ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER 23

by @hindatuauwal

Yafaɗi yana kamo fuskarta cikin tafukan hannayen sa tare da ƙoƙarin saka idanunsa acikin nata.



"Ƙwaro ne yafaɗa min a'ido....amma ya rigada ya fita."


Taɗora karin maganar ƙarshe ganin yabuɗe baki zaiyi magana.



"Oh! Sorry Liya sannu."


Kai ta gyaɗa tana kauda kanta gefe. Hannunta ya kamo. Taji kamar ta fizge amma ta daure. Suka zauna. Ya murza yatsunta da sukai haske yace



"Lalli na miki kyau Baby."


"Hakane."



Ta amsa ata ƙaice. Zuciyarta zafi yake mata, daze tai maka mata daya cikata tabar masa wurin. Tana buƙatar shaƙan iska daban da wanda take shaƙa a inuwa ɗaya dashi.




Bata ankara ba se jinshi tayi yana waya" Goggo don Allah idan Halima tana gida tazo da kayan lallinta duka tai ma Sweetheart. Oh Aliya."



Bataji mai akace ba. amma ta fahimci magana yake akan Halima ɗiyar Baba Rabi'u, kuma da Goggo Nusaiba mahaifiyar Haliman yake magana tunda ita bata da waya. Baicin su Aunty Nady ƴan ƙaryane ai da sai su zauna tai musu lallin. ko.....




"Yanzu Halima zata zo."



"Tom!" Ta amsa shi tana kallon wani wurin daban.



Bai saki hannunta dake cikin nasa ba ya buɗe littafinsa ya soma karatu. Ita kam sai saƙar zuci ta keyi tana karanta wasiƙan jaki har Halima ta iso.



Gaisawa sukayi da Ustaz Rayyan harda Aliya kasancewar duk sa'annine. Atare suka taso. Babu kunya Ustaz ya saki jiki yana cewa tai mata mai kyau. Halima tai ta dariya tana amsa shi.



Kasancewar zuciyar Aliya duk babu daɗi yasan yata yin musu shiru, da har ƙorafi sai tayi mata akan yanda tun bayan zuwan da sukayi da biki bata ƙara ganin ƙafafunsuba sai yau.



Ɗakinsa ya shige ya barsu.


Halima ta kalleta cikin tsokana tace"kaga mata ƴar gatan mijinta. har wani lalli yake sanyawa ai miki."



Aliya tai mata hararan wasa tana cewa"kyace haka mana tunda kin min laifi daga ke harsu Aishat da Siyama babu wacce ta ƙara tinawa dani, sai yau daya kiraki kika zo."



Kai ta rausayar tana bata uzuri da makaranta"wallahi Sissy kema kin sani makaranta ke ɓoye mu."



"Kune alhuda-huda."



Dariya Halima tayi tana cewa"zo mu fara lallin. baƙi da ja zan miki mai kyau, ki fito ki ragal abinki. Yaya Rayyan nata jaddadamin."



Yanda tai maganar ya sanya Aliya yin dariya harda ita Haliman.


Veranda suka fito. Aliya ta shimfiɗa musu tabarma. Halima ta fito da kayan lallin, ta zaɓi patterns ɗin da zatai mata amfani dashi. Ta soma jera mata suna hira akan yanda bikin zai kasance gobe.



Halima tace"ai masu abune da abinsu, ƴan ƙarya duk sun haɗu ba zama."



Dariya suka kwashe dashi atare. Aliya ta amsa da"Aunty's namu masu capacity."



"Kema dai kya faɗa. ɗazunnan naji ana cewa Aunty Jamila ta zo."



Aliya ta ɗanyi shiru. Batai mamakin jin Jamila ta zo tun yauba. Ita in akace tun kafin yau ɗinma tazo ba laifi bane.



Haka suka dinga hira atsakanin su tana mata lallin. Seda ze tafi islamiyya ya fito. asannan angama na ƙafa har anƙulle shi da baƙin leda ana jera na hannu.



"Wow!tun kafin agama lallin nasan zaiyi kyau. Nawa ne sadakin shi?."



"A'a Yaya kabada ko nawa ne."



Be jaba yasa hannu a'aljihu ya ƙirgo dubu goma ya bata, tanata godiya.


Ya sunkuya ya sumbaci goshin Aliya yana mata sallama. Tace mai adawo lafiya da murmushinta mai ƙayatarwa.



"Aliya irin wannan love haka... a'a Baba Sa'idu yazo ya kaini gidan miji."



"Ai baze kai kiba se kinfitar da mijin kinga laifin kine ba nashi ba."



Dariya suka yi atare. Ba'a cire lallin ba se ƙarfe shida. Aka ɗora baƙi abayan hannu. Badai su suka tashi agunba sai ƙarfe bakwai na yamma ta tafi gida.



Tun awannan lokacin lallin yakama yayi jajir yanata ɗaukan ido tare da fatarta dake glowing saboda hutu da kwanciyar hankali.



Wanka tayi ta sanya wata material pink color, ta feshe jikinta da turaruka, tai sallahnta na magrib anatse.



Sai bayan sallahn ishai yashigo lokacin tana falo azaune. Ta miƙe da murmushin dako fatar bakinta bata rufe ba ta amsa sallamarsa tace



"Sannu da dawowa."


"Yawwa Liyatah." Ya amsa da fara'arsa yana kamo hannayenta tare da ƙura musu idanu. 



"Masha Allah Wiffy." Ya furta yana sumbatan yatsunnata cikin shauƙi.



Hannunta ta zame daga cikin nasa. Ta nufi hanyar kicin tana cewa"bari na sako maka ruwan wanka."



Sororo yatsaya yana kallonta. Wannan wani irin abu Aliya tai masa? Tunda yake da ita bata taɓa mai haka ba.


Ta gabansa tazo ta wuce. A tilass ƙanwar dole yabi bayanta zuwa ɗakin nasa.



Abu kamar wasa duk yanda Ustaz yaso ganin yaja Aliya da hira adaren samm taƙi bashi dama. Seya jera mata magana uku ta haɗa amsa guda taƙaitacciya ta basa.



Sai yaji zaman duk ya gunduresa. Sukaje suka kwanta. Suduka babu wanda yayi bacci, gasu kwance atare da juna amma damuwa da saƙan zuci ya dabai bayesu.




             *ZAINAB*

Misalin ƙarfe hudu na la'asar.


Zaune take akan kujera ƴar tsugunu tana wanki Ramlat na mata ɗauraya tana shanyawa.


Anis na zaune yana faman karanta rhymes ɗinsa na fama wanda idan aka gyara masa zaice ba haka bane alhalin shiɗin ba dai dai yake yiba.



Sallah aka kira. Zainab na wankin ta tace da Anis"ɗan boko tashi kaje ɗakin ku ka taso Yaya Khalid."



Miƙewa yayi ya nufi ɗakinsu. Can da jimawa har Zainab ta soma kiran Anis sai gashi ya fito.



"Kai da nace ka taso shi yazo yai sallah shine kai zamanka ko?"


"A'a Mami Yaya Khalid ɗinne inata ta shin shi bai tashi ba sai yanzu daƙyar ya tashi."



"Shikenan wuce kaima kaje kai naka alwallahn."


Zuwa yayi ya wuce ta gabanta.



"Shi yanzu Yaya ya iya nauyin bacci gashi baya gajiya da baccin." Ramlat ta faɗi kanta tsaye.



Zainab ta ɗago kanta ta sauke ƙwayannin idanuwanta akan Khalid daya fito yana murza idanunsa.



Haka kawai sai taji jikinta yayi sanyi ƙalau. Zuciyarta ta shiga bugawa ahankali wanda baiyi kamada faɗuwar gababa.



Ta ƙurama Khalid idanu kawai tana kallonsa. Azahiri na gani da idanu babu abinda ya sauya daga Khalid.



Sedai matsalar baccinnan dake damunsa, tama ƙudurcema ranta idan taje kasuwa zata haɗomai maganin shawara ya soma amfani dashi.



Wani wurine dai acan ƙasan zuciyarta yake rawa aduk sanda ta ɗora idanunta akan Khalid. Jikinta na bata akwai wani abu atare dashi wanda idanuwanta basa iya gani.



Alwallah yayi suka fita atare suka je masallaci sukai sallah. Suna fitowa daga masallacin ya kalli Anis yace mai 



"Kaje gida zanje wani wuri na dawo."



"Yaya zan bika."


"A'a kaje kawai."


"Ya..."



Tsawa ya daka mai da ya sanya Anis yin shiru ba don yaso ba.



Khalid ya hararesa yana juyawa abinshi da sauri ya soma tafiya zuwa pharmacy din Emeka siyo tablets dinsa daya kare don baze iya hakurin jira sai gobe ba.




Tafiyan mintuna goma sha biyu ya kaisa zuwa shagon. Kamar yadda hallayar Emeka take da fara'ansa ya tari Khalid. 


Sun gama gaisawa kenan ya dauko maganin ya bashi ya karɓa yaji anriƙe mai hannu da ƙarfin gaske. Zuciyarsa ta tsinke, da jin riƙon yasan kowaye to majiyin ƙarfi ne.



       *ALIYA*

Aranar haka suka kwana suka tashi da safiya bata sauya zani ba.


Ya ɗauketa da kansa zuwa gidan bikin ya sauketa da sharaɗin in yamma tayi zai dawo ya ɗauketa.



Cikin gidan ta shiga. Dayike su suna babban gidane Allah bai basu ikon gina nasu gidan ba.




Sashin bikin ta shiga. Wasu manyan mata ta gani dan ƙam aciki, dangin babansu suna gefe awuri guda sun shimfida tabarma.



Cikin ladabi ta gaidasu, suka amsa da fara'a suna mata ya gida. Gefen Ummi ta zauna da murnanta. Kewan rashinta a ƴan kwanakinnan da bata gantaba ya taso mata. Da atsaye suke ba abinda ze hanata rungumeta. Sai kawai ta kwantarda kanta akafaɗarta. Ummi ta ture ta wai zata karyata. Itafa Ummi bilhaƙƙi kunyar ƴar fari takeyi da ita. Gaisawa sukayi. Aliya ta ɗauki Zahra daketa wasa ajikin Ummi tana cillata sama da mamakin yanda ta girma sosai abinta Masha Allah.




Ganin zamanta acikin manya babu daɗi yasan yata miƙewa daniyyar zuwa sashin su Halima.



Abakin ƙofan fita sukai kaciɓiss da amarya da zuganta ciki harda Jamila da tai matuƙar kyau cikin wata dakakkiyar less maroon color anyi mata ɗinkin pitted gown tareda amfani da bakin less ɗin zallah akai mata kwalliya dashi. Kasancewarta gwana kuma kwararrriyar ƴar gayu cikakkiya da tasan kan ɗauri da ado sai ta fito kamar ƴar tsanar zinare. Ko amaryan bata isa ta nuna mata komai ba.



"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta." Fadin Aliya acan ƙasan zuciyarta.



Jamila ta kalleta sama da ƙasa zuciyarta na tasowa daga ƙirjinta zuwa makogwaronta. Tai matuƙar kyau fiyeda kodayaushe. Abar maganar suturan data sanya ko gyalenta, azallan halittarta na karan kanta kawai ta sauya. Fatarta sai ƙyalli ta keyi tana ɗaukan ido alamar dake bayyanar da zallan kula da hutu in tace harda soyayya ma duka batai laifi ba.




Haba sai taji idanunta na zafi kamar anwatsa mata barkonu. Ta kalleta. Ta kuma kallo ta. "Wallahi Baba ya cuce Ni." Zuciyarta ta ayyana haka. Taja numfashi daƙyar tana ƙoƙarin dai-daita kanta.



Su kam mutane se suka tsaya suna kallon su da son ganin abinda zai faru.



Aliya ce ta soma sauke nata idanun akanta. Ta ɗauko murmushi ta yaɓama fuskarta tana gaidata.



"Ina kwana Aunty Jamila"


Manya!..ai se tagyara tsayuwa ta wani kalleta sheƙeƙe tace"ai da na ɗauka ba zaki gaidani ba tunda yanzu matsayin mu ɗaya Ni dake."



Sarai Aliya tagane abinda take nufi. So takeyi ta tankata su raba hali azagesu.



"Haba dai Aunty Ni na isa! Sannu da zuwa ya hanya."



"Lafiya."


Tunda ta amsa sai Aliya ta kauda kanta agareta. Ta gaida sauran yayyinnata da kawayensu ta wuce abinta.


Aɗakin su Halima ta taradda su Nafisa sai ta zauna itama acikin su suka dinga hira.



Uni zungur anan ɗakin sukayishi. Komai atare suka yi. Se bayan sallahn ishai yaro yazo yace mata ta fito inji Ustaz.



Atare dasu Halima suka shiga cikin gidan taima su Ummi sallama. Ta fito ta gansa atsaye ajikin mashin ɗinsa. Masu ɗaukan amarya sun iso sai hayaniya su keyi.



Da murmushi akan fuskarta ta ƙarisa inda yake.



"Sannu da zuwa."


"Yawwa Noor "


Idanu ta waro mai. Yau shine karo na biyu tun ranar da yayi zazzaɓi sai kuma yau daya kirata da wannan sunan. Kuma batasan mai yasaba acikin duk tarin sunayen dayake kiranta 'Noor' din yafi mata daɗi.



"Ina lallina."


Yai maganar yana kai hannu da zimman riƙo nata hannun, ta kauce. Hakan yabama idanunsa daman sauka akan jamila dake tsaye wani daga cikin abokan ango na mata magana tana amsa shi.



Jiyayi duniyar ta tsaya mai cak. Bai san mai ya riƙe idanunsa akanta ba, amma yanayin yayi daban dana baya.



Babu feelings, babu emotions, babu komai sai shiru kawai. tamkar ka haɗuda wani abu daka rigada ka wuce babinsa arayuwarka zuciyarka ta rufe ƙofar data buɗe masa har ya kaima karasa komai akansa.



Yayi murmushi mai sanyi. Ada kasancewar Jamila agabansa kaɗai ya isa yasan yashi rasa dukkan natsuwarsa. zai iya uni zungur zuciyarsa na riƙeda kalan numfashin daya shaƙa asanda take tsaye agabansa.



Ya sauke numfashi ahankali. kasancewar mutumin daka taɓa ƙauna agabanka batareda kaji komaiba bashine abin mamaki ba. Abin mamakin shine yadda duniyar take juyawa, sabon sauyi ke zuwa cikin rayuwa akodayaushe har mutanen da suka taɓa zama jigon rayuwarka suka koma mutanen da zaka haɗu dasu batareda kaji komai akansu ba.



Ya girgiza kansa kawai ya haye mashin ɗinsa.


Aliya tasa hannu ta share hawayenta da bayan hannu. Duk kallon da Ustaz yakema Jamila ta natsu da kyau ta kalla kuma ta fahimci yanda yanayinsa yasauya gabadaya.


Ya tabbata dai Jamila tana tsaye ƙyam azuciyarsa.