15
by @asmybaliyu
OMRI HAYATII
by..
Asmy b Aliyu
15....
kusan tare suka isa eatery din ita ta fara shiga da motarta tayi parking.
a wannan lokacin wayarsa ta soma ring.
hannunsa ya Kai ya dauki wayar Sai
yaga sunan Mami,bai shiga da motarsa cikin eatery din ba wuri ya samu gefe
yayi parking Yana daga wayar da sallama a bakinsa.sai dai muryar da yaji yasa
gabansa mummunan bugawa.muryar ya'r aikinsu bai damu da gaisuwarta ba
yake tambayar Mami fa??"a rikece take fadamasa Mami ce ta xame jiki ta fadi............a rikice yake fadin''"tana Ina Kuma waye tare daita?"nan maiaikin ta fadamasa tana tareda kaaka a falon Mamin,katse Kiran wayar yayi da mugun tashin hankali yayiwa motar key gamida reverse Yana barin bakin eatery din
tuni ya manta abunda ya kawosa wurin burinsa kawai ya isa ga maminsa
wani irin gudu yake shararawa akan titi.
######
da mamaki malaak ta kalli agogon dake makale a tsintsiyar hannunta kusan shudewar mintuna goma babu alamar mu'azzam zai qaraso dan Jim tayi tana ta tunanin to me zai tsiyarda shi har haka??"
ta bude handbag dinta ta ciro wayarta
tayi dialling lambarsa,Yana gafda isa gida Kiran malaak din ya shigo ya dauka ma
maikaikin ce ta Kara Kira. Sai yaga sunan malaak ,bai daga wayar ba ya cigaba da driving dinsa.....malaak tana ta kallon wayar har tagama ring ta katse Kara Kira tayi nan ma da alamar baxai daga wayar ba.
zuciyarta taji ta fara zafi lokaci daya
kasa jurewa tayi ta shiga motarta
ta tayar ta nufi bakin get dan tambayar security din dake aiki a wajen....
"Dan Allah kaga motar da muka shigo tare wacce ke bayana.ina kaga ya nufa dan Allah."ta sauke glass din motar tana tambayar security din dake tsare da get din wurin.ya juya motar ya tafi."
kallon security din take da mugun mamaki tamkar batagane hausarsa ba.kace me
malam ya tafi Ina?"
ya juya ya koma inda ya fito madam!"
wani irin gumi taji tana hadawa,
wani irin nauyi taji zuciyarta nayi mata
Meya samu mu'azzam??"wane irin abune
Wanda ya fita muhimmanci zai juya yabarta batareda ya Mata bayani ba.tambayoyi fal aranta itama ficewa
tayi a eatery din tana jin ranta na Kara baci akan abunda mu'azzam din yayi mata.
#####
Yana rike da hannun mamin har lokacin
da yagama dubata ta samu bacci
yadda maiaikin tayi masa bayani
fitowar Mami kenan daga kitchen tana
karasowa kaaka dake bayanta taga Mamin ta rike Kai kafin ta fara ganin dishi dishi
daga nan jinta da ganinta suka tsaya cak!!!
koda mu'azzam ya auna bp.ya dan hau
Kuma tana bukatar hutu daman Kuma tana da matsalar BP.Shima Abba daga office haka ya dawo ya tarar da Mamin
suma su fareeda duka hankalin kowa
ya tashi musamman mu'azzam sallah
kawai ke daga shi kusa ga Mamin.
itama Fadeela ta iso hankalin kowa ya tashi musamman da Mamin kusan awa biyu tana bacci cikin ta 3 bata farka ba
saboda alluran da mu'azzam yayi mata.
haka ya masu bayanin babu komai
ana so ta samu isasshen bacci ne,
da dare Ayusherh ta shiga kitchen ta hadawa Mami simple dinner da milk tea.koda Mamin ta farka angama sallar magrib, mu'azzam ya taimaka Mata ya rikata har zuwa kofar bathroom,Fadeela ta idar daita har cikin bathroom.ta umurci Fadeela akan ta hadamata ruwan wanka
Dan babu abunda take bukata a wannan lokacin taji ruwa a jikinta.fadeela ta hadawa Mamin ruwan wanka masu dan dumi ta fito daga bathroom din tabar Mamin,koda ta fito fareeda ta Kara gyara saman bed din ,sunyi zaune Suna jiran fitowar Mamin......Mami bata fito bathroom ba Sai da tayi wanka ta shiga cikin closet dinta dake hade da bathroom dinta ta sako doguwar riga daya daga cikin dogayen rigunan da ta ware dan yin sallah masu wasu irin laushi suma designer..
aka bude kofar toilet din sanyayen kamshinta ya fara ziyartar hancinsu
duka su 3 din suka daga Kai Suna kallon mamin da sauri mu'azzam ya taho
ya rika hannunta haka fareeda ta shimfifa mata sallaya.
suna zaune a dakin har mamin ta idar da sallah , Ayusherh CE ta shigo dauke da sallama Fadeela ta amsa mata tray da ta shigo dashi ta dora akan side table dake
gefen bed.Bayan Ayusherh ta aje
ta dauko madaidaiciyar carpert ta shimfidawa mami a kasa,kafin ta sauko da tray ta aje ta qaraso gaban mamin Cike da sanyi jiki take yiwa Mamin sannu.daga Kai Mamin tayi tana kallonta.mami na fara hadamaki tea kafin kici abinci?"duk da mamin bata bukatar jin cin wani abu
haka ta dagawa Ayusherh Kai da taga damuwa Karara akan fuskan Ayusherh din.
a natse Ayusherh ta duka tana hadawa Mamin milk tea da wata irin natsuwa a tare daita.ta dawo gaban Mami ta mika
Mata Sai dai kafin mamin ta karba mu'azzam ya karbi mug din.
A hankali ya furta thank you Queen.
Sai da ya tabbatar tea babu zafi
ya nufi bakin Mamin dashi.kusan rabi
Mami tasha,basu samu natsuwa ba
Sai lokacin.fareeda ta dora kanta akan kafadar Mamin,Sai yanxu hankalinta
ya fara dawowa jikinta. tunda suka dawo daga school sukaga halin da Mamin
take aciki kowa walwala da natsuwa ta dauke masa.sai yanxu da mamin ta dan sha tea suka samu natsuwar zuciya.
Mami ko a zuba abinci kadan?"Fadeela ta fada cike da kulawa a muryarta .Mami tace Sai zuwa anjima zataci.
har kusan 9 Suna zaune a bedroom din mamin har Abba,Sai bayan da mijin Fadeela yazo har cikin falon Mamin
ya karaso yayiwa Mami ya jiki.kafin sunyi nasu sallama Sun tafi.da sauri Fadeela tazo ta xauna gefen Mami ta rungumeta
cikin sanyi murya take fadin."Mami Allah ya Kara maki lafia mai amfani.murmushi Mamin tayi tana shafa kanta take fadin Amin thank you.
haka Fadeela tazo ta rungume abbanta,
ta dawo kan mu'azzam ta hada fareeda da Ayusherh da suke tsaye wuri daya tana
fadin su kula mata da Mami.....lokaci daya suka sakar mata murmushi,su suka rakata har parking lot anan Zatabar motarta
cikin motar Mijinta Zata koma,
Sai da sukaga fitarsu suka dawo cikin gidan.
Sai wuraren 11 ya baro bangaren Mami
dan lokacin Abba Yana tareda Mami hakama fareeda.wanka kawai yayi a gajiye daga shi sai short ya kwanta kan
makeken bed dinsa kafin ya jawo wayarsa,
Sai lokacin ya samu natsuwar Kiran malaak,gafda Zata katse ta daga sabida
tasan idan bata daga ba baxai Kara Kiraba
tasan raayinsa tasan tsarinsa.tana dagawa
ta zabi tayi masa shiru kawai batareda
tayi magana ba.yana jin yadda take fitar da numfashi tana saukewa a hankali.
ya riga da yasan laifinsa cikin sanyi murya yake fadin."Am sowiee .shiru ta sakeyi
Yimasa tana jin kalmar na tafasa mata zuciya .yinin yau ta kasa cin abinci saboda tsananin damuwar da take ciki.da mugun tunanin da ta shiga duk a lokaci daya,
ta rasa me tayiwa mu'azzam ya zabi
ya riqa azabtar daita ta wannan hanyar
Banda dirkawa cikinta drink da ta yini
tanayi kasa fadawa mum tayi dan tsabar takaici......bazakimun magana ba Ina baki hakuri?"me zan fadamaka.ai kasan idan kayi ba daidai ba kasan yadda Kuma xaka gyara kuskurenka."shiru yayi Yana jin
yadda take saukar da muryarta cikin
jin ciwon abunda yayi mata.
"Mami ce ta samu Attack.aranta take fadin
Allah ya kasheta kowa ma ya huta,
Amman a fili ta sauke ajiyar zuciya
cikin kwantar da murya take fadin."Amman da sauki ko??"ta samu sauki sosai,
Allah yabata lafia Allah yasa kaffara ne."
ya amsa da ameen,bari na Kashe na kira vidcall ka kunna data.bata jira me xaice ba ta katse Kiran,cikin minti 3 ta kirasa vidcall
farar fatarsa ta kurawa ido tana jin
tsikar jikinta na tashi lokaci daya,wani
irin mayen kallo take binsa dashi.
jin take tamkar tana acikin jikinsa yanayin da takejin kanta aciki dan wani irin feelings taji Yana taso mata,
Dan kallonta yayi rigar bacci ce ajikinta
kalar milk wacce ta lafe sosai ajikinta
lumshe idonsa yayi a hankali kafin ya budesu akanta.malaak ki saka hijabbb
ya fada Yana kife wayar kafin ta nemi hijab ta saka.jin tayi xuciyarta na mugun radadi
ta rasa kalar mu'azzam batasan meyasa duk zasuyi vidcall ba indai tana sanye da kayan bacci Sai ya saka ta rufe jikinta
Sai kace mutanen karkara tana mugun bakin cikin wannan hijab din da yake fadin ta saka.tasan Kuma idan ta tsaya yimasa gardama Sai dai a hakura da wayar Duka.
batasan ko kannensa dake halaliyansa,
basa zama da kayan bacci agabansa Sai da hijab dan wannan training din Mami ne
tun Yana shekara 15 su Fadeela nada kanunun shekaru,daga wayar yayi
Sai dai maimakon yaga hijab din doguwar riga ce mai maballai ajikinta.fuskar malaak San babu walwala.tana mamakin iya shegen mu'azzam shi da take kallonsa
babu Riga ajikinsa fa Sai itada ke da kayan bacci....karshe ita ta rika yimasa hirar
wani ya amsa ta wani yayi shiru saboda baccin da ya fara fin karfinsa,karshe dai
sulalewa wayar tayi ta koma gefe
murmushi malaak din ta saki kafin itama ta Kashe wayar Cike da farin ciki fal aranta.......
#OMRI HAYATII
#LOVE/FATE
#BEST LOVE
#ASMY B ALIYU
#***.