RU'UYAA (The dreams we never lived)
41. ...sweet bad little things...🖊️
by @autum17
Elevator na buɗewa muka fito, iske mutanen gidan mukayi zaune a parlor dukan su harda Hajiyoyin
'' ah Farzan daga ina kake haka?" Hajiya Wareesha ta kalle tsakanin mu biyun
Jin yayi shiru yasa na kalli sashen shi,na hango yar zufa a goshin shi yana buɗe baki amma ya kasa cewa komai
'' ke dalla me kike yi anan? bar wurin nan!" Arman yayi maganar yana hararata
'' daga ina kake?" Hajiya Hafsah ta maimaita ganin yana zufa,
'' ko dai wani rashin jin kayi?" kamar ƙaramin yaro ya fara girgiza kan shi yana shafa ƙeya
mutanen wurin suka tsare mu biyun da ido,su Seraphina kamar zasu cinye ni ɗanya
'' kai daga ina kuke bana son shashanci!!!" Hajiya Hafsah tayi maganar da ɓacin rai
'' ke bar wurin nan!" Hajiya Momma ta ƙara ƙanƙatar da idonta akai na
Na fara barin wurin ina zunɓuro baki naji Farzan yana sharara ƙarya
'' yeah ina zaune a masallaci through out today...yanzu na dawo daga can ɗin,sai na tafi asibi Fuuuuuuuck!!!"
tuntuɓen dana ci na faɗi hotunan suka watse a tsakanin mutanen wurin yasa ya ɗaura hannu saman kai yana zarar ido
Wurin yayi tsit, tashi nayi da sauri na fara tsince hotunan amma aikin gama ya gama kowa ya gani
'' ya Farzan hoto kayi da wannan yarinyar?" Huriyya ta tambaya tana turo baki
'' right!! Kana masallaci throughout kuma a masallacin aka ɗauke wa'yannan hotunan? you're such a bad liar!" Hajiya Hafsah take kallon shi da jan ido
Yayi ƙasa da kanshi yana taunar lips ɗin shi kamar zai huda su, mistakenly idon mu ya haɗu
'' you're so dead!!!" ya furta tare da yowa kaina,ba shiri na saki hotunan na kwasa da gudu,ai ba laifina bane ƙaryar da yake shararawa taban dariya har naci tuntuɓen
da ƙarfe takwas na zauna saman gado ina ciro mayukan ɗaya bayan ɗaya,man gashi ƙwara uku sai na jiki ƙwara biyu harda turaruka suma biyu..fesawa nayi a hannu na suna da bala'in daɗin daya gauraye ɗakin take
' kodai nima yar shan jini zai mayar dani yasa ya siya min wa'yannan turarukan masu nauyi haka?'
Mayarda komai nayi cikin leda na miƙe na wuce Diyaam dake kallona da murmushin zolaya na tafi sashen Khalil
Yana zaune a parlor yana video call da laptop...wuri na samu na zauna,ina wasa da hannayena
'' yanzu babu wani abu da zaki iya yi? I don't...'' ya runtse idonshi yana ƙoƙarin hana kanshi koma meye yayi niyyar furtawa amma ya kasa,murya ƙasa yace
'' i don't love her pls!"
'' listen Ibrahim,ba ko wane aure bane ake yi dan ana son juna, besides ba koda yaushe ne mutum ke samun abinda yake so ba..idan kuna tare a gida ɗaya wata rana zaka sota uhm?" aka faɗa cikin laptop ɗin
Khalil aure zai yi? naji zuciya ta tafara tashi kamar zanyi amai..wane irin aure kuma? ɗaure fuska nayi ina wasa da yatsuna gaskiya da sake...ehe
'' Ma,taya zaki min haka?" Ɗagowa nayi na kalleshi... expression ɗin fuskarshi yaban tausayi,kamar in mashi kuka.Ganin shi a haka yana karya zuciya ta sai kawai na fita daga sashen na tafi kitchen
Na iske su Seraphina suna wanke wanke sunyi ma ko ina kaca kaca..babu abinda suka iya...suna ganina idon su yayi ja da fushi
'' oya, kuyi aiki...Meye mace idan bata iya aiki ba? idan taje gidan miji ai sai ya koro ta!" suke goga haƙoransu kamar zasu cije ni dasu...jikin Mufeedah na tsuma...ɗage kafaɗa nayi
Na isa wurin cupboard na ɗauko madara da suga,na ɗaura tukunya saman gas na zuba sugan bayan ya dahu da kyau na haɗa alewar madara sai daya huce na yanka su manya da shape mai kyau...
Ɗaukar tray ɗin nayi na tafi ɗakin Khalil na ganshi zaune ya dafe kanshi..yana shafa ƙeya,kamar wanda duniyar tayi ma zafi bai san yanda zai yiba...
Ajiye tray ɗin nayi kusa dashi...nake kallon shi da tausayawa'' Khalil!" Na kira a tausashe...bayan minti ɗaya ya kalleni da jajayen idonshi,yayi min murmushin yaƙe
'' Oh..kitten!" Ya gyara zaman shi,muna kallon juna..banma san yanda zan lallashe shiba
'' ka dai na damuwa kaji? Jay d tace damuwa nasa mutum yayi saurin tsufa'' ya gyaɗa kanshi
'' yauwa ko kaifa...ga alewar madara kasha..'' na ɗauko na miƙa mashi..a maimakon ya karɓa da Hannun shi sai ya riƙe hannu na yakai bakinshi yana kallon cikin idona.
kunya ce ta saukar min lokaci guda murmushi yafara ƙoƙarin wanzuwa a Fuskata duk da nayi ƙoƙarin hanashi
Dole na sauke idona ƙasa na ɗauke fuskata gefe
''.are you shy?" Ya tambaya murya ƙasa...karɓe hannu na dake cikin nashi nayi na kasa dena blushing
'' Aaabeeeedaaah...!" ya kira sunan da wani irin salo idonshi a kaina. nima slowly na kalleshi,my gray eyes into his hazel ones...ina fatan baya jin bugun zuciya ta...abun kunyan zai yi yawa aiko?
'' You have the most beautiful eyes I have ever seeing!"
'' kai ma baka suna da kyau sosai!" Yayi murmushi
'' wai aure zaka yi?" nayi tambayar ina kallon gefe
'' ko kada inyi?'' ya dawo min da tambayar
'' kamar saurarena zaka yi!" nayi maganar ciki ciki ina turo baki
'' bakya so inyi auren ne?"
'' eh bana so kayi aure!'' na amsa da sauri
''.meyasa?"
Shiru nayi da wannan tambayar,meyasa bana so yayi auren? tunanin kasancewar shi da wata mace....da sauri na girgiza kaina ina haɗe fuska kamar ina faɗa da wani
satar kallon shi nayi naga idonshi a kaina da murmushin gefen baki.. his eyes half the size
'' kin zo ki nunamin wani abu ne?" ya sauke ajiyar zuciya tareda gyara zaman shi '' uh...eh..'' na miƙe tsaye ina jin dama dama a raina daya dena kallona
'' wannan Romo ya kawo min, na tabbatar kai kace ya siyo ko?" Na miƙa mashi
Ya karɓa yana dubawa '' i didn't !" Ya amsa min,ɗan zaro ido nayi...bai da mutuncin da zai siya min abu haka kawai inaaa...
'' me kike tunani?" Na ƙanƙantar da idona batareda nace komai ba, ya taɓe baki
Na ɗauki alewar da ledar mayukan na fita daga sashen..ɗakin Diyaam na koma na ajiye ledar , Diyaam bata ciki na samu wani plate na ajiye mana alewar sannan na tafi da sauran zuwa sashen Roman...
gaban ƙofar ɗakin shi na tsaya naja numfashi sosai sannan na ƙwanƙwasa bugun zuciya ta ya ƙaru sosai... buɗe ƙofar yayi saye da ƙatuwar baƙar riga mai guntun hannu da fankacecen wando baƙi iya guiwa... wani irin sihirtaccen kyau naga yayi min daya ɗage gira ya ƙanƙatar da idonshi masu min kyau ba tun yau ba...
'' yesss!!" ya furta yana kallon plate ɗin dake hannuna kafin ya dawo da kallonshi a fuskata..kalamai suka nemi suyi min tsiya...saita yanayina nayi na tura mashi plate ɗin gaba '' ga alewa na kawo maka!"
bai ko tambaya meyasa ba,bai ko ɗanɗana ba '' No thanks!" yayi maganar face flat zai rufe ƙofar a fuskata..haushi yaban sosai,shi bai san ya gode ma wanda ke ƙoƙarin faranta mashi ba...
Da sauri nasa ƙafata kafin ƙofar ta rufe ido ɗauke da fushi nace '' wai kai meyasa idan an baka abu baka karɓa?" sakin ƙofar yayi ya juya yana tafiya..tsakanin haƙoran shi yace '' saboda ban yarda da kowa ba!''
shigowa nayi daga bayan shi '' har Dani?"ya juyo yana kallona '' ke bakya cikin kowa ne?" girgiza kaina nayi
'' ni bana cikin kowa...ni Abeedah ce kaji!" Na ajiye plate ɗin saman table ɗin gaban madubi
'' whatever...ke ɗin nafi rashin yarda dake!"
''.saboda an rubuta a goshina...kayi nesa da ita,danger ce ko?"
'' ai ba'a buƙatar a rubuta...not after all the encounters I had with you...''
Da sauri nasha gaban shi,saura kaɗan mu haɗe..yaja baya yana murza goshin shi '' are you insane?" Yayi maganar da takaici
Marairaice fuska nayi '' i lost my sanity the moment I met you!" murya ƙasa nayi maganar ina ƙifta ido kamar yar tsana na haɗe bakina kamar ina jiran kiss...Roman kamar zaiyi exploding,idon shi na hagu na ƙiftawa da sauri sauri.. ya sauya hanya
Sai kuma naji ina jin fitsari, sautin rufe ƙofar baye kawai yaji
ƙanƙantar da idon shi Roman yayi kafin ya ɗauke daga ƙofar bayen ya dawo dasu kan alewar data ajiye
He can never bring himself to believe wai wani zai bashi wani abu batareda wata manufa ba, never! Not after the excruciating pain he experienced after being fed poison..once bitten twice a fool
ɗauke idon shi yayi dai dai nan ƙofar bayen ta buɗe..
'' ahah! Na tabbatar sai da ka lasa sanda bana nan!!" nayi maganar tare da matsowa kusa dashi ina leƙa fuskarshi
bai amsa min ba naga ya wuce toilet nabi bayan shi,bai ko damu daya rufe ba ya shiga wanke ko ina da ko ina a gaban idona kamar shiga ta bayen yasa infection a ko wane wuri a ciki
sakin baki nayi ina kallon shi har ya gama komai ya fito daga bayen
'' oh okay...ai da kace kada in shiga wannan cin fuska haka...''
'' da kika tashi shiga kin tambaye ni ne?" yayi tambayar yana tattare gashinsa da moon hair clip tare da kallona da ido guda
nayi shiru bance komai ba nake tafiya gefen shi tunda ɗakin nashi nada mugun faɗi
'' why are you tailing me? Ɗakina yayi kama da public room?"
'' tambayar kafa zanyi?" ya tsaya har sai dana kusa cin karo dashi
'' WHAT?" ya tambaya da ƙatuwar murya hannu naɗe a ƙirji. na matso gaban shi ina ware mashi idona
'' wai idona basu tuna maka da komai?" Sai daya gama bina da irritated look ya ranƙwafo,har numfashin sa na sauka a fuskata..baki tsuke yace
'' suna tuna min da wani abu!"
...'' meye?" Na tambaya da murna ina ƙara matso shi
'' A dying cow!" ya faɗa a gajarce idona cikin nashi
ya tashi tsaye da kyau sai dai ƙafar shi ta zame on absolute nothing yayi baya zai faɗi,hannu na miƙa zan kamoshi,daga ƙarshe na faɗa saman shi
My lips met his cold red ones,wani irin ɗaukewa numfashin mu yayi atare
Ya zaro hunter eyes ɗinsa like never before,yawu na suka dalalo zuwa cikin bakinsa dake buɗe tsabar shock, ba tareda ya shirya ba ya haɗiye yawun licking my lips in the process...
take naji wani irin yaryar a duk gaba ɗaya jikina dake rawa,ƙirjina kamar zai fashe
runtse idon shi yayi his face turned red,numfashinsa na fita da wani irin zafi, voice cold as Ice '' GET.OFF. ME.!"
yayi emphasizing ko wace kalma har lokacin idonshi a rufe,ina ganin yanda maƙogaron shi ke kai kawo
jiki na rawa na fara ƙoƙarin miƙewa daga saman shi,wani irin zafi ya turnuƙe ni,sai dai saboda yanda nake cikin rashin natsuwa yasa ƙafata ta zamewa ta haɗu da ƙasan cikinsa,his hands flew to my waist
na sake faɗawa saman shi,lips ɗin mu suka ƙara haɗuwa
'' FUUUCK ABIDAAAH!!!" He groaned wanting to bite his lips saboda zafin dayaji but he ended up biting mine instead saboda bakina na saman nashi,his face turned pale
yawun mu suka haɗu and my breath seized,the feel of his soft lips ... ƙwaƙwalwata tayi freezing..are we kissing?
ban gama wannan tunanin ba naji hannunsa a gefen wuyana,ya rausayar da kansa gefe his cold lips closing in on mine kissing me harder, batareda na shirya ba na runtse ido zafin jikin mu ya haɗu
Halshen sa na yawo a kowane kusurwa na bakina,yana ƙara matse ni da jikinsa.. bana ko fahimtar abunda yake yi. Kuma bana iya numfashi da kyau...duk na gama daburcewa
My mind was all over the place
was he licking lollipop wannan abu haka?
ina tsaka da wannan tunanin ya zare bakinsa , idonshi a lumshe
nice na fara buɗe nawa ina ji kamar inyi kuka ashe wannan Roman ɗin haka yake? ashe ba mutumin arziƙi bane
yanda idonsa suka sauya launi yaban tsoro sosai,nayi ƙasa da nawa da sauri har lokacin jikina bai dena rawa ba
with a ragged voice yace '' good kin samu abinda kike so ko?"
na kasa kallon shi,ya zare hannun shi daga jikina ''.you have 30...just 30 seconds ki fita daga ɗakin nan''
wani irin tuƙuƙi zuciya ta take wato yana nufin na kawo kaina wurin shi dan yayi min wannan mugun abun daya yi ko?
'' Otherwise I don't know what I might end up doing!" yayi maganar da barazana idonshi na fasa ruhi na
da irin saurin da ban san ina dashi ba na sauka daga jikinsa,na sheƙa da gudu batareda na sake juyuwa ba har na isa lambu
Na zauna bayan wata flower doguwa na takure wuri ɗaya,wani irin kuka ya ƙwace min,taya? Gaba ɗaya jikina ƙamshin sa yake
har lokacin ina jin bakinsa a nawa,jin ɗumi tsakanin ƙafafuna yasa naja jiki zuwa ɗakin mu bayan na goge fuskata
samun Diyaam nayi tana bacci na faɗa baye na rufe ƙofar kafin nayi ƙasa da wandona
idona kamar zasu faɗo da abinda na gani a ciki da mugun yawa
Wani sabon kukan na fashe dashi,na kalli bakina ta cikin madubi da yayi sunkucece kamar wacce aka naushe a baki,gaskiya dole inyi nesa da Roman ɗin nan,ba shi kaɗai ba harda sauran ma
Na cire kayan duka nayi wanka cike da jin kunyar kaina kafin na fito daga bayen
**
Roman ya daɗe kwance a inda ta barshi kafin ya tashi hannunshi dafe da inda ta buge da ƙafarta ya faɗa baye yayi wanka
Wasu baƙaƙen kayan ya sake sawa fuska a ɗaure
'' Fuck! I just licked her saliva!" ya furta yana shafa bakin shi
Sai kuma yaja tsuke tare da ɗauakar mukullin bike ɗinsa ya bar gidan
Na tsawon sati guda ban sake ganin Roman ba,naji daɗi sosai sannan na rage zuwa sashen Khalil..duk dai na kama kaina bayan abinda wancan mutumin yayi min
shigowa kitchen nayi idona ya sauka akan wani jar cike da chocolate,da sauri na ɗauko kujerar dining na taka ina tsalle dan in cimma shi amma na kasa
wurin tsalle tsalle na dungure kujerar,'' Ahh!" wata irin razanannar ƙara na saki jin zan faɗi ƙasa. Na runtse idona ina jiran ta Allah ta kasance
Sai dai kafin in sha ƙasa jikina ya haɗu da wani abun mai tauri at the same time yana da laushi
Gaba ɗaya ƙamshin kitchen ɗin ya sauya zuwa nashi,kaina ya mannu da ƙirjin shi har ina jiyo bugun zuciyar shi
nima tawa ta fara bugu in an insane speed,abinda yayi min a ɗakin shi ya fara dawo min akai in details yaushe ma ya dawo gidan?
'' idan baki tashi ba zan sake ki, ki faɗi!" yayi maganar a dake,da sauri na buɗe idona da suke rufe suka sauka cikin nashi
'' kayi abinda yafi haka muni kuma na rayu..so what's a little pain if you drop me?"
na ɗaure fuska,haushin shi ya cika ni kamar in make shi,idona cikin nashi da nake ji kamar suna yanka ruhina.. Runtse idonshi yayi as if trying to control his boiling temper for a second na ɗauka sakina zai yi in faɗi ɗin amma sai ya mayar dani ya ajiye saman dining dake kitchen ɗin
Sai a wannan lokacin nagane ashe bridal style ya ɗauke ni. man was his body so hot kamar in cigaba da kasancewa a jikin shi ƙamshin sa kamar winter. Sai na sake tuna abinda yayi min da sauri na katse wannan banzan tunanin
Ni da shi mun raba jaha. Shi kamar bai tuna abinda ya faru ɗin ba,kawai nima sai na yanke shawarar mantawa da hakan ya taɓa kasancewa tsakanin mu
'' kai haka jikin ka yake da zafi kamar wanda ya fito daga tafasasshen ruwan zafi?" nayi tambayar ina bin bayan shi da kallo
Ɗan dakatawa yayi da tafiyar na seconds
'' there you go again..ke komai sai kinyi tambaya akai?" Maganar ta fito kamar wanda aka yima tilas
'' matambayi baya ɓata!"a maimakon yaban amsa da Hausa sai ya juyo ya kalle ni ya ɓuge da yimin magana da italian wanda ni jagwalgwalo kawai naji yana yi
''.kam bala'i toh wai ina jin italian ne?" takaici yabi ya kamani,ɗage kafaɗar shi yayi irin ban damu ba ɗin nan
'' that's not Italian '' can ya amsa,toh wane yare ne?
cupboard ya nufa ya ɗauko Lipton ɗin nan nashi da cup ɗin da shi kaɗai ke amfani dashi ya zuba tafasasshin ruwa ciki ya tsoma Lipton ɗin...yana komai da sauri ne
Sai ya kai cup ɗin bakinsa ya fara kurɓar shayin da sauri harda zufa naga yana yi abu kamar abin dole
'' ka taɓa murmushi?" na sake tambayar bayan lokaci
'' tambayi Google!" Ya ban amsa yana yin gaba...bin bayan shi nayi muka shiga elevator tare
'' oh baka ji sabon update ba? Google sun dena amsa tambayoyi na lokaci.....''
'' kin cika surutu.." ya katse ni.. dafe kumatuna nayi na waro ido '' ashe ka lura?" Dogon numfashi yaja bai sake kulani ba..nima na ɗan yi shiru can nace
'' ɗan yimin murmushi...'' na tsaya gaban shi idona na ƙyalli..nake ƙifta su..
'' I'm allergic to smiling!" ya fita daga elevator bayan ya faɗi hakan...
ya shiga cikin lambu ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake wurin,na zauna gaban shi ina murmushi...share ni yayi yana cigaba da shan Shayin shi,wani baƙin ƙwaro ne naga ya sauka a fuskar shi yana tafiya zuwa wurin idonshi '' kalla wani ƙwaro a fuskar ka...'' nayi maganar da ƙarfi
tare da kai hannu na da niyar mare ƙwaron, tashi ƙwaron yayi hannu ya sauka a idon Roman... shayin da yake sha ya zuba a ƙirjin shi..'' Ahhhh!!!" ya saki ƙarar a razane...ya miƙe tsaye da sauri yana kakkaɓe rigar shi... jan idonshi daya sha mari ya sauka a kaina..
Da sauri na tashi tsaye ina ja baya '' wallahi naga ƙwaro saman fuskar ka..''
'' ƙwaro kika mara ko ni?" Ya tambaya yana matsoni fuskar shi tayi ja da fushi..jikinshi na tsuma..na bala'in tsorata da yanayin shi na haɗiye yawu ido waje..
'' this is the second time you slapped me..will you keep slapping me?"
'' yi haƙur...kus...''
''FUCKIN STAY AWAY FROM ME!!!" ya furta sannan ya fita daga wurin yana ƙunƙuni da girgiza kai kamar ya kasa yarda da abinda ke faruwa dashi duk saboda ni...
dama yasan wannan kalmar?nayi ma kaina tambayar ina bin bayan shi..sai kuma na tsaya,ba nace zan yi nesa dashi ba? well xanyi nesa dashi anjima
'' ashe kai Roman ɗin nan ka iya zagi da faɗin kalmar banza?" juyowa yayi,ba tare da na shirya ba naji bayana ya haɗu da bango,a gasp escaped my lips
hannayensa guda biyu yasa gefe da gefena yayi min rumfa har ba'a iya hangoni a wurin
na haɗiye iska ina kallon fuskar shi dake haɗe
can ya kawo bakin shi saitin kunne na, zazzafan hucinsa na haifar min da wani irin tingling sensation
'' i don't just know bad words..''ya furta ƙasan maƙoshi,sannan ya dawo da baƙaƙen idon shi cikin nawa dake waje kamar zasu faɗo
With an even deeper voice yace
'' I also know how to do bad things...very very sweet bad little things... !"
Was he tempting me?
Yanda fuskokin mu suke inches apart yasa ƙwaƙwalwata freezing,duk da jikin mu bai haɗu ba har ina jiyo zafin jikinsa mai haɗe da daddaɗan ƙamshin turare
ya karkatar da kansa gefe yana min wani ɗan iskan kallon daya sa na haɗiye iska
abunda ya faru a ɗakin shi na sake tunawa,tuni ƙwaƙwalwata ta fara ihu a cikin kaina
🌹 ❤️📖✨
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin ***..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️