maimaituwa a cikin kunnenta, ya shiga wankan Sunnah ne yanzu… Ta lumshe idanunta da ƙarfi, amma hakan bai hana kalaman su ci gaba da ratsawa cikin zuciyarta ba, raɗaɗi ya ratsa duk wata jijiya ta jikinta, ruɗani, kishi da ɓacin rai suka haɗu lokaci guda, suka mamaye tunaninta, ta tuna yadda ta kira shi da Mi Amor, cikin muryar da ke ɗauke da ƙauna da kewar da take masa, amma a maimakon ta ji amsarsa, sai wata mace ta ɗauki wayarsa, tana magana cikin nutsuwa, kamar wannan abu ne da ya saba faruwa a rayuwarta, wata mata da take tare da shi, wata mata da ta san inda yake, abin da yake yi, da kuma lokacin da zai fito, Inteesar ta haɗiye wani abu mai nauyi a maƙogwaronta, ba ta ko kalli tray ɗin abincin da Nana ta kawo mata ba, cikin sauri, ta cusa kanta a kan pillow, ta matse shi da dukkan ƙarfinta, sannan ta fashe da wani sabon kukan kishi mai cin rai, kuka take yi na fitar rai, tana jin kamar zuciyarta za ta fito saboda yadda take bugawa da sauri, a wannan lokacin, ba ta ma san ko abin da ya fi ɓata mata rai shi ne jin muryar matar, ko kuma yadda wannan ƙaramin abu ya tuna mata da gaskiyar da take ƙoƙarin kauce wa tun ranar da ta amince da Aliyu, ta san yana da mata biyu, ta san tana shirin zama matarsa ta uku, ta san cewa rayuwarsa ba za ta tsaya a kanta ita kaɗai ba, amma sanin hakan a baki ya bambanta da lokacin da za ta fuskanci gaskiyar da idonta da kunnenta, har yanzu ba ta taɓa jin zafin hakan sosai ba sai a wannan safiyar, a hankali, ta ɗaga kanta daga kan pillow, tana share hawayenta da bayan hannu, ta kalli wayarta da ke kwance a kan gadon, amma duk yadda ta yi, ba ta iya mantawa da kalmar da matar ta yi amfani da ita ba, “Ya shiga wankan Sunnah ne yanzu,” kalma ɗaya kawai ce, amma ta isa ta buɗe wani sabon ƙofa na tsoro a zuciyar Inteesar, duk wani tsoron abin da zai iya faruwa a gaba ya ninke a ranta, ta fara jin cewa ƙaddararta tana neman sauyawa zuwa wata babbar jarrabawa mai wuyar sha’ani, domin a wannan karon, ba tunani kawai take yi game da matan Aliyu ba, ta ji ɗaya daga cikinsu, ta ji muryar matar da take tare da shi a gidansa, kuma ba ta san dalilin da ya sa hakan ya fi duk abin da ta taɓa tunani zafi ba, ta sake cusa fuskarta cikin pillow, tana kuka a hankali, yayin da zuciyarta ke ƙara mata nauyin gaskiyar da take ƙoƙarin karɓa, kalma ɗaya kawai, amma ta tuna mata cewa, ba ita kaɗai ba ce, akwai wata mata da take tare da shi a gida, akwai wata rayuwa da yake yi wadda ba ta cikinta, kuma a wannan lokacin, Inteesar ta fara fahimtar cewa son Aliyu abu ne guda… Amma raba shi da wasu matan abu ne daban.