16
by @asmybaliyu
OMRI HAYATII
by...
Asmy b Aliyu
16......
washegarin ranar sosai mami ta samu sauki daga shi har Abba babu Wanda ya fita acikinsu Suna gida Suna jinyar mamin.
su fareeda Kuma Sun tafi school Suna shirye shiryen fara ezams na shiga ss3
zuwa 2 Fadeela ta iso gidan dauke da basket Wanda ta shiryawa mamin lafiyayyen lunch Wanda duka favourite food din mamin ne.
har bayan la'asar mu'azzam na gida sallah kawai ke fitar dashi.Yana zaune a falon Mami da laptop a gabansa Yana tura wani sako ta email ,Fadeela na baiwa Mami fruits sukaji sallamar malaak.wani irin faduwa gaban mu'azzam yayi bai yadda ya kalli kofar ba ya cigaba da abunda yake.
cike da fara'a Fadeela ta amsa masu sallama tana kallon malaak din dake bayan mum,gaba daya idanunta na akan mu'azzam din da yaki yadda ya kalleta.
da wani irin sanyin jiki ta karaso cikin
falon tana aje basket din dake hannunta
Wanda aka jera fruit Kala Kala aciki.
"Hajia Ayshaa ashe bakiji dadi ba.
Nima ga malaak nakejin bakida lafia
shiyasa yau da Zata zo na biyota naga ya jikin naki yake.hop da sauki?"mum
ta fada tana kafe mamin da ido
haka tana karantar yanayin mamin.
murmushi mami tayi tana fadin"wallahi da sauki Alhmdullahi.masha Allah haka akeso ai Allah ya Kara afuwa.mami ta amsa da ameen.nan malaak ta gaisheda Mami
tana mata ya jiki Mami ta amsa mata a sake.dakyar mu'azzam ya dago ya gaisheda mum din malaak dan jin yake idanun mamin na yawo cikin jikinsa
wani irin tsoro da fargaba yaji Yana ji lokaci daya.koda su kayi waya da malaak da safe ta tambayi jikin mamin.ya fadamata da sauki bata fadamasa Zata zo ganin Mami ba da ya hanata.
ya mike tsaye da laptop dinsa.
a daddare yake fadawa Mami shi xai fita.
Mami tayi masa fatan sauka lafia
tunda ya fito falon na Mami numfashin da yake ta riko ya samu Yana fitar dashi
a hankali.baiyi niyyar fita koina ba a yau,Sai dai saboda malaak ko wane lokaci tana iya zuwa bangarensa ya shiga
ya dauki car key da wallet dinsa ya fice
daga gidan.motarsa na fita malaak ta fito daga bangaren mami waya na a Kare a kunnenta kamar tana wayar,ta nufi bangaren mu'azzam da mamaki taji kofar rufe ta nufi parking lot.anan ta tabbatar da fita yayi saboda babu motarsa
takaici goma da ishirin ya hade mata
jin tayi wata tsanar mami na Kara cika
Mata zuciya.
Xata koma bangaren Mami sako ya shigo a wayarta daga mu'azzam.
na godiyar dubiyar da sukazo ita da mum dinta.takaicinsa ya hana yimasa reply
basu jimaba a gidan malaak ta uxurawa mum dinta akan su tafi tana so ta biya wurin tailor dinta.sukayiwa Mami sannu
da fatan Allah ya kawo sauki.godiya Mami tayi masu har bakin mota Fadeela ta rakasu.sai da taga fitarsu ta dawo cikin gidan.
Sai bayan ishaai mu'azzam ya dawo gidan duk a takure yake jinsa ya gaisheda Mami Yana tambayarta ya jiki.fuska babu walwala mamin ta amsa .ganin Mamin taki
sake masa yasa ya mike tsaye da nufin zuwa bangarensa mami ta dakatar dashi .
tsayawa yayi Yana kallon mamin.yau cikin dare ka siya ticket na zuwa Lagos
gobe kawai ka tafi.ya amsawa mamin da to.kafin yabar falon koda ya koma bangarensa jikinsa mugun sanyi yayi da yanayin maminsa,wanka kawai yayi duk
yunwar da yakeji bai nemi abincin ba
online ya shiga ya duba ticket ya siya
jirgin kaduna zai shiga zuwa Lagos
jirgin da xai tashi Karfe 4 na yamma,
########
da safe bayan Sun dawo sallar Asuba
shida mahaifinsa yake fadamasa
yau zai wuce Lagos da yamma.fatan Alkhairi Abba yayi masa,bangaren Mami
ya wuce kamar yadda ya saba.
ya samu mami tana azkar din safe kamar yadda ta saba,Yana nan zaune
kan soofa har Karfe 7 tagama sallar
ya gaisheta da yimata ya jiki
ta amsa fuska babu sakewa
jikin mu'azzam din ya Kara yin sanyi,
shiru yayi ya Kasa tashi daga inda yake
zaune.
Mami ta cigaba da hidimominta bata qara bin takansa ba jiya dakyar ta samu tayi
bacci Sai da ta kira hafsat marafa a waya
wacce ya'yanta ke kira mimi.suma duk haka suke kiranta batada wata shakikiyar aminiya irin hafsat da yayarta Asma'u
dake aure a katsina.itama ta kirata ta fadamata tana son mu'azzam yayi Aure cikin wannan shekarar zaman ya isa haka.
budar bakin yayarta ta tambayeta mu'azzam din Yana da matar da ya tsayar ne?"tambayar da yayar mami tayi mata
ta Kara jin kirjinta yayi mata nauyi da wani irin zafi.nan mami ta fadamata wacce
taga hankalinsa yafi karkata akanta.babu boye boye ta fadawa yayar tata bata yi Amanna da hada Auren mu'azzam da malaak ba bata inda suka dace.saboda halin uwarsu malaak din.yadda ta mayarda ubansu malaak din bawanta haka Shima
mu'azzam din zai koma bawansu,
haka mami ta basa watanni 6 ya fitar da matar Aure idan ba haka ba ita xata xabar masa da kanta.ta fito fili ta fadamasa
baxai taba Auren malaak Rano ba ko bayan ranta......tana jin yadda yayarta ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyi murya
take fadin."to ke Ayshaa idan shi Yana sonta fa."wannan badamuwata bane
ummi idan ma ya fara son nata
ya dakatar dashi.allah ya xaba mana abunda yafi zama Alkhairi .Musharraf ma da yake yayansa nayi nayi nida dad dinsa
har yanxu aure shiru mungaji mun saka masa ido.shiru Mami tayi tana sauraren
yayartata,,idan Kuma bai gabatar maki da Yarinyyar da zai aura ba nan da watanni shidda fa?"ke akwai wacce kike raayin ki hadasa daita ne.ajiyar zuciya Mami ta sauke
akwai ummi ga ya'r wajen hafsat marafa
ihsaan,nasan har yanxu ihsaan bata da tsayayye kin San rayuwar turai suke
babu ruwansu da auren wuri. kamar yadda akayiwa Fadeela,idan lokaci yayi bai Kawo mun ba zan gabatar masa da ihsaan a matsayin wacce nakeso ya aura.
murmushi kawai ummi tayi tana sauraren rigimar mamin,ta bata shawara akan tayi
magana da mimin idan ihsaan din batada tsayayye Kar ashiga hakkinta.haka Shima
ta jira mu'azzam din.zan jirasa ummi
Amman wlhi tallahi ko kwana daya baxan Kara akan watannin da na dibar masa ba.......daga nan sukayi sallama da yayartata.nan take ta Kira hafsat marafa
ta tambayeta yaushe ihsaaan din zasuyi hutu.saboda da ta kamalla digree dinta
ta jona Masters bata tsaya ba.nan Mami tace tana so tazo malesiya ta dubasu
idan Zata dawo Zata zo da ihsaan din ta dan kwana biyu a Nigeria.mimi tace xata tambayi ihsaan din.waya'nnan mutanen biyu dasu kawai tayi magana ta samu sassaucin abunda takeji a kirjinta
musamman jiya data Kara Shan mamakin
mu'azzam da ya turo malaak din itada mahaifiyarta a dubata....
"Mami wani laifin nayi Wanda ni ban
San shi ba."Ya fada da wani yanayi a muryarsa Yana kallon Mamin.ka tashi ka tafi dan Allah."Mami ta fada masa Kai tsaye,shiru yayi zuciyarsa babu dadi
kafin yabar dakin na Mami, breakfast bai fito akayi dashi ba haka Mami ta aika maikainsu takai masa bangarensa,
ganin haka da rana mamin ta kirasa a waya akan ya fito yayi lunch kafin lokacin tashin jirginsu yayi.dan sanyi yaji
aransa,babu bata lokaci ya fito
akayi lunch tareda shi.qarfe 4 nayi Mami da kanta ta fito kaisa airport har Abba Sai da yayi mamaki cike da tsokana yake fadin."Yau soyayyar Ibrahim ta motsa a kirjinki kenan."shiru kawai Mamin tayi
tana yiwa Abba wani kallon dashi kadai
yasan ma'anarsa tareda fareeda akaje
kaisa airport,Sai da Mami taga tashin jirginsu suka juyo zuwa gida....
#######
Wuraren qarfe 9 na dare tana dakinta
zaune a tsakiyyar bed da kayan bacci ajikinta Riga da wando masu santsi sosai,
ta hade kanta da gwiwa tayi shiru kawai,
tana cikin wannan yanayin wayarta dake gefenta ta fara ring harta katse wayar bata daga Kai ta kalli wayar ba,wani Kiran ya Kara shigo a fusace ta lalubi wayar gurin ta katse Kiran. Sai ta daga.sanyin
muryarsa ta fara jiyowa.duk wani zafi da ya taru acikin kanta jin tayi ya fara sauka
daga Kai tayi tana kallon sunan.
zuciyarta ta fada mata shine..............wata irin kwallah mai zafi da radadi ta taru acikin idanunta.
"Ya kike?"
kalmar da ya fara jefo mata kenan kalmar da taji kamar an watsa mata ruwan zafi.
Sai da ta hade wani abu da ya tsaya tsakiyyar makoshinta.kafin tace lafia kalau kaifa?"
tana jin numfashin da yake ja Yana saukewa kafin yace.Alhmdullahi
gani a garin Lagos."dan bude ido tayi
mamakinsa na Kara kasheta
ya tafi baiko Mata bankwana ba.allah ya taimaka ya bada abunda akaje nema.ta fada cikin takaita maganar dashi,zuciyarta takejin tana mugun tafasa tamkar xata kama da wuta.
kayi bacci ka huta akwai gajiya.
ok Sai da safe.murmushi tayi tana fadamasa Sai da safe Yana katse Kiran
tayi jifa da wayar ta bugi bango ta fadi ta tarwatse akan marbles bata damu Kuma da fashewar wayar ba.saboda kudin canjata ba matsalarta bane.......
wani irin ihun kuka ta saka tana takure jikinta wuri daya tana wani irin jijjiga
I hate you so much miss Ayshaa marafa
nasan ke kika shiga tsakanina da mu'azzam wannan ba mu'azzam din na bane bashi bane.....da wani irin sauri ta sauka daga kan bed duk abunda taci
Karo dashi kusa daita Sai ta tarwatsa
duka manyyan turarrukkanta tsadaddu
haka ta saka hannu ta watsar dasu Suna fashewa akan tiles,mum tana tun Karo dakin taji karar fashe -fashe da gudu
ta bude dakin ta karaso tana rike
malaak din da tayi lossing control dinta
har ta fara fita a hayacinta....
#ASMY B ALIYU
#LOVE/FATE
#LOVE/ROMANCE
#MU'ZZAM MARAFA
#MALAAK FAROOK RANO
#OMRI HAYATII
#***